Showing 33001 words to 36000 words out of 52998 words

Chapter 12 - RAMIN ƘARYA HAUSA NOVEL

24 Oct 2025

88

31&32



_________Sororo suka yi suna kallon ta, shigowa ta ida yi ciki, Hajara ma shigowa tayi, dan biyowa bayanta tayi, ta ji me yake faruwa, Gwaggo ta dubi Mama da kyau ta ce "To Amina yau dai Allah ya nufa, kuma ya yi ikonsa, ranar da na daWe ina jira Allah ya nuna mini ita, sai ku fara shiri saboda a kowane lokaci zaku ji ?an Waukar amarya a gidan nan".? Mama ta ce "?aukar amarya kamar ya?? ban fahimci zancen ba?"? "To ina nufin yau dai Allah ya nufi A'isha da zama matar aure, an Waura mata a yau Win nan, kuma a can ?auye, yanzu haka ma Sanusi ya na can a gaban sa a ka yi komai"

Tashin hankali wanda ba a sama sa rana ai gaba Wayansu basu san lokacin da suka mi?e tsaye ba, Mama ta ce "Gwaggo aure fa ki ka ce? Afnan Win ce za'a Waurawa aure ba tare da mun sani ba, kuma a ?auye?".

"?warai kuwa, sannan batun cewa ba ku sani ba wannan tsarina ne, kuma haka na ga damar yi, ko shi Wan ladin bai sani ba, dan haka aure dai ya Wauru"? ta ?arasa maganar ta na hura hanci, tare da kallon Maryam dake jifan ta da wani irin kallo da ta kasa tattance yanayin da take ciki, "Lafiya ki ke yi mini wannan kallon?? ko dukana za ki yi, ?aramar mara kunya saura ke"

"Ai wallahi ba wanda ya isa ya yi mini wannan aikin, ko ita da ki ka yi wa sai na ga wanda zai ja ta ya kai ta wani ?yauye can da sunan aure, wallahi kin kuru, ba dan ina gudun Sacin ran Baba ba, yau da sai na Wagawa kowa hankali a gidan nan, da sai kun ga yanda ake Wibar karan mahaukaciya".

"Au haka ma za ki ce? to kema a can Win zan sa a aurar dake in ya so sai na ga iya gudun ruwan ki".

"Ni duk ranar da ki ka yi mini wannan aikin,? dakuwa kin ?are yawo, dare zan bi na murWe miki wuya har sai kin Wauke wuta, sannan na kashe auren na dawo gida" .

Gwaggo za ta kuma yin magana ta ji Hajara ta ce "Wai Gwaggo ki na nufin Afnan dai aka Waurawa aure yau?"?.

"?warai kuwa Hajara, shi yasa ai na ce miki zan ba da mamaki".

Hajara bata kuma magana ba, bunzun-bunzun ta bar gurin kamar za ta faWi ?asa. Afnan kuwa mutuwar tsaye tayi, tun da ta ji cewar wai ita aka yi wa aure ba tare da ta sani ba, kuma a ?auye, ji tayi zuciyarta ta bushe, kukan ma ya ?i zuwar mata, a hankali ta shige Wakin su ta kwanta rub da ciki, sai sauke a jiyar zuciya take yi. Mama shiru tayi ta na mamakin wace irin ?iyayya ce Gwaggo take yi mata ita da ?a?anta.

Gwaggo juya wa tayi zata fita ganin ba wanda ya kuma tanka mata, kiciSis tayi da Baba, gaisheta ya yi ta amsa ta na faWin "Yawwa dama kai nake jira ka zo, ya amsa da "To Allah yasa lafiya".

Ciki ta kuma shiga ya bi bayanta, Mama na nan tsaye ta kasa ?wa?waran motsi, duban ta Gwaggo tayi ta ce "Lallai Amina sai yau na tabbatar da baki san ciwon kanki ba, in ban da rashin sanin ciwon kai, Allah ya nuna maka ranar auren Wan ka, amma ka kasa godiya ga Allah balle ki yi ?a murnar nan da iyaye ke yi, to ki je dan kan ki, aure ne dai an Waura, babu yanda za ki yi".? Baba ya ce "Gwaggo ban gane ba, wa aka Waurawa aure?".? "A'isha"

"A'isha kuma Gwaggo? Yaushe? kuma a ina aka Waura auren ban sani ba?"

"Au kai ma Win tuhuma ta za ka yi kenan? to a ?auye, ai na faWa maka cewar an yi mata miji a can, kuma a yau Win nan aka Waura auren, yanzu haka Wan uwanka na can a gabansa a ka yi komai". "To amma Gwaggo me yasa baki sanar da ni ba?"? "Saboda na isa ne, na isa na yanke duk hukuncin da na ga dama akan ka, da kuma iyalinka, ba tare da na nemi shawararka ba, ko na sanar da kai ba, idan kuma musu za ka yi dani, ko kana da ja akan hukuncin da na yanke ne sai in jiya? ko kuma nuna mini za ka yi ?arka ce? kai ka san zafinta?".? "A'a Gwaggo ba haka nake nufi ba, Allah ya baki ha?uri, Ubangiji ya basu zaman lafiya yasa gurin zamanta ne".

"Yawwa Amin haka na so ka ce tun farko, ke kuma ko baki sanya albarka a auren ba, addu'ar da ubanta ya yi mata ma ta wadatar, ki je can da ba?in halinki". Tayi maganar ta na hararar Mama sannan ta bar wurin.

Hajara tun da ta ji labarin an Waurawa Afnan aure, hankalinta ya tashi, tambayar kanta take yi ya aka yi har wani namiji ya amince da aurenta?? bayan Malamin nan ya ce ba namijin da zai kuma yin sha'awarta balle har ya ce ya na sonta, tsinuwa ta shiga yi wa Gwaggo babu adadi,? saboda ta wargaza mata shirinta, ba haka ta so ba, duk da irin yanda Gwaggo ta sa aka yi auren, amma ita sam hakan bai yi mata daWi ba, amma ko yanzu ba ?yakewa za ta yi ba, sai ta san duk yanda za ta yi ta raba auren, ko kuma ta hanata kwanciyar hankali a gidan mijin.

*********

Mami tun da ta koma sashenta bedroom ta shige ta kulle kanta ba ta fito ba, har su Alhaji Munir suka bar gidan ba ta sani ba, iyakar takaici da ba?in ciki yau Mudan ya ?unsa mata shi, yanzu duk burin da ta ce akan auren Mudan ya wargaza mata shi, saboda bashi da hankali, ta san tunda Alhaji ya yi wannan maganar sai wani iko na Allah zai sa ya kuma yarda da maganar auren, lallai za ta ci uban Mudan, kuma sai ya faWa mata wace shegiyarce yake so da har ta sa shi ya ruguza mata shirinta. Wayar Turai ta kira ta na Wauka tundaga yanayin muryar Mami ta san akwai damuwa.

"?awata lafiya na ji muryarki kamar da damuwa?".?

"Ki bari kawai dole ki ji ni cikin damuwa, Mudan na ?o?arin saka mini ciwon zuciya, ina cikin farin ciki, da nishaWi, amma Wan iskan yaron nan ya hargitsamini lissafi".

"Subhanallah Mudan Win? To me yayi miki ne?"

"Wai saboda tsabar iskanci irin nasa, da rashin sanin ciwon kai, har shi zai dubi idanuwan Alhaji ya ce masa wai a fasa aurensa da Sharifa, shi yana da wadda yake so, kuma abin takaicin a gaban iyayen yarinyar da ita kanta yarinyar".

Wani irin farin ciki ne ya luluSe Turai, amma sai ta fuske cikin yanayin damuwa ta ce "Amma ko Mudan bai kyauta mana ba, ina ganinsa mai hankali da tunani, amma zai aikata haka, to wai ma wace yarinya ce yake so da har zai ce baya son Sharifa?"

"Ina na sani tunda bai faWa ba, Wan iskan yaro, ina cikin jin daWina ya Sata mini rai, wallahi yanda ya ba?anta mini, shima sai na hana shi auren yarinyar da yake so, koma ?ar gidan uban waye".? "Ashsha ke ko ba a yi haka ba, yaran nan na yanzu sai a hankali, yanzu lallaSa shi za ki yi, sai mu ji wace yarinya ce yake so, ki yi ha?uri a bi komai a hankali, in dai auren shi ne da Sharifa sai anyi shi, dan ba ha?ura zamu yi ba".

"Hmmm abin da kamar wuya, gurguwa da aure nesa, ai tun da Alhaji ya ce ba za a yi auren ba, shikenan zance ya ?are".

"To dan ya ce ba za a yi ba, shikenan? sai mu zuba musu ido, ai ba ?yale su za mu yi ba, ki barni da su kawai, za ki sha mamaki. Yawwa wani irin farin ciki ki ke ciki ne? Kin ce ya wargaza miki farin ciki".

"Ki bari kawai, cikin Zainab dai ya fita gaba Waya, jiya a asibiti ta wuni"

"Ke haba dai da gaske?"

"Eh mana zan yi miki wasa ne, ciki dai babu shi, kuma daga wannan ba zata ?ara Waukar wani cikin ba".

Turai tayi wata mahaukaciyar dariya ta ce "Kai lallai Malamin nan ba ?aramin shege bane, al'amura sun tafi dai-dai yanda ake bu?ata".

"Aikuwa dai, sai kinga fuskar tsinaniyya duk tayi fari". Dariya Turai ta kuma sannan ta ce "To kin gani ko, da alama wannan Malamin ba wasa a aikinsa, dan haka zanje masa da zancen auren su Mudan, sai mu ji me zaice"

"To shikenan ba damuwa, duk yanda kuka yi da shi, sai ki sanar mini" . Sallama suka yi tare da katse kiran.

********

A can ?auye kuwa bayan an gama Waurin aure, gida suka koma, saboda kawu Sanusi yau yake son komawa gida, tambayar mai gari ya yi, batun tariyar amarya. Mai gari ya dubi sarkin fada ya ce "Sarkin fada ya za a yi ne? Yau za a je Wakko amaryar ko sai gobe?"

Sarkin fada ya ce "Ranka ya daWe batun tariyar nan, a Wan bani nan da kwana biyu, zuwa lokacin an ?ara gyara wurin da za a sata" . Mai gari ya ce "To shikenan ba damuwa, kai Sanusi ka ji abin da ya ce, sai ka sanar da Halima Win, idan ka je zan kiraka ka haWa ni da ita, na ?ara gaya mata".

"To ya yi Baba, ai babu komai, ai dama auren ne muke so, kuma an Waura, duk lokacin da suka shirya, sai suyi magana, ba sai sunje Waukarta ba, da kanmu zamu kawota". Godiya sarkin fada ya yi, sannan kawu Sanusi ya ce musu "Zai wuce, tsaraba suka haWa masa, aka bashi sadakin Afnan ya kamo hanyar dawowa gida.

********

Fitowa Mami tayi da ta gaji da zaman Wakin ta dawo falo, Huda ta gani a falon, zaune ta ci uban ado, sannan ga falon tsaf an ?ara gyara shi, kuma ta san wannan aikin Huda ne, tsaye tayi ta na kallon Huda, cike da mamaki, saboda yaushe rabon Huda da zaman falon, balle hatta gyara shi haka, ga wannan uban adon da tayi.

Kafin Mami tayi magana Mudan ya shigo falon, idanuwansa ne suka sauka akan Huda, take ya ji wani haushi da takaicinta ya cika mishi zuciya, juyawa ya yi zai bar falon Mami ta ce "Zo nan dan ubanka".



_Kuyi ha?uri da wannan ba yawa, yau ba na jin daWi ne._



Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA....* =ث?




_WRITING BY AMANAR COOL_
'?




*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*




Free book =???



Page 33&34




___________Cak ya tsaya ba tare da ya juyo ba, "Ba magana nake yi maka ba?" Mami tayi maganar cikin jin haushinsa, juyowa ya yi ya dawo ya zauna, kafin Mami tayi magana Huda ta ce "Ya Mudan. Why are you not picking my calls?".

"I have been busy" ya bata amsa ba tare da ya kalli inda take ba. Shiru tayi ba ta kuma kulasaba, amma ?asan zuciyarta ta ji haushin yanda ya ba ta amsa Win.

Dubansa Mami tayi da kyau sannan ta ce "Mudan wato saboda kai shashasha ne, baka da hankali, shine za ka yanke wannan Wanyen hukunci ba tare da sanina ba ko neman shawarata ba? Mudan ni zaka kunyata? Ka tozartani a gaban kishiya? Ka burbuWa mini ?asa a ido, saboda baka da tunani ina kwaSar bakinka amma sai da kayi abin da ranka yake so".


"Mami ni fa..." "Rufe mini baki ko yanzu nayi mugun saSa maka, Mudan na raina wayonka, tukuna ma ?ar gidan ubawa ye ka samu da har ka aikata mini wannan aiki?" .


Shiru ya yi mata, "Wai ba magana nake yi da kai ba? Ba na son wannan sabon iskanci da ka tsiromini da shi, ke Huda ki na da masaniya akan wannan maganar? idan ya faWa miki wani abin ki gaya mini".

"Wa ni rufamin asiri Mami yaushe rabon ki ga mun zauna da shi muna hira? I have no idea"

"Ko ma ?ar gidan uban waye, ai dole zan sani, tashi ka fita ka bani guri, sakarai kawai". Mi?ewa ya yi ya fita daga cikin falon. Da sauri Huda ta bi bayansa, da ido Mami ta rakasu, tayi tsaki.

Ya na fita Huda ta sha gabansa ta ce, "Ni zaka cewa uzuri ka ke yi? Har akwai uzurin da zai hanaka Waukar kirana, wai me ka ke nufi ne? Kar ka manta ina Wauke da cikinka a jikina. Dan haka stop mistreating me.


"Huda joking aside. Da gaske ki na da ciki?"

"Au ka Wauka wasa nake yi ne? To idan ka na ko kwanto sai muje asibiti mana"

"Aikuwa Huda indai ciki ne dake sai dai a zubar da shi, taya ki ke son mu kalli. Mami da wannan abin kunyar?".

"What! Impossible na je garin zubar da cikin na mutu a banza. I am really into it wallahi".

"Ok hakama zaki ce?"


"Eh na faWa Win, kuma wallahi ina dab da yi mana terere a bainar nasi"


Haushi ne ya sa Mudan barin wurin bai sake kulata ba, itama ciki ta koma, Mami na zaune a falo taga Huda ta wuce fuuuu ranta a Sace.


***********


Sai bayan magariba kawu Sanusi ya iso gida, kai tsaye inda Gwaggo ya wuce, cikin murna take yi masa ya hanya, zama ya yi, tare da cewa "Gwaggo sannu da gida" "Yawwa Wan albarka, ya gajiyar tafiya?"

"Gajiya kam akwai ta, na sha hanya, kin san tafiyar Wai rana a wannan ?auyen a kwai wahala" "Haka ne, amma ai mun gode Allah da yasa ka je lafiya ka dawo lafiya. To ya kabaro su Yaya Win?"

"Duk suna lafiya, sunce a gaisheki"

"Ma sha Allah, abu yayi kyau sosai, yau ina cikin farin ciki, burina ya cika. Amina ba yanda za tayi da ni, to ya batun Waukar amaryar? Yaushe zasu zo?"

Kawu Sanusi ya ce "Gwaggo bari na je dai na watsa ruwa, na ce sai na dawo muyi magana". "To shikenan, Allah yayi maka albarka". Mi?ewa yayi ya nufi sashensa.


Gaba Waya su Afnan a cikin damuwa suke hadda Baba. Duk da shi bai nuna musu irin ya damu Win nan ba, amma yanayinsa ya nuna hakan, Mama rasa abin yi tayi, tana son kiran ?an uwanta ta shaida musu abin da ke faruwa amma ta kasa sanin mezatace musu, shiru tayi abin duniya duk ya isheta, wani irin tausayin ?arta ne ya addabi zuciyarta, ta na tunanin taya Afnan zata iya rayuwar aure a wannan garin. Duk da shi aure nufin Allah ne, kuma babu inda baya kai mutum, amma ta na tausayin ?arta da irin zaman da za tayi a can Win.


Afnan kuwa tunda ta shiga Waki ta kwanta bata fito ba, ko kiran sallan magariba bai fito da ita ba, saboda ta na fashin sallan, da farko zuciyarta ?e?ashewa tayi kukanma ya ?i zuwar mata, sai dai tana tuna Haidar da irin kalaman da yake yi mata, ba ta san lokacin da wani kuka ya suSuce mata ba, kuka tayi kamar ranta zai fita. Duk wata tsanar Haidar da take ji ta nemeta ta rasa, wani irin tausayinsa take ji a zuciyarta, tana tuna irin magiyar da yake yi mata, da irin son yake cewa ya na yi mata, yanzu ya zai ji idan ya samu labarin aurenta? Tayi wa kanta tambayar da ba ta da amsarta. A hankali ta ce "Allah Sarki Ya Haidai, ka yi ha?uri, ka yi ha?uri, ni ma ban yi tunanin hakan zata faru ba, da na sani tun farkon zuwanka na baka dama. Amma ina ban san abin ya hau kaina ba, a lokacin, na kasa amsarka, sai ma haushinka da na ke ji. Ka yi ha?uri my Haidar, dama can ni ba matarka ba ce, i love you, I love you, i really love you my Haidar. Da sauri tayi istigfari data tuna da auren wani akanta take cewa tana son wani, duk da ba sanin mijin tayi ba, kuma ba sonshi take ba, amma ko ba komai za tayi ki yaye ha??in aure, gudun kar Allah ya yi fushi da ita.


"Aunty dama kina son Ya Haidar ki ka tsaya yi masa kwana kwana har ki ka yi wasa da damarki? Yanzu me ye amfanin Soyon da ki ka yi? ribar me ki ka ci? Kin ja an aura miki wani can wanda baki sanshi ba, baki taSa ganinshi ba, baki san halinshi ba, kuma wai tsabar mugunta a ?auye". Sai da Maryam tayi magana sannan Afnan ta san da ba ita kaWai ce a Wakin ba, dan bata san lokacin da Maryam Win tashigo Wakin ba.

A hankali ta tashi zaune, ta dubi Maryam sannan ta ce "Ni kaina bansan meyake damuba ba, Maryam a lokacin haushinsa nake ji, duk da ina jin daWin kalamansa, sai dai a ?asan zuciyarta sai na ji tsanarsa da haushinsa, Maryam bansan na damu dashi ba sai yanzu da aka yi mini wannan auren, na rasa ya zan yi, ina tausayinsa, ina tunanin halin da zai shiga. Idan ya samu labarin auren nan". Ta ?arasa maganar tana sakin wani sabon kuka, zafi take ji sosai a cikin zuciyarta,m.


"Aunty Afnan kiyi ha?uri, dan Allah ki daina wannan kukan, in sha Allah wannan auren sai sun yi ga abin da basu yi zato ba akansa, ina ji a jikina wula?antar da ake son a ga ke yi, ba za su taSa ganin hakan ba, mu ci gaba da addu'a Allah yana tare damu, kuma in sha sai sunji kunya". Haka Maryam ta ce gaba da rarrashin Afnan cikin kalaman kwantar da hankali da sa nutsuwa, kamar ba ita ce mai wannan rashin kunyar ba.


Kawu Sanusi tunda ya dawo Hajara ke Wauke masa kai, da hura hanci, ita a dole fushi take yi dashi, saboda an munafunceta da shi.


"Hajara" kawu ya kira sunanta, sai dai tayi masa banza kamar bata ji ba.

"Hajara" ya kuma kiran sunanta.

Kamar ta kuma shareshi, sai ta fasa cikin tsiwa da rashin sanin darajar miji ta ce "Lafiya wai da zaka zo ka dame ni da kira sai ka ce naci ban biya ba?"


Sakin baki yayi ya na kallonta, tare da tambayar kansa me aka yi mata? Take wannan abin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login