Showing 12001 words to 15000 words out of 52998 words

Chapter 5 - RAMIN ƘARYA HAUSA NOVEL

24 Oct 2025

84

ta ?i fitowa ne, saboda bata ga amfanin baWi ba rai ba, sai da ta tabbatar da Gwaggo ta bar gurin sannan ta fito, ta ce " Me yasa ba kwa jin magana ne? musamman ke Maryam garin yaya har ki ka hankaWeta, kuma ki ka kasa tsayawa ki bata ha?uri?".

"Mama ni fa ban san da ita a gurin ba, shine na zo a guje na hankaWeta ban lura ba".

"To kuma da ta zo sai ki ka yi mata rashin kunya, madadin ki bata ha?uri, yau Allah kaWai ya san irin masifar da wannan abin zai jawo".

Shiru Maryam tayi, tana zumSura baki,


*******

Abba ya kira Mudan, ya ce ya zo yana son ganinsa, babu Sata lokaci Mudan ya zo, Abba ya ce "Magana zamu yi da kai"

"To Abba Allah yasa ba wani laifin na yi ba?".

"Dama mun yanke shawarar haWa ku aure, kai da ?anwarka Sharifa ?ar gidan Alhaji Munir, dan haka, idan ka samu lokaci, ka shiya ka je gurinta ku dai-daita kan ku".

Wani farin ciki ne ya baibaye zuciyar Mudan, cikin jin daWi da zumuWi ya ce "To Abba, duk hukuncin da ku ka yanke akan mu dai-dai ne, na amince, kuma in sha Allah zan shirya yau da yamma na je, na gode sosai".

Abba ya ce "Ma sha Allah na ji daWin hakan sosai, Allah yasa ita ma ta karSe ka, kamar yanda ka karSe ta".

Tashi Mudan ya yi, yana jin kamar an yi masa albishir da aljanna, sallama ya yi wa Abba yana ?ara godiya, sannan ya fita.


Mami na zaune a bedroom Winta, tunda ta ji labarin cikin da Zainab ke Wauke da shi, duk wata walwalarta ta Wauke, zuciyarta ta shiga sa?a mata mugunta iri iri, ganin ?wa?walwarta, ta kasa hasaso mata mafitar da ta ke nema, yasa ta Wauki wayarta, ?awarta Turai ta kira, bayan ta Wauka babu gaisuwar komai, ta ce "?awata a kwai damuwa".

Turai ta ce "Damuwar me fa?"

Cikin ?unar rai ta ce "Wannan matar ce ke Wauke da juna biyu".

"What! wai ki na nufin kishiyarki ciki ne da ita? to ya aka yi aka haihu a ragaya? bayan mun san cewar mun toshe duk wata hanyar da muka san zata iya Waukar ciki".

"Mami ta ce "Ni ma dai abin ya bani mamaki, wannan matar na rasa yanda zan yi da ita, ta zame min jaraba".

"Kar ki damu ?awata, ki kwantar da hankalinki, zan nemo muna mafita".

"Yawwa ?awata ina godiya dan shine na ke sonki, duk lokacin da ki ka ganni cikin damuwa, ko matsala, ki na ?o?ari wajan ganin kin nemo mini mafita". "Haba kar ki dam???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?u yi wa kai ne".


Bayan fitar Mudan Abba ya kira Alhaji Munir, ya sanar da shi cewar ya gayawa Sharifa Mudan zai zo wajanta da yamma.

Ya amsa masa da "To" sun Wan taSa fira sannan suka yi sallama.

Alhaji Munir ya dubi Matarsa Fatima da ta yi kicin-kicin da fuska, saboda jin abin da aminin mijin nata ya faWa, ya ce "Alhaji Musa ne ya ce Mudan zai zo gurin Sharifa yau".

Cikin damuwa ta ce "Gaskiya Alhaji ni wannan haWin ba son shi nake yi ba, tun lokacin da ka zo mini da zance nan ban yi murna da shi ba, yaron nan kwata-kwata bai da ce da Sharifa ba".

"Fatima babu abin da Alhaji Musa zai nema a gurina na kasa yi masa, sannan Mudan tamkar Wa yake a gurina, dan haka bana son na sake jin kin yi wata magana akan zancen nan matu?ar ba alkhairi zaki furta ba, sannan kuma ki gaya mata ta shirya tarbarsa, kar ta kuskura tayi masa abin da bai dace ba".

Me?ewa tayi ba tare da tace masa ?ala ba ta bar falon, Wakin Sharifa ta je, ta sheida mata cewar ta shirya Mudan zai shigo yau su gaisa.

A gigice Sharifa ta mi ?e daga kwancen da take, cikin raunataciyyar murya ta ce "Momy what do you mean? . Dama dady bai dai na wannan maganar ba, Please Momy I cannot do it, auren Mudan tamkar salwantar da rayuwata ne Momy".

Ta ?arasa maganar ta na sakin wani marayen kuka.

Momy ta ce "Sharifa ki yi ha?uri, ba abin da zan iya yi akan wannan lamarin, maihaifinki ya gargaWeni akan maganar nan, ba muda zaSin da ya wuce addu'a, duk abin da yafi alkhairi Allah ya tabbatar mana da shi".

Ta na gama faWar haka ta bar Wakin, saboda ba ?ara min tausayin ?arta take jiba, tana fita a Wakin, ta kira wayar Hajiya Zainab, bayan ta Wauka gaisawa suka yi, sannan Fatima ta ce "Zainab ki na da labarin abin da su Alhaji ke shiryawa na auren Mudan da Sharifa?".

Ammi ta ce "Eh Alhaji ya sanar da ni, dama ina son idan na samu lokaci na zo har gida mu yi magana dake, saboda na san ba lallai ne wannan haWin ki yarda da shi ba".


"Zainab ke ma kin san wannan haWin kwata-kwata bai dace ba, sannan yarinyar nan ba son shi take ba, maganar gaskiya a kwai cutarwa a wannan lamarin".

"Na sani Fatima, amma ina son ki yi ha?uri, ki kau da kai akan komai in sha Allah Sharifa ba zata taSa tozarta ba".

Haka dai Zainab ta ci gaba da kwantar mata da hankali, har ta samu ta ha?ura, sannan suka yi sallama.



*******


Haidar ya rame sosai ya shiga damuwa, akan rashin goyon bayan da Ummansa ta?i bashi, ga rashin ganin Afnan da baya yi, sau uku yana zuwa gidansu baya samun ganinta, gaba Waya ji ya yi duniyar ta yi masa duhu, ya rasa inda zai saka ransa ya ji sanyi.

Umma na ankare da duk halin da yake ciki, tana tausayawa Wan nata, sosai, ta san so ta san yanda a zabarsa yake, ta san yanda yake hanawa zuciya da gangar jiki nutsuwa da kwanciyar hankali, tana fatan Allah ya kawo wa Haidar Wauki ya sanya masa ha?uri da juriya a zuciyarsa, ya bashi ikon yi mata biyayya akan duk uwanrnin da ta gindaya masa.


Bayan sallar azahar Gwaggo na zaune bakin iccen ceWiyar dake tsakar gidan, da Wan rediyonta ta na sauraro, Inna Hajara ce ta zo gurin ta ce "Gwaggo iska ake sha" "Eh Hajara yau garin ne akwai zafi, kuma hakan baya rasa nasaba da ranar da ake yi, shiyasa na ce bari na fito nan na sha iska."

Zama tayi a gurin ta na faWin "Haka ne kam, gaskiya yau ana rana sosai".

Hira suka fara yi, nan Gwaggo take gaya mata rashin kunyar da su Afnan suka yi mata, da iskanci da Maryam ta yi wa mai babur, Inna Hajara salati ta yi, ta ce "Wai yaran nan me suke son mayar da kansu ne?. Gaskiya yakamata ki Wauki mataki, mutanen gidan nan sun raina ki da yawa, yanzu ki dubi Bilki, saboda ta ga mijinta baya nan shine tunda ta je biki gidansu, har yanzu bata dawo ba, kusan sati Waya, kin ga wannan bai dace ba".

Gwaggo ta ce "Rabu da munafuka, cewa ta yi kwana uku zata yi ta dawo, duk zan yi maganinsu daga ita har marasa kunyar yaran nan".

Sannan ta kuma cewa "Hajara, wai yaushe yarinyar nan za ta dawo ne, ta kwana biyu fa a can? yakamata ta dawo gida haka, ina kewarta".


Washe baki Inna Hajara tayi, jin an ambaci ?ar gaban goshinta, cikin jin daWi ta ce "Gwaggo in sha Allah gobe ko jibi zasu dawo, ko jiya na yi waya da Shafa ta ce su na nan dawowa, dangin mijin na ta ne idan ta kai musu ziyara, ji suke kamar kar ta dawo".

"Aa ni kam idan ?anwarki zasu ri?e ita dake auren Wan uwansu su ri?e, amma ba da jikata ba".

Dariya Hajara tayi, ta ce "Ai zasu ma dawo".


******


Mami da Hudah na zaune a falon, Mudan ya fito cikin shiri, yana tafiyar yanga da kasaita.
Gyaran murya ya yi, ya Wan saci kallon gefen da Hudah ke zaune, ta sunkuyar da kai tana danna wayarta, sannan ya dubi Mami ya ce "Mami na shirya zan je gurin Sharifa, a yi mini addu'ar samun karSuwa".


KaWan ya rage Hudah bata kuma sakin wayar hannunta ba, wani irin abu ta ji yana ta so mata tunda ga kasan zuciyarta, yana bin lungu da sa?o na gangar jikinta. Me ya mudan ke nufi dani ne? ta yi wa kanta tambayar ba tare da ta samu amsarta ba.

Mami ta ce "To my son Allah ya bada sa'a, in ka je ka gaishe mini da sirikar tawa".

fita ya yi, ba tare da ya sake kallon in da Hudah ke zaune ba, saboda ya fuskanci yanayinta, da ruWanin da ta shiga, a halin da ake ciki sai dai tayi, ha?uri baya jin zai iya aurenta ya bar Sharifa.

Bayan fitarsa Mami ta ce "Daughter na manta ban sa nar miki ba, Abbanku sun yanke shawarar haWa yayanki aure da ?ar abokinsa Sharifa".

"Allah ya kyauta yasa da mu za'a yi".

Daga haka ta mi?e ta bar falon, da kallo Mami tabi Hudah tana tunanin me a ka yi mata, data shiga wannan damuwar.

Hudah direct bedroom Winta ta wuce, tana zuwa ta faWa kan gado ta saki wani marayan kuka, "Wallahi ya Mudan baka isa ba, ka yi kaWan ka lalata tawa rayuwar kai kuma ka inganta taka, matu?ar ina numfashi baka isa ka aure Sharifa ba, ko da hakan yana nufin bankaWuwar Sarnar da muka daWe muna yi ne".


Cikin zumuWi, Mudan ya isa gidan su Sharifa bayan sun gaisa da Momy, ta ce "A kai shi sashen ba?i" kai shi aka yi, sannan a ka kawo masa ruwa da lemo.

Kusan minti ashirin yana zaune Hudah ba ta fito ba, tana can Momy na daru da ita akan ba in da zata je, da ?yar Momy ta shawo kanta, ta shirya,

Ciki-ciki ta yi sallama, amsawa ya yi, ya na binta da kallo tare da karantar yanayinta.

Zama ta yi, ba tare data kula shi ba, da ?yar ta buWa baki ta ce "Sannu da zuwa ya hanya?"


"Alhamdulillah fatan ki na cikin ?oshin lafiya?".

Kawar da kai tayi, bata amsa ba, idanu Mudan ya zuba mata, ko ?iftawa ba ya yi, jikinta ne ya bata cewar kallonta yake, "Malam idan baka da abin faWa, tashi zan yi, dan ina da abin yi". Ta faWa kamar wadda aka yi wa dole.


"Ni ko nake da abin faWa, dama ce ba'a bani ba, Baby tunda ki ka shigo in da nake zaune baki kalla ba, ki sani soyayya ce ta kawo ni gurinki, kar ki yi tunanin auren haWi za'ayi mana, ina son ki sawa ranki cewar mu tamkar masoyan da suka daWe da gina soyayyarsu ne.


Da sauri Sharifa ta yi masa wani kallo, da ya kasa tantance ma'anarsa, baki ta buWe da niyar yin magana, sai kuma ta yi, shiru.

Ganin haka, yasa mudan cewa, "Bab feel free to share your thoughts".


Dubansa tayi, da so tayi ta share shi sai kuma tayi wani tunani, gara ta faWa masa abin da ke ranta, gyara zama tayi ta ce "Wanda nake fatan na aura mutum ne na musamman mai baiwa ta musamman a cikin dubban samari, shi ne wanda zan iya kasancewa tare da shi a cikin wuya ko daWi, domin na san tunaninsa a kullum bai wuce yanda zai inganta rayuwata ba".

"Waye shi?" Mudan ya yi tambayar cikin yana yi na rashin jin daWin abin da ta faWa.

"Idan lokaci ya yi, zaka san ko waye".

"I am speechless because of what you said Huda".

"To ni zan wuce, tunda baka da abin faWa, ni ina da abin yi"

Daga haka, Huda ta mi ?e tare da barin falon, ta bar Mudan zaune a gurin, binta da kallo, ya yi, yana jin zafin abin da ta yi masa. Shi ma tashi ya yi, ya bar gidan, ko sallama bai yi wa Momy ba.


*******

Sai bayan sallar isha Baba ya shigo gida, kai tasye Wakin Gwaggo ya nufa, da sallama, a zaune ya tarar da ita gama sallarta kenan, ya ce "Gwaggo barka da gida".


?in kula shi ta yi, balle ta amsa gaisuwar daya ke mata,

Gyaran murya ya yi, ya kuma cewa, "Gwaggo ina wuni".

Cikin hasala ta ce "Ka ri?e gaisuwarka bana bu?ata".

"Subhanallahi, Gwaggo me ya yi zafi?. Dan Allah idan na yi miki wani laifi ne ki gaya mini na baki ha?uri, kin san fushinki a gare ni masifa ne".

"?an ladi na gaji da kawo ma ka ?orafi a kan iyalinka, ina son in Wauki mataki da kaina, saboda kai ban ga alamar zaka iya tsawatar musu ba, ka zama zakaran Inna, sai yanda mace ta yi da kai".


"Gwaggo dan Allah ki yi ha?uri. Duk da ban san abin da suka yi miki ba, ina mai ?ara baki ha?uri, in sha Allah komai zai zo ?arshi, daga yanzu ba za su sake yi miki wani abun ba".

"Rufen baki, kullum zancen ka kenan, zaka Wau mataki, da iyalin na ka sun san cewar ka na da kataSus a gidan ka, ai ba za su yi mini rashin kunya ba, har su samu damar ya da ni a ?asa ba".

Da sauri ya Wago ya ce "Gwaggo ya da ke ?asa kamar ya?".

"Au to ?arya nake yi maka kenan, baka yarda ba?" .

"A'a Gwaggo Allah ya baki ha?uri, ba haka nake nufi ba, abin ne ya bani mamaki, Gwaggo garin ya ya hakan ta faru?".

Cikin masifa Gwaggo ta kwashe komai ta gaya masa, sannan ta ce tana son idan aka idar da sallar asuba, ya yi magana a masallaci. Duk mai son wannan yarinyar Afnan, ya zo za'a bashi ita sadaka.

"Gwaggo" yi mini shiru, wannan umarni nake baka, ba shawara ba, matu?ar ka yarda cewar ni mahaifiyarka ce, to ka aikata abin da na ce. Tashi ka bani guri, na gama magana.



Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA....* =ث?


Story & writing

By

Mrs Muttala (Amanar cool)





*YOUNG TALENT*
*WRITER'S ASSOCIATION*




Sadaukarwa ne ga Aysharcool



Free book
'?



Page 13&14




________Jiki a sanyaye Baba ya yi wa Gwaggo sallama, ya fita da isar sa sashensu, da Maryam ya fara cin karo, bata yi aune ba, ta ji saukar tagwayen maruka hagu da dama. A gigice ta dafe fuska, cikin tashin hankali da kaWuwa.

Murya Baba ta ji, cikin tsananin fushi da fusata, ya ke magana
"Baki da hankali ne?. Ke mahaukaciyar ina ce? Mahaifiyar tawa za ki yi wa irin wannan rashin mutuncin, saboda ba ki da kunya? to na fara gajiya da wannan halin naku, ba zai yiwu ku rin?a haWa ni da mahaifiyata ba".

Maryam kuka take yi, sosai marukan sun ratsa ta, za ta iya cewa tunda ta girma, ta yi wayo, Baba bai taSa saka hannu ya dake ta ba sai yau, sanadiyyar waccan tsohuwar, lallai Gwaggo za ta gane shayi ruwa ne.

Cikin rawar jiki da ruWani, Afnan ta ce "Baba Wan Allah ka yi ha?uri, in sha Allah ba za mu sake ba".

"Rufe min baki shashasha kafin na zo na make ki kema, ai ke da ita duk kanwar ja ce, da ne ki ke mai hankali, yanzu ke ma kin koyi halin da ba na ki ba. To bari ku ji daga yau duk wadda ta sake gaya wa Gwaggo ko da ba?ar magana ce sai na yi mugun saSa mata".

Shiru suka yi ba wanda ya kuma magana, sai da ya yi faWa sosai har Mama bai raga wa ba, sannan ya bar gurin, ya yi shigewarsa Waki.


Bayan sa Mama ta bi ta na mamakin sauyin halinsa lokaci Waya, a zaune ta same shi ya tsurawa guri Waya ido ya na kallo, zama ta yi a bakin katifar ta ce "Baban Afnan" shiru ya yi bai kula ta ba, ta sake cewa "Baban Afnan dan Allah ka yi ha?uri, in sha Allah ba za su sake ba".

"Kar ma su daina, zan yi maganinsu ne, sannan ina son ki kasance a cikin shiri, saboda a kowane lokaci za ki iya jin na ba da auren Afnan".

"Aure kamar?" ta yi tambayar ta na ?ura masa ido.

"Kamar yanda ki ka ji na faWa, aurar da ita zan yi ga duk wanda na samu, tunda ita ta gagara fitar da miji, Idan Allah ya kai muna rai gobe zan ba da sadakarta a masallaci ga mai so".


Cikin ?unar rai, da jin zafin maganar, ta ce "Haba Baban Afnan wannan wa ce irin magana ce, Afnan Win ce za ka ba da sadakarta, sai ka ce ta rasa mashinshini, gaskiya ni ban yarda da wannan abin ba".

Duban ta ya yi ya ce "Ke ki ke aurena ko ni nake aurenki? sannan maganarki zan bi ko ta mahaifiyata? to bari ki ji in faWa miki ke dai baki isa ki hana ni aikata abin da na yi niyyar yi ba, idan har ki na son zaman lafiya tsakanina da ke, dole ne ki yi biyayya wa umarnina".


"Ban taSa tunanin akwai ranar da zaka yi wa ?a,?anka irin wannan auren ba, sai dai a yanzu ba zan yi mamaki da hakan ban, duk abin da yafi zama alkhairi a cikin wannan lamarin, ina ro?on Allah ya tabbatar mana da shi" daga haka tayi shiru, bata kuma magana ba, saboda a yanda ta lura da mijin nata, komai zai iya faruwa idan ta ce zata yi wani yun?uri, ta na lura da shi kwana biyun nan ?iris yake jira sai ya hau faWa da banbami ba gaira ba dalili, ta rasa dalilin faruwan hakan, amma ba komai za ta ci gaba da addu'a komai ya yi farko zai yi ?arshe.


"Kin taimaki kan ki, kuma hakan shine zaman lafiya a gareki". Ya yi maganar tare da ?ara kawar da kansa gefe, shi kansa mamaki yake yi, me yasa yake yawan jin haushinsu har cikin ransa baya jin daWin hakan.


Da kallo kawai Mama ke bin sa, sannan ta mi?e ta Wauko masa abincinsa, ta ajiye.


******


Bayan fitar Mudan a gidansu Sharifa, kai tsaye gurin sharholiyarsa ya wuce, domin ya rage damuwar abin da Sharifa tayi masa, sai dai ya ?udiri aniyar auren ta ko ta na so, ko ba ta so, sai ya cika muradinsa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login