Showing 1 words to 3000 words out of 55418 words
*HAMSHA?IYAR UWA????*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Ku?in karatu ?600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ?ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Page 11*
Maman Nana ta gyara zama sannan ta ce, "Ni dai a tawa shawarar abin da na ke ganin za muyi shine muje mu samu Hajiya uwarmu ce mu fa?a mata cewa muna son ta yi ha?uri da wa?annan al'adun yanzu zamani ake ciki. Shamaki ya yi sauri fa?in ai kina ba Hajiya hujja da zamani kin tashi duk wani bayanin ki na baya ya ?are. Sanna duk bayani sai kin bata hujja. Maman tace To Kinji Maman Iman. Fatima tace aini nama rasa wane tunani zanyi domin duk ta inda ka zagayo Hajiya ta riga ta bi ta wuce, sai dai mu yi ta bakin Maman Nana Muje babu hujja ?in, mu bu?aci kawai ta bar waccan al adar harma mu bata misali da Afra tunda ta san da maganar. Duk suka yi tsit kowa na nazari, suka maida kwallon su kan A'isha Ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce, Ni kuma nawa ganin kar muje mu tsaya mu fidda yadda za mu tare matsalar in ta faru. Misali shi Shamaki ko yaya ya samu matarsa sai ya fa?a mata cewa budurwa ce, in ma jini ta ke bu?ata sai mu tanada shi mu aje. Batun girki kuwa sai mu rubuta mata a waya mu tura mata tana karantawa ta na yi da taimakon su Juma. Kunga mu fita a tunanin ya zata kalli abin kuma wane hukunci zata mana in muka tunkare ta da maganar. Kamar kowa zai amince da haka. Amma sai Shamaki yace ai bata ta?a bukatar ganin jini ba. Sannan da na mata ?arya take take ganewa kuma ku kun sani hakan sai ya fi komai zafi a gurinta.Sai dai ?argaren girkin in kuna ganin zata iya fahimta ita Babyn sai ayi hakan. Maman Umar ta ce Ni kuma nafi yarda da muje mu sameta mu ?an latsa mu gani ko zata yarda. In munga alamun bazata yarda ba sai kawai mu watsar da maganar mu bi abin da addu'a. Dan abin ya zo a ?urarren lokaci ne ai da mun saka ita yarinyar gurin koyon girki ko wata ?aya t¨¤ yi." To haka dai shawara ta tashi ba tare da sun samu mafita ba, amma sun yanke cewa za su je gidan Hajiyar a jibi su ?an latsa in da laushi sai su yi maganar. Maman Afra har ta fita ta dawo, tace da Maman Iman ki zo mana da kayan mu gani a gidan Hajiya. Maman Umar tace wane kayan me? Na DIJANGALA ENTERPRISE ?IN da take ta ko?a mana. Mama Iman tace ok Insha Allah zanzo da shi.
Shamaki ya numfasa tare da fa?in Allah ka bamu mafita. Cike da sarewar gwiwa da kuma addu'a Allah ya fidda shi. Ya nufi gida. Kafin ya kai an kira Isha'i ya isa suna raka'ar ?arshe, ya shiga ya suka ?arasa sannan ya ?ora, ya fito ya tarar da mutane suna kjranshi kamar kullum. Ya na ta sallamar su har Buhari masinjan Ofishin A'isha Maman Afra ya mi?o mishi takardun masu kayan ?aki. Ya amsa ya ce Malam Buhari zan duba a gida. Gobe sai kamin bayani. Malam Buhari ya ce akwai na Ujila a ciki wannan na saman tace ba su bi ?a'idar kawowa ba, amma mabu?ata ne in da hali ka saka hannu kai da Hajiya ita dai ta saka. Yace to ba damuwa zamu yi magana da Hajiyar. Ya gama sallamar kowa sannan ya nufi gurin Hajiyar. tana jan carbi ya zauna gefe kafin ta kammala. Ya ?auki takardar saman da aka ce ta gaggawa ce yana dubawa. Zai iya taimakon Yarinyar ko dan sunan Babynsa da take da shi, ya ?arsa hakan a zuciyar sa. Maimaita Rabi Abubakar, bai san sunan mahaifin ta ba, amma yasan da wahala su zo neman taimako domin ya kula cewa mahaifin Baby mutum ne mai wadatar zuci. zuciyar shi ta kasa nutsuwa ya gangara can ?asa gurin lambar waya ya duba lambobin da kyau, gaban shi ya fa?i, ya ciro yawa yana soma saka lambar sai ga sunan da ya sawa Baby ya fito. Soyayyata. Baya bu?atar sake sanin wata hujja iya wannan ta wadatar. Ya zare takardar ya aje gefe domin gagarumar matsala ce in har Hajiya ta ga wannan takardar, sannan ya ci gaba da duba sauran. Hajiya ta katse shi da fa?in "An shigo?" Ya dube ta da sauri na shigo sannunku da gida, ya gaishe ta cikin girmamawa ta amsa tare da tambayar kasuwa, ya ce Alhamdulillah. Sai kurum ya ji kamar daga sama ta ce "Ya kabaro 'yan uwannaka?" Ya zaro ido tare da fa?in na'am. Ta share zance da kallon takardun hannunsa, "Wa?annan kuma na menene?" Ya Kalli takardun cikin sanyin jiki tare da zargin wata cikin yan uwan nasa kenan harta sanar da Hajiya ko kuwa dai Hajiyar ce da kanta ta gano cewa sun yi zaman to ta yaya zata gano hakan. Yace, na masu bu?atar kayan ?aki ne. "Wancan fa da ka aje gefe?" Yawun bakinsa ya tsaya cak, ya hura iska tare da ajiyar zuciya, takardar wasu ne da Maman Afra ta ce ba su cike ?a'ida ba, na sakasu a gefe ne domin sai mun kammala da wa?annan. Ta tsura mishi ido. Wace number ka ?auka a takardar?" Zufa ta karyo mishi cikin sauri yace ta Maman Afra Anty A'isha. ,ta ce in kirata inji Malam Buhari da ya kawo sa?on,to naji ?iwar in tsaya binciko lambar ta a waya ta sai na ?auka a nan. Ta saki ?an murmushi mai sauti. "Kenan ita bata samu zuwa zaman ba?" A ina? Ya tambaya da sauri. dai dai lokacin da Juma ta shigo da sallama. Hajiyar ce ta amsa domin shi ya suma da mamaki gami da fargaba. "Juma tana gaida kai tunanin me kake yi ne?" Ta katse shi. Banji ba ne Juma sannu da ?o?ari. Juma tace ina amsawa, hidima ta zo ai dole abubuwa sun yi yawa. Yace Ummm haka ne. Ya soma kiran layin A'isha. Ta ?aga. Ya ce Maman Afra kina jina kuna lafiya? Tace lafiya lau,yace Malam Buhari ya kawo sa?o ya ce min kin sako wani Form na Ujila kuma kince muyi waya. Tace "Haka ne." To amma kinsan dai abin nan komai a tsare yake, zan maido miki ki aje shi su jira kamar yadda sauran mutanen suke bin layi, inhar muka fara irin haka za su iya sanar da wasu cewa mun basu agajin gaggawa kuma sai ki ga mutane sun fara zuwa irin wannan ro?on,ke kanki sai su ?ata miki tsari. Tace haka ne, kuma suma mutanen basu dawo ba, munyi da su zasu zo da mahaifin yarinyar yau amma shiru. Domin masu kawo takardar sunce marainiya ce, ita kuma takardar ta nuna cewa marasa ?arfi ne. In sunzo sai a fa?a musu su jira, sai a saka su a jerin wani watan ko?" Yace haka ya yi suka yi sallama ya ?ago kai ya kalli Hajiya wadda ke fa?awa Azima abinda zata zuba mata daga jerin abincin da Juma ta jere. Yace Naman Afra tace a gaishe ku. "Muna amsawa, ta fa?a ba tare da ta kalli gurin da yake ba. Azima tace Yaya Shamaki me za a zuba maka?" Barshi Azima sai anjima bani dai robar ruwan can. Ta mi?o masa tare da fa?in "Kamar ya yi sanyi da yawa." Hajiya tace Kije ki ci abinci zai fi bu?atar mai sanyin domin naga kamar ya yi zufa. Shamaki yace ai kuma yau ba zafi kuma ga AC ma. Tayi murmushi mai sauti. Ya san wannan murmushin na Hajiya na tuhuma ne. Ya soma tunanin yadda zai ?o?arta a bagarar da maganar, ya san Hajiya tana son ?ure shine. Ya mi?e bari inje in?an watsa ruwa. Tace to babu laifi. Ya kwashi fayal fayal ?in. Sai tace "Ajiye su zan duba." Duk da fa?uwar da gaban shi yayi sai yace to,ya ?an sake su kan ya kai ?asa suka tarwatse, sai ya tattara ya ha?a su ya saka na su Baby a tsakiya.
Ya tafi yana shiga ?aki ya soma fa?in Innalillahi wa'inna ilaihirra un. Ya zauna bakin gado ya ?auki waya da sauri ya kira layin Maman Umar yace maman Umar wai in tambaye ki. Tace "Injinka." Waya sanar da Hajiya mun zauna Meeting? " Tasani! Na shiga uku?" Ta tambaya cikin gaggawa kuma atsorace. Yace yanzu na zillo daga falon nata kuma ta?i fa?a min ya akayi ta sani,na ru?e fa ko dai acikin su Maman Nana akwai wadda ta yi subul da baki? Maman Umar ta ce babu,duk cikinmu Maman Afra ce kawai ta tafi, su gasunan kuma itama wallahi baza ta sanar da Hajiya ba. Yace to yanzu me zance mata tunda dole in koma yanzu dan akwai wata damuwar wadda tafi wannan ?aga hankali. "Wacece ?" Ta tambaya cikin sauri. Baya bu?atar su sani dan haka ya ce ki share kawai, amma wallahi kamar in nutse bana cikin natsuwa yanzu haka. Tace kawai ka nutsu in zaka koma ka tanaji wata.maganar ko labari ?ankko mata zancan masoyinta wannan zai ?auke mata hankali har mu tattauna yadda a kayi ta sani. Yace shike nan. Ya watsa ruwa cikin ?arfin hali, ya saka Jallabiya mai gajeren hannu sanan ya fita zuwa gurin. Hajiya ta gama cin abinci tana shan shayi ya zauna idanun shi suna kan fayal ?in, har yanzu suna inda ya barsu. Ya ?arsa a zuciyarsa cewa har Hajiya ta gama dubawa ne ta ajiye ko kuwa dai dama shine ya ke tsorata kansa.
Na gama tsifar kai na ce Jamila don Allah ki je gidansu Anty mai Saloon ki ce zan zo wankin kai, kuma ina son aja min gashi ance ?ari hu?u ne. Jamila ta kalli Umma ta ce Umma a tambayo? Umma tace dan Allah ku rabu da ni, ki ?auka a cikin dubu ukunki da saurayin naki ya baki ta walima nace Umma zanyi girki walima da cincin tunda ga lemo. Jamila tace Meat pie ake yi fa ko dounot. Umma tace, duk abinda zata yi ma dai ga su can ta ?auka, amma ki sani dai baza a yi girki ba, ana ta neman yadda za a yi a samu shi kafar a abinci biki za a ha?a a samu a fita kunya. Ga maganar kayan ?aki Abbanku ya ?i sam ya rubure ga ma?ota sun saka ido suga nuni kunya a samu na yarda min magana. Nace Umma tunda Abba baya so kawai a ha?ura da maganar Neman taimakon nan, tunda ai shi Yayan yace baya
da matsala dan ba a min kayan ?aki ba. Umma tace, " Aike sam baki da hankali musamman yanzu tunda ki ka samu wannan saurayin tashe rashin kunyar ki ta bayyana damuwar ki a kai ki, za a kai ki ba dai namiji ba. Kuma ki kasa kunne ki jini sosai wannan za?uwar da kike nunawa in ba?i suka zo 'yan biki ki ka sake ki ka yimin wannan giggiwar sai na sa?a miki, kayan ?aki kuma inma ba a yi ba koda naji haushi na banza ke za a yiwa gori. Nace to Umma kiyi ha?uri Allah ya bamu mafita. Jamila ta fita domin ta tambayo min gurin wankin kai. Matar nan da?yar ta amshi ?ari biyar wai gashina yana da cika da tsawo. Na yi mamakin ganin gashina har gadon baya matar tace wai dan ba mai na sa ba da sai ya fi haka tsawo. Nace zanzo da bikina ta sa min. Naje gidansu Umman Amina ina tambayar inda zan samu wadda ta iya Meat pie. Tace Amina ta rakani gidan wata amarya tana yi. Nan dai mukaje tace saidai taimin kwa?i inje gidanmu in murza in soya domin mijinta zai dawo yamma ta yi. Na siyo abubuwan da ta fa?a na kwa?i ta kwa?amin na ?auka mukaje Amina da Zuhra da Jamila suka tayani, na kifi ne da kayan miya dan ku?in bazai kai insai nama ba. Muka soye shi ra?ayau wai domin kar ya lalace. Na basu su 'yan tayin aiki sukace ya yi da?i sannan na kaiwa Umma nace gashi ta ?iba ita da Abbanmu sai a ?ulla sauran. Tace to shi saurayin naki kin ?ibar masa? Nace anan za a ?ibar masa . Umma tace "To a bari sai da sassafe yanzu dai in je in rufe.
Na yi wanka na shiga ?aki na kwanta ina ta tunanin banji muryar Mijina ba,kuma har yanzu bai ?aga kirana ba,duk da ?azu da safe yamin text ya ce fatan ina lafiya kuma in gaida su Umma. Na ce bari in sake kiranshi ko zai ?aga. Jamila tace mayya sai ki yi tayi. Nace ai ko tara bata yi ba. Na danna kiran layin gabana yana fa?uwa tsabar son da nake masa ko sunan dana sa mishi a wayar na kalla sai inji tsigar jikina tana tashi. Muryata ta soma rawa lokacin da sautin muryarsa ta doki dodon kunnena. Baby Ya ku ke? Lafiya lau Yaya lafiya baka zo ba,kuma baka min waya ba, na shiga damuwa da banjika ba. Yace ayyuka na Baby suna da dama kiyi ha?uri zan zo ba na fa?a miki ba rannan nace bazan ke samun zuwa akan lokaci ba?" Nace Kasan dai al?awari kaya ne ko? Yace "E." Na ce to ka san dai ka yi alkawarin zuwa filin saukar karatunmu domin kaga karatuna ko? Yace "Haka ne." Na ce to gobe ne da ?arfe goma na safe za a fara, dan Allah kazo ka ga karatuna. "Wai dama gobe ne?" Ya tambaya da sauri. Nace e mana. "To kuwa gara da kika tuna min gobe Lahadi insha Allah zan samu in zo. Cikin Farin ciki nace to ka gaida Hajiya da su Anisa,kuma ina gaida su Anty su duka. Yace duk zan fa?a musu. Nace to sai da safe yace to mu kwana lafiya.
Jamila ta lalle ni bayan na gama waya tace wai ke Yaya Baby har wani canza murya ki ke yi ba in zakiyi waya da Ya'yan nan, sanan wannan wayar taki ba a saka mata kati ne? Tunda aka baki ban ta?a jin kice a siyo miki kati ba, kuma rannan har Baabar Kurna ki ka kirawa Umma, sun jima suna magana. Sai lokacin na kula da haka na ce ta? tun katin da ya kawo a kwalin wayar kuma ai katin ?ari biyar ne. Jamila tace duba Balance ?inki mu gani, na tsurawa lambobin ido baya na danna bangane adadin ku?in ba. Na furta ina kallon Jamila. Tace, mu gani tace kamar ?ari takwas ko dubu takwas. Nace ko dai naira takwas ba. Muka sa dariya. Nace duk tsiyarsu ko nawa ne dai sai sun ?are domin kirana zantayi ?ila kuma ina cikin wani tsari ne wanda suke bada bananza. Jamila Tace 'hakane ma. Na sauke ajiyar zuciya na ce Allah na gode maka Ubangiji kamin komai.
Jamila tace Yaya Baby kina bani mamaki har cikin dare ina jinki kina yiwa Allah irin wannan godiyar, wallahi ba su Umma ba ko ni ina jin haushin yadda kika koma mara kunya lokaci guda. Na tausasa Murya yanzu wannan rashin kunya ce Jamila yi wa Allah godiya? Tace "Ai ba iyaka godiyar zaki tsaya ba, da banyi magana ba cewa zakiyi da ya ba?i miji kamar Yaya Aliyu a dai-dai wannan lokacin." Nace to Jamila meye laifin hakan kar ki manta a da fa ko kare bai ce yana sona ba har tsegumina ake a layi yanzu kuwa an dawo masu zaginma sai shige min suke yi. Jamila tace to ai shigewar ta munafirci ce, in kin yarda, ?azu da Umma tace in amshi rariyar da Umman su Nabila suka ara a gidan na samu Umman su Fati mai awwara,tun daga soro naji suna cewa wai ba'a san asalin Yaya Aliyu ba,babu bincike daga zuwa an ?au yarinya za a bashi. Wai ?ilama ba ?an ?asa bane ?arshe sai kin tara 'ya'ya ya gudu ya barki. Umman Fati ce da wannan dogon jawabin. Umman Nabila kuwa tace su suka sani dubi uban kayan lefe gashi sun saka aure da gaggawa kamar suna da wata tsiya ma ji ma gani dai mu 'yan rakiya ne har gidan ango muga abinda zasu kai mata." Nace Muna fukai ina son mijina haka, ko daga sama ya fa?o, kinsa Allah da nice naje sai na zage su, nifa Jamila akan Aliyu iyayena ne kawai suka fimin shi sai ku ?anne na. Jamila tace shiga nayi da sallama sai suka hau borin kunya na amso na dawo ko Umma ban fa?a mata ba. Nace Yawwa gara kar ki fa?a mata dama, cikin damuwa take. Ai basu ka?aiba ko gidansu Zuhra da suke 'yan uwanmu ai suna nuna ba?in cikin su. Kuma suma suna munafircin Yaya Aliyu na