Showing 27001 words to 30000 words out of 52998 words

Chapter 10 - RAMIN ƘARYA HAUSA NOVEL

24 Oct 2025

82

zasu, bari na shirya yanzu sai ka kai ne, na ga me yake faruwa". "To ai Mami ba mu san asibitin da suka je ba"

"Ina tunanin ba zai wuce asibitin da muke ganin likita ba, bari na fito sai mu tafi".


Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA....* =ث?




Story & writing

By

Mrs Muttala (Amanar cool)




*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*



Sadaukarwa ne ga Aysharcool




Free book
'?



Page 25&26




__________Abba gudu yake sosai kamar zai tashi sama, ko gaban shi baya gani, cikin ikon Allah ya isa asibitin lafiya, ko da ya isa a lokacin Ammi ba ta ko iya Waga hannunta, da sauri aka shiga ciki da ita domin bata taimakon gaggawa.


Mami ta na shiga Wakinta, ta saki dariyar mugunta, cikin murna da farin ciki ta fara taka rawa, sai da tayi mai isarta, sannan ta ce "Shegiya tsinanniyya, ki ka ce asiri baya kama ki, ni na san sai idan baki haWu da shegun ba, sai na ga ta yanda za ki Wauki ciki a gidan nan, yanda ban haifa ba, haka kema baki isa ki haifa ba, da dai ?addara ta sanya kin haifa tun kafin na zo gidan, to ba yanda zan yi, amma yanzu dai baki isa ba wallahi, ko da na haifa ni, ba zantaSa bari ke ki haifa ba".


Shiryawa tayi ta fito, a tare suka fita harabar gidan, Mudan ya buWe mata mota ta shiga, sannan ya ja suka bar gidan.

Abba ya kasa zama, ya kasa tsayi, sai safa da marwa yake yi, addu'a yake Allah yasa cikin bai fita ba, ji yake kamar ya shiga Wakin ya ga halin da take ciki. A Wakin kuwa da ?yar likitoci suka samu jinin ya tsaya, duk wani gwaji da yakamata su yi sun yi, sai dai ba suga abin da ya haifar da wannan matsalar ba. Sai dai cikin ikon Allah cikin bai fita duka ba, alluran bacci aka yi mata domin ta samu hutu, Abba na ganin fitowar Waya daga cikin likitocin da sauri ya isa gurin shi, yana tambayar shi wane hali take ciki, umarni ya ba shi da ya biyo shi, officer. Bayan shi Abba ya bi.

Bayan sun zauna likitan ya dubi Abba ya ce "Alhaji duk wani gwaji da zamu yi mun yi, amma bamu ga abin da ya haifar da wannan matsalar ba, amma Alhamdulillah mun yi nasarar tsayar da jinin, kuma wani ikon Allah cikin bai fita duka ba. Zamu bata maganin da zata yi amfani da shi, in sha Allah cikin zai yi, sai dai zai rage yawan kwanakin sa".


Tun da Abba ya ji cewar cikin bai fita ba, yake godiya ga Allah, cikin farin ciki ya ce "Likita na yi matu?ar farin ciki da jin cewar cikin bai fita ba, amma to wane hali take ciki?" "Ta na nan mun yi mata alluran bacci domin ta samu isashen bacci, saboda ta wahala sosai, yanzu bari na rubuta maka magungunan da za a siyo ta na tashi zata fara amfani da su". KarSar takardar ya yi, ya ?ara yi wa likitan godiya ya fita. Yana fitowa ya ga su Mami sun shigo, da sauri ta ?araso gurinsa ta na faWin "Alhaji lafiya? meyafaru ne? Mudan ya ce mini ya ga ka fito da Zainab a hannu ka sakata a mota, kun bar gidan, da jin hanka na san ba lafiya ba, shine hankalina ya kasa kwanciya, na ce ya kawo ni asibiti na gani ko nan ku ka zo".


Abba ya ce "?ar uwarki ce ba lafiya, haka kawai ta fara bleeding".

"Subhanallah! Alhaji ina fatan dai cikin bai fita ba?". Kamar wanda a ka kullewa baki ya ce "Yanzu dai ba abin da take bu?ata sai addu'a, da fatan Allah ya bata lafiya ". Cikin iya ?warewa a munafunci Mami ta fara matsar ?walla, ta na faWin "Zainab Allah ya yaye miki wannan matsalar, a ce da mutum ya samu ciki sai ya zubi, kai Allah ya yi mana maganin wannan masifar".

Ha?uri Abba ya bata, sannan ya mi?awa Mudan takardar maganin ya ce ya je ya siyo magungunan, karSa ya yi ya fita, wata likitace ta kuma fitowa daga Wakin da Ammi take. Tambayarta Abba ya yi ko za su iya shiga su ganta? ta ce "Za su iya ganinta, sai dai ta samu yin bacci, suyi a hankali kar ta farka, ana son ta samu isashen bacci".

Ko da suka shiga ta na kwance, fuskar nan tayi fayau, kallonta Mami tayi, tana addu'a kar Allah ya tashe ta, tana fatan daga nan sai kushewarta. Babu Sata lokaci Mudan ya dawo da magungunan, karSa Abba ya yi, tare da sa masa albarka. Sannu da jiki Mudan ya yi mata. Sun daWe zaune a Wakin, sannan Mami ta ce "Alhaji ya kamata ka je gida ka yi wanka, ka ci abinci, in ya so ni sai na zauna da ita kafin ka dawo, gudun kar ta farka ba kowa a kusa". "Saratu ba zan iya tafiya ko ina ba, sai na ga yanda yanayin jikinta ya yi, ki dai koma gidan ki haWa mini abinci, ki ba wa Mudan ya kawo mini, ki haWo masa da kayana ina so zan yi wankan a nan". Ba dan ranta ya so ba, haka ta ha?ura, ta so ya je gida domin ta ida nufinta akan Ammi, amma sai ta ce "To Alhaji hakan ma ya yi, bari mu wuce, Allah ya bata lafiya". Da Amin ya amsa, sannan suka bar Wakin.


***********


Bayan an tashi su Maryam daga makaranta, bakin titi suka fito domin neman abin hawa, wata mota ce ta zo, har ta wuce sai kuma ta dawo baya, dai-dai gurin su ta tsaya, duban motar suke yi, suna tunanin me ya tsayar da ita gurin su, sauke gilas Win motar aka yi, Sharifa ce, ta na murshishi ta ce "Sisters sannunku" Feena ta ce "Yawwa sannu" Maryam shiru tayi bata ce ?ala ba, Sharifa ta kuma cewa "Ina fatan dai kun gane ni? sannan idan ba damuwa ku zo na rage muku hanya, na ga kamar abin hawar zai yi wuyar samu a nan Win, ga rana ana yi sosai".

Caraf Maryam ta ce "Bama bu?ata, ki yi tafiyar ki". Feena ta ce "Haba Maryam me ye haka? wallahi Allah idan muka tsaya a gurin nan wahala zamu sha". "DaWina da ke Fenna gidadanci, shikenan bamu santa ba, bamu taSa ganinta ba, bamu san daga inda ta fito ba, sai ta ce muzo ta rage mana hanya, muku ma gamu kwaWayayyu sai muje".

"Wallahi Allah Maryam na san kin gane ta, ita ce fa budurwar da muka taSa haWuwa da ita a napep Win nan" . "To dan mun haWu da ita a napep kin san daga ina ta fito?" . Sharifa kallon ikon Allah take yi, duk da ta san Maryam Win na da gaskiya, nan ta ji yarinyar ta ?ara shiga ranta, "Haba ?ar uwa ki na tunanin zan cutar daku ne? dube ni ki ga na yi kama da masu cutar da mutane?". "Shi mugu ya na da kama ne? ai ba a gane shi ta fuska, kin ga mun gode ki yi tafiyar ki kawai".


An kai ruwa rana kafin Maryam ta yarda, suka shiga motar, Sharifa da Feena ce a gaba, Maryam na baya, Feena aka fara saukewa, Maryam cewa tayi a sauke ta a nan, amma Sharifa ta ?i sai da kaita har ?ofar gida, fitowa Maryam tayi, ta ce "Muna godiya" ita ma Sharifa fitowa tayi, tana ?o?arin shigewa gidan ne, ta ji "Sharifa ta ce "?awata tsaya mini na shiga mu gaisa da su Mama". Da har zata yi magana sai kuma tayi shiru.


Tare suka shiga gidan, ko da suka isa Mama na zaune, Afnan kuma na Waki, har ?asa Sharifa ta du?a ta ce "Mama barka da rana ya gida?" "Lafiya ?alau Alhamdulillah, Maryam wannan kuma wacece?" "Wata ce da muka taSa haWuwa da ita a napep, shine yanzu ta ganmu a bakin titi bamu samu abin hawa ba ta rage mana hanya" . "Ta ko kyauta, sannunki da ?o?ari, Allah ya yi albarka, tashi daga du?en zo ki zauna ga shimfiWa, ke Maryam kawo mata ruwa tasha". Tashi tayi hau tabarma ta zauna.


Ruwan ta Webo mata, babu ?yan?yamin komai Sharifa ta karSa tasha, sannan ta ce "To Mama zan wuce ina sauri ne, amma in sha Allah zan samu lokaci na kawo muku ziyara". "To shikenan, Allah ya kaimu muna godiya, Allah ya bar zumunci" tana ?o?arin mi?ewa tsaye Afnan ta fito daga Waki, da idanuwa Sharifa ke bin ta da kallo ko ?iftawa ba ta yi. Afnan ta ce "Mama ba?uwa muka yi ne?" "Eh tare da Maryam ta zo, ta rage musu hanya ne".

Sharifa ta ce wa Afnan "ina wuni"

"Lafiya ?alau ya kike?"

"Alhamdulillah"

Daga haka ta yi wa Mama sallama, har zata fita sake juyowa ta kalli Maryam ta ce "?awata ko rakiya ba zan samu ba?". Tayi maganar ta na murshishi. Mama ta ce "Aikuwa dai, wannan ?awar taki sai a hankali, sai dai kuma har zaki tafi ban san sunan ?ar tawa ba". murmushi tayi ta ce "Sunana Sharifa". "Ma sha Allah Sharifa Allah ya yi albarka, a gaida gida". ?ara duban Afnan tayi sannan ta juya, Maryam ta mara mata baya, har wajan mota ta tarakata ta ce "Na gode sosai, ki yi ha?uri da abin da ya faru Wazu, kin san wasu yaran masu kuWi akwai su da jiji da kai da raina mutane, ni kuma ba na son wula?anci, shi ya sa ki ka ga na yi hakan".

"Babu komai Maryam ai ki na da gaskiya, ina fatan dai zamu ?ulla ?awance dake?" "In sha Allah, ai na ga kina da kirki". "To ya yi ina godiya da amsa tayi na da aka yi sai na sake dawowa, yawwa Maryam wannan da na gani Auntynki ce?" "Eh ita na ke bi" "Ayya Allah Sarki, da alama dai tana da kirki" dariya Maryam tayi ta ce "Ai na fita kirki". "Ba shakka ni shaida ce ai". Shiga motar tayi ta na Wagawa Maryam hannu, ta ja ta bar gurin, ita kuma ta koma ciki.



*******


Mudan ya kawo wa Abba abinci da wasu kayan sakawa, wanka ya yi, ya ci abinci, sannan ya je ya yi sallan azahar, Mami ba ta farka ba sai misalin ?arfe huWu da rabi, da ?yar ta iya buWe idanunta, Abba sai jera mata sannu yake, a hankali ta yun?ara zata tashi Abba ya taimaka mata, ta tashi ya rakata SanWaki ta gyara jikinta, ta fito abinci ya zuba mata ya na bata a baki, bayan ta gama ci ya bata magungunanta ta sha, likita ne ya yi shigo, ya ganta a zaune, ya ce "Ashe ta farka kenan". Abba ya ce "Eh ta gata nan har ta ci abinci ta sha maganinta". "To ma sha Allah, ya ki ke jin jikin na ki da sau?i?".

"Da sau?i"

"Alhamdulillah, ina ga Alhaji zamu sallame ku, sai ta kiyaye shan maganinta akan lokaci, sannan kuma ta kiyaye yin wani dogon motsi saboda yanayin da ta ke ciki, ba a bu?atar tayi dogon motsi". Abba ya ce "In sha Allah za a kiyaye" . Sallama ya basu, tare da yi musu fatan Alkhairi, godiya sosai Abba ya yi masa sannan suka bar asibitin.


Mami na zaune ta na ?arewa Huda kallo, gaba Waya yanayinta ya sauya, sannan ga wannan sabon iskanci da ta tsiro da shi na rashin zama cikin mutane. Ta na ?o?arin yin magana ne ta ji alamun buWin get, tashi tayi ta li?a ta taga, tsaki tayi ganin su Abba ne, da har zata zauna sai kuma ta buWe ?ofa ta fita.



Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA...* =ث?




Story & writing

By

Mrs Muttala (Amanar cool)





*YOUNG TALENT WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*




Sadaukarwa ne ga Aysharcool



Free book
'?



Page 27&28



_________Ko da ta fito har Ammi ta fito daga mota, Abba na ri?e da ita, ?arasawa tayi gurin ta na faWin, "Alhaji yanzu nake cewa na koma asibitin Win, na ga ya jikin nata, saboda na yi kiran wayarka baka Waga ba, sai daga baya na tuna da ba waya a hannunka" "Abba ya ce "Kin ga sun sallame mu, jikin nata da sau?i". Ta dubi Ammi ta ce sannu Zainab ya ?arfin jikin? Allah ya sauwwa?e ya tsare gaba".


"Da sau?i Alhamdulillah, Amin ya rabbi" ri?eta ya yi suka shiga ciki, Mami na biye da su, sai harararsu take yi, a falo suka zauna, Abba sai lallaSata yake yi, takaici da haushi ne suka cika zuciyar Mami, mi?ewa tayi, tayi musu sallama ta fita. Abba ko da ya duba wayoyinsa yaga tarin kira babu adadi, kiran Alhaji Munir ya fara bi, bayan ya Waga ne suka gaisa Alhaji Munir ya ce "Ina ka a jiye wayoyinka ne na yi ta kira baka Waga ba?" "Ina asibiti ne, can na wuni, Zainab ce ba lafiya"


"Ashsha subhanallah! me yasa meta?"

"Irin waccan matsalar ce dai, sai dai a wannan karon Allah ya kawo sau?i cikin bai fita duka ba".

"Alhamdulillah, ma sha Allah, Allah ya tsare ya inganta, sai mun shigo dubiya" "To shikenan sai kun zo, yau fa na so mu haWu domin mu tsaida ranar bikin yaran nan, sai ga wannan matsalar ta faru" "Ni ma abin na raina sai dai na shigo Win" Abba ya amsa masa da to sannan suka a jiye wayar. Ammi tunda ta ji cewar cikin bai fita ba, ta tsare Abba da idanuwa, dubanta ya yi ya ce "Madam me, irin wannan kallon haka".

"Da gaske cikin bai fita ba?" tayi tambayar ta na ?ara tsareshi da ido.

"Bai fita ba, ya na nan, in sha Allah a wannan karon sai kin haifomini Baby mai kama da ke"

"Yanzu duk wannan jinin da na zubar kuma cikin na nan? Alhamdulillah Allah na gode ma, Please Alhaji ka yi shiru da bakin ka bana son kowa ya kuma sanin cewar ina da ciki, har Saratu bana son ta san cewar cikin bai fita ba". "To ya yi duk yanda ki ka ce hakan za a yi, Madam".


********


FaWa sosai Baba ya yi wa Maryam tare da ?ara gargaWinta, a kan Gwaggo, da ma sauran mutanen gidan, Maryam ta cika tayi fam, saboda ta tsani a yi mata faWa, gara a daketa da a yi mata faWa, daga Mama har Afnan ba wanda ya kulata. Afnan tunda Haidar ya yi mata maganar nan ta kasa samun sukuni a zuciyarta, kullum cikin tunani take, saboda maganganunsa sunyi tasiri a zuciyarta, ta na jin wani ba?on yanayi na shigarta a game da shi, wani lokacin ji take muryar shi na yi mata amsa kuwa a kunne, sannan gefe Waya ta na jin tsanarsa a ranta, wanda ta rasa dalilin hakan, shiru tayi ta tsura wa guri Waya ido, abin duniya ya isheta, ita ba ?awace da ita ba, balle ta neme shawararta, Maryam ce de abokiyar shawarata, ta san ko da tayi mata magana ba kulata za ta yi ba, tunda aka yi mata faWa, yau ba wanda zata kula a gidan nan.

"Afnan lafiyarki kuwa?"

Ta ji muryar Mama na tambayarta.

Cikin inda inda ta ce "Lafiya ?alau Mama, me ki ka gani?"

"Babu komai ne zaki zauna ki yi tagumi, kin tsurawa guri Waya ido".

Murmushi tayi bata kuma magana ba, saboda bata san me zata ce ba, ta san komai za faWa sai dai Mama ta dubeta kawai amma ba yarda za ta yi ba.


Haidar ma a nashi Sangaren tunda ya samu damar amayar da abin da ke zuciyar shi, ya samu sassaucin abin da yake ji, sai dai fargabarsa Waya Umman shi, da kuma ita karan kanta uwar gayyar, bai san ta?amammen matsayinsa a gurinta ba, shin za ta karSi tayinshi ne?. rashin wannan amsar ya ?ara Wugunzuma zuciyar shi cikin wasuwasi, da zulumi, ya na son kiran wayarsu sai dai ya na fargabar abin da zai ji daga bakinta, daurewa ya yi, ya lalubo lambar ya danna kira. Afnan na zaune, kusa da Mama kira ya shigo a wayar, hannu ta kai zata Wauki wayar ta mi?awa Mama, sai dai lambar Haidar ta gani, da yake Maryam tayi saving Winta da Ya Haidar. ?in mi?awa Mama wayar tayi, sannan itama ta kasa Waukan wayar.


Mama ta ce "Ke lafiya? ki bani wayata mana ana kirana, kin wani ri?e waya kin hanani"


"Mama ba fa ke ake kira ba"

"To sai ki kai wa mai wayar abarsa, tunda ba tawa ba ce" kafin Afnan tayi magana, wani kiran ya kuma shigowa. Afnan tsorawa wayar ido tayi, takaici ya hana Mama ta kuma yi mata magana, Maryam na zaune duk abin da ake tana kallon, wani haushine ya sake kamata, dan ta san wannan kiran daga ni Haidar ne, kamar wadda aka tsikara Afnan ta mi?e, Waki ta shiga da wayar, bin bayanta da kallo suka yi, mamaki ne ya cika zuciyar Mama. Ta na shiga wani kiran na kuma shigowa Wagawa tayi bata yi magana ba.

"Assalamu alaikum" ta ji an yi sallama, wata Soyayyar ajiyar zuciya ta sauke, ba tayi magana ba.

"Assalamu alaikum" a ka kuma yin sallama, kamar wadda a ka tilastawa yin magana dole ta ce "Wa'alaikassalam". Haidar jin muryar abar ?aunarsa bai san lokacin da ya mi?e zaune ba ya ce "Amincin Allah ya ?ara tabbata a gareki abar so da ?aunata, fatan ki na cikin ?oshin lafiya?". ji tayi zuciyarta ta buga da ?arfi, da sauri ta zauna saboda ?afafuwanta na neman kasa Waukarta.

"Afnan Afnan na san ki na jina. Please ki taimaka mini ki ba ni dama muyi magana dake ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login