Showing 48001 words to 51000 words out of 52998 words

Chapter 17 - RAMIN ƘARYA HAUSA NOVEL

24 Oct 2025

94

amma cikin hukuncin Ubangiji ka same shi a Sagas shi ka ke wula?antawa? Haidar ina nusar da kai amma ka ?i ka fahimta, yanzu mahaifar tawa ce ba za ka iya zuwa ba? To shikenan tunda baka so zan yi magana da shi, na bashi ha?uri, sai ka sauwwa?ewa Wiyar mutane, ta kama gabanta, kai kuma ka tsaya jiran wadda ka ke son Win, tashi ka ba ni guri tun raina bai ?ara Saci ba".


Haidar zai kuma yin magana, Umma ta hana shi, tare da umartar ya bar mata Wakin ta.

Tashi ya yi ya fita jiki ba ?wari, ya na jin sai dai Umma tayi ha?uri ba zai taSa zuwa gurin wata kucakar mace ba a ?auye, to ya je me zai yi mata? Idan suka gaji da jiransa dole su nemi mafita.


Da kallo Umma ta bishi, ta na mamakin ?arfi hali irin na Haidar, tunda take bai taSa nuna mata kafiya ba, sai wannan karon. A fili ta ce "Lallai barewa ba ta yi gudu Wanta ya yi rarrafe ba, ba za ta manta kafiya irin ta mahaifinshi ba, Allah Sarki rayuwa kenan".


Umma ba tayi aune ba sai jin zubar hawaye tayi a kan fuskarta, a duk lokacin da zata tuna Baban Haidar takan shiga damuwa marar misaltuwa. Goge hayen tayi, ta na tunanin irin hukuncin da zata Wauka akan Haidar, dan ta san ba ?aramin ya?i za ta yi dashi ba, a yadda ta ga ya dage Win nan, yanzu ya za ta yi da Yaya? Me zata ce masa? Haka dai ta shiga zancen zuci daga ?arshe ta yanke shawarar abin da zata yi.


Da sanyi safiyar nan, wasu hadda abin kari basu Wora ba, Gwaggo ta saka Sanusi ya kira mata Yaya Bala, Baba na zaune shi dai bai ce ?ala ba.


Mai gari na zaune Maryam na kusa da shi, ta ba shan koko da ?osai, ya ji ana kiran wayarsa, dubawa ya yi ya ga Sanusi ne, Waga wayar ya yi tare da yin sallama.


Amsawa Gwaggo tayi tare da faWin "Antashi lafiya Yaya ya mutan gidan?"


"Alhamdulillah Halima fatan kuna lafiya kuma?" .


Ta ce "Lafiya lau Alhamdulillah Yaya".

"To ma sha Allah, jiya dai A'isha a Wakinta ta kwana".

Gwaggo ta ce "Ma sha Allah, ashe ma abin bai daWe ba, sannu da ?o?ari Yaya Allah ya bar zumunci, ya ?ara girma" . Ya amsa da Amin

Sannan ta ce "To ita wannan mara kunyar me take nufi? Ko ba za ta dawo ba ne? Can zata zauna a gidan mutane ta ri?a yi musu rashin kunyar da ta saba yi, ko kuma ta kashe mata auren ma gaba Waya, idan kuma can Win take muradin zama ita ma sai a nemamata mijin a can".

Mai gari ya ce "Halima wai yaushe zaki daina wannan masifar ne? Shin babu inda zata zauna ne sai gidan A'isha? Da ki ke ta ha?ilon zata kashe mata aure, ba na son irin wannan halin naki, ki rabu da ita duk lokacin da tayi ra'ayin komawa gida, sai ta tafi, yarinya mai hankali ki na kiranta da mara kunya".

"Allah ya baka ha?uri Yaya, ina godiya sosai a gaishe mini da mutan gidan".

Ya ce "To zasu ji" daga haka Gwaggo ta kashe kiran, ta ci gaba da masifa, ba gaira babu dalili.


Mai gari ko dariya ya yi ya ce "Halima Allah ya kyauta". Maryam dai bata ce komai ba


Bayan hantsi ya fara fitowa Maryam ta ce gidan Afnan zata je, aka saka yaro ya rakata.


Afnan na zaune bayan ta gama karyawa, ta nemi guri Waya ta zauna, ta zuba uban tagumi, sallamar Maryam ta ji. Cikin farin ciki ta nufi Maryam ta rungumeta.



Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA....* =ث?




_WRITING BY AMANAR COOL_
'?




*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*




Page 47&48



__________Rungume juna suka yi suna murna kamar sun yi kwanaki basu ga juna ba, jan hannun Maryam tayi suka shiga ciki, Maryam sai rarraba ido take yi a Wakin kamar mai neman wani abu.

Cikin sanyin murya Afnan ta ce "Shi ne jiya ki ka tafi aka bar ni ni ka Wai kamar mayya".

Maryam ta ce "Aunty kema kin san ba zai yi yu na zauna ba, idan na zauna shi mijin na ki ya kwana ina?".

"Wane miji kuma? Ni babu mijin da na gani, ni ka Wai na kwana a Wakin nan".

"Kamar ya? Ban gane ke ka Wai ki ka kwana ba?"Maryam tayi tambayar da mamaki.

Afnan ta ce "Wai baya garin nan, jiya ne zai dawo motarsu ta samu matsala a hanya, shi ne bai samu ya ?araso ba".

Maryam ta ce "Ayya ashe da na sani na tsaya Win, yanzu Aunty ke ka Wai ki ka kwana kenan? To ina wannan tsoron naki? Ya ki ka yi da shi?". Maryam ta ?arasa maganar tana dariya.

"To ya na iya Maryam, addu'a na ri?a yi har bacci ya Wauke ni".

"Wai sannu da ?o?ari Aunty, ai ban yi tunanin za ki iya kwana ke Waya ba, sai gashi kin yi, dama komai kaga mutum ya ce bai iya wa, bai cimmasa ba ne. Ashe ko da na so na koma gida yau saboda nayi kewar Mama, dole na ha?ura sai zuwa gobe, dan fa sai na ga wanene aka aura miki, ai baki sani ba, Wazu masifafiyar tsohuwar nan kiran mai gari tayi wai na dawo gida hakan nan, idan kuma ba haka ba, ni ma sai a yi mini auren a nan, sai da ya taka mata burki sannan ta yi shiru, jarababbiya kawai".


Afnan ta ce "Maryam wai ki na nufin tafiya zaki yi ki bar ni?" Tayi maganar kamar zata yi kuka.

"Aunty to ya ki ke so nayi? Ke ma kin san dole ne na koma gida, munbar Mama ita ka Wai, kuma na san yanzu haka tana cikin damuwar rashin jin mu, sannan ga wannan tsohuwar ta fara mita, na san ?arshe a kan Mama abin zai ?are, ha?uri za ki yi Aunty in sha Allah gobe zan koma gida, sai dai bayan kwana biyu zan sake dawowa na duba ki".

Shiru Afnan tayi tana matsar ?walla ta san gaskiya Maryam ta faWa, ita ma tana son sanin halin da Mama ke ciki.

"Dan Allah Aunty ki yi ha?uri ki dai na kukan nan, in sha Allah komai yai tsanani maganin shi Allah" ha?uri ta shiga bawa Afnan da rarrashinta. Har ta samu ta saki jikinta suka ci gaba da hira.


********

Mami tun jiya da Mudan ya faWa mata wannan maganar ta kasa samun nutsuwa, ta rasa ma me za ta yi, wane mataki za ta Wauka, Shin wai ma ko Turai ta san da wannan maganar? To amma idan ta sani ai ba za ta yi mata shiru ba. ?aukar waya tayi ta kira Turai sai da ta kusa katsewa sannan ta Waga, bayan sun gaisa ne Mami ta ce "Turai idan kin samu lokaci zuwa anjima ki zo ina son ganinki, idan Hasina na nan ku zo tare".


Turai ta ce "To ?awata zan shigo Win, amma lafiya na ji muryarki wani iri?".

"Babu komai kawai dai sai kin shigo" daga haka Mami ta katse kiran.

Dariya Turai tayi jin Mami ta kashe wayar ta ce "Lallai ashe akwai chakwakiyya. Saratu za ki gane shayi ruwa ne, da alama Mudan ya isar da sa?on zuciyarsa gareki, aikuwa za ki sha ruwan mamaki, dan ki na ji ki na gani ke da Wanki sai dai kallo, matu?ar ba goyon bayan abin da yake so za ki yi ba".

Dariya suka kuma yi ita da Hasina.

Sannan Hasina ta ce "Momy wai na ji ta ce a zo dani, aikuwa zan yi wanka na Waukar hankali, sai na yi adon da zai gigita Mudan a gabanta".

"?warai kuwa ?ata ki yi, abinki lokacin ki ne yarinya".


********


Haidar kuwa kiran abokinsa Faruk ya yi ya ce ya zo gida yana son ganinsa, babu Sata lokaci ya zo, har Wakin Umma ya je ya gaisheta, sannan ya nufi Wakin Haidar Win. Umma ta so gayawa Faruk abin da ke faruwa, amma sai tayi shiru ta ?yale sa, ta san zai sanar da shi.

Faruk na shiga a zaune ya tarar da Haidar

Zama ya yi ya dubi Haidar da kyau ganin ya Wan rame

Faruk ya ce "Haidar me yake damunka ne na ganka haka hadda wata rama kayi?".

"Faruk ina cikin damuwa da tashin".

"Subhanallah abokina wace irin damuwace haka?".

"Faruk babban tashin hankali a yanzu na rashin Afnan dana yi, Allah ya gani ina son yarinyar nan, ban taSa tsintar kaina a tarkon so ba sai akan, ita ce mace ta farko da na fara so a rayuwata da sunan soyayya".

Faruk ya ce "To me yasa me ta da ka ce kayi rashinta?".

"Aure Faruk Aure Afnan tayi, ashe tana da saurayi ban sani ba, nake ta wahalar da kaina akanta, ashe shi ne dalilin da yasa ta kasa bawa soyayya ta muhimmanci take mini wasa da hankali. Faruk tun farko da nazo mata da maganar aure me yasa bata sanar da ni gaskiya ba? Sai zuwa nayi gidan su aka ce mini wai an Waura mata aure, a gaban idona aka sakata a mota wai za a kai ta gidan wani ba ni ba. Wannan abin ya tsaya mini a rai. Ina cikin wannan damuwar kwatsam Umma ta zo mini da wani zancen daya ?ara Waga mini hankali".


"Wane zance kuma?" Faruk ya yi tambayar

"Faruk wai an Waura mini aure da wata, kuma abin takaicin ma a ?auye, wai ni aka yi wa aure ba tare da sanina ba".


"What! aure fa ka ce? A ?auye kuma lallai Haidar kana cikin wani yanayi. Da farko dai ina mai baka ha?urin rashin masoyiyarka da ka yi, ka yi ha?uri Haidar dama can ba rabonka ba ce, wani bai auren matar wani. Ka cire ta a rayuwarka gaba Waya, saboda kaga yanzu ita Win matar wani ce, bai kamata ka ri?a tunanin matar aure ba, ko kuma ka ri?a nanata cewar kana sonta, hakan kuskure ne, kuma ya saSawa addini. Yanzu abin da ke gaban ka shi ne wannan auren da aka ?a?aba maka ya za kayi da shi? Ina amaryar take?".

"Ba zan iya cire son Afnan farat Waya a zuciyata ba, kai hasalima wallahi kullum kamar ?ara mini soyayyar ta ake yi a zuciyata, ka taya ni da addu'a kawai".

Faruk ya ce "To Allah ya sauwwa?e ya kawo maka sasauci a zuciyarka, yanzu dai ka ba ni amsar tambayata ina amaryar da aka aura maka take? Wai ma shin ya aka yi aka aura maka mata a can Win? Waye ya yi maka wannan Wanyen aikin Haidar?".

"Ka bari kawai wani Yayan Umma ne, haka kawai ya je ya nemamin mata ya Waura mini aure da ita, babu sani na, ita kanta Ummar biyayya ce tayi masa ba da saninta ya yi ba, sai bayan komai ya kammala yake sanar da ita. Yanzu haka ya dage akan lallai sai na je ?auye a can gidansa wai amaryar na can".

Dariya ce ta kusa suSucewa Faruk jin furucin Haidar na ?arshe, amma sai ya dake ya ce "Ikon Allah wannan wane irin aure ne? Sai kace wasan yara, ai yanzu an dai na irin wannan auren, maganar gaskiya ba a kyauta maka ba. To yanzu dai shiryawa za ka yi kaje can gurin amaryar ko? A can zaku zauna kenan?" Faruk ya ?arasa maganar kamar ya fashe da dariya.

Takaici ne yasa Haidar yi masa shiru, dan ya fahimci hadda tsokana a cikin maganar tasa.

"Haidar magana nake kayi mini banza".

"Kabari har kagama tsokana ta sai na baka amsa" Haidar ya faWa ya na ?ara Waure fauska.

"Allah ya baka ha?uri abokina, dan Allah ka amsa mini zaka je ?auyen ne?".

"Wallahi Faruk ba in da zan je, sai dai su san yadda zasu yi da ita, da aka Waura auren mai yasa ba a kawo ta nan Win ba, ni yanzu taimako Waya nake so ka yi mini".

"Wane irin taimako?"


"Faruk Umma ta ce lallai yau sai dai na shiya na je, kuma wallahi ba zan je ba, ni an cuce ni, ban taSa saSawa umarnin Umma ba sai a wannan karon, Faruk so nake yi ka je ka samu Umma ka ce mata ba ni da lafiya, na yi maka bayanin komai, tayi ha?uri in sha Allah yau zan je Win, amma ta bari yanzu zamu je gurin wani malami mu yi masa bayanin matsalar dake damuna idan muka dawo sai na shiya na tafi Win. Dan Allah Faruk kaje ka ce mata haka, saboda ta hanani fita, wai in dai ba zan bi umarnin ta ba, to ba zan sake fita ba nima, kuma sarai na gane nufinta dan kar inje gurin yarinyar da take tunanin ita ce nake ta damuwa akan ta".


Shiru Faruk ya yi kafin ya ce "Amma Haidar me ye fa'idar yin hakan?".

"Yawwa Faruk so nake idan ta amince na fita a gidan nan sai nayi sati ban dawo ba, idan mun fita ba da jimawa ba, sai ka kirata ka ce mata ai malamin da muka je gurinsa, baya nan amma an turamu gurin wani malamin sai dai ba nan garin ba ne, gashi nan mun kama hanya zuwa yamma zamu dawo, ka ga daga nan sai muce mata ai ya ce sai mun Wan kwana biyu dai-dai ya gama haWa maganin, daga nan sai mu ri?a yi mata dubaru".


"To amma Haidar kana ganin zata yarda?".

"Eh in sha Allah zata yarda ni dai yanzu ka taimaka mini ka je ka same ta Win".

"To shikenan Allah yasa ta amince, to amma kai yanzu ina zaka je idan ta yarda Win?"

"Ba in da zanje Wakin ka zan tare nayi zamana wallahi".

Tashi Faruk ya yi ya fita a Wakin, da sallama ya shiga Wakin Umma ta amsa masa ya zauna ya ce "Umma da ma yanzu Haidar ke gaya mini abin da ke faruwa, dan Allah Umma ki yi ha?uri in sha Allah zai je yau Win nan, shi ne ya ce na baki ha?uri fushi ki ke yi dashi, zai shirya ya je, sai dai Umma akwai matsala Haidar bashi da lafiya, yana jin kunyar faWa miki ne, amma in sha Allah yanzu zamu je gurin wani malamin da yake ba da maganin irin rashin lafiyarsa, sai mu karSo idan muka dawo ko zuwa bayan azahar ne sai ya wuce".


Shiru Umma tayi tana nazarin maganganun. Haidar Win ne ba shi da lafiya amma bai taSa gaya mata ba, to kuma bashi da lafiyar ne yake nuna mata alamar yana son aure? To ko dai yanzu ne matsalar ta same shi?

"Faruk ya aka yi bai taSa gaya mini cewar bashi da lafiya ba sai yanzu? Ko da yake ai shikenan, gun wane malami ne zaku je Win? Kuma a ina yake".

Faruk ya karkace kai ya shirgaga mata ?aryar cewar a nan cikin garin yake, yanzun nan ba da daWewa ba zasu je su dawo.

Ta ce "To shikenan Allah ya taimaka yasa ada ce". Da amin ya amsa yana barin Wakin. Ya je ya samu Haidar ya gaya masa duk yadda suka yi, cikin sauri Haidar ya shirya suka bar gidan hankalisa ?awance.

Su Hardai na fita sarkin fada ya kira Umma ya ji idan Haidar Win ya taso, nan ta shaida masa cewar babu fashi yau zai zo, ya je ya karSo sa?o ne ya dawo. Bayan sun gama wayar ta shiga nazari da tunanin rashin lafiyar ta Haidar ita abin ya bata mamaki kuma ya Waure mata kai.


***

Sharifa ta ce "Momy dan Allah yau ina so zan je na kawai Maryam ziyara"

Momy ta ce "Wace Maryam Win kuma?"

"Momy wannan sabuwar ?awar tawa da na baki labarin nayi".

"Au na gane, Sharifa akwai ki da na ci, ke da baki da sakin jiki da mutane amma kin na ce akan yarinyar nan".

"Momy ba za ki gane ba, ina son yarinyar ne, kin san idan ina son abu bana wasa".

"Haka ne, amma ka da ki yi tafiyar yamma, ke banma yarda ki tafi da kanki ba, ku tafi tare da direba".

"Haba Momy..." "Idan ba kya son direba ya kai ki sai dai ki fasa zuwan" Momy ta katseta

"A'a Momy na yarda".


Har azahar Maryam na in da Afnan Atika ta kawo musu abinci, tun Maryam tana saka ran ganin mijin yayar ta ta ya iso amma shiru, ka ke ji,

Ta ce "Wai Aunty har yanzu banga ya ?araso ba, ashe dai tafiyar da nisa kenan?".

"To Maryam ya za ayi na sani, ni fa banma san daga ina ne ya taso zuwa nan Win ba, ni dai kawai manta da maganarsa Win nan muci gaba da hirir mu".


Misali ?arfe uku Turai ta zo gurin Mami tare da Hasina, babu kowa a falo zama suka yi, ta kira Mami a waya ta ce mata tana falo.

Babu Sata lokaci Mami ta zo falon, dama tana Wakin Huda ne, ta duba jikinta yau ta tashi da zazzaSi ne.

Zama tayi suka gaisa Hasina ta gaisheta, sama-sama ta amsa mata, hakan ba ?aramin Satawa Turai rai ya yi ba, amma sai ta ?i nunawa.

Mami Mudan ta kira ta ce duk in da yake ya zo yanzu tana son ganinsa.

Da sallama ya shigo falon idanunsa ne suka sauka akan Hasina, cikin rawar jiki ya ?arasa shigowa falon. Ya ce "Laaaa Baby Hasina yau ke ce a gidan namu? ashe dai muna da babbar ba?uwa, Mami ya aka yi banga an kawo mata abin sha ba? ina Huda take ne da zata barta haka babu lemu, ke Huda Huda".

Ganin kamar Sata lokaci ne idan ya tsaya jiranta ya sa shi mi?ewa jiki na rawa ya Wakko ruwa da lemu ya je a gabanta.

Mamaki ne ya kusa kashe Mami

Cikin Waga murya ta ce "Mudan me zan gani?".



Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA....* =ث?





_WRITING BY AMANAR COOL_
'?




*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*




Page 49&50



____________Tsare ta ya yi da ido, saboda bai san abin da take magana a kai ba, cikin Waga murya ta ce "Ba magana nake yi da kai ba ne? Ka wani tsare da ido ka na kallona".

"Mami meyafaru ne?"

"Ban sani ba, dan ubanka wannan rawar jikin da ka ke yi na meye? Mudan kar dai maganar da ka gaya mini da gaskiya ce?".

"Haba Mami meye laifi dan anyi ba?i na kawo musu ruwa?".

Turai ta ce "Ikon Allah wai Saratu meya kawo wannan abin haka?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login