Showing 21001 words to 24000 words out of 52998 words

Chapter 8 - RAMIN ƘARYA HAUSA NOVEL

24 Oct 2025

96

ta yi masa ne suke dawo masa Waya bayan Waya, dafe kansa ya yi "Oh may God Me yasa na kasa ha?ura na bi umarnin Umma?. Ki yi ha?uri Ummana na kasa cika umarninki, zuciyata ta kasa ha?ura". Kira ne ya shigo a wayarsa, da ?yar ya iya cirota a aljihunsa, uban gidansa ne ke kira, Wauka ya yi kafin ya yi magana ya ji ya ce "Haidar batun tafiyar da na ce ka rakani ka yi zamanka ba sai munje tare ba, yanzu haka ma na kama hanya, shi ne na ce bari na sanar da kai".

Haidar ya ce "Mai gida Allah yasa ba wani laifin na yi ba?".

"A'a Haidar ko Waya dama wani dalili ne ne yasa na ce ka shirya mu yi tafiyar tare, to sai kuma dalilin ya janye, kar ka wani damu". "To ya yi mai gida Allah ya kai ka lafiya ya tsare hanya". "Ameen Ameen Haidar". Kashe wayar ya yi, ya tayar da babur Winsa ya bar gurin.

Afnan Waki ta shige tayi kwanciyarta, tana jin Maryam na yi mata magana amma ta shareta, maganganun Haidar ne ke ta amsa kuwwa a kunnenta, gefe Waya wani irin ciwo kanta yake mata kamar zai rabu gida biyu, Maryam ta ce "Aunty ya Haidar Win har ya tafi ne?". ?aga mata kai ta yi alamar eh Maryam za ta kuma yin magana Afnan ta ce "Please Maryam kar ki dame ni, ba na jin daWi".


Gwaggo ta sa kawu ya kira mata Yaya Bala mai gari na can ?auye, bayan sun gaisa ta ce "Yaya dama magana ce akan yarinyar wurin Wan ladi A'isha" . Ya ce ya ce "Subhanallah! wani abune yasameta?" "A'a ko Waya ina so a cikin dangi a duba a samu wanda za'a haWasu aure da shi, saboda nan garin ta?i ta fitar da miji, duk wanda ya zo nemanta sai ta ?i, tun suna zuwa har sun daina zuwan, to shi ne na ce bari na yi maka magana, tun da ta ?i ta fitar da miji a nan zansa a nema mata shi a nan gurinku, dan ni ba zan lamunci ganinta haka ba, yarinya ta na gwada ?ugu ita da uwarta, su kuma iyayen nata da yake basu da hankali, goya mata baya suke yi".

"Anya Halima ki na ganin wannan haWin zai yi yu kuwa? bana tunanin yarinyar nan za ta iya zama nan garin, duba da yanayin na ku garin, kuna cikin birni, yarinyar da ta tashi a birni, kuma ta yi karatun boko, ta ina za ta iya zama a nan, sannan ki na ganin ita uwar yarinyar za ta yadda ne? Ai ?warya ta bi ?warya".

"Haba Yaya, ka daina zancen amincewar yarinya, da ta iyayenta, ai abin da na ce ayi dole shi za ayi, babu wanda ya isa ya saSawa umarnina, a cikinsu, ni dai Yaya ina bu?atar ka yi mini wannan alfarmar, inda hali ma a Waura mata auren a can, in ya so sai a Wauki amaryar a kai".

Shiru ya yi, yana nazarin maganarta, sannan ya ce "Shikenan ba damuwa, an jima zan zauna da ?an uwa sai mu ji abin da yakamata ayi".

"To ya yi na gode sosai Allah ya ?ara girma, a gaishe mini da mutan gida, sai na ji ku".



*******


Abba ya dubi Mudan ya ce "Mudassir shin ka samu zuwa gurin Sharifa?" "Eh Abba na je" "To ya kuka yi da ita? ina fatan kun dai-dai ta kanku?" "Eh Abba babu wata matsala, ita ma ta aminta da ni".

"To ma sha Allah, dama haka na ke son ji, tashi ka tafi, Allah ya yi muku albarka".

"Ameen Abba na gode sosai" bayan fitar Mudan Abba ya kira amininsa, bayan sun gaisa ne, "Ya ce maganar yaran nan ce, yanzu na tambaye Mudan ya je gurin Sharifa, ya ce ya je har sun dai-dai ta kansu".


Alhaji Munir ya ce "Ma sha Allah na ji daWin wannan maganar, jiya nake tambayar Fatima Mudan ya zo, ta ce ya zo, sai dai ba ta san yanda suka yi da Sharifa ba, to ka ga ashema har sun dai-dai ta kansu, yanzu musa mu lokaci mu zauna, sai mu ga yanda za mu tsara lamarin". "To shikenan Allah ya tabbatar mana da alkhairi". Ya amsa da "Ameen " sannan suka yi sallama.


Haidar kai tsaye gida ya nufa, ko da ya isa Umma ta ce "Haidar ina ka je ne? Kai da ka ce mini zaku yi tafiya kai da mai gidanka, ko dai an fasa tafiyarki ne?" . "A'a Ummu ba fasawa aka yi ba, yanzu ma haka ya wuce" .

"To ka ce mini kuma tare zaku je, me yasa kuma baku tafi tare ba, ina fatan dai ba wani laifin ka yi masa ba?" "A'a Umma ba abin da na yi, dama akwai dalilin da yasa zamu yi tafiyar ne tare, to kuma yanzu dalilin ya janye shiyasa ya ce na yi zamana kurum".


Ta ce "To ya yi ba damuwa, Allah ya dawo da shi lafiya" . Da "Ameen" ya amsa ya na ?o?arin shigewa Wakinsa sai ya ji ana sallama, a ?ofar gida dakatawa ya yi, ya na jin kamar muryar Faruk ce ke sallama, fita ya yi waje domin duba mai sallamar, aikuwa shi Win ne, cikin tsananin farin ciki suka rungume juna, Haidar ya ce "Yau kaine a gari babu sanarwa".

Faruk ya ce "Eh wallahi ni ne, dama cewa na yi ba zan faWa maka ba, sai dai na yi maka zuwan bazata". Dariya Haidar ya yi ya ce "To zo mu shiga ciki ko".

Cikin gidan suka shiga, Umma na ganin Faruk ta ce "Ma sha Allah Faruku yau kai ne a gidan na mu? saukar yaushe?" "Eh Umma ni ne, Wazu nan na iso, mun same ku lafiya?". "Lafiya ?alau Alhamdulillah, to ya hanya? ya karatun? ina fatan dai ka kammala karatun duka?" "Eh Umma na kammala gaba Waya"

"Ma sha Allah to Allah ya yi albarka, yasa aci amfanisa kai da abokin naka" "Ameen ameen Umma mun gode sosai".

?akin Haidar suka shiga, abinci Umma ta kai musu, bayan sun kammala cin abinci ne, Faruk ya lura da ya na yin Haidar kamar akwai abin da ke damunsa, duban sa ya yi sosai ya ce "Haidar kamar akwai abin da ke damunka. What is problem?". Haidar ya numfasa sannan ya ce "Abokina damuwa kam akwai ta, ka san ba abin da zan Soye ma" .


"Eh haka ne na sani, me yake damunka ne? "

"Soyayya"

"Soyayya kamar ya? bangane ba?".

"Na kamu da soyayyar wata yarinya ne".

"To na ji ita yarinyar ba ta sonka ne? ko kuma akwai wata matsalar ne?".

"Abokina akwai matsala fa Umma ba ta bani goyon baya ba, sannan ita kanta yarinyar ban san matsayata a gurinta ba, kai in ta?aice maka yau ne na samu damar sanar da yarinyar cewar ina sonta" .

Faruk ya ce "Na ji, kenan Umma ka fara yiwa zancen yarinyar ko?" . "A'a ita ma ban fara faWa mata ba, ka san iyayenmu da saurin fahimta" nan Haidar ya kwashe komai ya gayawa Faruk ya ce "Faruk na so na ha?ura da zancen kamar yadda Umma ta bu?ata, sai dai ina na kasa ha?ura, ina son yarinyar nan sosai".

"To amma me yasa Umma za ta ce haka? duk da ta na da gaskiya, amma shi aure nufin Allah ne, kuma duk lokacin yinsa ya yi ko mutum bai da ko sisi Allah zai kawo masa buWi da mafitar yanda zai yi lalurar auren ba tare da kowa ya sani".


"Haka ne abokina amma ka ji bayanin da Umma tayi"

"To amma Haidar why can't you complain"?

"Faruk I can't complain because she is my Mom". Ya ce "To ka yi ha?uri ka bi umarninta mana, ka ha?ura da zancen yarinyar tunda ma baka da tabbacin ta na sonka". Shiru Haidar ya yi bai kuma magana ba, ganin hakan yasa Faruk juya akalar firar su zuwa wata firar da ban.

Da yamma Feena ta zo gidan su Maryam ta duba lafiya Maryam Win take, saboda yau ba ta je makaranta ba, duk rashin kunyar Maryam ba ta fashin makaranta, sai dai idan ta je ta ga ji da zama za ta gudu, ko da ta isa Mama sai Afnan ta tarar, Maryam ba ta nan, ta na gurin Inna Bilki da ta dawo daga unguwa shine ta je gaisheta, Afnan ta ce "Safeena zo ki zauna yanzu za ta shigo".

Feena ta ce "A'a aunty bari na je can na same ta". Afnan ta ce "To shikenan".

Feena na fitowa tayi arba da Zaliha Wiyar Inna Hajara wadda ita ma yau suka dawo, wani banzan kallo tayi wa Feena ganin ta fito daga ?ofar su Afnan, sannan ta ja tsaki tare da tofar da yawu, Feena ta ce "Ikon Allah ke kuma boyar Allah da wa ki ke?"

"Da ubanda da duk ya tambaya da shi nake" Feena ta ce " Me na yi miki da za ki zagar mini uba?"

"An zage shi Win, waye shi? da ba za'a zage shi ba". Ai ba ta gama rufe baki ba Fenaa ta kai mata wani bahagon mari, Maryam dake tsaye tunWazu ta na kallon su ta ce "Kin yi mini dai-dai ?arawa shegeya, ?ar iska, munafuka". Sha?e Zaliha Feena tayi, ta na kai mata duka, Inna Hajara jin hayaniya yasa ta fitowa, ganin ansha?e mata Wiya yasa ta kurma ihu ta na faWin "Gwaggo dan Allah ki zo zasu kashe mini yarinya yau yau da dawowarta".



Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA....* =ث?




Story & writing

By

Mrs Muttala (Amanar cool)





*YOUNG TALENT*
*WRITER'S ASSOCIATION*




Sadaukarwa ne ga Aysharcool




*Assalamu alaikum, ina yi wa Waukacin jama'ar musulmi barka da sallah, Ubangiji Allah ya maimaita mana, ya karSi ibadunmu.*



Free book
'?



Page 21&22




________Kamar wadda aka wuntsilo haka Gwaggo ta ?araso gurin, idanuwanta ne suka sauka a kan Feena dake ma?ure da wuyan Zaliha, Inna Hajara sai kiciniyar ?watarta take yi, amma ta kasa, wani ?aton icce dake ajiye a gefe Gwaggo ta Wakko da sauri ta je za ta kwaWawa Feena, cikin zafin nama Maryam tayi saurin ?arasawa ta janye Feena, aikuwa cikin rashin sa'a Gwaggo ta makawa Inna Hajara iccen a tsakiyar bayanta, ihu ta saki ta na zubewa agurin, Zaliha ma bajewa tayi a ?asa ta na mayar da numfashi, idanuwanta sun yi jajur sun firfito saboda azaba, Gwaggo ganin su Inna Hajara zube a ?asa, suna nishin wahala, yasa ta dubi Maryam dake tsaye a gefe ita da Feena sai tuntsura dariya suke yi, ta ce "Ku dai wa?an nan yaran iyayenku sun yi asarar haihuwar ku da suka yi, sun yi wankan jegon asara, tukuna ma ke ina ki ka jajiSo mana wannan mara kunyar yarinyar irin ki? ta na fama da wasu idanuwa kamar dillalin ma?aryata".


Maryam ta ce "Allah ya raba iyayenmu da haihuwar asara, kuma in sha Allah ba za su taSa nadamar haihuwar mu da suka yi ba, ga dai inda aka yi haihuwar asara nan. Uwa munafunce, ?a tambaWe, babu mashinshini, ko kare bai taSa zuwa ya ce ya na so ba" .


Dariya Feena tayi ta ce "Haba Maryam yo wani namiji ne zai zo ya ce ya na son wannan abar, abu gata nan ita ba mace ba, ita ba namiji ba, gata nan dai kamar an tada kare tsaye, ga wani uban hanci da ta ke fama da shi kamar an bugawa ?ato guduma a goshi, ai wannan dai babu lafiyayyen namijin da zai ce ya na sonta, sai dai ko in irin firgitatun nan masu taSin hankali, ko kuma makaho, ko makahon irin wannan da baya da Wan jagora".


Mi?ewa Inna Hajara ta fara ?o?arin yi, jin irin cin mutuncin da ake yi musu ita da ?arta, ?afa Maryam ta saka mata sai gashi ta kuma ?asa daSas, Gwaggo ta ce "Innalillahi wa inna ilaihim raji'un, Amina kin haifo mana jaraba, wannan yarinyar ke dai baki yi sa'ar hali ba, ke kuma Wayar marar kunya zo ki bar gidan nan tunda ba gidan ubanki ba ne".


"Ba inda za ta, ai ba gurinki ta zo ba, ke ?awata zo mu je ciki ba wanda ya isa ya kore ki da ga cikin gidan nan, tunda mutum ba shi ya gina sa ba, ehe ". Gwaggo sakin baki tayi ta na kallon su, tare da mamakin ?warewar Maryam a rashin kunya.

Inna Hajara ta dubi Maryam ta ce "Yanzu ni za ki yi wa wannan rashin kunyar da Wibar albarka? Gwaggo ki na ganin abin da yarinyar nan tayi mini".

Cikin tsiwa ta ce "Na yi miki, ai wallahi ma baki ga komai ba, ba dai ta?amarki munafurci ba, da son ganin an ?untata rayuwar wasu ba, in sha Allah rayuwar ki ce za ta ?untata da ke da duk wani mai goya miki baya". Daga haka ta ja hannun Feena suka bar gurin. Duk abin ake yi su Mama na jin su fitowa ne kawai basu yi ba.

Gwaggo ta dubi Hajara ta ce "Tashi ku yi ha?uri ku bar ni da ita zan yi maganinsu ne".

Ko da suka shiga da kallo kawai Mama ta bi su, ta girgiza kai ta ce"Allah ya kyauta". Dan lamarin Maryam sai addu'a.


*********


Sharifa ba ?aramin tashin hankali ta shiga ba lokacin da ta ji ?aryar da Mudan ya yi na cewar sun dai-dai ta kansu, tayi kuka sosai, sannan ta ?uduri aniyar komai zai za ayi ba za ta aure Mudan ba, sai dai a kashe ta idan ya so a Waura masa aure da gawarta.


Hudah gaba Waya ta sauya, ta rage zama tayi hirar da take yi da Mami, walwalarta ta ragu, sosai kullum ta na Wakinta.

Mami ta na ankare da sauyin da Hudah tayi,
shiga Wakin tayi ta tarar da ita a kwance, zama tayi bakin gadon da dubeta, ta ce "Daughter tashi zaune magana zan yi dake". Tashi tayi ta na yatsina fuska.

?are mata kallo Mami tayi sannan ta ce "Daughter me yake damun ki ne? gaba Waya kwana biyun nan kin sauya, baki da lafiya ne? ko an yi miki wani laifi ne?".

Shiru tayi ta?i magana, daga ?arshe ta du?ar da kanta ta na kallon ?asa.

Mami ta ce "Magana na ke yi da ke kin yi mini shiru" "Mami ni ba abin da ke damuna fa". "Ba abin da ke damunki kuma ki ka ?auracewa zama cikin mutane? Hudah ina ankare da ke, kin daina shiga harkar kowa a gidan nan, hatta Yayanki da kuke shiri da shi na ga yanzu kin daina kula shi, ki faWa mini idan wani abin aka yi miki? ko kuma shi Yayan na ki ya yi miki ba dai-dai ba ne?" .

"Ni fa ba abin da aka yi mini, kawai dai yanzu idan na zauna cikin mutane kaina ciwo yake yi".

Juyin duniya Mami tayi akan Hudah ta faWa mata me yake damunta, amma ?ememe ta?i, haka a dole ta ha?ura ta ?yale ta ba dan ta yarda ba abin da ke damunta ba Win, tashi tayi ta fita daga Wakin. Ta na fita Hudah ta je ta kulle ?ofar Wakin sannan ta dawo ta Wauki wayarta lambar Mudan ta kira bai Waga ba, sake kira tayi nan ma bai Waga ba. Sa?o ta tura masa "Na rantse da girman Allah idan baka Wauki wayar nan ba yanzu zan je na faWawa Mami duk abin da ke tsakanina da kai".


Mudan da ke kwance jikin sabuwar budurwar da ya yi, duk kiran da Hudah ke yi masa ya na gani Wauka ne dai ba zai yi ba, ?arar shigowar sa?o ya ji, duba sa?on ya yi, zumbur ya mi?e zaune, babu shiri. Jikinsa ne ya hau rawa, ganin abin da sa?on ya ?unsa.
Cikin rawar jiki ya danna wa Hudah kira saboda ya san tsaf za ta aikata hakan tunda har ta rantse.


Hudah na ganin kiransa tayi masa banza, sai da ya kira sau uku sannan ta Wauka, ta ce "Ashe ka na ginin kirana Wauka ne ba za ka yi ba? saboda yanzu ba ni da sauran wani amfani a gurinka?".

Shiru ya yi ya na sauraronta, ya na mamakin yaushe ta iya tsiwa, sannan ya ce "Ba haka ba ne, ba na kusa da wayar ne, lafiya dai? na ga kiranki ne"


"Au tambayata ma ka ke yi lafiya, wai Ya Mudan me ka Wauke ni ne? kar ka Wauka shirun da na yi ya na nufin na ha?ura, ina so a kullum ka sa ka wa ranka cewar ba ka da wata matar fa ce ni, duk da na san yanzu ba ni ce a gabanka ba, amma ina son ka sani ita wannan da ka ke zumuWi da rawar ?afa a kanta ba zaka taSa mallakarta ba, sannan ka zamana a cikin shiri domin a kowane lokaci zan iya sanar da su Abba halin da muke ciki. Saboda dole ne cin kasuwa da ma?iyi, ina ankare da kai kwata kwata yanzu hadda tsayawa ka saurare ni ba ka yi, to ni zan nemawa kaina mafita. Kuma ba iya abin da muke aikatawa ba har da cikin ka da nake Wauke da shi".


"What!? Ciki kuma Huda?"

"?warai ciki, ko ka kurmance ne da baka ji me na ce ba?"
"Haba Hudah na san babu wani maganar ciki. Wai me yasa baki yar da da ni ba? na fa Wa miki cewar you are the one my heart chose. Sannan batun ba na saurararki, na ga kin Wauka da zafi ne. I'm waiting for you to blow off steam so that we can discuss. So ya kamata ki fahimce ni".


"Ni ba wani daWin bakin da zaka yi mini yanzu, saboda an yi wal?iyya na ganka" daga haka ta kashe wayar, Mudan da fe kansa ya yi, ya ce "Wannan yarinyar an yi jarababiyya". Mi?ewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login