Showing 42001 words to 45000 words out of 52998 words

Chapter 15 - RAMIN ƘARYA HAUSA NOVEL

24 Oct 2025

91

na son a zo ana jira, kuma kin ji abin da na faWa miki". Ta na gama faWar haka ta bar wurin.

Baba ya mi?awa Mama maganin da ya zo wa Afnan da shi, sannan ya ce "Sai ta tashi ta shirya" da ga haka bai ko tsaya ba, ya juya ya fita.


Kuka Afnan take yi ba na wasa ba, Maryam ma kuka take, Mama kuwa Waki ta shiga ta kasa fitowa sai tausayin ?arta take ji, banda sharar ?walla ba abin da take. Da ?yar Bilki ta lallaSa Afnan ta tashi ta shiga wanka sai kuka take yi.


Gaba Waya unguwa ta Wauki anyi wa Afnan auen sadaka a ?auye, sakamakon kawu Sanusi da yake ta yaWa maganar a waje.


Sai yau Feena take samun labari, babu shiri ta zo gidan su Maryam, sai dai jikin ta ya yi san yi ganin Maryam Win na kuka, ita ma kukan ta fara.

Gwaggo kuwa da kanta ta bi ma?ota ta na sanar dasu batun auren Affan, sannan ta ce duk wanda ke samun zuwa ya shirya a je kai amarya da shi yanzu nan, sai dai a gidan Yayan ta ne za a kai ta, kafin mijinta ya ida gyara wurin da za a sakata. Mutane da son gulma nan fa suka ce za su je, sai dai wasu daga ciki mazan su ba su bar su ba, duba da tafiyar ta bazata ce.


Cikin abin da bai fi awa Waya ba, su Baba suka kammala duk wani abu da Gwaggo ta ce, sannan suka biWo babbar motar nan mai Waukar mutum goma sha takwas.


A lokacin Afnan tayi wanka ta sanya doguwar rigar atamfa, da hijabinta, banda kuka ba abin da take, Mama ma kukan take yi, ta na mamakin wannan aure haka ace babu komai da ango kewa amarya, babu kayan lefe, sadaki gashi basu ganshi da idonsu ba.


A ?ofar gidan motar ta tsaya a nan ciki suka bar kayan, suka shiga ciki, kai tsaye inda Gwaggo suka nufa, cikin murna ta fito da sauran kayan, ta mi?awa Hajara, ta ce ta kai mota. Ita kuma ta nufi wurin su Mama.

Ta na zuwa ta ce "A fito da ita ga motar nan ta iso". Babbar Yayar Mama ta ce "Haba ai kya bari ta gama ganawa da uwarta"

"Wace irin ganawa kuma, bayan duk tsawon lokacin da suka yi tare, dan Allah ban son Sata lokaci, ku fito da ita".


Afnan jin hakan ta ?ara riri?e Mama ta na kuka "Ta ce Mama dan Allah ka da ki bari a tafi da ni, Mamata ki yi mini addu'a".


Itama Mama cikin kuka ta ce "Afnan ki je Allah ya na tare dake, Allah ya baki ha?uri da juriya a gidan auren ki, Ubangiji ya wanzar da kwanciyar hankali a cikin rayuwar auren ki".

Gwaggo ganin Afnan ta ?i fitowa ya sa ta shiga Wakin da ?arfi ta jawo Affan ta na kuka ta yi waje da ita, Inna Bilki da su Maryam da ?awarta sai Bahijja da Aunty Murja yar Mama gaba Waya suka mara mata baya. Haidar na gefe cikin napep Win sa zuwansa kenan ya ga an fito da Afnan ta na gunjin kuka, an sakata a mota, su Maryam ma duk sun shiga motar da sauran mutanen da ke wurin.

Kawu Sanusi ne a gaban motar, Baba na tsaye ya na musu fatan sauka lafiya. Duk da ?asan zuciyarsa wani irin zafi yake ji, bayan mutane sun gama shiga motar ta tashi Gwaggo na Waga musu hannu har sai da mutar ta bacewa ganin ta, sannan ta kuma ciki.

A hankali Haidar ya sauke a jiyar zuciya ya ta da napep Win sa ya bar wajan.



Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA....* =ث?




_WRITING BY AMANAR COOL_
'?




*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*




Page 41&42




___________Mama kuwa kuka take yi sosai, irin kukan nan mai taSa zuciya, tunda Gwaggo ta ja Afnan ta fita da ita, gaba Waya ta rasa me yake yi mata daWi. Baba ne ya shigo ya tarar da ita cikin wannan ya na yin.


Zama ya yi, ya rasa me zai ce mata, domin shima abin na damunsa a zuciyarsa.


Kallon Mama ya yi da ta ke kuka ba tare da ta kula shi ba, tabbas tunda har Amina ta kasa danne kukanta ya san wannan al'amarin ba ?ara min taSata ya yi ba. Duk ha?urin ta amma yau ita ce ke wannan kukan.


Ya na so ya bata ha?uri amma ya kasa, gashi dai kukan na ta ba ?aramin Sata masa rai yake yi ba. Ganin ba daina kukan za ta yi ba, shi kuma ya na son bata ha?uri amma kamar an Waure masa baki ya kasa magana

Ya sa ya mi?e ya bar mata Wakin.


?ara fashewa tayi da kuka, ta ce "Ya Allah ka dube ni, Ubangiji ka shiga lamurrana da na ?a,?ana. Ya Allah ka kula mini da ?ata. Allah kashiga lamarin ta, ka kare ta daga dukkan sharri na mutum da aljan".

Ta ?are addu'ar ta na kuka ba na wasa ba.



Ikon Allah ne ya kai Haidar gida, da ?yar ya fito da ga cikin napep Win ya shiga gida, babu kowa a tsakar gidan Umma na Waki, kai tsaye Wakinsa ya buWe ya shiga kwanciyar rub da ciki ya yi, ba abin da ke yi masa yawo a idanuwansa sai fitowar da ya ga an yi da Afnan ta na kuka an sakata a mota, kenan da gaske an yi mata aure? Ji ya yi gaba Waya dubiyar na juya masa, ya rasa inda zai saka ransa, ya ji sau?i da raWaWin da yake ji, ?irjinsa zafi yake yi masa ba na wasa ba, zuciyasa na bugawa da ?arfi, wata irin fitinaniyar soyayyar Afnan yake jin ta na barazanar tafiya da numfashinsa.


Umma jin motsi ya sa ta fitowa

?akin Haidar ta gani a buWe, da mamaki ta ke bin Wakin da kallo, ta na tunanin me ya dawo da shi gida a irin wannan lokacin, kuma bai nemeta ba.


?akin ta nufa da sallama ta shiga, a kwance ta ganshi, ta daWe tsaye ta na ?are masa kallo, da ta ga alamar bai ji shigowar ta ba, dan ko sallamar da ta yi bai amsa ba, ya ta ce


"Haidar"

Shiru bai amsa, kuma bai motsa ba.

Ta kuma ce wa

"Haidar" nan ma Shiru

?arasawa tayi ta bubbugi ?afan shi, ta ce

"Haidar" da Wan ?arfi, sai a lokacin ya motsa da ?yar.


A hankali ya juyo, tare da buWe idon shi ya sauke su akan Umma da ta tsare shi da ido, ta na nazarinsa.


"Haidar lafiya ka ke kuwa? Me yake damunka na ga ka dawo gida yanzu? Bayan ba lokacin dawowarka ba ne".


Haidar ya furzar da iska mai zafi sannan ya ce "Umma ba na jin daWi ne"

"Ashsha subhanallah, me yake damunka? Kuma shi ne zaka shigo baka neme ni ba?"

"Ki yi ha?uri Umma ba na son Waga miki hankali ne".


"To kasha magani ne?"


"Eh nasha shi ya sa na dawo gida na Wan kwanta ko zan samu yin bacci". Da ido kawai Umma ke binsa. Ta mugun tausayin Wan na ta, ta na son yin magana da shi amma ganin ba shi da lafiya yasa ta ?yale shi. Ta ce "To Allah ya baka lafiya, ka samu ka yi bacci Win, in sha Allah ciwon kan zai ragu". Tashi tayi ta fita, ta na fita Haidar ya sauke a jiyar zuciya. "Ya Allah kai ka saka mini son wannan yarinyar a zuciyata, Ubangiji ka kawo mini sau?i da salama, Allah ka kawo mini mafita.



Sai bayan la'asar motar su Afnan ta isa, a ?ofar gidan mai gari ta tsaya. Har lokacin Afnan ba ta daina zubar da hawaye ba.

Kawu Sanusi ya fara fitowa, ya na gaisawa da mutanen da ke gurin.


Sauran matan fitowa suka yi, Aunty Murja ta ja hannun suka nufi cikin gidan, da murna aka tarbesu, kai tsaye Wakin Asabe uwar gidan mai gari aka wuce da Afnan. Saura matan kuwa shimfiWa a ka yi musu, sannan aka a jiye musu abinci shinkafa da wake, aka haWo musu da fura tasha nono.

Aka zubawa direba shima aka kai masa

Afnan ma an kai mata na ta, sai dai ko kallon shi ba ta yi ba, daga ?arshe ma tura fuskarta tayi cikin hijabi ta ci gaba da kuka.


Kawu Sanusi ko fada ya wuce ya gaisheda mai gari, suka gaisa da sauran jama'ar wurin


Mai gari ya ce "Sanusi ya hanya? Sannuku da ?o?ari kun sha tafiya, ita amaryar tawa an shiga da ita cikin gida? Ko da yake mijinta ya yi mini ?wace" ya yi maganar ya na murmushi


Kawu ya yi dariya ya ce "Eh an shiga da ita ciki"

Mai gari ya ce "To ma sha Allah, Allah ya sanya alkhairi a cikin wannan auren, ya kauda fita, sarkin fada ga amana nan an kawo muku Allah ya taya ku ri?o, za ta zauna a gidana zuwa jibi in kun kammala gyaran sai ta tare a Wakin ta".

Da Amin aka amsa, sarkin fada ya ?ara yi wa kawu godiya

Sannan mai gari ya tashi domin shiga cikin gida su gaisa da mutanen. Shiga ya yi suka gaisa cikin girmamawa.

Ya ce "Ina amaryar tawa ne?"

Asabe ta ce "Ta na Wakina".


Ya ce "To shikenan bari na ?yaleta yanzu zuwa anjima ma gaisa".

Kawu Sanusi ya ce idan sun kammala su tashi kar dare ya yi musu a hanya.


Aunty Murja da Bilki suka shiga Wakin da Afnan take, nan suka tarar da Maryam da ita suna kuka, zama suka yi suna rarrashinta tare da ba ta ha?uri, Aunty Murja ta ce "Afnan ki yi ha?uri, ki ci gaba da addu'a in sha Allah za ki ji daWin ha?urin da ki ka yi, ki rungume mijinki, ki yi masa biyayya, domin aljannarki ta na ?ar?ashin ?afarsa, ina son ki rungume ?addararki Afnan, haka Allah ya ?addara auren ki zai kasance, dan Allah ka da ki saka damuwa a ranki, gudun jawowa kanki wata matsalar, ki zauna da kowa lafiya, ki yi wa iyayen mijinki biyayya, sannan ka da ki wala?anta danginki na nan".


Kuka sosai Afnan ke yi kamar ranta zai fita, ha?uri ina Bilki ta cigaba da bata, sannan suka ce Maryam ta tashi su wuce ana jiransu, jin hakan ya ?ara Waga hankalin Afnan ta rirri?e Maryam ta na kuka


Asabe ta shigo Wakin ta ce "Wai ku fito ana jiranku, sauran matan har sun fita waje"


Aunty Murja ta ce "To shikenan mun tsaya bata ha?uri ne, gata nan sai ku cigaba da bata ha?uri da rarrashinta, sannan idan aka ji tayi ba dai-dai ba dan Allah ku tsawatar mata".


Asabe ta ce "In sha Allah zamu yi iya ?o?arin mu".


Mi?ewa suka za su fita Afnan ta mi?e ita ma


Kallonta suka yi Bilki ta ce "Ina kuma za ki je Afnan?"


Cikin kuka ta ce "Biyar ku zan yi Inna, dan Allah ku koma da ni". Tayi maganar ta na ci gaba da kuka.


"Haba Afnan ina kuma aka taSa yin haka? Ki dai yi ha?uri, in sha Allah nan da kwana biyu zamu dawo".

?ememe Afnan ta ce ba za zauna ba, sai da aka kira kawu Sanusi ya ce su wuce, dan ubanta ko ?ofar Wakin nan ta ?araso sai ya saSa mata.

Ri?e Maryam tayi ta na kuka sosai ta ce "Dan Allah Maryam ke kar ki ta fi ki bar ni".


Maryam ma ri?e ta tayi ta ce ba inda za ta je ta bar ta, takaici ne yasa kawu ya ce "Ku zo mutafi idan ta iya ita ma ta tabbata a nan Win".


Ba yadda ba a yi da Maryam amma ta ce ba za bisu ba, mai gari ya ce "Su yi tafiyar su zuwa gobe ko jibi dai-dai sun samu nutsuwa sai ta koma, haka aka yi su kawu suka kama hanyar komawa gida.


Afnan ganin Maryam a kusa da ita ya Wan kwantar mata da hankali, ta Wan saki jiki har suka samu cin abinci.


*********

Gaba Waya Mudan ya rasa suku ni a zuciyarsa, soyayyar Hasina ce tayi masa babakere a zuciya, baya ganin kowace mace face ita, komai yake yi tunanin ta ne a zuciyarsa, ge Waya ga fitanar Huda kullun da sabuwar fitana da tijarar da take zo masa da ita, ya rasa yadda zai da ita, gashi ya na kokwanto akan cikin da take i?irarin ta na da shi, shi fa baya jin idan ma gaskiya ne ta na Wauke da cikin ya kasance nasa ne. Dan baya jin iya shi kaWai take bi.


Tashi ya yi ya shiga toilet wanka ya yi a gurguje, ya shirya, makullin motar shi ya Wauka ya fito, in da motar shi take ya nufa, ya ja ya bar gidan. Kai tsaye gidan Turai ya nufa.


Turai na zaune a falo, ita da wata dillaliya, sai Hasina dake saman kujera ta Wora ?afa Waya kan Waya ta na taunar cingam.

Mudan ya yi sallama ya tare da afkowa cikin falon kamar wanda aka je ho.


Turai ta ce "A'a Mudan yau kaine a gidan namu babu sanarwa?"


"Eh Momy ni ne, fatan na same ku lafiya?".
Ya yi maganar ya na ?uwara Hasina ido, da tayi kamar ba ta ganshi ba. Alhalin hankalinta na kansa kawai mazewa ne tayi.


"To ma sha Allah, ka ce yau zumuncin ne ya motsa? To ya ka baro mini Mamin taku da Huda fatan su na lafiya?"

"Lafiya ?alau suke, sunce ma a gaisheki".

Murmushi Turai tayi jin abin da Mudan ya ce, ta sallami dillaliya sannan ta dubi Hasina ta ce

"Ke Hasina baki ga yayankin ba ne? Na ga ba ki gaishe shi ba".

Sai a lokacin ta Wago ta dube ta ce

"Barka da wannan lokacin Ya Mudan"

"Yawwa ?anwata barka ya ki ke?"

"Alhamdulillah" ta bashi amsa .

Turai ta kuma cewa "To ki kawowa Yayan na ki ruwa mana"

Mi?ewa tayi ta je ta Wakko masa ruwa da kofi sannan ta zuba mishi ta mi?a masa.

KarSa ya yi ya sha ruwan kaWan

Turai "Mudan jira ni zan Wan shiga ciki".

"To Momy ba damuwa, sai kin fito". Tashi tayi ta bar falon ta shige bedroom Win ta. Ya maida dubansa ga Hasina ya ce "?anwata hutawa Wai ake yi?".

"Eh" ta bashi amsa ta na Wan basarwa

?are mata kallo ya yi ya ce "?anwata wai ko na yi miki wani laifi ne? Ina magana ana amsa mini sama sama". "A'a, ni kuwa me za ka yi mini kai da ba guri Waya muke ba". "To ai na ga ina magana ne ana basarwa".

"No ba komai kar ka damu, ya Huda?"

"Ta na nan ?alau".

"Ok"

Mudan ya yi gyaran murya ya ce "Hasina wurinki fa na zo"

"Wurina kuma? To Allah yasa ba wani laifin na yi ba?"

"Ina ai ke ba kya laifi, komai ki ka yi dai-dai ne, Hasina magana nake so muyi mai muhimmanci, wato a gaskiya ba zan tsaya yi miki Soyon komai ba, sonki nake yi, kuma so na aure".

Da sauri ta kalle shi ta ce "So kuma ni Win?"

"Eh mana ko akwai haramcin auren mu ne?"

"A'a ko Waya kawai dai ina mamaki ne"

"Me yasa za ki yi mamaki dan na ce ina sonki da aure?".

"No ba komai". "To shikenan Hasina ba na son Sata lokaci ko jan aji irin wanda ku ke yi idan an ce ana sonku, amsa nake bu?ata, shin ki na ga za ki iya aurena?"


"To ka bani nan da kwana biyu zan yi shawara". Mudan na son musa mata amma ya kasa yi mata musun, ya ce "To shikenan, ina jiranki" suka yi musayar lambar, har zai wuce ta ce ya bari ta kira masa Momy suyi sallama. Kafin ya tafi, ya amsa mata da "To".

Ta mi?e ta kira masa Turai suka yi sallama sannan ya bar gidan.

*********


Sai bayan isha su Bilki suka isa gida kowa a gajiye yake, Gwaggo da ta samu labarin Maryam na can ba ta dawa ba, masifa ta shiga yi, ta in da ta shi ba ta nan take fita ba, ta ce dan kawai dare ya yi da sai ta je ta dawo da ita. Mama kuwa da ta samu labarin Maryam na can kasa magana tayi sannan kuma ta Wan ji daWin zaman Maryam Win ko ba komai Afnan za ta ji sanyi idan ta ga ?ar uwarta a kusa da ita.


Da dare mai gari ya shigo gidan ya na faWin "Ina amaryar take ne, ta so ga angonki nan ya zo zai duba ki"

Gaban Afnan ya buga da ?arfi jin an ambaci angonta, ka sa tashi tayi, sai da mai gari ya sake magana sannan ta mi?e a hankali tayi waje.


_A yi ha?uri da in da aka ga typing errors_



Amanar cool ce
'?
08163516796=ث? *RAMIN ?ARYA....* =ث?




_WRITING BY AMANAR COOL_
'?




*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*




Page 43&44



_____________Fitowa tayi daga Wakin ta tarar da mai gari zaune saman tabarma, Maryam ma fitowa tayi domin ganin wanene mijin na Auntyn ta ta, gaishe da shi suka yi, cikin sakin fuska ya amsa, ya na tsokanar su. Ya ce "Wato kin matsu ki ga mijin naki ko? To ai ke A'isha da ni ki ka aura na cike ta huWu dake, dan nafi wannan mijin naki komai".


Afnan murmushi tayi ta na takurewa guri Waya, ta na tunanin ta ina zai Sollo"

Dariya Asabe tayi ta ce "Lallai kam da alama ta matsu da son ganin angon na ta, tunda aka zo da ita ta na Waki ba ta fito ba sai yanzu".

Murmushi ya yi ya ce "A'isha"

Afnan ta Wago ta kalle shi ta ce "Na'am"

"Mijinki ki ke son gani?" Ya yi maganar ya na dariya ?asa-?asa.

Shiru tayi ta sunkuyar da kai, ya maida dubansa ga Maryam da ta yi shiru, ya ce "Ke Inna Isah azumin magana ki ke yi ne? Kin shiru ko ke ma a nan Win za ki yi aure? Ku fa saki jikin ku nan Win gidan ku ne".


Ita ma murmushin tayi sannan ta ce "Wai ina yake?"

"Shi wa?" Mai gari ya tambaye ta.

"Mijin na Aunty mana"

"Gani mana, ni ne angon ai, shiyasa na ce ta firo ga angonta".

Dariya Maryam tayi ta ce "A'a wallahi me za ta yi da tsoho?"??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Mai gari ya ce "Ai gara ni da mijin nata makaho ne fa" ya yi maganar ya na dariya.

Sannan ya kuma cewa "Ta kwantar da hankalinta gobe ba sai jibi za ta je Wakin ta, dan sarki fada ya ce masu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login