Showing 51001 words to 54000 words out of 61982 words

Chapter 18 - IG AJEEMAL book1 Hausa Novel

03 Sep 2025

1551

sabo da mutum lokaci daya , ammafa mutumne maisaukin kai, sede kuma kafin a fahimceshi abunda wuya

nima kaina dakike ganin nake aiki agdn nan ankai ruwa rana kafin ajmal yasuma sabawa dani , kingani nan yanzu kusan shekara goma nake nema agdn nan ina aiki ,

Tun bayan dawowarsu ammi Nigeria nasoma aiki agdn dominko da sunacan yankin turawa seda gabaya suka dawo Nigeria har nasamu daman zuwa aikatau dani da yata hajjo mukazo gdn nan neman aiki wata hajiace takawomu gdn nan , sede ita hajjo ba tare mukeba tanacan gdnsu heelah acan tasamu rabon nata aikin , nikuma nake aiki anan , tunda nafara aiki agdn nan bantaba samun matsala da waniba seta kan ajmal domin kuwa duk abunda nadafo na kawo daga yakalli yanayin abincin ko one spoon bazaiyiba seya tashi yabar gurin bazaiciba , idan ammi ta tambayeshi dalili seyace akoshe yake yaci abinci awaje,

kinsan dalili dayasa bayaci , barka tafadi tana kallon nisha , girgiza kai nisha tayi alamar "

Aa

saboda suba yan gargajiya bane bai iya cin abincin gargajiyaba, yafisabawa da abincinsu can yankin turawa saka makon duk yarintarsu da girmansu acan sukayi bai saba da abincinmu Nigeria ba nikuma shina iya kuma hajja mama ita take da bukatan abincin gargajiya, kuma shi take bukata adingayi sbd atunaninta gabaki daya jikokinta susaba da gargajiya al'adansu na gargajiya yadawo susanshi yabi jikinsu

yaran tunbasa sabawa da yanayin abincin harya zama musu jiki suka suma jin dadinsa , amma shi mutumin ko gwadaci bayayi sede yayi order daga waje , sam ammi batajin dadin hakan , dan haka tashiga bina kitchen tana nunamin yanda ake sarrafa wasu nau ikan abincinsu nacan dakuma abunda shalelen dan nata keso dakuma abubunda yafi bukata, dukda wasu nau ikan abincin bawani wahala ne dasuba

Tofa nanne akasamu yake zama yadanci nan dinma dayasan dasa hanuna wajan sarrafa abincin ba lallaine yaciba amma ganin ammice tashirya masa to nanne zaisamu yasawa abincin albarka,

hmm inzamu kwana muwuni ina labarta miki rayuwa irin na ajmal bazai kareba , yanada tsarabe tsarebe tamakar jariri , to daga bayade Allah yatakaita wahala domin ansanya ranar aurensu da heelah duk da bayida ra'ayin hakan hajja mama ita tashirya komai, duba dayanda heelah ta kwallafa ranta kansa tanuna tanasonshi , bada wani bata lokaciba hajja mm tasa aka shirya musu biki

tode kobayan auran bata sauya zaniba domin kuwa heelah sangartacciyace malalaciya ba abunda ta iya sezuwa office yau morning gobe nights ba uwar da take tabukawa ansha kawo mata yan aiki dazasu dinga taiYikawa sbd ita ko girkinnan nazamani bata iyaba , amma saboda bakin hali da mugun kishi irin nata haka take koransu haka yasa hajja mama tace adakata dakawo masu aiki hakanan azuba mata ido akwai rayuwarsuce bata waniba,

nitunda nake bantaba ganin rayuwar aure irin tasuba kowa cikinsu aikin gabasa yake kamar ba maurataba niwani lokacin ma har tunani nake ko taya akasamu cikin aheel oho dan naga kowanne su bayi da lokacin kansa balle agansu atare dan soyayyan nan tsakani mata da miji duk babu , uhm to koni meye nawa danazage naketa miki surutu haka, barka tafadi tareda mikewa tana fadin ,"

Yi hakuri na ajiyeki inata miki zuba nasan kuma ko breakfast bakiyiba yakamata muje kiyi breakfast, dan numfasawa nisha tayi tana fadin, "

Uhm nigaba daya koyunwarma banaji ,"

Aa yar nan ya kamata kisamu Abu kisawa cikinki ko kadanne dan haka biyoni muje nasama miki abun tabawa barka tafadi tareda shigewa gaba bamusu nisha tarufa matabaya,

nisha daga dining tazauna tana jiran barka da tashiga kitchen dan hadu mata breakfast, bawani jimawa tazo ta direwa nisha plate din chips da kwai tareda sandwich gefe ga sassanyar cornflake abunda nisha keso kenan , haka tazauna taci sosai batareda wani damuwaba tana kammalawa dakanta ta tattare kayan da tayi amfani dashi tayi kitchen, nan tasuma taya barka da wasu aikace aikacen duk da baba barka tanuna mata bata bukatar hakan , amma sam nisha taki hade takyaleta suka cigaba da aikin tare , sunayi barka na mata hira gamida bata wasu labaruka dasuka shafi rayuwan gdn da kuma halayen mutanen gdn da yanda komai yake tafiya , wunin ranar bakaramin dadi yayiwa nisha ba kasan cewarsu tareda barka tana mata fira duk setaji damuwarta yakau ahaka tawuni cikin alwala

Da dare kamar kullum bayan kammala dinner family din sun zauna sunsha fira abunsu anyi nishadi yanda yakamata wannan karun harda Daddy domin kuwa yau dawuri yadawo baiyi dare kamar yanda yasaba , ansha hira mai tsayi segurin 10 kowa yamike sukayiwa junansu seda safe daga bisani kowannensu ya hallarci makwancinsa, yarage daga ammi se Daddy, "

Tomudin memuke jira yakamata muje mukwanta dare yayi Daddy yafadi, dan kallonshi ammi tayi tana fadin "

kajeka kwanta zanbiyoka anjima,"

kedin mezaki zaunayi a parlourn, dan sunnar dakai kasa ammi tayi tana fadin, "

MODIBBO nakejira, na ajiye masa dinner dinsa , wani kallo Daddy yabi ammi dashi yana fadin,"

Ninarasa meke damunki , MODIBBO fa bayaro karami bane yagirma yanzu mata biyu garesa ga yaro shima ya haifa banga dalilin da zaki dinga takura kankiba ,"

Ammade karka manta daga MODIBBO har dan nasa ba macen datake kula dasu matar tashima kana ganin abunda bai taka kara yakaryaba tasa kafa tabar gdn ta nufi gdnsu tafake da zancen rashin lapia dukda dama ko tana nandinma ba abunda take tarewa , ita kuma barka aiyuka sun mata yawa yakamata atausaya mata taji da namu aikin ga shekaru sunja bai kamata taita zarya akanshiba

to yaushe zan tsaya amatsayina na uwa nazuba masa ido seyafito waje sannan yaci ammi tafadi cikin damuwa , Daddy tasowa yayi daga inda yake yadawo kujeranda take yazauna tareda dafa shoulder dinta yana fadin, "

To inbandake yanzufa matansa biyune mezai hana kisa nisha tadau nauyin wannan koba komai tahaka yauda gobe sesu saba har Allah yanuna musu randa zasu fahimci akwai alaka atsakaninsu ni inaga hakan kamar zaifi,"

Hmm kamar kana manta miskilanci irin nadanka , nayi kokarin gwada hakan amma abun baiyi kyauba domin barka tasameni bayan dawowana tafadamin abunda yafaru bayan tura nisha danayi side dinshi nan ammi ta karntuwa Daddy abunda barka tafadi mata tsakanin ajmal da nisha turatan da tayi side shi domin kaimasa breakfast takuma gyara masa bedroom

shiru Daddy yayi yana jinjina lamarin dan yasan halin dansa zai aikata , hmm allah ya kyauta abunda Daddy ya iya fadi kenan ammade bai kyautaba ya kamata kiyi masa magana bai kamata yatakura yar mutuneba dan tazo gdnsu nizanje nakwanta sekin shigo Daddy yafadi tareda haurawa sama yabar ammi agun azaune tana jiran dawowar ajmal,

Ammi ta dade a parlourn tana kaiwa da komuwa gami da leka window dan ganin shigowar ajmal but amma shiru harta gaji dajira har 11 naneman gautawa, han yatabbatar mata balle dawowarsa yanzu hakan yabata daman haurawa sama tanufi makwancinsu koda tashiga bedroom dinsu tuni tasamu Daddy yayi baccinsa , nan itama tasamu daman kimtsawa ta kwanta ,

washe gari dasafe ammi batayi kasa agwiwaba bayan ta sallami Daddy kamar yanda tasaba itama tashirya tanufo dining inda tasa barka tashirya mata breakfast din ajmal nan ta tarar dasu reeda suna karyawa yayinda nisha takecan bedroom tana sheka bacci suna ganin ammi suka shiga daga mata gaisuwa nan ta amsa tareda kai hanu ta dauki tray din abincin tafita tanufi bedroom din ajmal,

tanashiga parlourn shiru ba motsin kuwa aciki dan haka takarisa dining table ta ajiye tray din abincin saman table din tanufi upstairs, direct bedroom din ajmal tanufa ta tura kofar sallama dauke abakinta takarisa shigowa nan dinma de shiru baya bedroom din se motsin ruwa dataji daga toilet wanda hakan yabata tabbacin yana toilet, hakan yabata daman zama saman sofa dake dakin tana jiran fitowarsa ,

ba dadewa yafito yana daure da towel saman waist dinsa, ganin ammi zaune bisa kujera da wannan lokacin yasashi tsayawa daga bakin toilet yana kallonta da mamaki, duk da ammi uwace ga ajmal but seda gabanta yafadi because batayi expecting fitowar ajmal awannan yanayinba itade har kullum mamaki girman jiki irin na ajmal take gatsayi ga fadi duk da ba ta inda yabar Daddy sedeshi bayida girman jiki irin haka ko hakan yasamu asali da irin motsa jikin dayake yawan yine oho uwa uba ga kwarjini, dan kirkiro murmushi ammi tayi tayi tana kallon dan nata shima kallonta yake ko damuwa da yanayin da yake baiyiba yakariso yazauna gafe da ita yana fadin,"

Barka da safiya,

Yauwa barkade I hope katashi lapia ammi tafadi tana dubansa, ,"

Fine , gakanni a bedroom dinka sassafe koh breakfast nakawo maka ammi tafadi tana dan waige waige am ya ina aheel banganshiba dan tasan tare suke kwana, "

Yana gurin mommynshi , "
incede lapia yatafi gurinta ammi ta tambaya,"

Tunjiya yake kuka sena kaishi gurinta shine nakaishi ajmal yafadi yana dan hade gira , "

to ita heelah baranan dawowartane ko baka tambaya bane? Ammi tasake watso masa tambaya, "

babukatan hakan maybe tafi bukatan zama can ajmal yafadi tareda mikewa yanufi dresse mirror yadauki hairbrush yashiga tace kanshi, girgiza kai ammi tayi tareda numfasa tana fadin,"

MODIBBO dama inaso magana dakai jiyuwa yayi yakuma kallon ammin tasu wacce tamike daga inda take takariso inda yake tsaye tasuma cewa,"

Am jiya naturo nisha takawo maka breakfast sannan nace tashigo bedroom dinka tagyarama because naga yana bukatar gyara but sede banji dadin abunda yafaru tsakanin kuba , zuru ajmal yayi yana kallon ammin tasu yanda fiskanta yakoma yanayin damuwa, hand dinsa takama tarike cikin nata taci gaba dafadin,"

magan ganunda kamata sam bai daceba, wannan yarinyar dakake gani tamkar amanace agaremu bata dakowa semu daukota mukayi muka sanyata cikin family tazamto daya daga cikinmu idan bamu sotaba baikamata kyamaceta ko mutakurataba ita marainiyace koma rikon maraya akwai dinbun lada cutar dashi akwai zunubi,

yarinyar nan tunda tazo gdn nan bawanda ta kaunaceshi kamar danka tanason yaron sosai karkaga bayan tafiyarka heelah bata nan yanda nisha ke kula dashi wanda ko heelah da tahaifeshi bata masa irin wannan kulawar shima aheel din inka duba yanason nisha sosai kuma yashaku da ita cikin kankanin lokaci baikamata kadinga sauke fushinka akantaba harkana kokarin yimata sha maki da dankaba ,

karfa kamanta maison naka kai yakeso kamata yayi duk maison naka kajashi ajiki bakayi kokarin yageshi daga jikinkaba , yarinyar nan alkhairice agaremu ba sharriba wani lokacin abunda bamuso shiyake zama alkhairi agaremu abunda muke matukarsu wani lokacin ba alkhari bane, plsease kadauki yarinyar nan tamkar sauran yan uwanka,

bawani abu bane yasa naturota ganin nayi late shiyasa nace tazo takawo maka kuma bedroom dinka na bukatan gyara tunda yanzu ba mata kakedashi akusaba kuma nasan zaka bukaci wasu abun kafin matar taka tadawo but tunda baka bukata balaifi , ni inna samu time zan dinga ziyartarka

sorry maybe kana da abunyi nazo ina kokarin bata maka time, nibarinaje karnayi late koda akwai wani abunda kakeso kuma ? Ammi tafadi yayinda take zami hanunta daga nasa,"

No things ajmal yafurta slowly yana kallon ammin tasu jiki duk amace,"

Alright nibari nawuce sena dawo , ammi nagama fadin haka tajuya tafice tabar ajmal agurin wanda yarintsa ido magan ganun ammi se yawo suke masa bisa , kunne gaba daya kalamunta sun kashe masa jiki , shikanshi baisan meyasa yake kin yariyar ba bakuma dalili duk dacewa tun lokacin da yayiwa yarinyar warning yaji ba dadi baiga kyautawar hakanba kodan sonda take nunawa aheel baikamata yamata hakanba gashi yarinyar akwai tsafta ta iya aiki balaifi,

kusan karfe 9:30 nisha ta tashi daga bacci toilet tanufa tayi wanka tareda wanke bakinta tafito tashirya takimtsa cikin riga da skirt rigar tanada duguwar hannu White color se black skirt mai laushi tayi stoking harsaman stomach dinta dressing din yayi matukar yimata kyau, nan ta daure gashinta yayi style din donut tasanya back hula mai kwaliya irin na butterfly kamar wata yar baby haka tafito tayi tas da ita masha allah,

tana fitowa parlour tasamu su hajja mm da goggo rabi harsun suma yin breakfast dinsu, nan ta karisa garesu tana ta zuba murmushi, suma murmushin suke tunda suka hangota harta kariso tasuma gaishesu fiska cike da annashiwa suka amsa mata goggo rabi tasuma fadin,"

Kai sirkata kinyi kyau gaskiya sekace maizuwa gasar kyau ta duniya masha allah amaryanmu , kallonda hajia tayiwa goggo rabine yasa rabi tahadiye maganar tareda washe baki tana fadin, "

Kizauna mana kintsa atsaye , sumu sumu nisha tanemigu tazauna, "
yau kintashi da wuri kenan dan nasanki da bacci shiyasama nace kar atasoki ashema kintashi hajia tafadi yayinda ta turawa nisha plate din abinci gabanta, murmushi nisha tayi tana fadin,"

ai tundazu natashi natsaya shiryawane bansan kunfitoba da nafito tundazu ai, "

To ai shikenan maza kizuba abunda kikeso kisoma ci , nan nisha tashiga serving dinkanta tasumaci , sunaci suna taba hiransu ,"

Yakamata muke kirakani saloon nawanke kaina dan gobe ko jibi nakeson komawa kd , garinku ya isheni , dan zaro ido nisha tayi tana kallon goggo rabi muryan ciki nisha tace,"

Tafiya kuma ? dariya Goggo rabi tayi tana kwaikwayan maganan nisha tana fadin,"

Eh tafiya zanyi zakibini mutafi tarene , dasauri nisha ta gyada kai tana dan shagwabe fiska kamar mai shirin kuka because gaba daya taji ba dadi zasuyi kewar goggo rabi mai barkwanci , dariya dukansu sukayi daga Goggo rabi har hajia suna kallon nisha wanda tayi fiskar tausayi ,"

waneni natafi da matar mutane ammade wani lokacin zakuzumin hutu koh, Goggo rabi tafadi tana kallon nisha , gyada akai kawai nisha tayi because duk taji jikinta yayi sanyi ,"

oh allah ya kyauta da barin zance irinna rabi , hajia tafadi cikin zuciyarta tana kallon rabi yanda taketa zuba tana tsokanar nisha , harsuka kammala karyawa suka nufi parlour suka cigaba da hiransu anan,, suna cikin tsaka da hira daya daga cikin dake securityn dasuke gadi agdn yashigo cikin parlourn yana dan wul wulga ido ganin su hajia azaune cikin parlourn yasa yayi saurin daga musu gaisuwa ,

seda suka amsa daga bisani yasoma isar da sakon da akaturoshi ,"

Ogane yace nazo nakira bakowar yarinyar dake zaune gdn nan (nisha) hajiya da goggo rabi kallon juna daga bisani suka maida kallonsu da tayi zuru zuru da ido
🦚🦚AJEEMAL🦚🦚

Story and writing by oum amreesh❤️
DAGA ALKALAMIN
Khaleeseart Raeeys✍🏼
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Page4️⃣0️⃣&4️⃣1️⃣___________✍🏼 To ke kanji papan aheel nakira maza seki hanzarta kije , goggo rabi tafadi cikin rawar jiki tana kallon nisha dake rarraba idanu, asukwane nisha tamike tasuma kokarin bin bayan security suka fice tana biye dashi,

suna zuwa side din ajmal security yasa hanu yabude mata door seda yaga tashi yamaida kofar yarufe yakoma bakin aikinsa , Nisha tunda tashiga parlour taketa tsilli tsilli da ido dan bataga kowa a parlourn ba, hakan yasa ta tsayawa daga nisa tana yan kalle kalle,

jin motsin sakkowa tab tab yasa nisha tamaida kallonta ga upstairs , kallo daya nisha tayiwa ajmal yayinda yagama sakkowa tamaida kanta kasa , fiska bayabo ba fallasa yakariso yazauna bisa kujera yajanyo table din abinci gabansa yasuma zubawa kanshi abinci yafara ci , sam ko kula da inda nisha take baiyiba , kokadan baisan da tsayuwarta cikin parlour ba, cikin natsuwa yakecin abincin hankali kwance kamar ance ya dagokai carab idonsa yasauka kan nisha dake tsaye ta dukarda kai kasa , kauda kai yayi yaci gaba dayin breakfast dinshi kamar bai gantaba ,

seda yatabbatar cikinsa ya dauka yakoshi sannan ya dakata da cin abincin ya kai hanu yadauki coffee ya kuma yajigina da jikin sofa yansha ahankali yana latsa wayarsa , gaba daya nisha jitayi gaba daya tagama gajiya da tsayuwa duk da yaganta but baice mata komaiba , "

Ke! cikin hanzari nisha ta dago takalleshi jin yana magana "

Come here ajmal yafadi yayinda ya dire cap din coffee saman table yana kallon yarinyar da mamakin hali irin nata tayi silent dayawa taita wani noke noke kamar mara gaskiya , cikin natsuwa nisha ta kariso kusa ta tsaya tana kallonshi , shikuwa seda yagama karemata kallo tsaf sannan yace,"

ke kurmace ?

Ahanzarce nisha ta dago tana girgiza kai alamar"

A'a, "

tsayuwar mekike acan? ajmal yakuma tambaya ,

jiwata tambaya nisha tafadi cikin zuciyarta , azahiri kuma cewa tayi ,"

bakai katura akirani kanason ganinaba tafadi tana dan turo baki, dan hade gira ajmal yayi daga bisani yamike yana fadin,"

Kigyaramin bedroom dina kafin nadawo , bajira amsawartaba yawuceta yawuce upstairs yanufi bedroom baki bude takebin bayan ajmal da kallo harya kurewa ganinta ,"

hala yamance ba aikatau take zaman yi agdnsuba koda yaga tagyara masa wacan time dinma saboda amminne , mutumin da koda tabauta masanma ba lallai yaji dadi ya gode mataba duk da ita dinma zatayine ba dan yaji dadin yagode mata bane sede tayi dan kanta, ta dadai tana tsaye agurin tana surutai cikin kokon zuciyarta , jin takun sawayen ajmal na sakkowa yasa tayi saurin maido da tunaninta tashiga tattare kayan breakfast din dake kan table tashiga kiciniyar fita daga parlour ,

ajmal yana karisowa parlourn yanufi inda ya ajeye key din motarsa ya dauka yafice daga parlourn shima yanufi motarsa daya daga cikin security yanufo cikin sauri da nufin budewa mai gidansa murfin kofa but ajmal ya dakatar dashi bayaso , yawanci kusan kullum se anyi hakan da zaran ajmal yafito zaifita se ansamu daya daga cikin security's wani yatasu zai budemasa mota seya hana because bayaso , hatta driving yafi bukata yayi da kanshi se inwani time din yanajin kasala ko ya taso office yagaji to yana bukatan agaji but akasin hakan tofa yafi gane yayi da kanshi, yana shiga motar yamata key mai gadi yabude kofar gate ajmal yasakai yafice,

Nisha tana karisawa parlour yanda tabarsu goggo rabi da hajia haka tazo ta tarar dasu se fira suke suna raha, asukwane ta wuce kitchen ta ajiye tray din abincin tafito parlour indasu hajja mma suke ta zauna tadanyi shiru kai sunkuye , "

Ke lafiya kuwa kiranme ajmal ke miki , goggo rabi ke tambayar nisha , murmushinda baikai zuciba nisha tasake tana fadin ,"

bakomai wai bedroom din shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login