Showing 18001 words to 21000 words out of 52998 words

Chapter 7 - RAMIN ƘARYA HAUSA NOVEL

24 Oct 2025

97

Sanusi zai yi magana kenan ya ji ana kiran wayarsa, duba wa ya yi yaga ?anensa ne Umar, Wauka ya yi bayan sun gaisa ya mi?awa Gwaggo wayar, karSa ta yi ta ce "Yau ka ga damar kirana, tun yaushe rabon da ka yi magana da ni, amma na san ita waccan shashashar matar taka ka na kiranta, saboda ka na gudun zuciyarta, na rasa me yake damunku kaida Wan ladi, gaba Waya kun susuce akan mata sai yanda suka yi daku".


"A'a Gwaggo wallahi ba haka bane, ina yawan kiran su Yaya akan su haWa ni da ke, lokacin kuma basa gida, ke kuma gashi ba wace dake ba, an ce a siya miki waya kin ce a'a, ba za ki ri?eta ba ta saka ki yin ?arya ba, amma ki yi ha?uri in sha Allah za a ki ya ye" .


"Na ji ai dama haka ka ke kullum, tukunna ma kai ka bawa matarka damar tafiya tayi zamanta? daga zuwa biki".


"Gwaggo ba zamanta tayi ba, ba ta da lafiya ne, shiya hana mata dawowa, amma in sha Allah yau za ta dawo".


"Ai dama kun iya kare matanku kamar me, haka dai Gwaggo tayi ta yi musu mita, idan ta ce wannan, ta wancan, sai da ta yi mai isarta sannan suka bar gurin.


*******


Bayan Hudah ta gama karyawa, sallama tayi wa Mami ta fita, kai tsaye gidansu Nusee ta wuce, a Waki ta sameta, zama tayi ta na faWin "Wash! Allahna". Nusee ta ce "Sis lafiya na ganki haka a birkice? ni duk kin Waga mini hankali, tunda na ji kin ce ba lafiya. What is problem?".


"Sis ki bari kawai ina cikin wani hali ne".

"Me yake damun ki?" wane irin hali ne ki ke ciki haka, Sis kin gan ki kuwa hadda rama na ga kin yi fa".


"Ai zaki iya ganin abin da yafi rama a tattare da ni, Sis wai kin san cewar ya Mudan aure za a yi masa, kuma abin ba?in cikin da takaicin a rasa wadda za a haWa shi da ita sai wannan yarinyar ?ar rainin hankalin Sharifa ?ar gidan Alhaji Munir, abokin Abbanmu".


Da ?arfi Nusee ta wuntsilo daga saman gado ta ce "What wa ki ka ce?. Do you mind repeating that".

Hudah ta ce "Wai Sharifa".


*Sai Monday kuma in Allah ya kai muna rai da lafiya, a yi week lafiya*


Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA....*=ث?



? ? ? ? ? ?? Story & writing

? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?? By

? ? Mrs Muttala (Amanar cool)




? ? ?? *YOUNG TALENT*
*WRITER'S ASSOCIATION*




Sadaukarwa ne ga Aysharcool




Free book
'?



Page 17&18




__________ Nusee ta ce "Ki na nufin wannan yarinyar mai wula?anta mutane, lallai akwai gwarama kenan, ai ni wannan yarinyar kwata-kwata ba ta burge ni ko kaWan, tun lokacin? da muka taSa samun saSani da ita, wani zuwa da na yi gidanku muka haWu da ita, ta zo gurin wannan kishiyar Mami Win, ki na yi mata magana ta na wani share ki har nake ce mata me ta taka da ake yi mata magana ta na share mutane, buWar bakinta sai cewa tayi.? Ai ba kowace jaka take kulawa ba, sannan kuma bata hulWa da marasa kamun kai. Ai wallahi ranar ba dan Mami ta hana ni ba so na yi in zazzaga mata rashin mutunci".

Hudah ta ce "Hmm ?awata wallahi ba wata macen da ta isa ta auri ya Mudan matu?ar ina raye, ko da ba Sharifa ba ce, Sis ya Mudan ya bani mamaki, ban yi zaton zai iya amincewa da auren wata macen ba, bayan ina raye, wallahi da ace babu abin da ya wakana tsakanina da? shi, to tabbas zan iya ha?ura da so shi, na jira har Allah ya fito mini da wani mijin, but ya Sata mini rayuwa, shine namiji da ya fara sanina a matsayin ?a mace, ya mayar da ni tamkar matarsa, ba tare da ya yi la'akarin cewa ni ?anwarsa ce? ba. Ya dasa mini soyayyarsa a zuciyarta, tare da yi mini al?awarin zai aure ni. Tun ba yanzu ba nake yi masa magana akan mu nunawa iyayenmu cewar mu na son junanmu, wannan nu?u-nu?un da muke ba in da zai kai mu. Na tabbatar da Abba ya san cewar mu na son juna tabbas ba zai Sullo da wannan zancen ba, amma ina ya ya ?i bari mu sanar da su, ko alamar hakan bai bari sun gani ba, wallahi sai da wannan maganar ta aurensa da Sharifa ta ta so, na gane cewar dama can ba aurena yake son yi ba, kawai ya na yaudarata ne domin cimma burinsa. Na yi wauta da na biye wa namiji har muke aikata irin wannan abin. I will rather not. Amma wallahi zan nuna masa gaba da gabanta aljani ya taka wuta, ba zai more ni a banza ba".

Nusee ta ce "Sorry dear,? i am not happy about this, kuma dole ne na taya ki ya?in neman ?ancinki, sannan ke ma da laifinki, kuma dama ki ka ba shi, tun da dai ba ta ?arfin tsiya ya yi miki, ni akwai Wan iskan namijin da ya isa ya yi mini haka kuma ya zauna lafiya, ai wallahi ya yi kaWan".

"Sis ni ma fa ba barin sa na yi ba, ke ma kin san ba zan ?yale shi, ba sai na yi duk yanda zan yi na ga an fasa auren nan, ko da kuwa asirinmu zai tonu ne, daga ni har shi in yasonduk abin da za??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i tafasa ya daWe bai ?one ba".

"Yawwa ?awata haka nake son ji, idan ta kama ma ki gaya wa Mami duk normal ne, ai ranar biyan bu?ata rai ba a bakin komai yake ba bari na tashi na shirya sai mu wuce school Win".

Da "To" Hudah ta amsa mata sannan ta Wan kwanta, kafin ta gama shirin.

******

Abba da Ammi na zaune, Abba tsokanarta ya ke yi wai ?an uku za ta haifo, Mami tayi sallama, tare da shigowa, amsa mata Ammi tayi, cikin sakin fuska. Duk da ta na mamakin me ya kawo Mami sashenta, rabon da ta zo gurinta har ta manta, zama tayi tana murmushin munafunci.

Abba ya ce "Hajiya yau kuma ziyarar ce ta motsa".

Dariya tayi ta ce "Na zo duba jikin ?ar uwata ne, kuma na taya ta murna, Allah ya raba lafiya ?ar uwa" tayi maganar tare da kallon Ammi. Mami ta ?ware wurin iya kissa da kisisina, duk ?iyayyar da ta ke wa Ammi ba ta taSa nunawa a gaban Abba, sai dai wani lokacin takan nunawa Ammi Win.

Ammi ma murmushi tayi ta ce "Ina godiya sosai Allah ya bar zumunci".

Abba ya dubi Mami ya ce "Wai ya zancen Mudan, ya je gurin Sharifar ne?? ban ji Alhaji Munir ya yi mini zancen ba".

"Eh ya je, sai dai ni ma ban san yadda suka yi ba, kasan Mudan da shiririta, har yanzu ba mu zauna da shi ba, sai dai in kiran sa zaka yi ka tambaye shi".? "Eh to zan tambaye shi Win, saboda ba mu son auren nan ya Wauki dogon lokaci".

Sun Wan taSa hira,? sannan Mami tayi musu sallam ta fita,?? tana fita Turai na kiranta, sai da ta ?arasa sashenta sannan ta Waga kiran, bayan ta Wauka ne, Turai ta ce "?awata ta kaina, amarya a gidan alhaji Musa, mun yi magana da malamin, na yi masa bayanin komai, ya ce mini nan zuwa gobe komai zai kammala, sai dai ita kishiyar taki ce za ta ba da matsala amma kar a damu, zai tura aljanin da zai shiga jikin Alhaji? duk lokacin da ya je kusantarta, shi kuma sai ya yi amfani da wannan damar ya zubar da cikin, sannan kuma ya lalata mahaifar, sannan aljanin zai ci gaba da zama a jikin alhaji, domin ya saka rashin jituwa a tsakaninsu".

Mami ta ce "Kai gaskiya ?awata kin gamamini komai, wannan abin ya yi, ina godiya sosai, kuWin da na tura miki sun isa ne?".

"Ai ba godiya tsakaninmu yi wa kai ne, kuWin sun isa, yanzu kawai mu zuba ido mu gani".

"Tom ya yi ?awata duk da haka dai na gode sosai, yawwa dama ina son gaya miki Mudan fa ya kusa zama babban mutum".

Turai ta ce "Babban mutum kamar ya? bangane ba? aiko yanzu shi babban mutum ne".

"Ke wannan girman na da banne, aure za a yi masa, shi da Sharifa ?ar gidan alhaji Munir abokin Abbansu".

zaro ido Turai tayi ta ce "Wai ki na nufin Mudan ne zai yi aure? kai ma sha Allah, ki ce zamu yi biki na ke ce raini, to amma suna son junansu kuwa?".

"Haba ?awata ina ruwanmu da suna son juna ko ba sa so mu dai burinmu a yi auren can su ?arata"? Turai ta ce "Haka ne kuma to Allah yasa da mu za ayi".? "Ameen ?awata na gode sosai ". sallama suka yi.

Suna aje wayar Turai tayi shewa ta ce "Aure Mudan da sharifa, ina ba zai yi yu ba, ai Mudan ba shi da wata mata fa ce Hasina, ?ata kuma matu?ar ina numfashi ita zai aura, na ga ta in da zai aure wata macen".

********

Haidar ne ya yi shirinsa tsaf cikin farin yadi, ya yi kyau sosai so yake ya je unguwar su Afnan, duk da Umma ta hane shi amma ba yadda ya iya, so yake ya je ko Allah zai sa ya ganta, ko gaisawa ne su yi, kafin su wuce garin da zai raka uban gidansa.

Lokacin da ya ?araso unguwar, a ?ofar gidansu ya tsaya, ya Wakko wayarsa ya fara kiran Maryam, Mama na zaune ta ji ana kiran wayarta, Wauka tayi, kafin tayi sallama Haidar ya ce "Assalamu alaikum, ?anwata"? Amsa masa tayi ta ce "Wa ke magana?" .

Shiru Haidar ya yi, Mama ta kuma cewa "Waye?"?? "Haidar ne"? "Haidar wane Haidar Win?" wuff Maryam ta fito daga Wakinsu ta na kwance ta ji Mama na ambatar sunan Haidar, ta ce "Laaa Mama ya Haidar ne mai napep Win ya Wakko mana kayanmu lokacin da zamu dawo nan gidan" tayi maganar ta na karSar wayar a hannun Mama.

Sakin baki tayi ta na kallon Maryam, tana mamakin me ya haWa su da lambarsa.

Maryam Wakinsu ta shiga ta na faWin "Hello ya Haidar ina kwana"?? "Lafiya ?alau Alhamdilillah ?anwata, ya ki ke? ya gida? ya auntynki kuma? fatan duk ku na nan lafiya?".

"Lafiya ?alau, ya Haidar kwana biyu ka Suya"? "Eh ayyuka ne suka yi mini yawa, yanzu haka ina ?ofar gidanku, na zo mu yi sallama, za mu yi tafiya ni da mai gidana ne shine na ce bari na zo mu gaisa"? "To bari mu fito".

Duban Afnan tayi dake kwance, ta rufe idanuwanta, tun da ta ji Maryam na waya da Haidar, ta ce "Aunty tashi mu je waje ga ya Haidar can ya zo".?

"Ki je dai ke, ni ba in da za ni".

"Haba aunty kin ji matsalar ki, yanzu ke dan Allah ba ma ki yi farin ciki da zuwansa ba, ai ko dan wula?ancin da ake son yi miki kya kula shi, dan Allah ki tashi mu je, ko na gaya wa Mama".

Sanin halin Maryam na shegen naci, sannan kuma ta san tsaf za ta gawa Mama, yasa Afnan mi?ewa ta ce "Ba na son takura wallahi, ni dai mu je".

Fita suka yi a Wakin, suka cewa Mama za su je ?ofar gida su dawo. Haidar na tsaye ya ?urawa ?ofar gidan ido, ya na duban ta ina zai ga fitowarta, kamar daga sama ya ga Afnan ta fito, Maryam na biye da ita, wani irin farin ciki Haidar ya tsinci kansa a ciki, wanda har ya kasa Soyuwa a fuskarsa, ?arasowa suka yi, tare da yi masa sallama, fuskarsa Wauke da fara'a ya amsa yana kallon Afnan da ta Sata fuska, ta na kawar da kai, Maryam ta ce

"Ya Haidar mun barka tsaye ka na jira, ka yi ha?uri ka san halin auntyn tawa, hukumace sai da rarrashi".? Ta yi maganar tana dariya.

"A'a ba komai ?anwata, kar ki damu, ai ku manya ne dole a jira ku". Dubansa ya kai ga Afnan ya ce

"Ranki ya daWe an tashi lafiya? ya ki ke? ya ?arfin jikin na ki? ina fatan da sau?i?".

"Alhamdulillah" shine abin da ta ce, a ta?aice, ta yi shiru ba ta kuma magana ba, haushine ya kama Maryam, ganin irin amsawar da tayi masa, "Haba aunty, wannan abin da ki ke yi ba kyau wallahi, ta ya bawan Allah ya zo gaisheki da jiki kuma ki na yi masa haka, gaskiya wannan bai dace ba".

Galala Afnan tayi ta na kallon Maryam, ta na kuma mamakin yanzu ita Maryam a irin halinta har ta san abin da ya da ce, da wanda bai da ce ba.? "Maryam wai ina wasa dake ne? ni sa'arki ce? wai me yasa ki ka raina ni ne?".

"Ba wani raini gaskiya na faWa, wallahi wannan abin bai da ce ba". Haidar murmushi ya yi ya ce "Haba ?anwarmu, a yi ha?uri ai ta amsa, ni ban ga laifin hakan ba".

"Au haka ma zaka ce' wato shigar mata ma ka yi, lallai ya Haidar ka na ruwa tsundum, Allah ya fitar da kai, ni dai bari na wuce dan na san ba gurina aka zo ba, ka ga tafiyata" daga haka tayi shigewarta gida.

Dariya ya yi, sannan ya mayar da dubansa ga Afnan da ta juya masa baya, ya ce "Gimbiya wannan sarautar ta isa mana, a taimaka mini a juyo haka nan, ina so zamu yi magana mai muhimmanci".

"Ka faWi duk abin da za ka faWa, na ga ai kunne ke ji, ba idanu ba"

"Haka ne amma yakamata a ce mun fuskanci juna Afnan, saboda muhimmancin maganar da zan yi miki".

Afnan jin ya kira sunanta yasa ta ji wani iri, ji tayi zuciyarta ta buga da ?arfi! a hankali ta juyo, sai dai ba shi take kallo ba, duk sai ta ji ta a takure, gashi ko inuwarsa ba ta son kalla, ita mamaki ma take me ye ya tsayar da ita, me yasa ba ta bi bayan Maryam ba.

Muryar Haidar ta ji ya na faWin "Afnan. Dukkanin abin da zaki ji daga gareni, babu ?arya ko niyyar yaudara a cikinsa, yanzu ko kuma a gaba. Gundarin abin da magana ta zata ?unsa zuwa gareki kalmar so ce. Amma fa idan za ayi mata gunduwa gunduwa ba na tsammanin zan iya warware miki zare da abawa. Ranki ya daWe kamar da wasa tarbiyyarki ta saka mini so da ?aunarki cikin ?an?anin lokaci a cikin zuciyata, idan da zan samu yanda nake so, dake na ke fatan shiga babban dandalin masoya na wannan duniyar, da kuma wanda ke a ?iyama. Ko da ban samu yanda nake so ba, ina fatan zaki rubuta sunana a maWaukakiyar fadar zuciyarki, a matsayin masoyi mai daraja, ko da ba ni ne farkon shiga a ciki ba. Ki tausaya mini, ki tallafe ni, ki amince da ni, a cikin zuciyarki Afnan. Son ki ya gama shiga jikina, ka da ki bar ni shawagi tamkar tsuntsu a sararin samaniya".


Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA....*=ث?




Story & writing

By

Mrs Muttala (Amanar cool)





*YOUNG TALENT WRITER'S ASSOCIATION*




Sadaukarwa ne ga Aysharcool




Free book
'?




Page 19&20





_________Afnan wani irin yanayi ta tsinci kanta a ciki, ta ji duniya tana jujjuya mata, ga wani jiri da yake Wibarta, yana kai ta can wata uwa duniyar da bata taSa tunanin zuwa ba, tunda take ba ta taSa tsayawa ta saurari saurayi ba, balle har ta tsaya jin irin wannan soki burutsun da wannan Win yake faWa mata, riskar kanta tayi da jin wani ba?on al amari da ta kasa tantance me take ji a zuciyarta ta, a hankali ta Wago da fuskarta ta dube shi, ido huWu suka yi da juna, da sauri ta sunkuyar da kanta, cikin rawar murya ta ce "Na gaji da tsayuwa ina so zan shiga gida".


Murmushi yayi, tare da shafa gemunsa, ganin yadda ta diririce baki Waya lokaci guda. Ya numfasa ya ce "Ina fatan ba maganganun nawa ne, suka sanya miki gajiyar ba?" Ta girgiza kai ba tare da ta Wago ba.


Ya jinjina kai ya ce "To ya yi ba damuwa, ba zan takura miki ba, haka kuma ba zance dole sai kin ba ni amsa a yanzu ba, na baki dama ki je ki yi shawara, amma dan Allah ka da a yanke hukuncin da zuciyata ba zata iya Wauka ba, a taimaki bawan Allah wanda zuciyarsa tayi rauni akan abin da yake so da muradin kasancewa tare da shi".

?afafuwanta ne su ka hau rawa, hakan ya tilasta mata juyawa ba tare da ta ce masa ?ala ba, ta na ?o?arin shiga gidan domin kaucewa abin kunya ta faWi a gabansa. Haidar ya kuma cewa "Afnan" cak ta tsaya sai dai ba ta juyo ba. Zuciyarta ta tsananta bugawa, wani irin gumi ya din ga keto mata, saboda yadda ?wa?walwarta ta karSi amon muryarsa da ya yi amfani da ita gurin kiran sunanta.

Ya ce "Babu mamaki yadda idanuwanki ke satar zuciya, haka murmushinki yake ?ara saurin buguwar zuciyata. Ki sani ke ce gaskiyar rayuwa, ke ce asalin burin da na ke fata, ke ce gaskiyar mafarkin da nake kowane dare, ke ce farko da ?arshen kowane tunani da nake yi. Afnan wata?ila ba zan samu damar sanar dake a kullum ba, amma ki sani kalmomin da ke bakina ba za su iya gabatar da shau?in da nake ji a kanki ba".

Da sauri ta ?arasa shiga ciki, jin zuciyarta na bugu da ?arfi!

Murmushi Haidar ya yi, ya na girgiza kansa, wani irin sanyi ne ya ji yana ratsa zuciyarsa yana bin ko wane sassa na jikinsa, a hankali ya juya ya bar ?ofar gidan, yana jin sa cikin tsananin farin cikin yau ya samu damar ganin Afnan, kuma ya amaryar mata da abin da ke cikin zuciyarsa a game da ita, babur Winsa ya shiga ya na ?o?arin tadawa Ummansa ce ta faWo masa a rai, maganganun da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login