Showing 24001 words to 27000 words out of 52998 words

Chapter 9 - RAMIN ƘARYA HAUSA NOVEL

24 Oct 2025

85

ya yi, ya mayar da kayan jikinsa, bai ko kalli inda budurwar da suke tare ba, ya bar Wakin, yana tunanin da gaske Huda na da ciki, ko kuma duk dan ta yi masa barazana ne.

********


Yaya Bala ya tara dangi a fada, bayan ya sallami mutanen fadar, ya sanar musu maganar da Gwaggo ta zo da ita, shiru suka yi, kowa da abin da yake sa?awa a ransa, ganin hakan yasa ya ce "Kun yi shiru baku ce komai ba, da wa kuke ganin za a yi wannan haWin?". ?aya daga ciki ya ce "Anya ranka ya daWe wannan haWin zai yi yu kuwa? duba da yanayin yarinyar da kuma inda suka tashi, ta ina yarinya kamar A'isha zata iya aure a nan, in banda rigima irin ta Yaya Halima, ni dai da za abi shawarata, abar wannan maganar, su jira idan ta samu wanda take so a can Win sai a aura mata, da gabar azo ayi wannan haWin abun ya zo bai yi daWi ba, zumuncin mune zai samu matsala. Kuma komai lokaci ne".

Kowa a gurin ya yi na'am da wannan shawarar da Habibu ya zo da ita, Yaya Bala ya yi gyaran murya ya ce "Ni ma na yi wannan tunanin, kuma na shaida mata hakan, to amma kun santa da kafiya, ta ce ba wata matsala. Ni ina ga tun da ita ta bu?aci hakan kuma rashin yin abin da take so Win shima wata rigimarce, gara mu duba wanda ya dace a cikin yaran nan sai a haWa su Win, sannan zamu iya yi wa yarinyar miji ko ba a cikin dangin mu ba, a cewarta ita dai a tsayarwa yarinyar da miji shine burinta".


Habibu ne ya kuma magana ya ce "Ranka ya daWe ban tari numfashin ka ba, amma a ?ara duba lamarin nan, ina ga matsalar rashin yin sa ta fi sau?i, a kan wadda za a iya samu idan an yi shi, ba fata nake ba, amma a ha?ura da maganar" . Nan fa kowa ya nuna rashin goyon bayan lamarin, hatta samarin yaran dake gurin kowa ?in karSar tayin ya yi.


Sarkin fada dake zaune a gefe, shikaWai ne mai unguwa ya ce ya zauna a gurin, saboda kusancinsu da shi, ya zama kamar Wan gida shima. Gyaran murya ya yi ya ce "Allah ya taimakeka idan an bani dama ina so zan yi magana".

Mai unguwa ya ce "Sarki fada faWi maganarka, ai kaima Wan gida ne".


"To ranka ya daWe ina godiya, na ce in ba damuwa, me zai hana ku haWata da wani, tunda harkar ta kasance haka, kuna tsoron yin wannan haWin a tsakaninku, gudun kar zumuncinku ya samu matsala".

"Haka ne sarkin fada ka kawo shawara, sai dai dawa zamu haWa ta Win?" "Ni in ba damuwa akwai wani Wana, idan zaku bashi yana so, ko a yanzuma sai na biya sadaki a Waura auren". "Sarkin fada wanne daga cikin ?a,?an naka?" . Mai gari ya yi tambayar.

Nan ya faWa musu wanda yake nufi, a cikin ?a,?ansa. Duban sauran ?an uwa ya yi ya ce "To kun ji abin da sarkin fada ya ce, me kuka ce kun amince ne? a sanar dasu?" . Gaba Waya suka ce sun amince da hakan. Mai gari ya ce "Ma sha Allah Allah ya sanya alkhairi, zan yi waya da Halima Win na gaya mata, to amma sarkin fada ina yarinyar zata zauna a nan Win ko a can?"

"Ranka ya daWe a nan zata zauna tukunna"

"To ma sha Allah, hakan ma ya yi"

Daga haka mai gari ya sallami kowa, bayan sun bar fadar ne ya rage daga shi sai sarkin fada, wayar kawu Sanusi ya kira, ya yi sa'a yana gida, ya umarci ya kai wa Gwaggo wayar, kai mata ya yi bayan sun gaisa ne ya gaya mata duk yanda suka yi, da kuma wanda za a haWa su Win, babu tunanin komai ta ce "To Yaya hakan ma ya yi ma sha Allah, ai dama bu?ata ta dai a yi mata mijin" sannan ban son Waurin auren ya wuce gobe ko jibi. Mai gari ya ce "Haba Halima gaggawar me ki ke yi ne, ai ki na bari a Wan shirya wasu abubuwan".

"A'a Yaya ni dai ayi duk yanda na ce, baka san halin uwar yarinyar ba, idan aka ja lokaci, za ta iya bin duk hanyar da ta san za ta lalata lamarin, idan ta kama ko a masallaci ne a Waura auren a gobe, ba sai kun tsaya jiran su Wan ladi ba, kuma kun isa ku aurar da ita"

"To shikenan Allah ya kai muna rai" "Amin Yaya na gode sosai" sallama suka yi, ta na cewa kawu ya kira mata Wan ladi sai gashi ya shigo, ta ce "Yawwa dama kai zan sa a kira mini yanzu"

"To Gwaggo gani Allah yasa ba wani laifin na yi ba?"

"Yanzu dai baka yi komai ba, dama magana ce akan wannan yarinyar" nan ta gaya masa duk yanda suka yi da Yaya Bala.

Shiru Baba ya yi bai ce komai ba, duban shi tayi ta ce "Ya na ji baka ce komai ba, ko abin bai yi maka daWi bane Wan ladi?" "A'a Gwaggo Allah ya sanya alkhairi, yasa hakan shine mafi alkhairi" "Ammeen daya fi maka dai, tashi ka bani guri".



Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA....* =ث?




Story & writing

By

Mrs Muttala (Amanar cool)




*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*





Sadaukarwa ne ga Aysharcool




Free book
'?




Page 23&24




__________ Cike da sanyin jiki Baba ya bar gurin, har cikin zuciyarsa yake jin Wacin abin da Gwaggo ke shirin aikatawa, dan kawai ba yanda zai yi ne, ko da ya shiga bai cewa Mama ?ala ba, ita ma da ido kawai take binshi da kallo, dan yanzu shakkun yi masa magana take yi, sai dai tana lura da yanayinsa da ya ?ara sauyawa, gaba Waya komai cikin sayin jiki yake yin sa.


******

Turai ta sake kiran Malamin domin ta ji ya ake ciki sun ji shiru har yanzu, bayan sun gaisa ne, ta ce "Dama kira ne na yi na ji ko an samu yin aikin kuwa?. Domin mun ji shiru ne har yanzu". Ya ce "Yanzu haka ina kan yin aikin ne, wato matar ce akwai tsari sosai a jikinta, ta na da ri?o da ibada, ba ta wasa, sannan ta na yawan zama da alwala, a duk lokacin da na tura Wan aikena gurin ta, baya ganin komai sai duhu, hakan ma mijin nata ba ta wasa gurin nema masa tsarin Allah, amma duk da haka shi zamu iya yin galaba a kan sa, zan yi amfani da lokacin da zasu kasance cikin rashin tsarki, sai na tura Wan aiken nawa ya shafe jikin mai gidan, zuwa gobe zaku ga abin da zai faru".


Ta ce "To ya yi Malam ba damuwa, sai dai ko yanzu na zo da wata bu?ata ce, akwai wani yaro Mudassir da na ke so ?a ta ta aura, sai dai matsalar a yanzu haka batun aura masa wata yarinyar ake yi. To ina son a lalata wancan maganar a dasa masa soyayyar ?a ta Hasina a zuciyar shi, ya zamana ba ya ganin kowace mace sai ita".


Dariya ya yi, ya ce "An gama wannan aiki ne mai sau?i, Mudassir ki ka ce sunansa ko?"

"Eh yarinyar da ake so ya aura sunanta Sharifa"

Dariya ya sake yi ya ce "Ai yarinyar da ake son haWa su auren ba ta son sa, kuma ma ba zai aureta ba, sai dai akwai yarinyar dake son shi, kuma a nan cikin gidan su take".

Turai ta ce "Babu wata budurwa a gidan da ga shi sai ?anwarsa Hudah ne" . To shikenan zan saka masa soyayyar ?ar ki mai tsanani a zuciyar shi, ko uwarsa ta ba shi umarni in dai Hasina ta ?i amincewa da wannan umarnin, to tabbas ba zai bi shi ba" . "Yawwa Malam ina godiya sosai, hakan ya yi zan turo maka sa?o". "To shikenan" daga haka Wif ta ji ya kashe wayar, dariya tayi ta ce "Hauka ake yi, da zan bari Mudan ya auri wata macen, ai gara tawa ?ar ta shiga a dama da ita, muma mu kwashe rabonmu. Har zata a jiye wayar sai tayi tunanin kiran Mami ta faWa mata yanda suka yi da Malam, kiran wayar tayi.


Da sallama Mami ta Waga wayar ta na faWin "?awata ina tunanin kiran ki sai gashi kin kira, kin sanni da gajen ha?uri, kwana biyu ban ji motsin komai ba".

Turai ta ce "Kiran da na yi miki kenan, yanzu muka gama magana da malamin" nan ta faWa mata duk yanda suka yi da shi. Mami ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ta ce "Wannan matar na rasa wace irin mace ce, da asiri bai cika yin tasiri akanta ba".

"Haba dai ke ko ri?o da addini ne, sannan ga ibada, kuma kin san zuciyarta a wanke take tas kamar ta Aysharcool ba ta nufin kowa da sharri" "Dakata! Turai sau nawa zance miki ba na son irin wannan maganar" . "Allah ya baki ha?uri, ni Win ce ba na sanin lokacin da maganar ke fitowa".

Mami ta ce "Ba na so ki daina, kin ma Sata mini rai, sai na huce zan sake kiran ki". Daga haka ta kashe wayar.


Washe gari da safe


Ammi na kwance akan kujeran falonta, ta rufe idanuwanta, ta na addu'ar da ta zame mata jiki a ko da yaushe, "*AMANTU BILLAHI WA HADAHU, WAKAFARTU BILJIBTI WA??AGUTI, WA AMSAKATU BIL URWATIL WUS?A, LAMFISSAMI LAHA, WALLAHU SAMI UL ALEEM, HASBIYYALLAHU WAKAFA, WASAMI ALLAHU LIMAN DA'A, WALAISA WARA ALLAHUL MUNTAHA*" domin neman tsarin Allah da ga dukkanin wani sharri, idan mutum ya ri?e yin wannan addu'ar safe da yamma, in sha Allah, Allah zai kareshi da ga dukkan wani abin ?i.


Abba ya zo ya zauna a kusa da ita, a hankali ta buWe idanuwanta, suna haWa ido ta sakar masa murmushi, shi ma murmushin ya yi ya ce "Shine aka dawo falo aka bar ni a Waki, wannan Babyn ya na so ya hana Abban shi rawar gaban hantsi, gaba Waya ya hanani sakewa da matata" ya yi maganar ya na jan karan hancinta. Kunyace ta kamata ta rufe idanuwanta, ta na dariya, shi ma ita yake yi ya kuma cewa "Ni dai gaskiya a san yanda za ayi dani, ana shigar mini ha??i da yawa, kullum sai dai ayi wanka a caSa mini ado, a saka wannan turaren da yake isar da goron gayyatarki a gurina, amma ba a bari na amsa gayyatar" ya du?ar da kansa dai-dai cikinta ya ce "Haba Babyn Abban shi ka taimakawa Abbanka, ya na cikin wani hali".

Ammi ji tayi kamar ta nutse a gurin, don kunya, wani lokacin idan Alhaji ya tashi abubuwa yake yi kamar wani ?aramin yaro, sam baya jin kunyar sakin baki ya yi ta Sarin zance, ba ta ankara ba ta ji ya Wora hannushi akan cikinta yana shafawa, ya ce "Madam magana fa na ke yi, a san yanda za ayi da ni".

"To me ka ke so ne?"

"Yunwa na ke ji"

"To ai na gama haWa mana abin kari muje dining sai ka ci"

"No ni ba irin wannan nake so ba"

Sarai ta gane me yake nufi, amma sai ta ce "To wane iri ka ke so?"

"Irin wannan wanda idan ina..." da sauri ta rufe masa baki ta na dariya ta ce "Wai me yasa ka ke abu kamar wani yaro? kai fa yanzu babba ne, ka girma, irin waWannan abubuwan su Mudan zaka barbwa su yi ba kai ba".

"Au saboda ni ba namiji ba ne? ko kuma ni ban san soyayya ba? ni ma ai yaro ne a wurinki, in dai a wannan fannin ne babu babba ba yaro, kowa ya iya allonsa ya wanke, ai wannan gabar ba a wasa, komai tsufan ma aurata kar su ji kunyar nuna wa junansu soyayya, matu?ar suka samu keSewa, to balle ni da na ke dake. Tubarkallah ma sha Allah, komai gashi nan Sul-Sul abin cin jarirai Win nan kullum kamar ?ara mi?ar da shi ake yi". Ya ?arasa maganar ya na dariya.


Ita ma dariyar take yi sosai dan ta lura mijin na ta yau abin yake ji da shi, ta na dariya bata yi aune ba ta ji ya Waga ta cak ya yi Wakinsa da ita.



******


Tun da safe Maryam ta yi shirin zuwa makaranta, ta na so ta tambaye Baba kuWi ta na jin tsoro dan yanzu shakkun shi take yi saboda sauyin da ya yi, gashi kuma tun jiya ta lura gaba Waya yana yin shi ya ?ara canzawa, sannan ta san idan ta ce Mama ta bata, ba za ta bata ba, sai ta titsiyeta da tambayar me za ta yi dasu. Ba dan ranta ya so ba haka ta ha?ura da tambayar kuWin ta karSi iya na abin hawa da na cin abincinta, a gurin Mama ta fito, ta na fitowa ta ci karo da Zaliha ta fito daga gurin Gwaggo da Wari biyar a hannunta. Ba ta kulata ba ta nufi hanyar fita, sai ji tayi Zaliha ta ce "Aikin banza a haka dai zaku ?are a yawon barbaWa, ana fakewa da zuwa makaranta ana yawon bin kwararo da Wakuna maza, wallahi duk ranar da yarinya ta kwaso ciki, ko kuma cutar ?anjamau, to ba a gidan nan ba, sai dai tayi can gidan uwarta, ita da ta Waure muku gindi ku ke yin yanda kuka ga dama..."

Ai bata gama rufe bakinta ba, cikin tsananin zafin rai da tafasar zuciya Maryam ta kai mata mari hagu da dama, ta rufe ta duka, dambe suka fara, Maryam ta dage iya ?arfinta ta ke kai wa Zaliha duka, dama can ta na jin haushinta, Zaliha na son tayi ihu domin a kawo mata Wauki, amma idan ta tuna cewar ita da Maryam Win duka ?an sa'a Waya ne, sai ta daure, da dai taga azaba zata sha dan Maryam tafi ta ?arfi nesa ba kusa ba, sannan ta fita ?warewa a wajan iya tijara da masifa, yasa ta daddage iya ?arfinta ta ?wala ihu tare da kiran Gwaggo.

Gwaggo da Inna Hajara har rige-rigen fitowa suke yi, Inna Bilki da Afnan ma fitowa suka yi, dan duk sunji uban ihun da tayi, Gwaggo ce ta fara ?arasowa, Maryam wata irin hajijiya ta yi wa Zaliha ta in gizawa Gwaggo ita, sannan ta du?a ta Wauki Wari biyar Win da azaba tasa Zaliha sakin ta daga hannunta, tayi ficewarta da ga gidan, taga-taga suka yi zasu faWi ?asa da sauri Inna Hajara ta ri?o su. Baban su Afnan ne ya zo gurin ya na faWin "Lafiya me yasa meta? tun daga ciki na ke jin ihunta".


Cikin masifa da Waga murya Gwaggo ta ce "Wannan bala a iyar yarinyar ce Maryam ta same ta ta dinga jibgarta kamar ta samu jaka, tun da ta ga ta fita albarka jiki, har take ?o?arin haWa ni da ita gaba Waya ta daka, saboda ba ta da kunya, wallahi wannan yarinyar da a asibiti aka haife ta zance an hurhura mana ita, dan duk zuri'armu babu mai wannan mugun halin sai ita". Baba ya ce "Yi ha?uri Gwaggo bari ta dawo gidan zan Wauki mataki". "Dalla can rufe mini baki, me zaka iya yi? bayan ka mai da kanka zakaran Inna, sai yanda mace tayi da kai, to bari ka ji na faWa maka na gaji da halin wannan yarinyar, ina ga haWawa za ayi da ita a aurar dasu can ?auyen gaba Wayan su, kowa ma ya huta da wannan bala'in, kuma wallahi kuWina da ta Wauka sai an biya ni, dan bazan bar mata Warita biyar a banza ba". Ha?uri ya ci gaba da bata, ya Wakko dubu Waya a aljihunsa ya mi?a mata, sannan ya fita daga gidan gaba Waya, ci gaba da masifa tayi.


Bahijja Wiyar Inna Bilki ta dubi Afnan ta ce "Aunty Afnan shin wai ita wannan tsohuwar wa take cewa za ayi wa aure a ?auye?" kafin tayi magana Gwaggo ta ce "Uwarki da ubanki, marasa kunya kawai, ni nan dai-dai na ke da duk wani mara kunya" . Baki Bahijja ta murgaWa ba ta kuma magana ba, ganin hakan yasa Inna Bilki ta tasa ?eyarta a gaba suka bar gurin. Afnan ma hararar Gwaggo tayi ta ce "Kwaci kan ku". tayi shigewarta.


Hannun Zaliha Hajara ta ja suka bar wajen, ya rage sai Gwaggo dake tsaye ta na faman masifa, babu irin abin da bata cewa Mama da ?a,?anta ba, sai da tayi mai isarta sannan ta koma ?ofarta.


Maryam na fita a hanya ta haWu da Feena, suka ?arasa bakin titi abin hawa suka tara, cikin napep Maryam take bawa Feena labarin abin da ya faru yanzu kafin ta fito, aikuwa me za tayi in ba dariya ba, a haka suna firar har suka ?arasa makaranta.


*******


A gigice Abba ya diro daga kan gadon ganin Ammi dafe da mara ta na mur?ususu. Hankalinshi bai ?ara tashi ba sai da yaga jini ya fara bin ?afarta, nan ya ?ara giWimewa, cikin tsananin tashin hankali ya saka dogowar rigar jalabiyarsa, ita ma ya saka mata, Waukarta ya yi ya fita da ita harabar gidan, a lokacin har ta fara galabaita, da sauri ya sakata a mota, bai ko tsaya kiran direba ba, ya ta da motar ya bar gidan, duk abin nan a kan idanuwan Mudan ya na tsaye a ?ofar fitowa daga Sangarensa. Da sauri ya shiga gurin Mami, ta na ganinsa ta ce "Lafiya kuwa na ganka haka?".


"Mami ina ga gidan nan babu lafiya, Abba na gani ya fito da Ammi, ya saka ta a mota ya bar gidan, kuma fa da kansa ya ja motar".

Zumbur Mami ta mi?e tsaya, ta ce "Subhanallah, ka ga Mudan bari na kira shi na ji me yake faruwa, ko da yake na san ba lallai ne a ce ya fita da waya ba, amma dai a yanda ka faWa mini tabbas asibiti ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login