Showing 45001 words to 48000 words out of 52998 words

Chapter 16 - RAMIN ƘARYA HAUSA NOVEL

24 Oct 2025

601

aikin sun kammala komai yau". "Habawa makaho fa? Ina ba dai Aunty Afnan ba".

"To shikenan bari ku gani Allah ya kai muna rai gobe za ku shaida" haka dai mai gari ya ci gaba da jansu da hira har suka Wan saki jikin su.


"Atika wai kin san amaryar yaron nan ta na garin nan, yau iyayenta suka zo da ita"

"Haba dai, ashe Allah ya taimake mu da aka kammala aikin nan yau, kenan ta na can gidan mai gari?"

"Eh ta na can, mun yi magana da mai gari ya ce gobe za a kawo ta, ni yanzu damuwata yaron nan ban san yadda zau Wauki wannan auren ba, kar ya zo ya wala?anta ?ar mutane ya sani jin kunya. Duk halaccin da aka yi mini akan auren nan, tunda bayan sadaki ban ba da komai da ake yi na aure ba".

Atika ta ce "Haka ne mai gida, amma ba na jin zai iya watsa maka ?asa a ido, ba na tunanin ko ni na ba shi umurni zai ?i bi. Duk da ba ni na haifeshi ba balle kai, in sha Allah babu abin da zai faru sai alkhairi".

"To Aitika Allah ya sa, ya kauda duk wani abin ?i".

Da Amin ta amsa sannan ta kuma cewa "Amma yakamata ace ya na nan saboda ka ga ba zai yi yu a kawo masa amarya ba, kuma baya nan".

"Eh haka ne, zan yi magana da shi in sha Allah goben nan zai zo kafin tariyar matar tasa". "To Allah ya kai muna rai gobe Win".

"Amin ya rabbil alamin"


Washe gari

Haidar ya je gaishe da Umma, zama ya yi jiki a sanyaye

Duba na tsanaki Umma tayi masa ta ce "Haidar wai jikin ne har yanzu? To ko dai asibiti zaka je ne? Gaba Waya ina lura da kai tun jiya nan kamar wanda aka yi wa wani abin, anya Haidar babu abin da ke damunka kuwa?".

Shiru Haidar ya yi, ya lumshe idanuwansa Afnan na yi masa gizo

"Haidar magana nake yi maka, ka yi mini shiru"

"Umma babu abin da ke damuna, kawai ba na jin daWi ne".


Umma ta gyara zama ta dube shi da kyau ta ce "Haidar me yasa ka ke son Soye mini damuwar ka ne? A tunaninka ba zan iya gane ka na cikin damuwa ba ne? Kar ka manta mahaifiyarka ce ni, babu wata damuwa da za ka shiga na kasa fahimta. Haidar in ma akan wannan maganar da muka yi da kai ne ya sa ka cikin damuwa, Haidar ba na yi hakan ne dan na ba?anta maka ba, sai dan ina son ka fara tsayawa da ?afafuwan ka ne. Duk abin da mutum ya tsara da ban wanda Ubangiji ya tsara da ban, kuma tsarin Allah shi ne dai-dai. Haidar ina son ka kasance mai yarda da ?addara, komai ka gani ka Wauka haka Allah ya so kuma ya tsara maka faruwar shi a rayuwa. Duk abin da Allah ya yi dai-dai ne, sannan Allah ba zai taSa Worawa bawa abin da yasan ba zai iya Wauka ba, sai dai in shi bawan ya kasa yarda da ?addarar da ta same shi Win, idan damuwar yarinyar nan ce ka saka a ranka, ka yi ha?uri ka cire ta daga rayuwarka, ka rungume abin da ke ga banka a yanzu".


A hankali Haidar ya kalle Umma jin ta na mishi wasu maganganun da ya kasa fahimta.

"Umma abin da ke gaba na a yanzu? Na kasa fahimtar in da maganganu ki suka dosa".


"Haidar kenan zan fahimtar da kai, ina so ka fara cire damuwar da kasawa ranka, ba na son ganinka cikin damuwa hankali na tashi yake yi".

"To Umma in sha Allah, ki ci gaba da taya ni da addu'a, don ita na fi bu?ata a yanzu".

"Addu'a ai kullum cikin yi maka ita nake Haidar Allah ya ya yi maka abin da ke damunka, ya shiga cikin lamarinka. Allah ya baka ikon yi mini biyayya a kan komai Haidar".


Ya amsa da Amin, ya na rufe idon shi alamar bacci yake ji.


"Haidar je ka kwanta, na ga kamar bacci ka ke ji, zuwa anjima zamu ?arasa maganar, kayi ?o?ari ka cire damuwa a ranka".

"To Umma" ya mi?e da ?yar ya fita daga Wakin Umma ta bishi da kallo ta na jin tausayin sa, ko ya zai Wauki wannan lamarin idan ya ji? Ta na dai fatan ya kasance mai biyayya.


********


Da safe Huda na zaune a falo Mudan ya shigo, zama ya yi a falon, ba tare da kalle Huda ba, wayar shi ya fara dannawa, ya kira wata lamba har kiran ya tsinke ba a Waga ba, sake kira ya yi, ya na jin an Wauka tun kafin a yi magana ya ce

"Hello bab good morning. Ya ki ke? Ya Mom ina fatan kin tashi cikin ?oshin lafiya?".

Wata irin zabura Huda tayi ta mi?e tsaye, ba tayi wata wata ba ta zo ta ?wace wayar daga kunnen shi ba tare da ya kula da tasowarta ba, ta buga wayar da ?asa ta na huci.


Cikin mamaki da ruWu Mudan ya mi?e tsaye bai tsaya komai ya Wauke Huda da bahagon mari.

"Ba ki da hankali ne? Ke mahauciyar ina ce? Ke har kin isa dan ina waya da wata ki ce za ki buga mini waya da ?asa, wawuyar banza mara tunani...." Ai bai ?arasa ba ya ji murya Mami cikin tsawa ta ce

"Mudan ya isa haka, Huda Win ka ke jifa da wannan kalaman? Lallai Mudan ka girma, akan wata banza za ka zagar mini ?a har ka dake ta...." "Mami ki daina kiranta da banza, Hasina ba banza ba ce". Ya tari numfashin Mami da wannan maganar.

"Hasina Mudan Hasina na ji ka ce? Wace Hasinar ka ke magana akanta?" Mami tayi maganar ta na tsare Mudan da ido.

Cikin rashin kunya, da rashin tsoro ya ce "Hasinar Momy Turai mana, ita ce budurwata kuma ita ce wadda nake son aura, shi ne saboda ba ta da hankali ta ga ina waya da ita za ta buga mini waya da ?asa"


RuWewa Mami tayi, ta rasa me za ta yi, tsabar ta ruWe, fuuu ta juya ta koma Wakin ta, har lokacin Huda na dafe da kunce ta kalli Mudan ta ce "Wallahi sai ka yi nadama da dana sanin wannan abin da kayi mini, mugu azzalumi, macuci".

Du?uwa Mudan ya yi ya Wau wayarsa ya bar falon, bai kuma kula ta ba.


********

Afnan bayan sun karya, suna zaune a Waki ita da Maryam, Asabe ta shigo Wakin da sallama.

Amsawa suka yi, zama tayi na ajiye kofin hannunta, sannan ta Wakko wani ?aramin kofi ta tsayawa Afnan maganin da ke cikin kofin da ta shigo da shi ta mi?a mata, karSa tayi ta ce "Me za a yi da shi?"

Asabe ta ce "Kamar ya ban gane ba? Sha za ki yi mana".

"To maganin meye? " Afnan tayi tambayar ta na tsuke fuska.

Asabe ta ce "Ai gara ki saki fuskarki, maganin sanyi ne, da muke dafawa amare, ke har ?an mata za su iya amfanin da shi".


Maryam ta ce "Kenan ni ma zan iya sha?"

"Eh mana idan ki na so kema gashi nan sai ki Wiba ki sha".

Afnan kuwa kasa yarda tayi ta ce ba za ta sha ba, ita a tunaninta maganin mata ne.

Titsiyeta Asabe tayi ta saka ta a gaba, dole ba yadda ta iya ta sha, sannan ta kuma kaWa mata wani gari da nono, nan ma da ?yar Afnan ta sha.

Asabe ta ce "Ba na son shegantakar banza, ana nema miki ?anci ki na wasa. Ko haka ki ke so a kai gidan mijin naki, babu wani Wan gyara? Salon ya jiki salam kamar kazar da aka dafa babu gishiri, idan ki ka san daWin wannan abin da kan ki za ki zo ki na cewa aba ki".

Wata irin kunya ce ta kama Afnan, ta ji kamar ?asa ta tsage ta shiga, Maryam kuwa me za ta yi in ba dariya ba, dan ta lura matar akwai ban dariya.

Asabe ta kuma cewa "Yo to Maryam ai gaskiya nake gaya mata, anjima fa za ta tare a gidan mijinta, to ana bata kuma ta ?i karSa, yanzu ma so muke a je a gyara mata Wakin".

Maryam ta ce "Dan Allah idan za a je Wakin nata zan biku".

"To shikenan, sai an tashi zan yi miki magana".

Tashi tayi ta fita daga Wakin

Maryam ta dubi Afnan ta ce "Aunty wai ba in da zamu samu aron waya ne mu kira Mama?"

"Maryam ni ma tunanin da nake yi kenan, amma bari zuwa anjima idan mun samu mai ara mana waya, ko kuma mu a ri ta mai gari".

"To shikenan"


Babu Sata lokaci aka je Wakin amarya har da Maryam, cikin murna da sakin fuska Atika ta tarbe su, tayi musu jagora Sangaren da Wakin amaryar yake, Waki Waya ne, da baranda, sai banWaki da wurin da huwar abinci, ba laifi an gyara Wakin anyi shafin suminti a ?asan Wakin an saka farar ?asa, Wakin sai ?amshi yake. Duk da haka sai da Afnan ta faki idon mutane tayi kuka. ?akin ya yi kyau an shinfiWa ledar ?asa da kati fa, sai labulayin da aka saka, aka ajiye mata sauran kayanta a gefe Waya. Saboda Wakin na da girma.


Bayan sallar isha matan mai gari da sauran ma?ota, suka haWu domin kai Afnan Wakin ta, nasiha sosai mai gari ya yi mata, banda kuka ba abin da take yi, haka aka Wauke ta zuwa Wakinta.



Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA....* =ث?





_WRITING BY AMANAR COOL_
'?




*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*




Page 45&46



__________?an kai amarya ma sun samu tarba ta mutunci da karramawa a wajen Atika da ma?ota da ta gayyato, nasiha aka ?ara yi mata sosai kafin suka bar gidan, ba yadda Afnan ba ta yi ba akan Maryam ta zauna, amma ?ememe Asabe ta ?i barin ta, ta tasa ?eyarta gaba, ta ce "Yo hauka muke yi da za a bar miki ita, shi angon na ki ki kai shi ina?".


Afnan na ji na gani aka watse gaba Waya, aka barta ita kaWai, tsoro ta rin?a ji, ga damuwa tayi mata yawa, hakan ya sa ta fashe da kuka. Tunanin Mamanta da ya addabi zuciyarta, ya ?ara bijiro mata, tasan Mama na cikin damuwa ita ma.


Sarkin fada ne ri?e da waya a hannunsa, wata lamba ya kira ana Wauka.

Ya ce "Wai ya aka yi haka ta faru ne? TunWazu nake saka ran ganin yaron nan ya zo amma shiru bai zo ba, ya ku ke so na yi da ?ar mutane ne? Ko so ku ke ku nuna mini ban isa ba ne? Yanzu gashi an kawo Wiyar mutane babu shi ba alamar shi, shin hakan dai-dai ne? A kawo Wiyar mutane a Waki a ajiyeta ita kaWai kamar mayya? Gaskiya ban ji daWin wannan abin ba, yanzu da bai zo ba ya kuke so na cewa iyayen yarinyar nan? ko Wazu sai da mai gari ya tambaye ni, na ce masa ai yana hanya yau zai ?ara so. Shin ko so ku ke dangi suyi mini dariya? dama suna jin haushin shiga lamarin ku da na ke yi".


Shiru ya yi ya na sauraran abin da ake gaya masa a cikin wayar


Daga baya ya ce "To shikenan, amma ya tabbatar da gobe ya zo garin nan, in ma zaman ne ba zai iyaye a nan ba, sai ya Wauki matar tasa". Da ga haka ya kashe wayar ya na cigaba da masifa. Dan ba ?aramin Sata masa rai suka yi ba.


Atika ta dube shi ta ce "Ka yi ha?uri mai gida, gaskiya bai kyauta ba, ni kaina banji daWin wannan abin ba, wallahi da na kalli yarinyar sai da ta ba ni tausayi, yarinya kyakkyawa da ita, kuma da alamu akwai nutsuwa a tattare da ita".


Sarkin fada ya ce "Ni ma ina jin tausayin yarinyar, musamman yanzu sai Allah yaron nan in ba kunyata ni zai yi ba".


"Ka yi ha?uri in sha Allah hakan ba za ta faru ba, ni yanzu damuwata yadda za ta kwana ita kaWai a Wakin nan, gashi yanzu mu ba yara ne damu ba, balle ace su taya ta kwana, Wazun ba yadda ba ta so a bar mata ?ar uwarta ba, aka ?i, na so na saka bakina akan a barta Win. To ina gudun su gane mijin baya nan".


Tsaki ya yi, ya na faWin "Yara basu a je komai sai shirme da shiririta, ana yi musu gata ba sa gani".

Ha?uri Atika ta shiga bashi, da ?yar ya yi shiru ya daina mitar da yake.


Allah sarki Mama tun jiya cikin damuwa take, tunanin yaranta ya saka ta a gaba, ga Baba ya yi halin ko in kula da ita, ta na son ko da muryarsu ne ta ji, tana son sanin halin da suke ciki. Duk da tasan inda suke ba za a cutar da su ba.

Sai dai idan ta tuna da rashin sanin wane irin miji Afnan ta aura abin na Waga mata hankali, da ?ara saka ta a damuwa. Duk da ta na yi mata addu'a da fatan Ubangiji ya haWa ta da miji na gari mai tsoron Allah, haka dai ta kasance cikin damuwa, komai cikin sanyi jiki take yinsa.


Afnan ta daWe ta na kuka sai da ta ji kanta ya yi ciwo kamar zai rabe mata gida biyu, sannan tayi shiru ta daina kuka. Tun ta na baza ido, da jiran tsammanin ganin wanene mijin da Allah ya haWa ta zama da shi a matsayin abokin rayuwa, amma shiru babu shi babu alamar shi, tsoro ne ya ?ara kamata, ta du?un?une guri Waya, ta fara tunanin to kodai mijin baya sonta ne? Shi ma auren dole ne aka yi masa.

Ta na nan zaune tayi jugum idan ta gama wannan tunanin sai wannan a haka har bacci ya Wauke ta.


Kiran sallar farko a kan kunneta a ka yi shi, a hankali ta mi?e zaune, ta kunna filitar hannun da ta gani a Wakin, can gefe ta hango buta, mi?ewa tayi ta Wauki butar tayi waje, dudubawa tayi har ta ga inda banWakin yake, bayan ta fito alwala tayi ta koma Waki, Wankwalinta ta shimfiWa tayi nafila sannan ta zauna ta na lazimi, sai da aka yi assalatu ta mi?e tayi raka'atanin fijir, sannan ta gabatar da sallan asuba.


Zama tayi ta na addu'a tare da yi wa Allah ki rari, ta na kai masa kukanta, ta na nan zaune ta ji ana sallama.


Amsawa tayi, ta tashi tsaye fitowa tayi, haske har ya fara bayyana.


Atika ce ta shigo domin ta duba ya ta tashi

Afnan a murya ta gane ta, saboda jiya da aka je da ita wurinta fuskarta a rufe take.


Du?awa tayi har ?asa ta ce "Ina kwana Inna"

"Lafiya ?alau Alhamdulillah, fatan kin tashi lafiya? Ya ba?unta da kuma kaWai ce?"


"Alhamdulillah"


"Ki yi ha?uri na rashin ganin mijin na ki, jiya abin hawa ne, ya lalace musu a hanya, da yake baya gari, kin san ?arfen nasara bashi da tabbas".

Sunkuyar da kai tayi ta ce "Babu komai".


Atika ta ce "To ma sha Allah, dama zuwa ne nayi na duba ki, bari na je a haWa abin kari sai aka kawo miki".


"To" ta amsa

Atika ta juya ta bar gurin, Afnan bin gidan da kallo tayi, a fili ta ce "Alhamdulillah Allah na gode ma da wannan ni'imar da ka yi mini".

?aki ta koma tayi zaune, tare da yin tagumi


Kamar kullum yau ma Haidar bayan ya dawo daga masallaci, ya shiga Wakin Umma domin ya gaisheta, zama ya yi ya ce "Umma barka da safiya, fatan kin tashi lafiya?"

Shiru tayi ba ta ce masa ?ala ba, ta ci gaba da jan carbi

Gyaran murya ya kuma yi, ya ce "Umma barka da safiya...." "Dakata ri?i gaisuwarka ba na bu?ata, kuma ka tashi ka fitar mini a Waki".

"Subhanallah! Umma fushi ki ke da ni har haka? Please Umma dan Allah kiyi ha?uri, ki fahimce ni, Umma ba zan iya jure ganin fushinki a gareni ba, da wanne zanji?".


"Haidar tunda nake da kai ban taSa baka umarni ka bijire mini ba sai jiya, ka ba ni mamaki Haidar, a tunanina duk hukuncin da zan yanke a kanka batare da sanin ka ba, kuma ka karSa ka yi mini biyayya a kai. To Wan uwana ma ya isa ya yanke shi akan ka, amma sai kanuna mini bai isa ba, ni ma Win da na ke ganin na isa na tursasaka ka nuna mini a wannan karon ban isa da kai ba. Tunda nake da Wan uwana ban taSa jin shi kin tsananin fushi irin na jiya ba. Kuma duk a dalilin abin da kayi, ai ko ya ya ne ya kamata tunda na ce ka je, ka je Win. Haidar ina ilimin ka yake? Ina tunanin ka? Da har zaka kasa karSar ?addararka da hannun biyu, ka yi tunanin hakan baya cikin tsarina a yanzu, amma da Allah ya ?addari lokacin yinsa ya yi ai na ha?ura na karSa. Idan baka sani ba, wannan abin ta wani fannin gata a kayi maka, amma tunda ka nuna ba ka so, zaka iya yanke duk hukuncin da ka ke ganin ya dace, wu?a da nama a hannunka suke".


Shiru Haidar ya yi, tabbas maganganu Umman shi sun ratsa shi, sai dai ba ya jin zai iya zuwa wannan garin ya yi zama ko da na kwana biyu ne, sannan Umma da take maganar gata aka yi masa, shi babu wani gata da aka yi masa, a auren dolen da aka ?a?aba masa, kuma auren ma wai a ?auye, shi bayan takurawa da ?ara jefa shi cikin damuwa da aka yi, a halin yanzu yadda yake ji, tunda ya rasa Afnan, babu wata macen da zata ?ara burge shi. Gyara zama ya yi, ya ce


"Umma dan Allah ki yi ha?uri na Sata miki ran da na yi. Duk abin da ki ka gani ban yi dan na Sata miki rai ba, Umma ni ba ?in karSa nayi ba, zuwa canne ba zan iya ba, me yasa ba a zo nan Win ba?".


"A ta?aice dai ko yau Win ba zuwa zaka yi ba Haidar? Wato kunyata ni ka ke son yi ko? Haidar kasan illar abin da ka ke shirin aikatawa kuwa? Abin da nake ganin yafi ?arfin yinka a yanzu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login