Showing 30001 words to 33000 words out of 52998 words

Chapter 11 - RAMIN ƘARYA HAUSA NOVEL

24 Oct 2025

87

da ta minti biyu ce, kar ki ce zaki share ni, zuciyata ba za ta iya jurar hakan ba, Afnan ki sani wallahi ba ni da wasu kalmomi ko ma auni da za su iya bayyanar da son da na ke yi miki, ni dai ina sonki, ina ?aunarki, ba zan gaji da furta miki wannan kalmar ba, saboda ke ce burin zuciyata, farin cikina, cikar mafarkina, wallahi Afnan matu?ar ba za ki iya ?irga teku ba, to ba zaki iya ?ididige adadin son da na ke yi miki ba. Tunda ya fara magana idanuwanta suke a lumshe, ta kasa ?wa?waran motsi, banda luguden dakan turmin amare babu abin da zuciyarta ke yi.


A hankali Haidar ya kuma kiran sunan ta, buWe idanuwanta tayi cikin sanyayar muryar ta ce "Na'am"

"Kin bani damar ne? ina so zan tambaye ki"

"Eh ina jinka"

"To ina godiya da wannan damar. Afnan dama tambayar da zan yi miki akan zancen da na yi miki ne, ina fatan baki manta da maganar da na zo miki da ita ba? tun lokacin da na bar ?ofar gidan ku na ke cikin zulumi da fargaba, saboda ban san wane matsayi zan samu a gurinki ba, Afnan ina fatan zuwa yanzu kin gama yanke shawararki a kaina? ina son sanin matsayina, ina fatan na samu gurbi a zuciyarki ko da kwatar wanda ki ke da shine a zuciyata".


Shiru tayi ta rasa abin da za ta ce masa.

"Bab ki yi magana mana"

Wani tari ne ya tirni?eta jin ya kirata da Bab take ta katse kiran, ta na mayar da numfashi, a fili ta ce "Ya Allah, wai me yake shin faruwa dani ne?" kallon wayar tayi ta na jijjuyata, ?arar shigowar sa?o ta ji, ko da ta duba shi ne.

"_Please Afnan ki tausayawa zuciyar da ta mato a kanki, rashin samun amsarki zai iya saka zuciyata wani hali, ki sani cutar sonki ba ta da magani a gurin likita sai dai ke. Afnan duk abin da zaki yi mini ba zan iya ja baya a soyayyarki ba, a duniya duk wanda ya same ki a matsayin masoyiya wallahi ya gama yin babbar nasara, a rayuwar shi, domin kin kasance mace wadda ta mallaki duk wani abu da ake bu?ata a gurin nagartacciyar mace, samunki ba ?aramar nasara ba ce a rayuwata_".


Ta maimaita sa?on yafi a ?irga, ta rasa ta ?amammen abin da zata ce masa, yanzu babban abin da yafi damunta bai wuce tsanarsa data ke ji ba, tarasa dalilin hakan, har zata a jiye wayar, sai taga rashin dacewar ?yaleshin da tayi, amsa ta tura masa.

"_Ka ?ara bani lokaci_"


Haidar na ganin amsarta, ya yi murmushi, tare da maido mata da

"_To gimbiyata duk yanda ki ka ce hakan za a yi_"

Ya na gama tura mata kiran mai gidan shi na shigowa, Wauka ya yi bayan sun gaisa ya ce "Haidar kayana sun iso yanzun nan, kuma gashi ba na nan dan Allah ina son ka je a sauke su a gaban idonka, ka saka ma sauran yaran ido sosai, ka yi sauri Allah yasa ban takura maka ba, gashi yamma tayi" .

"Tauyayi mai gida, a'a babu takura, bari na hanzarta na je"

"To shikenan, ina ga gobe ma zan dawo, amma sai na biya wani gurin kafin na iso gida".

"Ma sha Allah, tafiyar ba mai daWewa ba ce, Allah ya dawo da kai lafiya". Da Amin ya amsa, sannan suka yi sallama.


Mai gari ya dubi sarkin fada ya ce "Sarkin fada ina muka kwana akan zancen auren nan? maganar ta na nan ne? saboda ina so gobe idan Allah ya kai muna rai bayan sallan juma'a a Waura auren nan" .

"Ranka ya daWe ta na nan, dama ina jira na ji daga gareka"

"To shikenan, gobe idan Allah ya kaimu sai a Waura auren, zan sanar da iyayen yarinyar" da Amin sarkin fada ya amsa.

Bayan isha mai gari ya kira kawu Sanusi, ya nemi ya haWa shi da Gwaggo, kai mata wayar ya yi bayan sun gaisane ya ce "Halima dama akan zancen auren A'isha ne, in Allah ya kai muna rai gobe bayan sallan juma'a za a Waura auren, hakan ya yi, ko ki na da wata shawara ne?" "Ma sha Allah, Yaya amma na ji daWin wannan maganar, ba ni da ja akan duk abin da kace, Allah ya kai muna rai".

"To shikenan, sai ki sanar da su Abbakar Win domin su zo da wuri a yi komai da su" "In sha Allah za su zo na gode sosai Yaya, Allah ya bar zumunci" . Da amin ya amsa, bayan sun gama wayar ta dubi Sanusi ta ce "Ka ji duk yanda muka yi da shi ai?"

"Eh Gwaggo na ji" "To ina so ka yi shiru da bakin ka, ko Wanladi bana son ya sani, sai bayan an Waura auren, saboda ya na sani zai gayawa matar shi, ni kuma ba na bu?atar hakan, na fi so sai dai ta ji ance Waukar amarya za a yi, ka shirya gobe tunda safe ka kama hanya ina son a yi komai a gabanka"

"To Gwaggo wannan shawara taki tayi, tun yanzu zan fara shiri".

"Yawwa Wan albarka tashi ka je, sai da safe Wun".


WASHE GARI

Tunda safe kawu Sanusi ya yi wa Gwaggo sallama ya kama hanya.


Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA....* =ث?




Story & writing

By

Mrs Muttala (Amanar cool)




*YOUNG TALENT WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*




Sadaukarwa ne ga Aysharcool




Free book
'?



Page 29&30



__________Misalin ?arfe goma na safe Alhaji Munir da iyalinsa suka zo duba jikin Ammi, a falo suka tarar da su, Abba na bata shayi a baki, zama suka yi, tare da gaisawa, sannu da jiki suka yi mata, Sharifa ma gaisheta tayi, ta na sunkuyar da kai ?asa, ganin Abba kusa da ita kamar zai shige jikinta, basu daWe da zama ba sai ga Mami ta shigo, zama tayi ta na yi wa Ammi sannu da jiki, ta gaida Alhaji Munir, sannan ta dubi Fatima ta ce "Hajiya Fati barka da safiya, ya ki ke ya gida?"

"Lafiya ?alau Alhamdulillah, fatan mun same ku lafiya?" "Alhamdulillah mun gode Allah, za a ce".


Sharifa a dole ba dan ranta ya so ba, ta ce "Barka da safiya Mami" sai a lokacin Mami ta lura da Sharifa dake zaune a ?asa ta laSe gefen kujera, "Ah Daughter ashe tare kuka zo? ai ban lura dake ba, lafiya ?alau, ya ki ke ya karatu?" . Tayi maganar cikin iyayi wai ita mai sirika.


Ta amsa mata da "Alhamdulillah"

"To ma sha Allah, Allah ya taimaka, tashi a ?asa mana ki hau kujera" ?ara sunkuyar da kai tayi, ta kasa tashi. Abba ya dubi Mami ya ce "Ina Mudan da Huda? suma yakamata su zo" "Huda na Wakinta, shima haka, bari na kirasu".


Mudan na kwance abin duniya ya dame shi, tunda Huda tayi masa zancen ta na da ciki ya ke cikin fargaba, da tashin hankali, ya kasa sukuni, sannan ya na son sanin gaskiya ne ko dai ta faWa ne, dan ta Waga mishi hankali, to amma ai ba abin mamaki bane dan ta ce ta na da juna biyu, lumshe idanuwansa ya yi, ya na jin zuciyarsa na ?ara buWewa, ba?on al amarin da yake ji a tattare da shi na ?ara kutsa kanshi a cikin zuciyarsa, ?ara rufe idanuwansa ya yi, hoton fuskarta ne yake yi masa gizau. ?arar kiran da ya shigo wayarsa ne ya sa shi buWe idon, Mamina ya gani a kan fuskar wayar, Wauka ya yi, ya ji ta ce "Ka zo Sangaren Zainab yanzun nan" daga haka ta kashe wayar, tashi ya yi, ya fita.


Huda ma Mami ta kirata, ba dan ranta na so ba, haka ta nufi sashen ita ma. Ita ta fara shiga da sallama, amsawa suka yi, ta gaishesu ta nemi guri akan kura tayi zamanta, idonta ne ya sauka akan Sharifa, nan take ta ji zuciyarta na mata zafi da raWaWi, wani irin azababben kishi ta ji ya na ta so mata. Muryar Mudan ta ji, yana gaisawa da su Abba, sannan ya gaida Ammi da Momyn Sharifa, shima zama ya yi, sarai ya ga Sharifa amma sai ya yi banza da ita kamar bai ganta ba, saboda a yanzu ko fuskarta baya son gani.


Abba ya ce "Mudan ba ka ga ?anwarka Sharifa ba ne? na ga baku gaisaba". Dady ya ce "Ai ita yakamata ta fara gaisheshe, tunda ita ce ?arama" dariya Abba ya yi, ya ce "Ina ga kunyarmu suke ji ne, bari muyi musaka ranar bikin nan da wuri". Mami ta ce "Lallai kam gara a yi a gama, ba sai an saka dogon lokaci ba" Daga Huda har Sharifa da kuma uban gayyar Mudan, kowa da abin da yake ji kuma yake sa?awa a ransa, cikin takaici da kishi Huda ta ce "Mami zan iya tafiya?" "Ki tafi ina? bayan duk ga ?an mu a nan, wato kin fi so ki je ki ?unshe kanki a Waki kamar wata amarya? to ba inda zaki" . Kamar ta zunduma ihu haka take ji.

Sharifa kuwa ji tayi zaman falon ya isheta gaba Waya, mi?ewa tayi ta nufi hanyar bedroom Win Ammi, Mami ta ce "A'a Sharifa me za ki yi a Waki? ki fa saki jikinki, ki daina jin kunyar mu, mu fa iyayenki ne ba surukai ba, dawo ki zauna ?ar albarka". Ba yanda ta iya haka ta dawo ta zauna, Huda sai binta take yi da wani mugun kallo, su Ammi na lura da hakan, sannan sun san cewar zancen auren yasa Sharifa za ta bar falon.

"Ni dai Abba da za a bi shawarata a daina zancen auren nan gaba Waya, a ha?ura da maganar" Mudan ne ya yi wannan maganar, ya na kawar da kai gefe kamar ba shi ya yi ba.


"Kai Mudan wace irin magana ce wannan? akan wane dalili zaka ce a fasa auren? bayan da bakinka ka ce mini ka na sonta?" Abba ya yi maganar fuskarsa a murWe babu alamar wasa. Shiru ya yi bai yi magana ba, cikin takwaici da jin haushi Mami ta ce "Ba magana ake yi maka ba? wannan ai iskanci ne da rainin hankali, dan ubanka tun farko da a ka zo ma da zance mai yasa baka ce a'a ba sai yanzu?".

Dady ne ya yi gyara murya ya ce "Ku bi shi a hankali, a ji ta bakin sa, kai Mudan me yasa ka ce a fasa auren" .

"Dady ba komai, kawai ni dai ba na son auren ne, a yi ha?uri, a bar wannan maganar, dan Allah".


"Wallahi Mudan baka isa ba, ka yi kaWan, ni za ka kunyata, auren ne ba ka so? saboda shashanci, to muddin kaga ba a yi auren nan ba sai dai in ita Sharifar ce ta ce ba ta sonka" Mami ta ?are maganar cikin masifa da Waga muraya. Sharifa da Momy wani irin farin ciki ne ya mamaye su, sai hamdala suke yi a zuciyarsu, Huda ko da ta na da halin tashi ta taka rawa da tayi, rabon da ta ji farin ciki a zuciyarta tun kafin ?ulluwar wannan maganar. Ammi kuwa sam ba ta ji daWin abin da Mudan ya ce ba, duk da ta san Sharifa da Mamanta ba son auren suke yi ba, amma ta so a yi auren ko Allah zai sa Mudan Win ya yi hankali ya rage wannan yawon da yake yi.


"Mudassir"

"Na'am Abba"

"Me yasa tun farko da na yi maka maganar baka nuna rashin amincewarka ba sai yanzu?"

"Abba a lokacin ina jin sonta ne a raina"

"To yanzu fa? ba ka sonta ka ke nufi ko me?"

"Abba dan Allah ka yi ha?uri, ba wai rashin kunya ce zan yi maka ba, ba kuma nuna mak??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a cewar baka isa ka bani umarni ba ne, Abba a yanzu ina da wadda nake jin sonta a raina..." bai ?arasa ba ya ji saukan mari a fuskar shi, Mami ce cike da ba?in ciki ta ce "Rufe mini baki, sakarai mara hankali, ana ?o?arin yi maka gata ka na yi wa mutane iskanci da shirme, to matu?ar ni ce uwarka Sharifa za ka aura". Dady ya ce "Saratu koma ki zauna abin duk bai kai haka ba. Zama tayi ta na ciga ba da masifa shikuma uban gayyar ko a jikinsa.

Dady ya dubi Sharifa ya ce "Ke ki faWa mini idan ke ce ki ka masa wani abin? ko ki ka nuna masa ba kya sonsa"

"Wallahi Dady ba abin da na yi masa, kuma ni ban ce masa ba na sonsa ba, ai gashi nan da bakinsa sai ya faWa" Abba ya ce "Kama bakin ki Sharifa, ai dama na san ba za ki ce haka ba, kuma shima ya bani mamaki, amma ba komai, tunda har ya iya dubin idonmu ya ce baya so, to tabbas ba za a yi auran ba, gara da ka faWi tun kafin a yi auran a zo ana samun saSani, dan haka na janye wannan maganar, auran dole baya cikin tsarina, Allah ya fito mata da wani mijin, kai kuma ya haWaka da wadda ka ke so Win".

"Haba Alhaji ya za ka ce haka, dan me za ka biye masa, shi Win banza, ai bai isa ba" Mami tayi maganar kamar za ta yi kuka.

"Haba Zainab ya isa mana, shi fa zai zauna da ita, sannan ya ce ya na da wadda yake so, to gara abar shi ya aure wadda yake so Win, daga yanzu ina son abar wannan maganar kar a ?ara ta da ita". Duban Mudan tayi da yake ta murmushi ta ce "Ka kyauta Mudan, kuma da ni ka ke zancen, sai na ga wadda zai aura maka wadda ka ke so Win" ta na kai wa nan ta mi?e fuuu ta bar falon, Huda ma bin bayanta tayi, ta na jin kamar an yi mata albishir da aljanna, shima tashi ya yi kamar wani munafuki sum-sum ya fita.

*********


Afnan da wani matsanancin ciwon kai ta tashi, da ?yar ta iya fitowa waje, ga wata kasala da ta take ji, gaba Waya ba ta jin daWin jikinta, Mama na zaune, ita ma zaman tayi, Mama ta dube ta ta ce "Lafiya dai? na ganki haka kamar wadda aka zarewa jijiyoyin jiki" "Mama kaina ne ki mini ciwo, sannan ba na jin daWin jikina" "To Allah ya sauwwa?e, tashi ki je Wakina ki duba akwai maganin ciwon kai na nan, ki sha" amsawa tayi da "To" sannan ta mi?e ta Wakko maganin ta sha. Bayan ta sha ne ta ce "Mama ina Maryam?"

"Ta na Makaranta, ba ta dawo ba, ina ga matsalar abin hawa ne, tunda yau juma'a ce ba daWewa suke yi ba". "Eh haka ne kuma"


Inna Hajara ta zo har Wakin Gwaggo, bayan ta zauna ta ce "Gwaggo wai ni ko mai Sanusi ya je yi a ?auye? na tambaye shi ya yi mini shiru, da ga baya ya ce idan ya dawo koma minene zan ji" "Eh ni ce na umarce da hakan, saboda ba na son kowa ya sani sai komai ya kammala" Hajara ta ?ara lan?washe kafa ta karye muraya ta ce "Gwaggo faWa mini mana ba wanda zai ji, ai kin san ni ba irin sauran ba ne". "Hajara ki yi Ha?uri zuwa anjima zaki ji koma minene, akwai abin da nake shiryawa ne akan wa?ancan yaranne" Hajara ta ji haushin rashin faWa matan da ba ta yi ba, amma da ji ance akan su Afnan sai ta ji sanyi a ranta, nan ta fara aikin na ta na ?ara ruru wutar ?iyayyar su a zuciyar Gwaggo.


Sai wuraren ?arfe Waya kawu Sanya isa ?auyen, an yi masa tarba mai kyau, Mai gari ya ce "A'a ya muka ganka kai Waya ina shi Abbakar Win?"

"Ai ba zai samu damar zuwa ba ne, ya na da wani babban uzuri ne, shiyasa ya ce ni na zo, ai na wadatar tunda dama ni ne ma Waurin aurenta"

"To ya yi ba damuwa, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, yanzu sai ka shirya saboda lokacin zuwa sallan juma'a ya yi, kowa da shirinsa zai je, ana idarwa sai a Waura auren"

Shiryawa kawu ya yi gaba Waya mutanen gidan kowa ya shirya, suka nufi masallaci, dama ansanar da jama'a tun jiya cewar akwai Wauren auren da za a yi bayan an idar da sallan. Sarkin fada ma ya zo da ?an uwan shi.

Bayan sallan juma'a ne, jama'ar suka shaida Wauren auren Afnan wanda kawu Sanusi ne ya bada aurenta akan sadaki dubu hamsin.

A dai-dai lokacin gaban Afnan ya buga da ?arfi, haka kawai sai ta saki kukan da ba ta san dalilin yinsa ba, daga Mama har Maryam da kallo suka bita, suna mamakin me ya sakata kuka kuma.


Ina Hajara na zaune ta ji ana kiran wayarta kawu Sanusi ne, ta na Wauka ya ce "Hajara kawai Gwaggo wayar" ba Sata lokaci ta kai mata, Gwaggo na amsa ya ce "AnWaura yanzun nan" guWa Gwaggo ta rafka sannan ta nufi sashensu Afnan Win

Ganin kukan na Afnan ya?i ?arewa yasa Mama ta ce "Ke wai wane irin abu ne haka za ki saka mutane a gaba ki na kuka babu laifin zaune ba na tsaye"

"To Amina ai dama duk wanda ya tsinci kansa a irin wannan ranar dole ne ya shiga wannan yanayin, kuma ya yi kukan rabuwa da gida". Juyawa suka yi suna kallon Gwaggo dake maganar ta na yi musu murmushi.



_Gaskiya zan daina yin posting Win nan, saboda rashin comment, comment Winku shi ke ?ara mana ?arfin gwiwar yin typing. To ba kwa yi, dan haka zan daina yi._


Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA....* =ث?



? ? ? ? ?

_WRITING BY AMANAR COOL CE_
'?
??




*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*




Sadaukarwa ne ga Aysharcool



Free book =???



Page

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login