Showing 9001 words to 12000 words out of 52998 words

Chapter 4 - RAMIN ƘARYA HAUSA NOVEL

24 Oct 2025

95

ta sa'arsu ce, daga ta faWa musu gaskiya".

Maryam ta ce "Wallahi Baba ?arya take, Inna Hajara munafukace, ba haka aka yi ba, Aunty bata san komai ba".

Duban Maryam Mama ta yi ta ce "Me ya haWa ku da ita Maryam ba kya jin magana ko, kinga abin da ki ka jamana ko".

"Mama ni fa ba wani rashin kunyar dana yi mata" nan ta kwashe komai ta gaya musu, tsaki Baba ya yi, tare da Waukar buta ya yi alwalar magariba, ya? bar gidan.

FaWa sosai Mama ta yi wa Maryam, akan komai Hajara zata yi, kar ta ?ara kulata.

Afnan tsayuwa ta yi, guri Waya, ta kasa motsi, sai da Mama ta yi magana kafin ta Wauki buta zuwa alwala.

****


Haidar cikin damuwa yayi wunin yau gaba Waya, daga baya ma ha?ura yayi da Waukar fastoinja ya koma gida.

Mamaki ne ya kama ummansa, ganinsa a gida, ba lokacin dawowarsa ba.
Kasa Soye mamakinta tayi ta ce "Ya na ganka a gida ne, lafiya dai ko?"

Ya jinjina mata kai, ya ce "Lafiya ?alau" ya buWe Wakinsa ya shige.

Wuri ya nema ya zauna, a gefen katifarsa, ya Waukko wayarsa, ya duba number da Maryam kira shi da ita, ya kira sai dai aka ce a kashe guntun tsaki yayi, ya ajiye wayar a gefe.

*****

Abba ne ke waya da Alhaji munir, bayan sun gama magana akan harkokin kasuwancisu, Alhaji munir ya ce "Abokina ina muka tsaya ne akan maganar yaran nan" Abba ya ce "Dama ina son yima maganar, to bari nayi in shedawa uwar yaron, na ji ta bakinta" Alhaji munir ya ce to ba damuwa Allah ya tabbatar mana da alkhairi" Abba ya amsa da Amin, sannan suka yi sallama.

Duban Hajiya Zainab dake zaune a gefen sa ya yi, ya ce "Madam ya ne? kwana biyu nan kin sauya" ko dai baby ne ya sauya mini ke" murmushi ta yi ta ce "Wani irin baby, a ina ka ga babyn" . "A cikin matata mana, amma naga Soye mini ake yi, ban san dalilin hakan ba".

"Ni fa ba ni da komai" ta faWa tana dariya" shi ma dariyar ya yi, ya ce "Wai sai yaushe zaki dai na jin kunyata ace mata da mijin ta ba zata iya gaya masa tana da juna biyu ba" idan ba a faWa mini ba, waza'a faWama".

Hannu tasa ta rufe fuska tana dariya, tsokanarta ya dinga yi, sannan ya ce "Allah ya inganta mana, yasa babyn nan rabonmu ne " da amin ta amsa.

"Ya ce buWe fuskar mana
magana zamu yi" buWewa ta yi tana kallon shi,
Abba ya ce "Dama Alhaji munir ne yake son a haWa auren Sharifa da Mudan, me ye shawarar ki a kai".

Kafin ta yi magana, suka ji ?arar faWuwar abu, da sauri suka dubi ?ofa, Hudah ce wayar hannuta ta subuce, sakamako jin furucin da Abba ya yi.

Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA....* =ث?





Story & writing

By

Mrs Muttala (Amanar cool)




*YOUNG TALENT*
*WRITER'S ASSOCIATION*



Sadaukarwa ne ga Aysharcool



Free book
'?



Page 9&10


______Jikinta ne ya Wauki rawa, ta ji jiri na Wibarta, da sauri ta dafa Waya daga cikin kujeran falon.

Cikin sauri Abba ya isa inda ta ke, ya ce "Subhanallah Daughter me yake damunki? baki da lafiya ne?".

Girgiza kai ta yi, ta ce "Abba jiri ne nake ji" sannu ya yi mata, sannan ya Wakko mata wayarta, ko da ya duba wayar fuskar wayar, ta farfashe, abu ne mawuyaci idan ba ta ci screen ba.

"Ya salam kin ga screen Win wayar ya samu matsala".

KarSar wayar ta yi tana kallo, idanunta ya ciko da ?walla, Abba ya ce "Sorry my Daughter, zan sa Yayanki ya kai ki ki za Si kalar wayar da ki ke so" murmushin ?arfin hali ta yi, ta ce "To Abba na gode".

Hajiya Zainab tsaye ta yi tana ?are mata kallo, mamaki take me zai sa Hudah ta shiga wannan tashin hankalin, lokacin Waya saboda kawai ta ji maganar za'a haWa yayanta aure da wata, abin da ta gani kwanaki ne ya faWo mata a rai, kawar da wannan tunani tayi , ta ce "Sannu Hudah jirin ya sauka ne?" Waga mata kai ta yi, tana ?o?arin mi?ewa ta bar wajan, Abba ya ce "Zaki iya tafiyar ne?"

"Eh Abba zan iya na daina jin jirin"

Ammi ta ce "Hudah ina fatan ba wata damuwa?" tayi maganar ganin Hudah zata fita ba tare da sannin me ya kawo ta ba, "A'a Ammi ba damuwa, dama na zo na gaisheki ne." Ammi ta ce "To ina godiya sosai ki gaishe mini da ummanku".


*****

WASHE GARI

Da safe, Baba ya ?ara shaidawa Afnan cewar ta fito da mijin aure, idan ba haka ba zai aurar da ita ga duk wanda ya ga dama.

Mama ta ce "Haba Baban Afnan, ka san yarinyar nan ba saurayi ne da ita ba yanzu, masu nemanta Win duk sun dai na zuwa, addu'a yakamata mu yi Allah ya fito mata da miji na gari, komai na da lokaci, idan lokacin auen ya yi babu zato, ba tsammani sai ka ga an yi." Bai kamata ka din ga yadda da ziga, da maganar abin da ba ka gani, ka tabattar ba.

A fusace ya ce "Rufe mini baki, mahaifiyata za ta yi ?arya ne? dama na daWe da sanin cewa ke ce ki ke goya mata baya, samari nawa ne ke bibiyar ta amma ta ?i kulasu, to na ga ji a wannan karon ko ta fito da miji ko na ba da sadakarta ga duk wanda na samu".

Yana gama faWar haka ya yi wucewarsa, ya na fita ya ci karo da Gwaggo a tsaye, ta na jin duk abin da suke faWa.

Bayan sa Mama ta bi da kallo, tana mamakin sauyin da ya yi lokaci Waya.

Afnan kuwa kuka take sosai, dan ba ?aramin tashin hankali take shiga ba a duk lokacin da ta ji Baba na yi mata faWa akan aure, musamman daga jiya zuwa yau ta ji abin yafi damunta, mazan sun ?ara fita a zuciyarta gaba Waya.

Mama ta ce "Wannan kukan ba shine mafita a gareki ba, addu'a zaki yi har Allah ya fito miki da miji, tun farko ke ki ka yi wasa da damarki Afnan, abin da nake yi miki gudu kenan dama, gashi kuma ya zo".

Gwaggo suka gani ta shigo musu ko sallama babu, ta ce "Au saboda an yi miki zance aure shine ki ke wa mutane kuka, saboda jin daWin uwarki ta goya miki baya, to wallahi ko kukan jini zaki yi aure ba fashi, sakarar yarinya kawai, wato kin fi son ki zauna ki na gwada girma ke da uwarki da ta ke Waure miki gindi, to baku isa ba, dole ne ki fitar da miji, in ba haka ba wallahi ?auye zan sa a bada sadakar ki".

Har Gwaggo ta ?are faWanta, ba wanda ya tanka mata.


*****

Haidar tun jiya daya shiga Wakinsa, bai sake fitowa ba, ganin haka yasa Ummansa shiga Wakin ta duba lafiya yake, a kwance ta tarar da shi, yayi zurfi a cikin tunani, ya kasa samun Maryam a waya, balle ya ji ya jikin Afnan. Kuma zuciyarsa na ci gaba da wassafo masa kamaninta a cikin idanunsa. Yana matu?ar son ya sake jarraba komawa, ko Allah zai sanya ya dace ya kuma ganinta.

Umma ta ce "Haidar ba ka da lafiya ne? me ya ke damunka?".

Mirginawa ya yi ya tashi zaune,
ya ce "Ba wani damuwa Umma kawai jikina ne ba daWi"

Umma ta ce "Haidar yaushe ka fara Soye mini damuwarka, rashin jin daWin jikin ne zai saka, ka din ga zaman Waki, ko zuwa in da nake baka yi".

Zama Umma tayi a bakin katifar, ta ce "Haidar ni fa mahaifiyar ka ce, duk duniya baka da kamata, baka saba da Soye mini damuwarka ba, kar ka fara a wannan karon, ka gaya mini me yake damunka, ka ji shalelen Umman shi".

Haidar tsintar kansa ya yi da jin kunyar faWawa Umma cewar ya kamu da son wata ne, sunkuyar da kansa ya yi, ya kasa magana, ganin hakan yasa "Umma ta ce Haidar ka yi magana mana ina sauraron ka".


Umma ta ?are masa kallo, jin ya?i cewa komai, sai sunkuyar da kansa yake yi kamar sabuwar amarya. Ta numfasa ta ce "Haidar ko sirika zaka kwaso mini ne? Wannan sunkuyar da kan, da magana.
Da sauri ya Wago ya kalleta, jin yadda ta ramfo shi, lokaci guda haka.
Murmushi ta yi cikin dattaku ta ce "Labarin zuciya, ai a tambayi fuska. Ban tari numfashinka ba amma ina ga ka a jiye maganar auren nan a yanzu, duba da halin da muke ciki, ba mu da ?arfin tunkarar aure a yanzu, wata rana abincin da zamuci ma wuya yake mana, in ba kwanakin nan da Allah ya haWa ka da bawan Allah nan da ya baka babur Win nan muka samu sau?in wasu abubuwan ba, to ka ga bai kamata ka jajiSo maganar aure a yanzu ba, ka yi ha?uri da zancen aure yanzu, ka ?ara tsayawa da ?afarka tukuna, ka fitar da ita a ran ka, mu ci gaba da addu'a, tun da ka kammala karatunka a ko wane lokaci Allah zai iya sa wa ka samu aiki".

Haidar Ya ce "To Umma na ha?ura Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi, ki taya ni da addu'a Allah ya ci re mini abin a rai na".

Umma ta ce "In sha Allah zan ta yaka da addu'a, Allah ya yi maka albarka"


*******

Gaba Waya Hudah ta rasa nutsuwarta, kwana tayi kuka tana tunanin me ye makomarta, shekenan ita ta tashi a tutar babu, ji tayi ba zata iya ha?ura wata macen ta aure ya Mudan ba, idan ba ?arya kunnenta ya yi mata ba, kamar Wiyar Alhaji Munir ta ji Abba ya ambata, ke nan hakan yana nufin Sharifa za a aurawa Ya Mudan. Da ?arfi ta ce "Impossible ni a rasa da wa za a haWa shi sai wannan yarinyar da ta raina wa mutane wayo, kowa kallon Wan iska take masa, dole na nemawa kaina mafita, ko da Hakan yana nufin tonuwar asirin sune.

Abba na Wakinsa Mami ta shiga da sallama zama tayi a bakin gado ta ce "Ashe ka shigo ban sani ba" Abba ya ce "Eh lokacin dana shigo ki na toilet ne" "Ok" ta ce.

Duban ta Abba ya yi ya ce "Dama ina son magana dake, Alhaji Munir ne ya zo mini da zancen a haWa Mudan da ?arsa Sharifa aure, shine na ce ya bari na shawarce ki na ji me ye ra'a yin ki, ko Mudan Win ban yi maganar da shi ba, bari na yi na fara jin ra'ayinki".


Washe baki Mami tayi ta ce "Alhamdulillah ai dama wannan ranar nake jira, ranar da zan ga Mudan ya fitar da matar aure, kai ma sha Allah wannan haWin ya yi mini daWi sosai, Allah ya sanya alkhairi, ya kai mu lokacin aure zamu musha biki na ke ce rai ni". Tayi maganar ta na ?o?arin mi?ewa tsaye.

Abba ya ce "Ina za ki kuma?" . "Alhaji zan turo maka Mudan Win ne ka yi masa maganar".

"Dawo ki zauna zanne me shi da kaina"

Zama tayi tana wani shu'umin murmushi, wanda ita kaWai ta san ma'anarsa.

Abba ya ce "Hajjaju wannan murmushin duk na jin daWin auren ne?"

"Eh ba dole na ji daWi ba, Mudan zai zama babban mutum".

Murmushi ya yi ya ce "To ga wani abin farin cikin daya kuma samuwar mu, ?ar uwarki Zainab ta koma samun juna biyu, sai a taya mu da addu'a".

"Gabanta ne ya yi mummunar faWuwa, amma ta daure, cikin kissa, da kisisina, ta ?a?alo wani munafukin murmushi, ta ce "Ma sha Allah, Allah abin godiya Allah ya inganta, ya raba lafiya" Abba ya amsa "Ameen".

Mami ji ta yi duk Wakin ya yi mata duhu, wani irin tu?u?in ba?in ciki take ji a cikin zuciyarta, lokaci Waya farin cikin da take ciki ya juye ya koma ba?in ciki, zagi ta din ga Wirkawa Ammi a zuciyarta.

Zumbur ta mi?e kamar wadda aka tsikara, ta ce "Alhaji zan je in dan kwanta, ina jin kaina na yi mini ciwo" ."To Allah ya ?ara afuwa, ki sha magani kafin ki kwanta" ficewa tayi har tana haWa hanya ta bar Wakin.


*****

Yau ma Maryam ta yi halin na ta, na guduwa daga makaranta, ita da sabuwar ?awar da tayi Safena, wata yar unguwarsu ce da halinsu ya zo Waya, Safena na son Maryam sai dai Maryam Win bata sakar mata fuska ba, sai ?an kwanakin nan, dalilin wani faWa da Safinar ta shigar mata ne har ta fara kula ta.

Suna tafe a hanya sun yi wujiga-wujiga ga zafin rana Maryam ta dubi Safina ta ce "Feena wai babu sauran canji ne a hannun ki? wallahi duk na gaji da tafiyar nan" feena ta ce "Ko ficika bana magani" murmushi Maryam tayi ta ce "Yau za'a yi taSara kenan, zo muje.

Feena ta ce "Wace irin taSara kuma?"

"Ke dai zuba ido ki sha kallo"

Bakin titi suka ?arasa suna tarar abin hawa, wani Wan adaidaita sahu suka tsayar, har ya wuce su kaWan ya dawo, Wauke yake da wata matashiyar budurwa a ciki, tambayarsu in da za su ya yi, bayan sun faWa masa, ya ce "Su shiga" shiga suka yi ba tare da sun kula budurwar dake ciki ba.

"Sannu" ku budurwar ta faWa Feena ta ce "Yawwa sannu" Maryam ba ta ko kalleta ba, balle har ta amsa mata, kallon Maryam budurwar take yi, Maryam na lura da irin kallon data ke yi mata,
?wafa tayi ta ce "Malama lafiya, ni fa bana son kallo, kin wani tsare ni da ido sai kace ki na bi na bashi" murmushi budurwar tayi "Ta ce sunana Sharifa ba Malama ba, Allah ya baki ha?uri".

TaSe baki Maryam tayi bata kuma magana ba.

Ko da suka ?araso unguwarsu Feena aka fara saukewa, da yake gidansu ne a farkon layin, feena sai raba ido take yi, saboda ta san basu da gaskiyay, Maryam ta ce "Su tafi ita za ta biya shi kuWin" tun Kafin napep Win ta tsaya, Maryam ta dira da mugun gudu ta afka cikin gida, cikin rashin sani, tayi wa Gwaggo dake tsaye bakin hanya, wani wawan bangaza ba tare data kula da tana tsaye a gurin ba.

Ihu Gwaggo ta saki tana zubewa a gurin, Maryam ko ta kan Gwaggo bata tsaya bi ba tayi shigewarta sashensu.

Bala'i mai napep Win ya fara yi, yana zage-zage tare da faWin "Wallahi zai iya shiga har cikin gidan nan, shi za'a gwadawa iskanci, da rashin kunya".

Gwaggo dake kwance baje-baje a ?asa, jin ana zage-zage a ?ofar gida ta yun ?ura da ?yar ta tashi, fita ta yi ?ofar gidan.

Yana ganin Gwaggo ya ?ara masifa yana faWin "Sai an biya shi kuWinsa, ko ya shiga har cikin gidan nan ya yi wa yarinyar nan shegen duka".

Tambayar shi Gwaggo tayi "Me yake faruwa?" ya kwashe komai ya gaya mata.

"Ka ga zo mu je na kai ka har gurin Uwarta a biya ka kuWin ka, ko ka yi mata tsinanne duka, wannan fitinaniyar yarinya Allah ya a gajemu da ita".

Da sauri sharifa ta fito daga cikin napep Win ta ce "A'a Inna baza a yi haka ba, kaga Malam zo muje, ni zan biya kuWin".

Ya ce "Ta kuru wallahi da yau taga yanda ake rashin kunya" Gwaggo ta ce "Nima ban so ta ce za ta biya ba, na so muje har gaban uwarta, ta ji Wibar albarkar da ?arta tayi".

Tada napep Win sa ya yi suka bar wajan Sharifa mamakin Maryam ya cika zuciyarta, gashi yarinyar ta burgeta, har so ta yi ta ?ullah ?awance da ita, sai taga yarinyar na shan ?amshi, murmushi tayi a fili ta ce "zan sake dawowa" dan har cikin ranta ta ji tana son Maryam Win.

Cikin gidan Gwaggo ta koma da masifa ta shiga ?ofar su Maryam, tana faWin "Ina take shegeyar yarinya mara kunya, ni zaki hankaWe kasa ki gudu saboda baki da hankali".

Mama na banWaki ta ji Gwaggo na masifa, ?in fitowa tayi ta nemi kujerar dake ciki tayi zamanta.

Afnan na Waki kwance ta ci kuka har ta gode Allah ta ji masifar Gwaggo ,fitowa ta yi a Wakin ta ce "Haba Gwaggo wai meyasa ki ke son aibata mu ne, sai ka ce ba jininjiki muke ba, ke kullum cikin yi miki ba dai-dai muke ba". Afnan tayi maganar cike da jin haushin Gwaggo, saboda ta san duk ita ce ke ziga Baba a kan zancen ta fito da miji.

Baki bude Gwaggo ke kallon Afnan da idanuwata ya yi ja, ya kumbura saboda kuka.


Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA* =ث?



Story & writing

By

Mrs Muttala (Amanar cool)




*YOUNG TALENT*
*WRITER'S ASSOCIATION*




Sadaukarwa ne ga Aysharcool



Free book
'?



Page 11&12



_________"Lallai wuyanki ya yi kauri ni ki ke gayawa wannan maganar, saboda bani da girma da mutunci a idanuwanku? kun Wauke ni banza, ba laifinku bane, laifin ?an ladi ne daya kasa tsawatar muku, ya bar ku ganda-ganda har ku ke gani kun isa dai-dai ku ke da kowa. Amma ba komai, yau zan yi maganin abin, ke kuma Wayar marar kunyar yau sai kin san kin han?aWe ni".

Maryam ta ce" Idan kin ga dama kar ki sa a bar ni da rai, ni na ce ki tsaya a hanya ne".

Kuka Gwaggo ta fashe da shi ta ce "Ni ku ke ci wa mutunci, saboda kun samu dama, Amina ki na jin abin da ?a,?anki suke yi mini amma baki tsawatar musu ba, ba komai bari shi wanda nake da iko da shi ya zo" ta na gama faWar hakan, ta bar gurin.


Mama na banWaki zamanta duk abin da suke ta na jin su,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login