Showing 39001 words to 42000 words out of 52998 words

Chapter 14 - RAMIN ƘARYA HAUSA NOVEL

24 Oct 2025

604

waya da Malamin ta akan zancen Auren Mudan da Hasina, ya ce "Ta kwantar da hankali, ya fara aiki akan lamarin, kuma aikin ya fara tasiri a kan yaron, dan yanzu haka baya ganin ko wace mace sai ita, a halin yanzu a kowa ne lokaci zai iya kai kansa ga Hasina".


Cikin zumuWi Turai ta ce masa "Ai Malam na ga alamun nasara, dan yanzu haka yaron ya ce baya son yarinyar da a ke son haWa su aure da ita, an janye maganar auren gaba Waya".

Dariya Malamin ya yi ya ce "Dama na san hakan za ta faru, ki zuba ido ki ga abin da zai biyo baya, na riga na saka masa soyayyar Hasina a zuciyar sa, a yanzu duk wanda ya ce zai hana shi auren ta, ba zai saurare sa ba, ko da kuwa mahaifiyar sa ce".


Turai tayi shewa ta ce "Da kyau Malam aikin ka ya na kyau, ina so a ?ara rura wutar soyayyar Hasina a zuciyar sa, zan sake turo maka wasu kuWin, uwar ta sa ma na so a rufe mini bakin ta, sai dai ina ga, a barta cikin hayyacin ta, ina so na ga yadda za tayi, idan taga Wan ta ya bujirewa umarnin ta, dan na san ba lallai ne ta yarda da batun auren sa da wata ba. Tunda ta ?wallafa ranta akan auren sa da waccan yarinyar".

Malam ya ce "Kin san mahaifiyar ta sa kenan?".


"Eh Malam ?awata ce".

Dariya ya kuma yi ya ce "To shikenan duk yadda ki ke so haka za a yi, ni in dai da kuWi babu abin da ba zan yi ba" . Ya na gama faWar haka ya katse kiran. Turai tayi dariya ta ce "Saratu kenan za ki ga abin da baki zata daga gare ni ba, mu je zuwa".


********


Bayan fitar Gwaggo Bilki ta ja hannun Mama suka zauna, ta dube ta ta ce "Aunty Amina maganar da na ji a bakin Bahijja gaskiya ce? Wai an Waurawa Afnan aure? Kuma a ?auye?".

Mama ta ce "Gaskiya ne Bilki, yanzu haka maganar da ta ke yi kenan, wai sai a shirya ta yau a kai ta, bayan babu abin da muka shirya, tunda ba ta sanar da kowa zancen auren ba, kwatsam ta zo da maganar wai an Waura mata aure, hadda shi kansa Baban su bai sani ba, daga ita sai Sanusi ne suka shirya abin su".

Inna Bilki ta ce "Amma wannan tsohuwar tayi asarar hali wallahi, ni shiyasa ki ka ga ko fitowa ba na yi, kullum ina lunguna zama na, dan wallahi ba ha?uri ne dani ba, ba zan iya Waukar wannan abin da take yi miki ba. To kuma yanzu ke yarda za ki yi a kai ta can ?auyen kuma?".


"Bilki ya zan yi? Ban da in zubawa sarautar Allah ido, ni na rasa wace irin ?iyayyace Gwaggo take yi mini ni da yara na".

"Ai ba ke ka Wai take nuna wa tsana ba hadda ni, sai dai taki ta fi tawa, kuma hakan bai rasa nasaba da waccan munafukar Hajaran, ki yi ha?uri Aunty Amina, in sha Allah Afnan ba za ta wula?anta ba, kuma sai sun ji kunyar duk abin da suka aikawa Afnan ina ji a jikina, yanzu dai bari na tashi akwai wasu kaya da na zo da su, kayan masu kyau ne bari na Wakko su sai a fara bata su tayi amfani da su kayan na da kyau da inganci, idan Bahijja suka dawo daga islamiyya sai tayi mata ?unshi, jarababiyya ai tunda ta ce sai an yi tariyar nan, wallahi ikon Allah ne kawai zai hana faruwar hakan".


"Mama ta ce "To shikenan, da so nayi ma a fara ba ta maganin sanyi tukuna, kafin ta fara shan maganin mata Win" .

Bilki ta ce "Kar ki damu hadda na san yi akwai, shi ma ya na da kyau sosai, yawwa kin sanar da ?an uwan ki batun tariyar ta yau Win?".

"Ko batun auren ban sanar da su ba"

Bilki ta ce"Haba Aunty Amina me yasa baki gaya musu ba? Ai wannan ba abin da za ki Soye musu ba ne".

"Wallahi Bilki gaba Waya na ruWe ne, ina tunanin taya zan faWa musu maganar ne".

"Haba Aunty ai ha?uri za ki yi ki sanar da su, tunda dai kin san dole za su sani, ya kamata ki kira su yanzu ki sanar da su, ina Afnan Win take? Bari na je na Wakko kayan" . Ta ?are maganar ta na mi?ewa tsaye.

Mama ta ce "To shikenan bari na kira su, Afnan Win ma na Waki ba ta jin daWin"

"Subhanallah to Allah ya bata lafiya, ai ko wannan abin na janyo mata zazzaSi, kai wallahi Allah Gwaggo ba tayi dacen hali ba"

Mama ta ce "Kai Bilki Gwaggo ce fa"

"Eh ita Win ai gaskiya na faWa"

"To Allah ya kyauta, duk wanda ya yi na gari kansa ya yi wa".

Fita Bilki tayi, ita kuma Mama ta Wauki wayar ta, Baba ta fara kira bayan ya Wauka ta faWa masa abin da Gwaggo ta ce, sannan ta ce masa Afnan ba ta jin daWi ya aiko mata da maganin zazzaSi, babu kowa a gidan balle su karSo mata a shago.

Baba kamar wanda aka tilas tawa yin wayar dole, haka yake amsawa Mama. Ya ce "Ta bari gashi nan tafe gidan".

Bayan ta gama wayar da shi ne ta kira gidan su domin ta sanar dasu abin da ke faruwa.


Gwaggon kuwa ce ma Hajara tayi ta kira mata Sanusi a waya ya zo yanzu ta na son ganin sa. Bayan Hajara ta kira mata shi ne babu Sata lokaci sai gashi ya zo.


Ya ce "Gwaggo gani Allah yasa lafiya?"


"Ina ku lafiya Sanusi Amina na neman kai mu jahannama, yarinya da auren ta, amma Amina ta bata damar wani ?aton ya zo gurin ta".

Kawu ya ce "Wani kuma ita Aminar?"

"Kwarai kuwa sai da na fatattake shi sannan ya bar ?ofar gidan nan, to dan haka na yanke hukunci yau a gidan mijinta za ta kwana, maza kira mini Yaya a waya ya shaidawa gidan mijin nata yau za a kawo musu amaryar su, mun hutar da su, ba sai sun zo Waukar ta ba".

Kawu ya ce "To Gwaggo wannan shawara ta ki tayi, dama me ye amfanin zaman ta a gidan bayan da auren ta". Ya ciro wayar sa daga aljihu ya dannawa Yaya Bala kira.


?auka ya yi suka gaisa sannan ya mi?awa Gwaggo wayar, amsa tayi bayan sun gaisa ta ce "Da ma Yaya magana ce akan yarinyar nan A'isha ina so yau ta tare a Wakin ta, saboda ban ga amfanin zaman ta a gidan nan ba, shi ne na ce bari na faWa maka sai ka sanar da gidan mijin na ta in sha Allah yau za a kawo ta Wakin ta".


Yaya Bala ya ce "To ban tari numfashin ki ba Halima, amma anya tariyar nan za ta yi yu a yau Win nan? saboda basu ida gyara Wakin da za a sakata ba, ina ga ki yi ha?uri tariyar ko zuwa jibi ne, dai-dai sun kammala aikin sai a kawo ta Win".

"To shikenan Yaya amma dai ko gidan ka ne sai a kawo ta ta zauna in ya so idan sun gama aikin sai ku sa da ta da Wakin ta ko?".

"To shikenan ba damuwa hakan ma ya yi sai a kawo ta nan Win" . Godiya tayi masa sosai sannan suka yi sallama.

Ta ce wa kawu Sanusi ya je ya biWo mota idan aka yi sallar azahar sai su kama hanya, dan hadda shi za a je. Ya amsa da mata da "To" sannan ya tashi ya fita.



Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA....* =ث?




*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*



_WRITING BY AMANAR COOL_
'?




Free book =???



Page 39&40



____________"Why Afnan i m deeply in love with you. Ya ki ke so na yi da rayuwata? Afnan you are the one my heart chose. Ta ya za ki yi mini haka? Me yasa tun farko ba ki faWa mini ki na da saurayi ba? Sai da ki ka bari na faWa soyayyar ki, Afnan what do you mean da Soye minin da ki ka yi?".

"Dan Allah ka yi ha?uri, ni ma ba da sanina hakan ta faru ba, ka yi ha?uri, ka yi ha?uri my Haidar".


"Afnan Afnan"

Cikin razani ta farka da ga baccin daya Wauke ta sakamakon kiran da Mama ke yi mata, cike da mamaki Mama ke bin Afnan da kallo, jin ta na ambatar sunan namiji a cikin baccin ta, abin da ko a fili ba ta taSa yi ba.


Afnan kuwa sunkuyar da kai tayi ta na tuna mafarkin da tayi da Haidar.


Mama ta ce "Afnan lafiya ki ke kuwa? Waye Haidar? Me ye ala?arki da shi da har ki ke ambatar shi a cikin baccin ki? Ko a zahiri bantaSa jin sunan sa a bakin ki ba, waye shi?"


Cikin kasala da sanyin jiki Afnan ta ce "Mama ni ma ban san shi ba, kawai sharrin mafarki ne"


Shiru Mama tayi ta na ?are mata kallo sannan ta ce "Allah ya kyauta, zazzaSin ya sauka ne?"


"Eh ya sauka da sau?i"


"To Allah ya ?ara afuwa, ta so ga Bilki nan na jiran ki".

Ta amsa da "To" Mama ta fita a Wakin, ita ma a hankali ta mi?e ta fita daga Wakin, a zaune ta tarar da Inna Bilki ta na ri?e da kofi a hannun ta, ta na juya wani abu da bata san ko meye ba, zama tayi ta gaishe ta.


Cikin sakin fuska Inna Bilki ta amsa gaisuwar, tare da yi mata ya jikin.


"Da sau?i" Afnan ta ba ta amsa, tare da tambayar Mama su Maryam basu dawo daga makaranta ba. Mama ta ce "Suna hanya ba su fara dawowa ba".


Inna Bilki ta dubi Afnan ta mi?a mata kofin hannun ta ta ce "KarSi ki shanye wannan abin". Duban kofin tayi, ta kalli Inna Bilki sarai ta gane meye amma sai ta ce "Inna wannan fa?"

"Maganine" ta ba ta amsa.


"To ai na ji dama, zazzaSin ma ya sauka"


?aure fuska Bilki tayi ta ce "KarSi kisha ba na son gardama" ganin babu alamar wasa a fuskar ta, ya sa ta karSi kofin tsikar jikinta na tashi ta kafa kofin ta shaye.

Ta na gama sha ta ji zuciyar ta na tashi, ya mutsa fuska ta fara yi. Inna Bilki ta ce "Kar ki yarda ki amayar da maganin nan, ko anjima sai kin kuma sha, sauran kuma sai dai ki tafi da su can, ki ci gaba da amfani dasu".


Kafin Afnan tayi magana Hajara ta shigo da sallama amsa mata suka yi, su na binta da kallo, Hajara ta ce "To gamu mun shigo ko ba a gayyace mu ba, mu ma a yi shirye shiryen tariyar da mu" ta maida duban ta ga Mama ta kuma cewa "Amina to barkanmu su Afnan dai an yi arzikin shiga daga ciki, duk da auren na haWi ne, Allah ya nuna wa ?an baya".

Bilki tayi caraf ta ce "Yawwa barka dai, ai ba ita za ki yi wa barka ba ni, domin ni ce uwar Afnan, yarinya kam tayi arziki babba, kin san ko a kai tallan ka kuma asamu wanda zai siya arziki ne, wasu ba na jin ko tallan su a ka kai za su samu masaya, dan abin rabo ne, kowa na son siyen abu mai inganci da kyaun kallo".


Hajara sakin baki tayi kamar garkar wawa, ta na bin Bilki da kallo. Da ga bisani ta ce "Bilki ina fatan dai ba magana ce ki ka faWa mini ba?".


"Akan me zan faWa miki magana Hahara? Amsa ce na baki dai-dai da maganar da ki ka yi".


Wani takaici ne ya ?ular da Hajara, domin sarai ta gane magana Bilki ta yaSa mata, amma sai ta danne ta ce "Amina ba wani abin da za a yi ne? Kin san fa su mutanen ?auye abin magana baya musu wuya. Duk da dai abin ya zo a bazata, gara a shirya Wan wani abin da za a kai ta da shi, saboda gudun barwa yaro abin faWa".



Mama ta ce "Hajara ba abin da zan yi, wa?anda suka haWa auren su je suyi, idan kuma ba za suyi ba, sai a kai ta hakan, in ya so gidan mijin idan ba za su iya karSarta a haka ba, sai a dawo mini da ita".


"Subhanallah Amina in jin dai ba baki ki ke yi wa auren ba? Ahh bai kamata ki na irin waWannan maganganun ba gaskiya".


"Wai ke Hajara me ye naki a ciki ne, dama abin da ya kawo kenan? to ina ruwan ki, tayi wa auren baki sai ki je ki faWa, dama aikin ki ne kin saba".

Ita ma Hajara cikin masifa ta hayayya?owa Bilki "Wai Bilki ina ruwan ki da ni ne? Na sakaki a magana ta ne?".


"Eh kin sakata, ai ita ba munafuka ba ce, sannan ba ta son ganin Wan uwanta a damuwa, ita Win ta Wauki damuwar Wan uwanta ta ta ce". Gaba Waya suka juya duban su zuwa ga Maryam da shigowar ta kenan, ta ji Hajara na wannan maganar.


Hajara ta ce "Maryam ni ki ke gayawa magana haka? Saboda baki da kunya?"


"Eh na faWa Win uwata ce ke, ko dan kunga kwana biyu na Waga muku ?afa shi ne za a zo har inda muke a yi muna rashin kunya".

Mama ta ce "Ke Maryam ba na son na sake jin bakin ki a wurin nan".

"To Mama sai ta zo har...." "Ba na ce ki rufe mini bakin ki ba, maza zo ki wuce daga wurin nan".


Hajara ta ce "Korar me za ki yi mata? Ai duk abin da tayi dai-dai ne, tun farko idan ba a basu damar yin hakan ba ai ba za suyi ba".

Mama ta ce "Hajara ba na son tashin hankali, dan Allah idan har fitina ce ta shigo da ke wurin nan ki yi tafiyar ki". " Ai ko baki kore ni ba tafiya zan yi, dan ba zama zan yi ba, wato tunda ita wadda ta haWa auren tafi ?arfin ku shi ne kuka juye haushin ku a guna? To aure dai ne sai dai ku mutu, kuma ?auye ne zuwa babu fashi".


"Ai wasu suna biWar ko na ?auyen ya zo ya ce ya na son su basu samu ba, to Alhamdulillah ita Win da har ta samu na ?auyen, idan fitsari banza ne kaza tayi mu gani" Bilki ta bata amsa.

Haka dai suka yi baran baran kafin Hajara ta bar wurin.


Maryam zama tayi ta na ?un?uni, don ta ji haushin hana ta maganar da Mama tayi.

Afnan da tunda aka fara magana ko tari ba ta yi ba, sai yanzu ta ce "Mama wai tariyar me na ji ana magana ne?".


Mama ta ce "Hmmm Gwaggo ce ta ce lallai yau sai kin tare a Wakin ki..." Kafin Mama ta ?arasa magana Maryam ta yi wata zabura ta ce "Bala'i amma wannan tsohuwar ba Allah a ranta. Allah ya kasheta kowa ma ya huta".


Mama ta ce "Ke Maryam ki na da hankali? Gwaggon ki ke yi wa fatan mutuwa? Kar ki manta ita ta haifi mahaifin ku, kar na sake jin wannan maganar a bakin ki, idan ba haka zan yi mugun zaSa miki".

Kuka Afnan ta fashe da shi ta ce "Mama wallahi ba inda za ni, ko lafiya ba ni da, abari sai na warke tukuna".


"Ai Afnan sai dai ki yi ha?uri, tunda har ta furta hakan, to wallahi babu wanda isa ya hanata". Cewar ina Bilki. Maryam kam ta cika tayi fam da ta na da iko, da ta la?aWawa Gwaggo shegen duka ko sanyi ta jiya.

Rarrashin Afnan Bilki ta shiga yi, tare da bata ha?uri, ta ce "Ki yi ha?uri Afnan bawa baya wuce ?addarar sa, duk abin da ya same shi da sanin Ubangiji, kin ga su Bahijja sun dawo daga makaranta, yanzu sai ta zo tayi miki ?unshi".


Cikin kuka ta ce "A'a Inna ba na so, ni a barni a haka".


Sallama Baba ya yi ya shigo, amsa masa suka yi, suna gaishe shi, bai ida shigowa ba sai ga Gwaggo ta shigo babu sallama, sakamakon zuwan da Hajara tayi, ta faWa mata ?arya da gaskiya.


"Eh lallai Amina kin gawurta, wuyan ki ya yi kauri ya isa yanka, sa?on ki ya same ni, to ina son ki sani, wallahi na rantse da girman Allah duk ki ka kashe auren nan, ke ma sai naki auren ya mutu, ke ma wannan A'isha Win duk ki ka ?i zama a gidan auren ki, to sai dai ki zauna a gidan nan ba tare da uwarki ba. Ke kuma Wayar marar kunya na san maganin ki, sai kin gane baki da wayo, ina ji dai Umar Wana ne ko? To bari ya dawo ki ga mai zai faru". Tayi maganar ta na nuna Bilki.


Da sauri Baba ya dubi ta ya ce " Subhanallah Gwaggo lafiya? Mai ya yi zafi haka".

"Tukuna saurara mini ban fara zuwa ta kan ka ba".


"Ke kuma jarababbiyar yarinya, da tayi gadon masifa can dangin uwarki, duk ki ka ?ara yi wa Hajara rashin kunya to ba ita ki ka yi wa ba, uwarki da ubanki gasu nan su ki ka yi wa".


"Kai kuma na dawo gareka, ina son maza maza ka je kasuwa ka siyo mata katifar kwanciya, da filo, da zanin gado, ka haWo mata da labulayen Waki guda biyu, ni kuma nan ina da tukunya, da buta, da bokitin wanka. Hadda kwanukan cin abinci, Ina so yau Win nan a sada ta da gidan mijinta, kuma yanzu nan, nake bu?atar ka je kasuwa, ka kira Wan uwanka a waya ku haWu ku je tare a siyo komai da ya kamata, sai ku biWo mota a can. Tunda na ga uwarta ba ta da niyyar yin wani abin arziki".


Shiru Baba ya yi dan har cikin zuciyar shi ya ji babu daWin wannan abin da Gwaggo tayi.


"Ya na ji kayi shiru ne? Ko kaima gardamar za ka yi mini ne? To wallahi umarni ne na baka ba shawara ba, maza ka wuce yanzun nan, kar ku Sata mini lokaci".


Jiki a sanyaye Baba ya amsa da "To Gwaggo"


Ta kuma duban su ta ce "Ke kuma sai ki tashi ki shirya, don ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login