Showing 1 words to 3000 words out of 61982 words

Chapter 1 - IG AJEEMAL book1 Hausa Novel

03 Sep 2025

1513

🌴🌴 IG AJEEMAL 🌴🌴
Story and writing by Oum AmReesh ♥️
(Khaleeseart Raeys ✍️)
Free book📚


Book 1

GARGADI
banyarda wani ko wata yayi amfani da wani sashi na littafinaba ko yayi anfani fashi awani waje ko hadamin document ba tareda sahalewataba, koda allah nabar mutum zaibin kaduna,

TSOKACI
wannan littafin k'irk'irarren labarine banyi dan wani ko wataba , nayine dan nishadan tarwa fadakarwa

GODIYA
ya allah yanda nafara rubuta wannan littafin bani daman kammala shi lapia tareda mika sakon da nakeson isarwa,

game neman karin bayani ko bada shawara whatsapp number 08105565439

Face book name:
Khaleeseart Abdullahi Raeys
My group novel
Six novel khaleeseart hausa novel

Bismillah

Kyakykyawar yarinyace matashiya ketafe kan hanya tana ta tika sauri tamkar kafarta zai tsinke, yanda hanna yanta ke rungume da jikinta tana ta rawar sanyi saka makon ruwanda aketa zabgawa, pink lips dinta se rawa yake, yayinda manyan kyawawa idanuwanta maso dauke da hawaye falciki, gari yayi shiru hanya bakowa se takun sawayenta it tab tab, sauri take kamar mai shirin firewa sama, sautin kukantane kakeji yakara tsananta da alama akwai wani abu datake juyawa cikin ranta, kuka takeyi sosai fiskannan yayi jawur dashi ahankali take furta

" innalillahi wa'inailaihi raju'un abunda take ta dada furtawa kenan yayinda take cigaba da tafiya, ita kanta ba tasan inda take jefa kafartaba itade tasan tafiya kawai take , wani razanannen horn ne yaduke dodon kunnenta wanda yasa kyakykyawar yarinyar rudewa da razana,

jikintane yadau rawa idonta daker take budeshi saboda ruwan da ake, cike da kidima tasuma tunanin kwaucewa tareda kokarin yin gefe , akwai batayi auneba sejinta tayi timm tafadi kasa, motar da ta taho yabugeta , allah ya taimaka bata ji wani rauniba, se dan buguwa da tasamu, head dinta yadan bugu ta baya se hand dinta da takwanta akai, wani razanannen ihu tasaka tafara kokarin tamikewa kamar wacce tazauce tana kokarin zurawa da gudu taji anrukota, kafin tayi wani yunkuri seji tayi anwaketa da mari tass, nanfa tarike gefen face dinta tasuma kokarin magana, kafin tace Wani abu se murya ta tsinkayi da cewa,

" hi you wani irin rashin hankali ne yake damunki da zakizo kitsaya inda kikeso, kinzo kinwani tsayawa mutane akan hanya, ko titin na gidan kune,?are you crazy "

yafaɗi yana jijjiga ta, ganin bata bashi amsaba kanta sunkuye yasa, cikin takaici yaja wani guntun tsaki yana fadin,"matsa kibani waje stupid girl look at you da Allah yafada tareda cillata gefe, tunda yafara magana bata dagu ta kalleshi ba kanta na kasa tanata barzar kukanta, yabugeta da mota kuma ya tsaya yana mata wasu surutai, still bata mata time dayayi, daga kai tayi tareda bin bayansa da kallo time din har yashiga mota yayi mata key yayi kanta dashi kamar zai bugeta, nanfa tamatsa dasuri shiko yayi gaba abunsa,

" Allah ya isa ya allah kasakamin " tafaɗi tareda cigaba da tafiyar ta, bata dau lokaciba takarisa gida,,,

kutsa kai tayi cikin gidan dan ko sallama batayiba takutsaciki, kuka takara fashewa dashi yayinda takarisa inda mahaifiyar tata take kwance tafaɗa jikinta,

" umma kitashi mutafi asibitin nan akwai, naje duk inda muke tunanin za asmu Abba but ban sameshiba, har gdn Mami nakuma zuwa baya nan, na tambayeta ina yashiga ina za asameshi Amma secewa tayi itama bata saniba, nashiga ukuna nikam," tafaɗi tana kuka,

"umma ya zanyi please kitashi mutafi "
tafaɗi tareda kokarin dagata amma inaa takasa, bin mahaifiyar tata tayi da kallo idonta ya kafe , still numfashinta ya tsaya cak kamar bacecciya, tashi tayi dasauri tafara yin baya baya tana fadin," a'a umma karkimin haka tafada tana tana sake binta da kallo, inna lillahi wa'inailaihi raju'un tafadi tareda juyawa tayi waje da gudu, a dadaiba tashigo dagudu cikin rudu, gefenta nadauke da wata mata wacce ta taimaka mata suka daga umma suka fito da ita suka kutsata cikin adaidaita,

"NEESHA Allah ya sauwake yabata lapia" matar tafaɗi

" amin nagode "

Nisha tafada tareda tallafe mahaifiyar tata tana mai cigaba da kuka, har cikin asibitin suka shiga, Nisha tafara kokarin kokarin fito da ita, da sauri nurses dinda ke wajan suka suma kokarin taimaka mata, nan suka daurata gadon potien suka turata izuwa ciki domin duba lapiyarta, itama Nisha binsu take tana surutai har aka isu room din da za ashiga da ita , nanfa nurse din suka dakatar da ita suna fadin "tajira anan, jikin sanyin jiki Nisha tazube saman gwiwowinta tashiga rera kuka mai tsuma rai,

Doctor ne yakunna kai zai shiga cikin room din cikin hanzari Nisha ta tareshi tana fadin," doctor dan allah ka cece ran mahaifiyata ita kadae garan karka please karkabari tamutu.., bata kai ga marishe batuntaba, doctor yayi saurin cewa,

" haba baiwar Allah kefa musulmace kizama mai hakuri mana ran mahaifiyar ki ba ahanunmu yakeba agurin allah yake duk yanda yaso zaiyi ikonsa, ki roki Allah yafito da ita lapia, mukuma zamuyi iya kokarin gurin cetota daga hadari, don't worry comforting you mind " yana gama fadi hakan yakunna kai cikin room din,

"Hasbunallahu wani'imal wakil" abunda ta faɗi kenan takuma zubawa kasa tahada kai da gwaiwa tana cigaba da kuka kasa kasa, jitayi kanta yayi bala'in sarawa yakuma yimata nauyi seyanzu ta tunada da abunda yafaru da ita dazu,
shafa goshinta tayi inda kanta yadan fashe tana sake fadin allah ya isar mata, wasu sabbin hawaye ne suka shiga sakeyin zarya saman face dinta, tana cikin wannan yanayin taji ana faɗin,

" baiwar Allah tasu muje ko?" da sauri Nisha ta dago tana kallon nurse din da ke tsaye kanta, tashiga faɗin,
" yauwa ya umman nawa take tabude ido tana cikin koshin lapia,? "nurse din batace kalaba se jan hand din Nisha datayi takaita dressing room ta zaunar da ita, tashiga mata dressing wajan da taji ciyo agoshinta dayake dan fidda jini, seda ta kammala gyara mata ciyon nurse din tasuma kokarin mikewa,

" bakice min komaiba" Nisha tafaɗi tana kallon nurse din, itama kallonta nurse din tayi tana faɗin,

" sorry doctor zaizo yamiki bayani karki damu" nurse din tafaɗi tareda ficewa, bata dade da fitaba doctor ya shigo room din, zuro taimasa da ido yayinda yake karisuwa ciki,

" yadai ?

yafaɗa yana kallonta, bata cemasa koamiba se tambayar ummanta da take, shima baice wani abuba se cewa yayi tabiyoshi office yamata bayani yana faɗin haka yajuya itama bayansa tabi yana shiga office din yazauna bisa kujera itama yama nuni da tazauna, bai musuba ta zauna kamar yadda yace tana mai kallonshi, shima kallon nata yayi tareda dauko wani file ya ajiye agabansa yana kallon Nisha da itama kallon nasa take,

" bakida dan uwa namiji ko mahaifinki kode wani naki? shiru Nisha tadanyi daga bisani tace

"babu ni kadaice dagani se mahaifiyata"

" okay no problem" Doctor yafaɗi yana dan gyara zama, cikin kagowa da sun sanin halinda mahaifiyarta take ciki Nisha tasuma faɗin,

" bakace min komaiba gameda ummataba , kode tamutune , kafadamin tamutune ko tana raye"
gyara murya Doctor yayi yashiga bata amsa da cewa," mahaifiyarki tanada rai amma a hanlida ake ciki yanzu tana cikin mswuyacin hali mahaifiyar ki tana da hauwan jini ga jiwon zuciya , amma ayanzu duk wannan bayida wani nasaba da halinda take ciki ayanzu, kodar mahaifiyar ki yasamu matsala duk2 za amata aiki kuma ba asu aikin yaja dugun time, ana bukatar kudi so ina bukatar sa hanun ki anan" ya mika mata wani file, tunda yafara magana daga inda take tagagara kwakwaran mutsi se hawaye kawai, daker ta iya sa hanu ajikin takardan ta dago ta kalleshi,

"doctor kudin harnawa ake bukata?"
numfashi yadanja kafin yace,

" 5 million naira, because fitar da ita waja mukeson yi (indian)

"nashiga ukuna wlh doctor ko dubu 10 bamudashi ayanzu balle wadannan kudaden daka lissafomin yanzu, wayyo ya zanyi" tafaɗi tareda mikewa da sauri tayi waje da gudu batareda taji mai zai kara faɗiba, tana fita bata zame ko inaba sae gd,

tana tafe tana kuka tareda tunanin ina zata samu wadannan kudaden, to mesukeda shi da zasu sayar susamin wannan kudin to ko gdnsu suka sayar bazasu sami wadannan kudinga da wannan tunanin ta tsaya cak ta tsaida mai adaidaita sahu, tamasa bayanin inda zata, basu dau wani lokaciba hanya ta kawosu gd, nan ta sallameshi tashiga gdn, shiganta keda wuya tajiyu sautin muryoyi daga cikin gdn, dasauri takarisa ciki..,

tsayawa tayi tana karewa tsakar gidan kallo ganin yanda akayi kace kace dashi, yansu dake daki duk anfito musu dashi waje, wasu gardawan samarine suketa fito musu da kayan suna wula kanci dashi, gefe kuwa ta hangi matar abbanta wacce ake kira da Mami, waro ido tayi sosai dan ta tabbatarda abunda idonta yake gani gskyne ko karya, tabbas bakarya bn, mami ce daga nise tsaye ta hade hanu akirji se wani jijjiga take tana hararo Nisha tana fadin,

" in kingama kallon banzan naki sekizo kifara kwashe muku komatsan kayan naku kifara muku gaba dashi kusan inda dare yamuku dan wlh bazaku kara kwana gd nanba, Zama yakare muku daga yau,,"
da sauri Nisha takarisa inda mamin take tana faɗin,

" wai mai kike fadane ? incede nan gdn gdn mune halak malak bafa haya muke ba gdn mahaifinane to meyasa zamu bar gdn kuma,? ina mukedashi wanda yafi nan " cikin kuka Nisha tafadi kasa tareda kama kafafuwan mami tana fadin,

" dan Allah inda wasa kike kidena yanzu haka umma tana asibiti batada lapia kuma haryanzu banga idon abba,...bata kaiga karisa maganartaba taji ta fincikota ta dauketa da mari tass,

" lallai fa yarinyar wato nine namiki wasan, to ki kalli cikin idona ko kinga wasa acikinsa, bawasa nakeba inma kina wannan tunanin gwara kidena, nan gdn gda nane bana mahaifin kiva, au dama ku amarkinku keda uwar taki nan din gdnkune,? To zaifi muku kyau kutashi daga wannan mummunan mafarkin, mahaifin ki ya dade da mallakamin wannan gdn kungako gdn nan mallakinane, kudena tunanin zakuci gadonsa, domin kuwa bazaku taba ciba, matsawa tayi kadan saitin kunnen Nisha tasuma fadin,

" Hashim ya muku nisa daga yaudin nan bazaku sake sashi aidanun kuba keda uwar taki har abada kuwa kunyi bye bye daga yau, tunda mami tasuma zan tukanta Nisha takasa cewa komai se kallo kawai datake bin mami dashi se idanuwanta da keta ambaliyan ruwan bakinciki, da ker ta iya bude baki tasuma fadin,

" mekike nufi da haka,? nacewa bazamu sake sa abba adunmuba kwata kwata nakasa gane inda maganarki ta dosa" dan ja dabaya mami tayi tana faɗin

" yo ai dama ke yarinya ce bazaki fahimceni ba amma inkika sanar da ita uwar zata gane ta fahimta , tana fadin haka taja hanun Nisha tayi waje da ita tareda kayan nasu gaba daya, kuma kulle gdn tayi gaba abunta, hankali Nisha ba karamin tashi yayiba gaba daya ta kidime,

' to yau ina nasan zan shiga taredani da kayan nawa, oh allah wannan tani irin rayuwace'

matsawa tayi tasuma lalumar wayarta cikin wata back, takoyi sa'a tasameta sede glass din wayan tadan tsage sbd buguwar da yayi, makotansu tashiga tayi mata bayanin abunda yafaru cewa antashesu daga gdnsu, ta taimaka ta ajiye mata wasu kayanta tunda taga kamar akwai space dinda za'a ayi killace kayan tunda bawani yawane dasuba, matar bataja maganarba tabi nisha suka suka kwaso kayan wayanda bazasu iyaba suka nemi taimakon samari aka killace kayan, bayan gama Nisha tacewa matar bari taje ta dawo yanzu,

"to " kawai matar tace mata, Nisha tasa kai tafice, tana fita tasa hanu tazaro phone dinta tayi dealing wani number kamal ya baiyana screen phone din wayar batayi wani ranging sosae ba aka dauka,

"hey babe how are you today antunu dani kenan, I hope de kina lapia?"

"balafiya" Nisha tafaɗa,

" so what happened, cikin sanyin murya nisha tace," fadamin inda kake nazo nasameka but in kana nan "

" alright ina nan but jiya nadawo inda bukatar yiyuwar zuwana senazo ba matsala yafaɗi,

"aa ba damuwa nizanzo,"

"okay ina masaukin bakin Daddy I hope baki mance gurin but zan turo miki da address abunda yafaɗa kenan yakatse wayar, bada bata time yasake hankado mata da address din inda yake, wani goron numfashi Nisha taja daga bisani ta tattara nutsuwanta tasamu daman tsaida mai adaidaita tamasa bayanin inda zai kaita, basu dau wani dugun lokaci ba mai adaidaita ya direta gefen wani gd dan madedeci gdn ya hadu kuma ya tsaro duk dacewa bayida wani girma , sallamar mai adaidaita tayi, sannan matsa tana dan waige waige kamar mara gsky, bakowa wajan shiru yake, hanu tasa ta tura kofar geat din takuwa jita abude, gabantane yafidi hangenshi datayi daga kofar parlourn yana kaiwa da kawowa da alamar ita yake jiran isuwarta,

wani murmushi yasakar mata yayinda take kokarin karisuwa harta kariso kallonta yake yana murmushi, tsayawa tayi itama tana binshi da wani kallo, daga bisani tasunkuyar da kai kasa tana kokarin suma yin magana, shiiiii taji yakatseta dacewa,

" mushiga ciki yana kokarin bude kofar parlourn danufin shiga, cikin hanzari Nisha ta katseshi da cewa,"

"aa kar kadamu maganar ba mai tsayi bace zata yiyo muyita anan" dan hade gira yayi yana faɗin,

" ni bazan iya tsauwa ananba, idan maganar is very important ne kya shigo daga ciki" yana faɗin haka yajuya yashige ciki abunsa, lumshe ido tayi tanajin wani abu aranta jitayima kamar tajuya ta tafi abunta,

"hey you fita nakesonyi ana jirana outside" yana gama faɗi hakan yajuya yakoma, cikin sauri tabi bayanshi ta tura kofar tashiga,

azaune tasameshi yana zaune yana amsa call, hakan yabata daman tsayawa tana kallosa har yagama wayan yamaida kallonsa gareta, have a seat mn yafadi, batareda wani musuba Nisha tazauna,

"I'm hearing you so what happened"
kamal ya tambaya, cikin rawar murya Nisha tasuma magana,

" dama umma tace batada lapia shine nakaita asibiti, to shikenan akace se ammata aiki, sekuma tadanyi shiru ta dago tana kallonsa wanda shima haryanzu ita yake kallo yayinda take maganar, dan gyara zama yayi yana faɗin,

" subhanallah meya sameta, nanfa Nisha takora masa bayanin abunda doctor yace dakuma kudin da akeda bukata" daga bisani tasunkuyar da kai akunyace, cikeda tausayawa ya tasu daga inda yake zaune yakuma kusa da inda take yana fadin,

" naji duk bayaninki karki damu ki kwantar da hankalinki, nadau duk wani nauyi da duk wani abunda akeda bukata, cikin hanzari da murna ta dago takalle shi tana faɗin,

" nagode kamal allah yasaka maka da mafificin alkhari,"

" ameen" kawai yace yamike ya nufi bedroom ya tattaro duk wani kudaden dake cikin dakin ya tusasu cikin wata back , kaida kaga kudin kasan bana nigeria bane , cikin hanzari yadawo parlourn ya tattara da Nisha inda yabarta , yana isowa inda take ya kalleta yana faɗin,

" let's go " cikin hsnzari Nisha tasuma faɗin,

" bakace jiranka akeba? baseka min rakiya ba kabarshi karka wahalar da kanka wajan rakaniba zanje da kaina, hakan ma nine da godiya,

" aa tare zamuje nima inaso naga jikin umman naki yafaɗa tareda shigewa gaba yana kokarin bude door din, koda budewarshi yaja yatsaya yana bin yarinyar dake tsaye bakin door din tana kallonsa , kyakykyawar yarinyar ce duguwa kala larabawa siririya mara jiki, tana sanye cikin wani duguwar riga black abaya tayi mata kyau sosai, tayi rolling din kanta da gyale, murmushi tayi masa yayinda take kokarin karisuwa ciki,

" yadai kake kallona kamar baka taba ganinaba? tafaɗi yayinda idonta yasauka kan Nisha dake bayansa tana zazzare ido kamar mara gsky, shiru yarinyar tayi tana karewa Nisha kallo, wannan kuma wayece Kamal yarinyar ta tambaya tana nuna Nisha, shiru yayi baice mata komaiba yamaida kallonsa ga Nisha wacce itama shi take kallo, bataji mai zaiceba ta amshi jakar hanunsa tawuce dasauri, juyawa yayi yamaida kallonsa ga yarinyar da tayi masa zuro tana kallonsa hawaye fal idonta, waje tasamu tazauna tana wani huci na takaici da bakin ciki, shima jiki ba kwari yanemi gu yazauna kusa da kujeran da take,

"Nabilah meya kawoki kuma wayafa miki ina nan?

"Hajiya ce " abunda tafada kenan tayi shiru, shima shirun yayi baicemata Kala ba, kallonsa tayi tana fadin,

" ya Kamal wata yarinyace tafi yanzu kuma mai tazoyi,? nabilah ta watso masa tambaya,

" taimako tazu namata abunda yace kenan ya mike,

" wani irin taimakone wanda baza iyashi awajeba se anshigo ciki, kunkillace kanku, ?

"Kee ! mekike nufi ne, mekike son cewa? ya tambaya cikin daga murya,

"ya Kamal kasan ina sonka ina kuma kishinka bayanda za'ayi nazo na tarar dakai da wata raina yamin Dadi, kai bazaka taba canzawa bane, katunafa iyayenmu suna kokarin hada auranne nida kai nan da yan wani lokaci, inasonka kaima kuma nasan kana sona but hakan bazaisa kadena kula wasuba, induk baka duba wannan yakamata kasan mahimmanci alkawari, kayiwa Daddy da su Hajiya alkawari kadena abunda kake katuba ba laifinka bane , hakan yasa big bro yasa atsaida ranar bikinmu , amma sekuma kazo kasaba alkawari, kazo kadauko wata yar iska kuzu kuna cin,. am..tass taji yawanketa da mari seda taga wasu taurari, wani ihu tasa tareda zubewa saman capet,

" ni dan kine da zakizo kinamin magana son ranki, kina faɗamin duk abunda yazo bakinki, let me tell you something baki fini sanin abunda zanyiba kuma bake zaki faɗamin abunda yadace nayiba, kitashi ki tafi kikoma inda kika fito, inyaso sekije kibasu labarin abunda kika gani cewa kinganni da wata yafaɗi tareda fizgota yarakota har bakin kofa yamaida kofar yarufe, kuka takuma fashewa tareda rugawa da gudu tayi waje tashiga motar ta taimata key,..

tunda Nisha tabar gurin kamal ba inda tazame se asibiti akokarinta nashiga wayarta tayi kara, nan taduba screen din wayan taga friend dintane Salma dazuma taga miss call dinta bata daukaba tacigaba da tafiya, direct office din doctor tanufa batakaiga karisa waba ta hangoshi yafito daga wani room, seda takarisa inda yake tasuma mika masa kudin, cikin hanzari ya dakatar da ita tareda faɗin,

" biyoni office wucewa gaba ta kuwa tarufa masa baya, suna shiga yamika mata wani takarda yace tasa hanu, bada wani jinkiriba Nisha ta karba ta sanya hanu, daga bisani Doctor ya karbi jakar hanunta suka fita,

" zan iya ganin ummata Nisha ta tambaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login