Showing 15001 words to 18000 words out of 52998 words

Chapter 6 - RAMIN ƘARYA HAUSA NOVEL

24 Oct 2025

86

kuma idan ta shigo hannunsa sai tayi da na sani da nadamar abin da tayi masa.


Mami na zaune kira ya shigo wayarta, ko da ta duba Turai ce, cikin zumuWi ta Waga wayar, ta ce "Hello. Aminiya ta hannun dama, yanzu nake tunani kiran ki, sai gashi kin kira, ya ake ciki kin samo mana mafitar ne?"


Turai ta ce "DaWina da ke gajen ha?uri, ai kya bari mu gaisa".


"Ba zaki gane bane, mu a je gaisuwar nan a gefe, yanzu me ye labari? dan wallahi a yanda nake ji Win nan komai zan iya aikatawa matar nan, ta tsaya mini a ma?ogarona, ni fa har zarginta nake, anya ba asiri tayi mini ba, akan rashin samun cikin nan nawa, ki duba ki ga shekarata nawa a gidan nan ko Sari ban taSa yi ba, ni dai ba juya ba ce, balle a ce bana haihuwa, amma kullum ita ce ke Waukar ciki a gidan nan ban da ni".


Dariya Turai tayi, ta ce "Haba ?awata, faWi dai wani zancen ba wannan ba, ke ma kin san Zainab ba zata aikata hakan ba, wannan matar zuciyarta tsarkakakiyyace, kamar ta Aysharcool, shiyasa ki ka ga wani lokacin duk abin da muke yi mata baya tasiri, saboda ta dogara da Allah, sannan gata da son ibada".

Cikin fushi da ?unar zuciya, Mami ta ce "Turai me ki ka nufi ne? ki na nufin ni bana tsoron Allah ne? ko kuma ni kin kafurta ni ne?".


"Ni fa ba haka nake nufi ba, kin san halina, duk da ina da mugun hali, amma hakan ba zai hana ni faWar gaskiya ba, komai Wacinta".


Mami ta ce"Ba na son irin wannan maganar, zamu iya samun saSani dake, matu?ar ki na mini irin wannan zancen, ki ri?e gaskiyar in dai akan wannan matar ne".

"To na ji mu bar wannan maganar Allah ya baki ha?uri zan ki ya ye". "Da dai yafi, yanzu ya ake ciki?"


"Yawwa mun yi magana da wata ?awata ne, ta ce mini zata haWa ni da wani malaminta, aikinsa kamar yankan wu?a, ba irin aikin da baya yi, kuma shi ko mutum bai je ba, zai iya yi masa aiki, kuma yasa a kawo masa har gida, sai dai aikin na sa akwai tsada sosai, sannan kuma aikinsa yafi tasiri ne akan masu saka ce da ibada, kin ga kenan ba lallai aikinsa ya yi tasiri akan kishiyarki ba, sai dai a yi wa shi mai gidan. Duk da ita ma Win zamu gwada yi mata mu gani ko za mu yi nasara".


Nisawa Mami tayi ta ce "Wannan matar an yi tsinanniyya, ba komai, kin san kuWi ba matsalata bane, ni dai burina cikin ya fita, sannan a lalata mahaifar ta yanda ba zata sake Waukar ciki ba, amma kuma ki na ga idan asirin bai yi tasiri a kanta ba ta ya za a yi cikin ya bar jikinta? ko kuma ta Sangaren Alhaji ma za a iya samun
nasara ya zubi".

"Eh to wannan dai ne ban sani ba, yanzu dai sai na yi magana da malamin, tukuna na ji me zai ce".

"Tom shikenan ba damuwa, ina jiranki duk yanda kuka yi ki taSo ni, zan tura miki kuWi, idan ma basu isa ba sai ki yi mini magana". "Ok sai kin ji ni" Turai tayi maganar tare da kashe wayar.


Sai bayan isha Mudan ya dawo gida, a gajiye, kai tsaye sashensa ya wuce, a falo ya zauna, ya na rage kayan jikinsa, tsabar gajiya ko ?ofar bai tsaya rufewa ba, ji ya yi an banko ?ofar da ?arfi, da sauri ya Wago da kansa, Hudah ya gani tsaye ta na bin sa da wani irin kallo, gabansa ne ya yi mummunar faWuwa, ji ya yi shakku, da tsoro, haWe da razani, sun yi masa dirar mikiya a zuciyarsa, ya ji Hudah tayi masa wani kwarjini, tunda yake bai taSa ganin Hudah a irin wannan yanayi na Sacin rai ba, kuma ya san hakan baya rasa nasaba da abin da ya faWa Wazu a gabanta. Tattaro jarumtarsa ya yi, ya Soye duk wata fargaba, ya ce "Suweety lafiya na ga kin shigo ba ko sallama? kuma na ganki cikin yanayi na damuwa?".


Lallai wato a duniyar ?an iskan ma. Ya Mudan tantirin ?wallon Wan iskane, cewar Huda a zuciyarta, "Kar ka raina mini wayo me ka Wauke ne? ko kuma ni ?aramar yarinya ce da zaka yi wa pretending kamar baka san me nake nufi ba, to wallahi wallahi wallahi. Ya Mudan ka yi kaWan baka isa ba. Kuma ka bani mamaki, ka yi mini abin da ban taSa tunani ba, sannan kasa wa ranka cewar ba zaka taSa auren Sharifa ba, wato ni ka rusa mini rayuwata, kai kuma ka na ?o?arin inganta taka ina matsayin ?ar uwarka ta jini, amma zaka iya yi mini wannan cutar, idan har kai zaka iya guduna, ba zaka rufa mini asiri ba, tom wa ka ke tunanin zai rufa mini?".


"Please Hudah ki fahimci ni, ni fa ban ce ba zan aureki ba, sannan ba fa ni na ce zan aure Sharifa ba, wannan haWin na su Abba ne, kuma kin san ba zan iya ce masa a'a ba, dan haka ki kwantar da hankalinki, aure tsakanina dake ba fashi, but ina son ki ba ni dama na fara auren Sharifa, kafin" bai ?arasa maganar ba, Hudah ta katse sa da faWin "I don't like mistreatment Ya Mudan".

"Haba Hudah ba zancen wula?anci ba ne, kin san fa you are the one my heart chose so kar ki wani damu".

Kallonsa kawai tayi, ba tare da ta kuma magana ba, ta juya ta bar falon, don idan ta tsaya ba abin da zai hana ta ?undumamasa uwar ashar.

Ajiyar zuciya ya sauke, ganin ta fita ya ce "Jarababiyya kawai, sai dai ki yi ha?uri, aure ne dai ba fashi, sai na aure Sharifa".



******


Mama fitowa tayi waje, bayan ta a je wa Baba abincisa, ta tarar su Afnan basa gurin sun shige Wakinsu, Wakin ta shiga ta same su, Maryam sai cika take, ta na batsewa, zama tayi ta dube su ta ce "Shiyasa a ko da yaushe nake cewa ku kasance masu ha?uri, da kawar da kai akan komai. Duk abin da za a yi muku a gidan nan, na ce ku yi ha?uri, ku yi kamar ba ku ji ba, ba ku gani ba, amma ina, kun kasa fahimta, musamman ma ke Maryam, na rasa in da ki ka Wakko wannan rashin ha?urin, yanzu ki du bi abin da ki ka jawa kan ki, rabon da Babanku ya dake ki tun ku na yara".


"Wallahi ba wani rashin ha?uri, kawai dai an tsanemu ne, kuma duk abin da Baba zai yi mana ziga ce, irin ta Gwaggo da wancan ba?ar muna fukar matar mai shegen kai kamar an yi dakon alewa, wallah Mama duk ranar da wannan figagiyyar ?arta ta dawo, duk abin da tasa aka yi mini akan ta zan rama".

Dariya ce taso suSucewa Mama, jin Maryam ta ce "kan Hajara kamar an yi dakon alewa" amma sai ta fuske ta ce "Ai kin ji matsalarki rashin ha?uri, tom ko kusa kar in ji kin taSa yarinyar nan".

Sannan ta dubi Afnan ta ce "Afnan ina so zamu yi magana dake, kuma ina son duk abin da ya zo miki, mai kyau ne ko akasin haka, ki Wauka tun ran gini tun ran zane Allah ya ?addara hakan a cikin kundin ?addarar rayuwarki, sannan komai ya faru da mutum da sanin Ubangiji".

Cikin yanayi na rauni, da buguwar zuciya, Afnan ta ce "Mama meyafaru? wani abin ne ya faru da ni ko kuma yake shirin faruwa da ni?".

"Afnan mahaifinki ya na son aurar dake ga duk wanda yasa mu" nan ta gaya musu duk yanda suka yi da Baba.


Wata irin zabura Afnan tayi, ta mi?e tsaye, jikinta ya Wau rawa, da sauri Maryam ta mi?e tsaye ta ri?e Afnan dake ?o?arin faWuwa, ta ce "Aunty Afnan ki kwantar da hankalinki, ki natsu, in sha Allah kin fi ?arfin a yi miki irin wannan auren, sai dai mu ji ana yi a wani gurin, ba dai nan gidan ba".


"To ki bari idan aka tashi Waura mata auren ki hana, ko kuma ki bi dare ki kashe mijin". suka ji an yi maganar daga bakin ?ofar Wakin.


Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA....* =ث?




Story & writing

By

Mrs Muttala (Amanar cool)




*YOUNG TALENT*
*WRITER'S ASSOCIATION*




Free book
'?



Page 15&16





_________Da sauri suka kalli ?ofar Gwaggo ce da isowarta kenan, ta yi sallama a tsakar gidan ta ji shiru, daga baya kuma sai ta ji ana magana a Wakinsu Afnan, shi ne ta zo da niyyar zazzaga musu masifar suna ji tana sallama suka yi banza da ita, sai dai ta na zuwa ta ji Maryam na wannan maganar.

Shigowa ciki tayi, tana bin Afnan da kallo, gaba Waya ta fita hayyacinta, cikin ?an?anin lokaci, ri?e baki tayi ta na salati ta ce "Yanzu ke saboda lalacewa, da sangarta, maganar auren ce ki ke wa wannan haukar? to wai ke '?ar nan idan ba a aurar da ke ba ji?a ki ki ke so a yi a sha ki me ki ke nufi? ko kuma kin fi so ki zauna a gida ki na gwada girma ke da uwarki?".


Har Maryam za ta yi magana sai kuma ta yi shiru, sakamakon ganin Afnan na dafe kanta, ta na wani gunjin kuka, ita ma Maryam kukan ta fara ta na faWin "Aunty ki yi ha?uri in sha Allah, Allah yana tare dake, duk mai son ?untatawa rayuwarki, da son ganin kin shiga damuwa, Allah ba zai ba shi iko ba, ko da sun yi nasara na Wan lokaci ce". Tayi maganar tare da kwantar da Afnan Win a kan katifa.

Baba ya shigo Wakin yana faWin "Hayaniyar me na ke ji a Wakin?"

Gwaggo ta ce "Shafafiyya da mai Win ku ce, take ?o?arin kashe kanta, saboda da an yi mata zance aure, to ki sani komai za ki yi aure dai ba fashi, matu?ar ina raye".

Gaba Waya jikin Baba ya yi sanyi, har cikin zuciyarsa yana jin babu daWi, ganin halin da Afnan take ciki, ga Maryam sai kuka take, abin da ya tsana kenan, ganin iyalinsa cikin damuwa, sai dai bai san abin da yasa yake yawan jin haushinsu ba.

Cikin sanyin jiki ya ?arasa inda Afnan ke kwance, ya ce "Ke lafiya? me ye ki ke yi haka? ba na son shashanci. Ke sake ta".
Ya cewa Maryam, cikin damuwa. ta ce "Baba dan girman Allah ka yi ha?uri, ka da ka yi wa aunty Afnan irin wannan auren, wallahi na yi maka al?awarin za ta fito da miji idan aka yi mata haka ba a kyauta mata ba".

Shiru ya yi, ya zuba musu ido, ganin hakan yasa Gwaggo cewa "Lallai Wan ladi ban ?ara tabbatar da kai soloSiyone ba sai yau, yanzu tsabar an raina ka, an mayar da kai jelar ra?umi, sai yanda aka yi da kai, '?arka ce zata dubi tsabar idonka ta gaya maka wannan maganar, to bari na gani umarninta zaka bi ko nawa" tana gama faWar haka, ta bar Wakin, abin da ya kawota ma bata tsaya yi ba.

Shima fita ya yi daga Wakin, Maryam ta dubi Mama da tayi jugum, ta ce "Mama yanzu ba wani abin da zamu yi ne, ki duba halin da take ciki fa".

"Maryam ki rufawa kan ki asiri, ki ?yale su duk abin da za su yi su je su yi, in sha Allah, Allah yana tare da ita" daga haka ita ma ta bar Wakin, rarrashin Afnan Maryam ta ce gaba da yi, ta re da bata ha?uri.

Bayan fitar Gwaggo daga Wakin, cikin takaici ta nufi sashenta, a hanya ta ci karo da kawu Sanusi, ta umarce da ya biyo ta Waki, bayan sun isa ne take gaya masa irin kalar rashin kunyar da su Maryam suka yi mata, sannan kuma da hukuncin da ta yanke. Kawu Sanusi ya ce "Yawwa Gwaggo kin yi mini dai-dai, dama hakan shi ya fi, tun farko yakamata a yi wannan tunanin, amma ko yanzu bata Saci ba, in sha Allah gobe ko bai yi magana ba ni zan yi".

"Yawwa Wan albarka, shi wancan bita zai-zai Win bai kira ka bane?"

"A'a Wazu ma mun yi waya da shi har ya ce in haWaku, to lokacin bana gida na ce masa ya bari sai na koma gida zan kira shi, yanzu kuma dare ya yi sai da safe zan kira miki shi".

"To ya yi Allah ya kaimu safiyar lafiya, sai na ji idan shi ne ya bawa matarsa damar tafiya tayi zamanta, kamar an aiki bawa garinsu".

Sallama kawu ya yi mata sannan ya bar gurin.



WASHE GARI

Bayan an idar da sallar asuba, Baba tunani yake ta ina zai fara yin wannan bayanin, yana wannan tunanin ne ya ji kawu Sanusi na cewa "Jama'a. Assalamu alaikum ina yi wa kowa barka da asuba, kamar yadda kuka sani cewar a gidanmu muna da yara '?an mata kusan su huWu, kuma ko wacce a cikinsu ta kai mizalin aure, to daga cikinsu muna so zamu aurar da babbarsu, wato A'isha ?ar gidan yayana Abbakar, inda mai bu?ata ya yi magana, sai ya ba da sadaki a Waura musu aure ko nan da kwana biyu ne".

Shiru jama'a suka yi ana kallon kallon. Liman ya yi gyaran murya ya ce "To jama'a kun ji abin da Malam Sanusi ya zo da shi, dan haka inda mai ra'a yi sai ya yi magana, a taru a rufawa juna asiri. Sannan ba abin kunya ba ne, dan uba ya nema wa 'yar sa miji, mutuncinta yake son karewa".

Nan fa kowa ya ce a'a, a wannan yanayin da ake ciki wa zai Wauko zancen aure, duk da ya kasance auren sadaka ne, amma ai muhallin da mutum zai zauna shima ba ?aramin jidali bane, shi kuma wani cewa ya yi "Inda cikin ?annenta ne da yana so" haka dai kowa ya din ga fadar albarkacin bakinsa, daga ?arshe aka bawa kawu Sanusi ha?uri, tare da addu'ar Allah ya fito musu da mijin aure.

Baba wani irin takaici ne ya kama shi, ya ji gaba Waya ya muzanta, wai ?arsa Afnan ce kowa ya ce baya so, sai ka ce mai wata ba?ar kama, yarinyar dake da farin jini, ga ta kyakyawa, tsananin damuwa yasa ya tashi ya riga Kowa fita daga masallacin, ko huWubar da ake yi bai tsaya saurara ba.


Bayan kawu Sanusi ya dawo daga masallaci, ya je gaishe da Gwaggo, sannan ya faWa mata duk yanda aka yi, shiru tayi ta na nazari sannan ta ce "Anya Sanusi wannan abin ba shiryawa kuka yi ba kai da Wan ladi ba? tukunna ma ina Wan ladin yake?" . Kawu ya ce "Ai ya riga ni dawowa, tun Wazu shi ya dawo" .

"Au ya dawo amma shi ne ya gagara biyo wa ya gaishe ni? eh lallai ya nuna mini bai ji daWin abin da na yi ba, kai kuma Sanusi ka faWa mini gaskiya anya babu wata ?ullaliya ko? saboda na yi mamakin abin, wai kun faWi yarinyar kuwa?" .


"Haba Gwaggo ta ya ki ke tunanin za a haWa kai da ni a munafunceki, wallahi na yi maganar, kuma Ai'sha na ce musu".

Gwaggo ta ce "Ikon Allah ina ga dai yarinyar nan ?auye zamu aurar da ita, kowa ma ya huta" .



*******


?arfe takwas da rabi Hudah tayi shirin zuwa school, ?awarta Nusee ta kira bayan ta Waga babu sallama ba komai ta ce "Sis ki na gida ne?" Nusee ta ce "Eh lafiya dai?" "Ina fa lafiya ganinan zuwa yanzu" "Ok sai kin zo". Ko da Mami ta ga Hudah ta shirya, mamaki ne ya kama ta, saboda Hudah ba ta son zuwa makaranta a kan lokaci, amma wai yau ita ce ta shirya tun lokacin zuwan su bai yi ba, saboda ta ce mata sai ?arfe tara da rabi zata je, dubanta Mami tayi ta ce "Daughter yau ke ce da shirin makaranta tun lokacin zuwan na ki bai yi?".

"Eh Mamina kin san yau zamu fara jarabawa ne, sannan kuma akwai abubuwan da muke son dubawa ne ni da Nusaiba, kin san ita Win she is brilliant shiyasa na shirya da wuri".


Mami ta ce "Haka ne to Allah ya ba da sa'a ya taimaka"

Ta ce "Amin Mamina ni dai, zan yi missing Winki sosai, kafin na dawo, i feel sad with out you".


Murmushi Mami tayi ta ce "Haba daughter, sai ka ce wadda za ta yi tafiyar kwanaki, yanzu dai ki tashi ki karya, sai ki wuce". "To Mami".


******


Tunda Baba ya dawo daga masallaci, ya shige Waki bai fito ba sai yanzu, Mama ta so tambayarsa akan maganar Afnan, sai kuma tayi shiru gudun kar ya rufeta da faWa, ta san koma me ye za ta ji.


Kawu sanusi ne ya shigo da kansa, ya ce masa "Ya zo Gwaggo ta na kiransa" sai a lokacin ya tuna da bai je gaisheta ba, da sauri ya bi bayansa.


Cikin ladabi Baba ya ce "Gwaggo barka da safiya ina fatan kinsha lafiya?" "Lafiya ?alau, wato inda ban aika a kirawo mini kai ba kenan ba zuwa zaka yi ka gaisheni ba?" . Ba haka ba ne Gwaggo Wazun raina ne a Sace shiyasa" "Me ye zai Sata maka rai? bayan dama haka kuke so, kai da iyalin na ka, to bari ka ji tunda na yi niyyar sai an yi wa yarinyar nan aure a yanzu, wallahi ba wanda ya isa ya hana sai Ubangiji da ya halicce ni. Dan haka zan yi waya da ?an uwana na can ?auye, su bincika cikin dangi a samu wanda za a haWa su aure".


Baba ya ce "To Gwaggo ba ni da ja akan umarninki, duk abin da ki ka ce haka za a yi, Allah yasa hakan shi yafi alkhairi".

Kawu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login