Showing 33001 words to 36000 words out of 61982 words
goggo rabi tai mata agaban friend dinta, karya da gaskya duk ta hada tafadi,
wani zazzafan huci Hajiya jumana ta furzar tana fadin," lallai kuwa dama nasan arina yanda naga suke wani haba haba da yarinyar, to sun tabo tsuliyar dodo yanzu akan wancen sha sha shan yarinyar har rabi ta iya daukan hanu tamareki?
wato bare yafi dan gd kenan, lallai zasu san sunshigo gunata musamman yarinyar nan , tunda ammi tazu tana wani introducing dinta agurinmu, nidama tunda naga yarinyar bai ta kwanta min arai bane, kuma nasan bahaka banza tashigo gdn nan ba, harta samu karbuwa haka,
gashi ta dalilinta aka mari gudan jinina, to kuni da na haifeki yatsama ban taba gwada mikiba balle taba lafiyar jikinki, hmmm ba komai tashi kizauna, umma tafadi,
seda suka zauna akujera, Hajiya jumana takalli heelah cikin tausayawa da takaici na marin ta da goggo rabi tayi, janyuta tayi jikinta tana fadin," kiyi hakuri kikyalesu kuma kibarni dasu,
daga zuwar yarinya ana kokarin amayarmin da ya kamar ganga, nan gaba kuma bansan me zai faruba matsawar wannan yarinyar tana gdn,
Ina mijin naki yake umma ta tambaya tana duban heelah, tashi tayi daga kwanciyar da tayi jikin umma tana fadin,"baya nan yayi tafiya yau kwansa biyu,
Yaushe kenan zai dawo umma tasake tabaya, bansani because bai sanar da niba nikuma ban nemisaniba tunda bai sanar daniba, heelah tafadi tana dan tura baki,
hmm wato de haryanzu yana nan da zafin kanshi da miskilanci, because bakida mahimmanci kinsan tafiyarshi da dawowansa ne komai? umma tafadi,
nima bansaniba heelah tafadi atakaice, hmm yayi kyau wato kekuma ga shasha sha kizauna kina basa jiran daki da yaronsa koh,
shiga agogo sarkin aiki ko bikin dan wansama baya gabasa, hmm zamu hadune, Hajiya jumana tafadi tareda mikewa tana fadin,"
yanzude kitashi ki kimtsa nizan tafi zamuyi waya, daga nan tayi mata sallama tafita, tana fita tashiga motar ta taimata key, maigadi yabude mata tasa kai tafice,
ban garan yan dinner kuwa guraren karfe 10:30 aka suma watsewa masu tafiya suka suma tafiya gdajensu, amarya da kawaye da yan uwa tuni anwuce dasu gd jensu,
haka bangaren kamal yan uwa da abokan arziki kowa hankali ya tattara ya kuma gd,
salma da fauzee da suran kawayan su fadeela tuni sunyi gaba because dama su basu wani dade wajanba suka tafi
su fadeela motar kamal suka shiga , se motar dake tafe bayansu abokinsa md yana jansu ammi ,
sanu ahankali suke tafiya har allah yanufa suka iso, mai gadi yabude musu geat sukashigo tareda nufan compound din gdn sukayi parking,
nan kowa yafo yanufi sashensu, because kowa yadibo gaji da bacci aidonshi,
Kamal tsayawa yayi gun md seda sukayi sallama tareda yiwa md godiya har seda yaga fitanshi daga bisani shima yanufi nashi ban garan,
Su Nisha suna shiga seda sukayi sallar isha dinda basuyiba daga bisani kowa yayi shiri cikin night dress daga bisani suka kwanta,
washe gari Friday da safe akashiga yin walima tareda saukan Allah Qur'ani mai girma, gd yasake cika da yan uwa da abokan arziki,
bayan sakkowa daga sallahn jumma'a cikin masallaci aka daura auran KAMAL ABUBAKAR MUDIBBO BATURE, tareda amaryarsa NABILAH MUHMMAD MODIBBO BATURE yan uwa da abokan arziki kowa ya samu halarta masallaci da aka daura auran ,
Da misalin karfe 4:30 motan angwaye suka shiga zarya gdnsu nabilah, domin daukota akaita gdnta na sunna,
goggo rabi da kanta tashiga ta dauko, tanata kukan rabuwa da mom dinta, mom nayi itama nabilah nayi haka suka rabu abun ba Dadi, gwanin ban tausayi, nan aka kutsata cikin mota aka dauki hayar gdnsu kamal,
anan ban garan kamal aka sauketa tareda wasu kawayanta, masu dan debe mata kewa, duk da gdn yakasan ce ba bakonta bane but yau setaji gdn yamata daban,
seta kasance tamkar bakowa, guraren magarib kawayeda suke tareda ita suka shiga yimata sallama suna watsewa daya bayan daya, gashi parlourn ba kowa ita dayanta,
aban garan cikin gd kuwa nan ma gd yayi shiru duk yan barka kowa ya watse ya kama gd,
guraren karfe 8 su reeda zaune saman bed sunjeru kamar kifi gwan gwani suna latsa wayarsu, Nisha nadaga kwance tana kallon picture dinsu da fadeela ta tura mata cikin new phone dinta,
goggo rabi ce tayi sallama tashigo tasamesu cikin yanayida sukeciki, jin mutsin shigowar goggo Rabi yasa suka dakata da danne danne dasuke awayoyinsu, nisha kuwa ta tashi daga kwanciyar da take tazauna,
Goggo rabi, seda takallesu daya bayan daya daga bisani tasuma fadin, " sako nazu nafada muku yayanku kamal yace kunbar masa amarya ita kade, dan haka kubar duk abunda kuke kuje kutayata fira,
Khaleeseart Raeys ✍️
08105565439🌴🌴 IG AJEEMAL 🌴🌴
Story and writing by Oum AmReesh ♥️ ( khaleeseart Raeys ✍️)
Free book 🥰
Page 23, nabilah amarya tana can katafaren parlourn mijinta jikinta sanye cikin kayaceccen lulubi irin na amare, sezuba kamshi take ,
Jin anbudu kofa hakan ya tabbatar mata da angonta kamal ne ya iso, dan haka cikin natsuwa tadago tana kallon kofar domin ganin shigowar sa,
ga mamakinta setaga ashe su fadeela ne suka shigo daya nabin daya, bata kaiga karisa ganin shigowar su ba , nabilah tadukar da kai kasa tana sakin wani goron numfashi,
Amarya kina nan ke kadanki reeda tafadi tana tambayar nabilah yayinda take kokarin zama kusa da ita,
Gyada kai nabilah tayi tana murmushi batareda ta dago takallesu ba,har
friends din naki suntafi? nadauka zasu tsaya se ango yazo ae, fadeela tafadi tana yar dariya,
wannan karon nabilah dagowa tayi danufin magana , karaf idonta yasauka kan Nisha dake zaune takurawa guri guda tana kallonsu,
,
Oh my God nabilah tafadi yayinda tamike tsaye tana kallon Nisha, itama Nisha mikewa tayi wacce duk taji jikinta yasuma bari, se yanzu idonta yayi tuzali dana nabilah,
saka makon ko wajan dinner bawai ta ganetabane because irin ado da bride makeup datasha ba lallai tagane ainihin face din taba,
haka itama nabilah bata kula da Nisha wajan dinner ba because attention dinta baikai wajan Nisha ba, "
meyakawo wannan stupid girl dinnan cikin gdn nan, ? nabilah tafadi tana kallon Nisha datayi tsaye hawaye na shirin wanke mata face,
" Fareeda da fadeela sake baki sukayi suna kallon ikon Allah, but sun gagara cewa komai sun koma kasa gane meke shirin faruwa, ahankali nabilah take matsawa kusa da Nisha tana kallon ta, duk da nisha tadan canza but hakan bazaisa nabilah tamance da face din yarinyar da tagansu tareda kamal gdn masaukin uncle dintaba,
yarinyar da kamal harya iya daukan hanu ya wanke ta damari saboda tafita mahimmanci wani irin azabebben kishin yaturnike nabilah , because Allah yagani yanda take bala in son kamal da kuma kishinsa, tun ranar da idonta yagane mata Nisha da kamal sun kebanta hankalinta yakasa kwanciya takuma kasa mancewa da ranar,
Wani kukan kura nabilah tayi tareda yin hakan Nisha, Nisha naganin haka yasa tajuya da gudu tana kokarin fita daga parlourn, aiko kafin tayi wani yunkuri nabilah ta janyo hand dinta takai hanu danufin marin face din Nisha, carab taji anrike hand dinta,
Kallon kamal tayi dake rike da hanunta yashiga tsakanisu da Nisha datayi kasa dakai tana sharce hawaye, gefensa nadauke da md tareda muhaiseen dayazo tun farar safin da aka daura auran kamal,
ganin yadan kamal ya rike hanunta gam yana binta da kallon cikin wata siga yasa nabilah tashiga kiciniyar kwace hand dinta danufi auwatar da abunda tayi niya because idonta yarufe,
kamal kuwa yanda yaga nabilah na kokarin kaukawa dashi yasa cikin bacin rai yatureta gefe wanda hakan yasa tashiga tangal tagal tana neman faduwa, cikin hanzari kamal yarikota tareda daidaita mata tsayowa yana fadin," I'm sorry ba danufi nayiba, baikai ga karisa maganar ba nabilah tadukar dashi, tana fadin," ba hakurinka nakeda bukatan jiba , seda ta zame jikinta daga rikon dayayi mata daga bisani taja gefe guda tatsaya tana kallon Nisha tana fadin,"
meye dalilin zuwan yarinyar nan gdn nan, duk haduwar dakukeyi awaje ahakan bai wadatar ba seta biyoka har inda kake tarabeka meye hadinka da ita da har take bibiyar rayuwarka haka, nabilah tafadi cikin kunar zuci, parlourn ne yadau shiro kamar bakowa cikinsa, su fadeela mamaki yagama cika kwakwalwarsu haka muhaiseen yakalli Nisha yakali nabilah gefe kuwa ya maida kallonsa ga kamal da nabeela ta tsaresa da ido, shimade yakasa gane inda zantukansu ya dosa, shide yasan sanadin zaman yarinyar agdn kuma ya dade dajin labarin ta gurin reeda dakuma goggo rabi wato mahaifiyar sa, md kuwa kai sunkuye because already dama yasan komai ,
kamal jan hanun nabilah yayi suka nufi sofa, zaunar da ita yayi shima kuma zaman yayi, kuma yiwa abokan tafiyarshi md da muhaiseen tayin zama, yakuma kumarci su fadeela dasu zauna suma, banda Nisha datake tsaye kai sunkuye tana ta jan hanci," kizo kizauna kamal yafadi yana kallon Nisha datayi tsaye abun tausayi, gagara daga kafarta tayi shiyasa takasa matsawa tazauna, se reeda ne tamike daga zamar da tayi tanufi Nisha tareda rukota suka taho tazaunar da Nisha daga bisani itama tazauna, nabilah se bin Nisha take da wani mugun kallo, haka kamal shima Nishan yake kallo face dinta yayi jawur gwanin ban tausayi , daga bisani yamaida kallonsa ga nabilah da ta tsareshi da eyes, ahankali yasuma magana da cewa,
niba abunda yake tsakani na da ita but bun dade da sanin juna hasalima akwai abubuwan da suka faru abaya wanda bawanda yasanda faruwanso,
TUNABAYA******____________________________*****
Wata kyakykyawar motar hadaddiya tsa daddiya write color takunna kai a million tana tasheka gudu bisa hanyar kan wata layi cikin wata anguwa, kai kace wanda yake tukin ba hankalisa yakeba,
Yammane lis gari yarufa yanayin gari na damuna, yayafine take diga dis dis, saka makon tsagaitawa da ruwa yayi, Matasan yan matane guda biyu dake tafe suna tafiya suna fira , jikinsu sanye da inform hijab yarufe musu jiki kirib se dan sawayansu da ake hangowa cikin black socks, da alamar antashesu daga mkrnt suna kan hanyarsu takomawa gd,
duk da dan yayyafi dake hakan bai hanasu tafiya slowly yanda sukeba, da alama suna cikin nishadi a cikin firan dasuke,
jin wani mahaukacin hon yasasu firgici yasa sukayi saurin watsewa junasu kowa yafara kokarin yin takansa, cikin tsurita da rudu, daya tayi hanyar motar da take kokarin bi, jikake gauu, motar data tahu ta bugeta, duk da bawani bugeta yayi sosaeba because yalura da ita but yayi kokarin taka Burkin allah yariga da ya iko da tsautsayi yadan bugeta,
dasauri wacce suke tafiya tare tayi kan kawarta dake kwance tana duka salati tana kiran sunan ummynta , da Nisha tana fadin tazu ta taimaka mata takaita gurin ummynta, wayyo namutuna, itama Nisha duka sallallami tashigayi , tana kiran sunan, salma
nanfa motar tafara yin reverse danufin cigaba da tafiya tabar gurin, oh my God meka aikata haka, kuma kake kokarin tafiya kamar baka san kayiba? dayan yafadi yana kallon mai driving din, " mekuwa nayi baka ganin ita tashigo gabana bawani bugeta nayibafa kawai tsoritace tayi tafadi, mai driving din yabashi amsa, yana kokarin cigaba da tafiya, cikin hazari dayan matashin ya taka Burkin motar tareda zare key yabude motar yafito, daga bisani yazagayo ya bude gdn gaba yafito da abokin tafiyar tasa, yatusa keyarsa zuwa ga gurinda yan yan matan ke tsugune Nisha na tallafe da salma, guri yayi tsit se muryan salma dakakeji tana ta duka salati ita dakko daga farko Nisha ta karshe mata karshe,
seda suka kariso yadan duka kusa dasu yana musu sorry, but daga Nisha har salma ba wanda ya dago yakalleshi balle susan abunda yake Fadi,
ganin basu amsashiba yasa yamike yana kallon, dayan yana fadin," kb yanzun kaga abunda kayi fa taji ciyo kanta yafashe ga head dinta se bloodshed yake yanzu se muyi hanzarin zuwa mukaita hospital abata taimako , "lallai fa gsky banida time kasan sauri muke yaushe zamu tsaya biye wadan nan, kadubafa magana ake but sunyi shiru sunajin mutane, wani tsaki kb yaja tareda ciru kudi cikin pocket dinsa ko irgawa bai yiba ya watsawa su Nisha yana fadin," kuje hospital aimata magani, rashin hankali da nutsuwa darashi kula yajawo muku,... tas kamar walkiya yaji andaukesa da mari , cikin hanzari ya dafe gefen fiskar sa yana kallon Nisha datayi tsaye agabansa cikin fusata da bacin rai,"
wato shi talaka abun wulakancine dacin mutunci koh? kabuge yar mutane baka iya cemata sannuba kana kokarin zaginta, rashin hankali da rashin kula yawuce wanda kayi yanzu, karike tsiyarka allah zai saka mana, nisha tafadi tareda watsa masa kudin a face dinsa, tanufi inda salma take akwance, tafara kokarin tallafo ta,
Dukansu matasan tsayawa sukayi suna kallon karfin hali irin na yarinyar da harta iya daukan hanu ta daurashi face din namiji irin kb, tab dayan harde hanu yayi bisa karjinsa yakalli Nisha yakalli kb daya sake baki yana rike da kuncinsa, azafafe kb yayi kan Nisha dayan yarikoshi yana bashi hakuri tareda tausansa,"
Please kamal kyaleni nakoyawa yarinyar nan hankali naga kamar hankali bai wadaci kwakwal wartaba , bata san waye niba dan haka kabarni nafada mata,
daga cikin motar dasu kamal suka paka wata matashiyar budurwa dirarriya cikin wata irin shiga, sanye take cikin t shirt skintight ko ina ya dame , fitowa tayi tatsaya daga jikin motar tana kallon su kb da kamal keta faman rirrikeshi, tabe baki tayi tareda zaro phone dinta tayi dealing numbern kb,
bawani ratane tsakanisu suba baifi kayi taku 5 zuwa shida ba ka isa garesu, but baza ta iya karisawaba hakan yasa takirashi, kb najin wayarshi tashiga kara yasa, cikin fusata yaciro yaduba yaga mai kiransa, ganin baby nice dinsace takira yasa yamaida kallonsa ga wajan da motarsu yake yahangota jin gine tana kallonsu, wani kwafa yasake yana kallon Nisha da dake tallafe da salma har sun mike suna shirin barin gurin, lips dinsa yakuma ciza daga bisani ya kwace hand disa daga na kamal yawuce shi, yanufi motarsu, shima kamal din bayansa,
suna zuwa gurin motar kamal yanufi seat yazauna haka kb itama yarinyar bude motar tayi tashiga suka ta da motar suka wuce,
ahankali Nisha take takawa da salma because kafarta yasamu rauni shima , Nisha jitake kamar ta daga salma domin tarage mata ra dadin datakeji, amma batada wannan karfin da ta taimaka, basu wani dade atafiyarba suka iso gdnsu salma, duk dama sun kusa isowa gdn wannan tsautsayin ya afka dasu,
tundaga kofar gd kanin salma ya hangi yar uwarshi salma nisha narike da ita, hakan yasa yawatsa aguje cikin gd domin afadin abunda yagani, Nisha nashiga da salma cikin tsakar gdn ta ta tarar dasu ummyn salma da babanta dayi alwala yana kokarin fita masallaci because magarib ya gabato, da kuma faruk kaninta suna tsaye suna jiran shigowasu,
ummyn Salma tana ganin Nisha tareda yarta anrokota magashiyan yasa tayiyo gunsu dasauri tana tambayar abunda ke faruwa, ba da wani bata lokaciba nisha tashiga tsaiyanu musu abunda yafaru, " oh allah kai amma wayan nan yaran basu kyautawa kansuba,wani irin rashin imani ne haka ummyn salma tafadi yayinda take kokarin tallafo salma da jiki yayi tsami, hmm Allah kyauta yakuma kara tsarewa, kushiga da ita bari naje nataho da mai adaidaita se mukaita hospital, baban salman yafadi, tareda sakai yafice faruk ma yarufa masa baya, har dakin ummyn salma Nisha ta taimaka suka kaita suka tsaunar da ita suna mata sannu, daga bisani Nisha tai musu salma zata koma gd tareda fatan samun sauki, takuma sheda musu gobe in allah ya yarda zata dawo, haka sukayi sallama Nisha tafice tanufi haryar gdnsu,
kasan cewa gdnsu salma da Nisha bawani rata sosai nan da nan ta iso, cikin dan ma dai daicin parlourn su gwanin shaawa Nisha ta tar da umma na tsaye takasa tsaune takasa tsaye, umma nagani Nisha tashigo da sallama taja wani dugun ajiyar zuciya, tareda tin karo Nisha tana tambayar ba asin rashin da wowar nisha da wuri because bata saba hakanba shiyasa hankalin umman nata ya tashi, nan fa nisha tashiga labarta mata rashin kyautawa da su kb sukayi musu dakuma raunin da salma tasamu, harta kaisu ga bata lokaci haka, tabbas itama umma bataji dadiba takuma nuna damuwarta da halinda da salma take ciki, takuma yi allah yakyauta yakuma kara tsare nagaba,
awannan ranar Nisha ta kwanta da bakinciki da takaicin wadan nan samarin especially wannan mai zubin mashayan wanda taji dayan yakira da kb daka ganshi kasan kwa kwalwarshi akwai gyara acikinta, talk din shima wata iri babu dadin ji bugu da kari ba furci mai Dadi, amma de ko banza rada din datakeji yaragu inta tuna da marin data masa koba komai tasan tabar masa wani gibi azuciyarsa da zai dingajin haushi da takaici,
washe gari Sunday kamar yanda Nisha tayiwa salma alkawarin zata dawo haka kuwa akayi, guraren karfe 10, tana gama breakfast tayiwa umma sallama danufin zuwa dubo kawarta salma, nan umma tasheda mata tagaishesu itama inshallah allahu tana tafe domin zuwa ta dubata, in allah yasa tasamu saukin jikinta itama because ita dinma bai tacika lapia bane,
to Nisha tace mata ga nan tafice tanufi hanyar gdnsu salma,
tundaga nisa Nisha ta hango wata jibgegiyar mota red color afake kofar gdnsu salma cikin matsuwa ta karisa shiga ciki hade da sallama tana dan wul wul ga ido , daga tsakar gdn nisha tayi turos tana kallonsu, anshin fida taburma , salma nazaune jikinta sanye da hijab tajin gina bayanta da filo leg and head anyi dressing dinsu, gefe kuwa matasan samari guda biyu , saurayin salma wato muhammad bello wato mb se gefensa saurayin jiya kamal , suna zaune dukansu sun tsura mata ido suna kallonta , itama kallonsu take tana kokarin karisawa ahankali
Khaleeseart Raeys ✍️
08105565439🌴🌴 IG AJEEMAL 🌴🌴
Story and writing by Oum AmReesh ♥️ (khaleeseart Raeys ✍️)
Free book 🥰 ga masoyana ina alfahari daku ina kuma godiya da fatan alkhari much kauna nagode sosae 🤝
Page 24
Seda takarisa kusa da salma, daga bisani tashiga gaishe dasu mb kasa kasa, seda suka amsa mata cike da washe baki, sannan takalli kawarta salma wacce itama itan take kallo tana murmushi,
Nisha tambayar salma tayi yajiki, nan salma tace jiki alhmdllh, daga haka Nisha tasuma kokarin mikewa, "ina kuma zakije salma tafadi tana kallon Nisha, zanje mugaisa da ummy ne, to ae bata