Showing 3001 words to 6000 words out of 52998 words

Chapter 2 - RAMIN ƘARYA HAUSA NOVEL

24 Oct 2025

80

irin na matar ka da kinibibi yasa kuka bar nan Win."

Baba ya ce "Gwaggo kin san dalilin daya sa muka bar gidan nan masifar Hajara da tashin hankali ta ne yasa na kama mana wancan gidan, Amina ba fitinaniyya bace, bata son tashin hankali, dan Allah ki yi ha?uri Gwaggo ki bari muci gaba da zama a can Win."

Wani banza kallo ta yi masa sannan ta ce, "Amma dai ?an ladi kai ragon maza ne, yanzu mace ce zata juya ka to wallahi baka isa ba, matu?ar ni ce na haifeka. Wallahi sai kun bar gidan nan a nan nake, bu?atar ku zauna, shashasha kawai wanda bai san ciwon kansa ba, ban da sakarcin banza ga Wakuna a nan amma ka je kana haya, saboda almubazaranci to ba dani za ayi wannan iskanci ba."

Shiru ya yi, bai kuma magana ba ji zuciyarsa na masa zafi da ciwo, wani irin abu ne haka Gwaggo ke shirin aikata musu?

Ganin hakan yasa ta ce "Tashi ka bani guri na riga na gama magana kuma a gobe nake son ku baro gidan nan."

Jiki a sanyaye ya ce "Dan Allah Gwaggo, ki bari mu ?arasa cinye kuWin hayar gidan, tun da na riga na biya, ko watanni shida bamu ci ba"

Gwaggo ta gyaWa kai ta ce "TaSWijan, ina faWa kana mayar mini? Umarni nake baka ba shwara ba, bana bu?atar zamanka a in da ka ke, kusa da ni nake son ka dawo, na din ga ganin abin da ka ke aikatawa. Wancan lokacin ma dan ba yadda zan yi ne, na bari ka bar gidan nan, yanzu kuma na ji bana bu?atar zamanka a nesa da ni".
Ya yi shiru yana mamakin wannan hukuncin na Gwaggo, da ta yanke cikin gaggawa ana zaman lafiya.
Ya risuna ya ce "In sha Allah, za ayi yadda ki ka ce" ya mi?e tare da yi mata sallama.

Yana fita ya ga Hajara, tana raragefe a wurin, tana ganinsa tayi saurin barin gurin da alama laSe ta yi.

Girgiza kai ya yi ya bar gidan ji ya yi ba zai iya tafiya kasuwa ba, kai tsaye gida ya koma, saboda damuwa, bai san ta ina yakamata ma ya fara yi wa iayalansa bayani ba.

Ko da ya isa gida, yanayinsa ya nuna wa mama akwai damuwa a tattare da shi, kuma sun yi sallama a kan cewa zai wuce kasuwa, kuma sai gashi ya dawo.

Zama ya yi ya dafe kansa.

Mama ta ce "Baban Afnan lafiya na ga kamar akwai damuwa."

Ya kalleta ya ce "Amina, Gwaggo ce" da sauri ta ce "Subhanallah me ya same ta"?

Amina Gwaggo ta ce, "Bata son zaman mu a nan gidan sai dai mu koma can gidan da zama."

Cikin tashin hankali Mama ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihim raji'un Baban Afnan me yasa Gwaggo zata ce haka? Wani laifin muka yi mata?"

Ya ce "Na san wannan ba shirin kowa bane sai na Sanusi da matarsa, dama ya daWe yana yi mini magana akan hakan ba tun yanzu ba, duk shi ne yake ziga Gwaggo. Ni kaina bana son zaman gidan nan, lokacin da muka zauna ma, me zaman namu tare ya haifa banda fitintinu. Ba wai bana son zama kusa sa mahaifiyata ne ba, tashin hankali da gutsuri tsomar mutanen gidan ce ba na so"

Mama ba ?aramin tashin hankali ta shiga ba, tunanin irin zaman da zata koma yi ne a gidan take yi, ba'a son ta ba'a son ?a?anta, me tayi wa bayin Allah nan haka da suke son ?untatawa rayuwarta data ?a,?anta.

Muryar Baba ta dawo da ita hayyacinta ji tayi yana faWar ku "Fara shirya kayan ku dan ta ce gobe take son mubar gidan nan."

Kukan da Mama ke ?o?arin haWiyewa ne ya bayyana, ta ce "Baban Afnan gobe fa wani irin lamarine wannan?"

Ya ce "Amina ha?uri zamu yi, in sha Allah komai zai zama tarihi."

******

Hajiya Saratu na hakimce a katafaren falonta waya take yi, da ?awarta. Hajiya Turai, Hudah ta shigo falon ko sallama babu, zama tayi akan Waya daga cikin kujerun falon tana jiran Mami ta gama waya, bayan ta gama wayar ne Hudah ta ce "Mami ba ni da isassun kuWi a account Wina, ina da 'yan bu?atu kuma, ina son zan je stor6" Mami "Ta ce, to sarkin kashin kuWi, zan tura miki kuWin shikenan?."

Hudah ta ce, "Eh Mami na gode. Yawwa Mami ki sa Yaya Mudan ya kai ni Dan Allah."

"Ke me yasa ba zaki ce ya kai ki ba?"

"Please Mami ya fi jin maganarki. Kuma ga garin da rana sosai, ba na son hawa abin hawa na haya"

"To na ji zan yi masa magana, idan kun kammala siyayyar ku biya gidan Hajiya Turai ku karSo min sa?o kin san Abban ku ya kusa dawowa."

"To ya yi Mamina"


*******

?akin su Afnan Mama ta je ta ce "Su haWa kayan su saboda gobe zasu bar gidan" Kafin Mama ta ?arasa magana, Maryam ta ce "Mama tafiya zamu yi ne ina zamu je kwana nawa zamu yi?. Kai Alhamdulillah naji daWi za ni huta da zuwa school na wasu kwanaki, zan samu sau?in dukan Malam Emeka, Allah dai ya kwashe masa albarka, ko da yake ina yaga wata albarka tunda ba shi da hasken musulunci, shige arnen banza".

Kallonta Mama take baki buWe

Duban ta tayi ta ce
"Mama lafiya na ji kin yi shiru?"

Cikin jin haushinta Mama ta ce, "To tsohon gidan mu zamu koma da zama, saboda Gwaggo ta ce bata bu?atar zaman gidan nan, can take so mu koma da zama, kuma a goben nan, ku fara shirya mana kayan mu".

Wata uwar ashar Maryam ta lailayo ta makawa Gwaggo ba tare da ta san tayi ba, sannan ta ce "Wallahi ba uban daya isa ya mai da ni wannan ba?in gidan".

Mama ta ce "Aifa kanki ake ji"

Ta dubi Afnan data yi musu zuru da ido ta kasa magana, sakamakon ?ullewar da cikinta ya yi, ta ce "Ke Afnan ku fara haWa kayan ku kin ji".

A hankali Afnan ta ce "Mama wai da gaske can zamu koma Win?"

Ta ce "Afnan ya muka iya wannan umarnin Gwaggo ne, bamu da zaSi sai ha?uri".

Kuka Afnan ta fara tana faWin "Mama wannan zigar su kawu ce, saboda basa son farin cikin mu".

"Afnan mu yi ha?uri komai lokaci ne, idan an yi, hakan ne don a ba?anta muna ai Allah baya zalunci, kuma duk wanda aka zalunta zai saka masa, mu yi ha?uri mu rungumi ?addara".

Maryam sai zage-zage take tana faWin "Wallahi ba zata yi ha?uri ba, duk shegiyar matar data gaya mata cuta sai ta gaya mata mutuwa, komai tshofanta sai ta rama".

Mama fita ta yi, a Wakin tana goge ?wallah ta na jin zuciyarta na mata zafi!


WASHE GARI

?arfe goma da rabi su Afnan suka gama shirin su saboda su isa da wuri su yi gyaran gurin da zasu zauna.

Ma?ota Mama ta shiga su yi sallama, tambayarta suke yi Lafiya kuwa zasu tashi haka kai tsaye Mama ta ce "Babu komai tsohon gidan su ne zasu koma" haka dai suka yi sallama cike da kewar juna, dan Maman Afnan akwai kirki.


Maryam ta fake idon su Afnan ta Wauki wayar Mama Waki ta shiga, lambar Haidar ta saka a wayar ta danna kira ringin biyu aka Wauka tare da yin sallama, bata amsa sallamar ba ta ce "Ya Haidar ina kwana" nan take Haidar ya gane Mai magana "Lafiya ?alau ?anwata ya kike? ya Auntynki?".

"Lafiya ?alau Alhamdulillah"

Haidar ya ce "Sai yau aka ga daman kirana" murmushi tayi ta ce "Kayi ha?uri muna son kiranka Allah bai nufa".

Ya ce "Ba komai na gode sosai ?anwata yanzu kuma sai yaushe?"

Maryam ta ce "Uhum ai zamu rin?a kiranka muna gaisawa in sha Allah".

Zai yi magana tayi saurin cewa "Ya Haidar na ce in ba damuwa kuma ba kada wani uzurin ka zo ka Kai mu unguwa".

Dariya Haidar ya yi ya ce "Ashe dai ba haka kawai aka kira ni ba, to kun shiryane na zo?"

Ta ce "Eh amma dai muna da kaya da yawa, napep Win ba zata Wauke mu da kayan ba".

Ya ce "To bari na nemo wani, sai mu zo mu biyu".

"Yawwa ya Haidar sai kunzo"

Kashe wayar tayi jin motsi, Afnan ce ta shigo tana faWin "Me ki ke yi a Waki ne? ki fito muje neman abin hawa" Maryam ta ce "Ai ba sai munje ba na kira ya Haidar".

Kallon ta Afnan tayi, ta ce "Wane Haidar kuma?" dan ita ta manta da zancen wani Haidar.

Maryam ta ce "Wanda muka karSi lambarsa mana."

Afnan bata ce komai ba ta bar Wakin, dan lamarin Maryam sai dai addu'a.


*****

Misalin 11:00Am jirgin su Abba ya sauka a Nigeria, rantsatin motoci ne suka zo Waukarsa a airport Win, Waukarsa suka yi, sai gida.

Hajiya Saratu na zaune ta ji parking Win motocin, cikin iyayi ta ?ara gyara Waurin Wan kwalinta ta zo bakin ?ofa ta na jiran isowarsa.

Sai dai yana fitowa Sangaren Hajiya Zainab ya nufa

Wani irin malulun ba?in ciki ne ya daki zuciyar Saratu ji tayi kamar za tayi bindiga saboda ba?in ciki, ?wafa ta yi ta bar jikin ?ofar Wakinta ta wuce cike da jin haushi, da takaicin abin da Alhaji ya yi mata, sai cika take tana batsewa.

Alhaji kai tsaye gurin uwar gidansa ya wuce Hajiya Zainab tana zaune ta cancaWa ado sai baza ?amshi take yi, yana shiga falon sai da ya lumshe idanuwansa, wani irin sihirtaccen ?amshi ne ya daki hancinsa, irin wannan ?amshi baya jin sa a ko ina sai gurin uwar gidansa, Hajiya Zainab mace ta gari.

Yana nan tsaye ya ji ta rungume shi tana faWin "Barka da zuwa kyakyawana, ina godiya ga Allah daya dawo min da kai lafiya."

Murmushi ya yi yana sumbatarta ya ce "Uwar gida ran gida, in babu ke babu gida, fatan na same ki lafiaya?".

Ita ma murmushi tayi ta ja hancinsa tana faWin "Lafiya ?alau Alhamdulillah Alhajina." tayi maganar tare da jan hannunsa ta nufi Wakinsa da shi.


*******

Babu Sata lokaci Haidar ya zo shida abokinsa, ko da suka zo har su Afnan sun fitar da kayan gaba Waya.

Kayan aka saka sannan suka kulle giWan haka suka bar unguwar cike da kewa suna jin ransu babu daWi,
Afnan sai wani shan ?amshi take dan kar Haidar yaga damarta.

Ko da suka isa gidan a ?ofar gida suka ga Baba yana sallamar yaran da ya nema su fitar masa da sharar Sangaren da zasu zauna, saboda ya ragewa su Mama aiki shiyasa ya riga su zuwa.

Sauke kayan aka yi ana shigar dasu ciki.

Baba ya ce wa Haidar "?an samari nawa ne kuWin ku?"

Haidar ya sunkuyar da kai ya ce "Baba ku bar shi kawai ba sai mun karSi kuWi ba."

Ya ce "A'a Wana baza'ayi haka ba ku karSi kuWinku nema fa kuka fito yi."

?in karSa Haidar ya yi

Cikin jin haushi Afnan ta ce "Wai kai wane irin mutum ne? ka karSi kuWin ka mana."

Murmushi Haidar ya yi ya shiga babur Winsa ya tada suka bar wajan.

Afnan ta kalle Maryam ta ce "Dama abin da ki ke nema kenan".

Cikin gidan suka shiga da sallama lnna Hajara ta amsa tana faWin "Ungulu ta dawo wa gidanta na tsamiya kenan".

Wani banzan kallo Maryam ta yi, mata sannan ta ce.


Amanar cool ce
'?
08163516796https://www.facebook.com/share/18qRMydDNb/

*Domin karfafa mana qiwwa ku yi following tare da liking shafinmu na Facebook >??

=ث? *RAMEN ?ARYA....*=ث?


? ? ? ?? Story & writing

? ? ? ? ? ? ? ? ?? By

Mrs Muttala (Amanar cool)



?? *YOUNG TALENT*
*WRITER'S ASSOCIATION*



Sadaukarwa ne ga Aysharcool



(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE


Free book
'?


Page 5&6


_______"Sannu aku mai bakin magana, ke ce ungulu ba uwata ba, ke dai wannan matar idan ba sa ido da munafurci kika yi ba, ba zaki ji daWi ba, a dai ji tsoron Allah a gyara hali".

Gwaggo kamar wadda aka jefo daga sama ta zo tana faWin "To jarababbiya, daga shigowarku har kin fara halin naki".

Cikin ?un?uni maryam ta ce "Ai kece jarababiyyar tsohuwa, ki na kusa da kushewa amma kin ?i ki dena masifa, kawai kin saka mun dawowa wannan gidan saboda mugunta".

Tsawa mama ta daka wa Maryam ta ce "Kar na sake jin kin yi magana a gurin nan"
?un?uni ta fara tana harare? Gwaggo ta ce "Ihu bayan hari kenan, ai duk wannan rashin tarbiyyar a wurinki suka gani suke koyi".

Maryam zata kuma yin magana Mama hana ta, ta ce su wuce. Wucewa suka yi suna jin Gwaggo na bambami Inna Hajara sai zigata take.

?angaren da za su zauna Wakuna biyu ne, Wakin Mama suka fara shigar mata da kayan ta, kafin suka shirya nasu Wakin.

********

____Wanka Abba ya yi ya shirya sannan ya ci abinci. A tsanake ya dubi zainab, bayan ya kammala cin abincin, ya ce "Madam"

Ta dube shi ta ce "Ya aka yi ne?"

"Ai gani na yi, ki na ta wani kyau da she?i, anya ba ajiya na yi a wurin nan ba?" Yayi maganar yana nuna cikinta.

Ta shafi cikin nata, tana murmushi ta ce "Eh mana, ka ajiye abinci da soyayyarka a ciki" murmushin shi ma yayi, ya ce "Ai shikenan idan? ya fito ai zamu gani" murmushi ta cigaba da yi tana satar kallonsa.

Sai da aka fara kiran sallah azahar sannan ya fito daga Sangaren Zainab, ko da ya isa bangaren Hajiya Saratu bai same ta a falo ba, kai tsaye Wakinta ya nufa. Kwance ya same ta, sai Sata rai take, dubanta ya yi ya ce "Hajiya lafiya dai na ganki a kwance, baki san na dawo ba".

Tashi zaune ta yi, tana Wan Sata fuska ta ce "Kaina ne yake yi mini ciwo, sannu da zuwa" amsawa ya yi tare da faWin "Kin sha magani?" Waga masa kai tayi tana mi?ewa tsaye, fita ya yi a Wakin, tabi bayan sa a Wakin sa tasame shi, zama tayi tana faWin "Na zata a falo zan same ka mu ci abinci, duk da na san dai a ?oshe ka ke, baka bu?atar wani abinci" duban ta ya yi?ya ce "Ina bu?ata mana, kema ai zan ci naki girkin, yanzu zan je masallaci bari na yi sallah sai na zo" ya faWa tare da barin Wakin ?wafa Saratu tayi ta ce "Zanyi maganin ku daga kai har ita".

******

Tun da su Afnan suka shige Sashensu basu fito ba, har aka yi sallahr la'asar sai a lokacin ne Baba ya shigo gidan, Wakin Gwaggo ya fara zuwa, bayan ya gaisheta ne, ta ce "?an ladi ina mai ?ara? gargaWinka akan Ka ja wa matarka da ?a'?anka kunne, bana son rashin kunya da tashin hankali, kowa ya tsaya a matsayin sa. Gaba Waya ta lalata yara, babu tarbiyya babu girmama na gaba. Ni da na san haka ne, babu yadda za ayi na bari ka je waje ka kama gida ku zauna".

Cikin damuwa ya ce "Gwaggo wani Abin ya faru ne?"

"?warai kuwa Wazu daga shigowar su sheWaniyar yarinyar nan ta fara rashin kunyar data saba, to ba zan lamunta ba"

Ya ce "To, ki yi ha?uri Gwaggo in sha Allah zan yi musu magana, hakan ba zata sake faruwa ba".

"Da dai yafi, dan ba zan Wauki iskanci a wannan karon ba, dan yana daga cikin dalilan da ya sanya na ce sai kun dawo gidan nan, wannan rashin tarbiyyar ta yaranka" ta yi maganar tana hura hanci.

Sallama ya yi mata yana jin ransa duk ba daWi, wani irin Lamari ne? daga dawowar su har Gwaggo ta fara ?orafi, har da kiran yaransa marasa tarbiyya.

Ko da ya isa a zaune ya samu su Afnan na tsintar shinkafa, ya zauna a kan tabarma dake shimfiWe a gurin, sannu da zuwa su suka yi ya masa, amsawa ya yi yana faWin "Afnan sarkin aiki, ba kya gajiya da aiki" murmushi tayi ta sunkuyar da kai
ya kuma cewa "Afnan ina fatan dai baki mance da maganar da na yi miki ba, akan zance fito da miji" .

Kasa amsa masa tayi, saboda bata san me zata ce masa ba, ta sunkuyar da kai, tana wasa da shinkafar data ke tsinta.

Ganin haka, ya ce "Afnan bana nufin takurawa rayuwar ki ne, ina son na aurar dake ne, kamar yanda ko wane uba yake burin auran da ?arsa. Ki yi ha?uri da yawan matsa miki da nake yi, hankalina ba zai taSa kwanciya ba, sai na ganku a Wakunan mazajenku".

Afnan ta jinjina kai a hankali, ko zancen auren ba ta so, idan Baba yana maganar nan, sai ta ga kamar ya gaji da ita ne.

Maryam kuwa dariya tayi ta ce "Wa ya ga Aunty Afnan a gidan miji, za a sha miskilanci".

Kallon ta Afnan tayi bata ce komai ba, Mama ta ce "Ke za'a cewa haka ba ita ba, ke kuma mijinki sai ya yi ha?uri kafin ya iya zama da halinki".

Murmushi Baba ya yi ya kalli Maryam data yi kicin-kicin da fuska ya ce "Maryama sarkin rigima kema Allah ya nuna mini na aurar daku gaba Waya".

*****


Hausawa suka ce, sabo turken wawa, sai dai ga Aliyu Haidar, shi bai yi sabon ba, amma kewa ta addabe shi.
Yanayin yadda ?wanjinsa yake motsawa, a duk yayin da ya cuWa kayan da ke gabansa, ya ?ara tabattar da ?arfinsa.
Sai dai kamar yana jin daWin wankin da yake yi, domin kuwa lokaci zuwa lokaci ya kan saki murmushi.
Tun da suka rabu, fuskarta ba ta daina yi masa gizo ba, mussaman yadda ta ha?i?ance, a kan lallai sai ya karSi kuWinsa, alhalin sam ba ta iya fushin ba ma.
Sai kuma Maryam, yanayin halayyarta ya burge shi, ba ta da Soye-Soye ko kaWan.
Gudun kar wankin hula ya kai shu dare, ya sanya yayi niyyar zuwa unguwar su Afnan, da zarar ya kammala abin da yake yi.

******

Bayan Abba ya dawo daga masallaci, a falon Hajiya Saratu, suka zauna suna cin abinci. Bayan sun kammala ne, Hudah ta shigo yi masa sannu da, zuwa.
Cikin jin daWin ganinta Abba ya ce "Hudallahi, ki na lafiya ina yayanki ne? bai san zan dawo bane? tun da na dawo ban ganshi ba, na yi missing Winku sosai fa, anya kun yi missing Win Abba?"
Huda ta yi murmushi ta ce "Abba ka san Yaya Mudan? yawo ne dashi, baya zama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login