Showing 27001 words to 30000 words out of 61982 words

Chapter 10 - IG AJEEMAL book1 Hausa Novel

03 Sep 2025

1542

na ciyo da safe zaizo sugaisa,

aban garansu fadeela kuwa bayan ammi ta tashesu, wanka sukayi tareda alwala suka fito sukayi sallah, suka shiga shirin makaranta kamar yanda suka saba, banda Nisha daketa sharan baccinta because tana up,

yau seda suka tsaya sukayi breakfast mai dan sauki Barka tamusu sukaci , daga bisani suka tattara izuwa part din Hajiya domin rage time because yau akwai sauran time nan suka tarar dasu Daddy da kamal tareda ammi an kacame da hira da raha da wasa nanfa suma suka shiga aka cigaba da damawa dasu,

se wajan 8 sukayiwa su ammi sallma suka wuce, haka su Daddy da kamal basu dadeba suka tashi kowa yanufi bedroom dinsa dan shiryawa, nan ammi tanufa musu baya tanufi kitchen domin shiryawa Daddy nashi breakfast din, bayan ta kammala komai nan ta haura upstairs tanufi bedroom dinsu, ba adadeba suka fito tareda Daddy suka nufo downstairs , dining suka nufa Daddy ya zauna nan ammi tashiga zuba masa abunda yakeso tamika masa tareda hada masa coffee, nan yasuma ci, kamal yashigo shima cikin shirinsa maikyau gwanin shaawa, yazauna yashiga karyawa shimade ammince ta zuba masa abinci ta tura masa gabansa yadauki spoon yasunaci,

suna kammala wa, suka mike kamal yakarbi jakar hanun Daddy suka nufi hayar fita ammi na musu asauka lapia, nan ammi tashiga domin sanar da barka cewa adaura wani girkin, nan tabata umurnin abunda za adaura daga bisani tafito wajansu goggo rabi suka cigaba da hiransu, se guraren karfe 9:30 suka tattara izuwa babban parlourn domin karyawa,


kamar yanda ammi tashedawa barka haka tayi takammala komai tajere inda yadace, suna suwa suka zauna a dining din, nan kuwa yashiga diban abunda yakesu yaci,


seda suka kammala, ammi tamike tanufi bedroom dinsu Nisha domin dubata , koda tashiga sesamu tayi ta tashi daga bacci saka makon dazu datazo tasamu tana bacci,

Nisha kokarin mikewa tayi ganin ammi datayi tana shigowa yasa takuma tazauna daga bakin gadon tana kallon shigowar ammi,

Murmushi ammi tashiga yiwa nisha yayinda takariso tazauna kusa da ita, nisha Nisha tayi saurin dagawa ammi gaisuwa tana fadin,"

ammi brk da safiya antashi lapia, lapia kalau Nisha yajikin nake I hope everything is fine, gyada kai nisha tayi hadeda sunkuyar da kai kasa tana wasa da yan yatsun ta,

ammi ce tasake magana dacewa," to yanzu kitashi ki kimtsa seki fito parlour kiyi breakfast ammi tafadi yayinda tamike tsaye tana sake fadin," ki hanzarta nima bari nashirya nazo nawuce office karna makara, tana fadin haka tajuya tafita,

nan Nisha tayi hanzarin fadawa toilet tayi wanka tafito jikinta daure da towel tazauna kan stool din dake wajan dress mirror tazauna tashiga shafa mai tamulke ko ina ajikinta, yar Hoda tanema tadan shafawa fiskarta tareda lipstick , baby face din nan takara kyau, mikewa tayi tanufi hanyar ma ajiyanda kayansu yake, tanemi wani riga da wando pakistan red color wandon white color mayafinsa ma haka, tasaka tareda daura mayafin ahakanta tafito mekyau da ita kamar wata ba india,

parlour tanufo bakowa a parlourn, jin mutsin ammi nakokarin sakko daga downstairs cikin shirinta nazuwa office hakan yabawa Nisha daman tsayawa tana jiran sakkowan ta,

ammi ganin Nisha datayi tasaki wani kayaceccen murmushi takariso tana fadin, wow my daughter kinyi kyau sosai, sankuyar dakai Nisha tayi tana dan murmushi batareda tace komaiba, muryan ammi taji tana fadin," yanzu se kikarisa dining breakfast najiranki, nibari nawuce se nadawo, Allah yakiyaye hanya nisha tafadi, ameen thanks my dear ammi tafadi tareda sakai tafice,

nisha karisawa tayi tazauna bisa table din dinning tashiga farayin breakfast, seda ta kammala tamike domin nufa part Hajiya because wunin jiya kaf batazo anyi fira da itaba,

tana isuwa kofar parlourn takejin muryoyinsu ana kyakyatawa hada wata bakowar muryan da bata san da itaba, da sallama abakinta tareda tura door din tashiga, zaune suke goggo rabi nagefen Hajiya,
.
ganin Nisha dasukayi yanda dakatar da daga hiran dasuke suka tsura mata ido suna jiran karisowarta, ahankali takariso hade da dukawa kasa tashiga gaidasu,

amsawa sukayi cike da fara'a da sakin fiska, musamman goggo rabi ganin yarinyar datayi taji ta kwanta mata a rai tashiga zuciyar ta itama, ga mamakin Nisha seji tayi goggo takamu hanunta tareda zaunar da ita akujera tana fadin," ko bancanki daidai nasan wannan beautiful girl din kuke bani labarin ta, tafada tana kallon Hajiya, itacede kincanki daidai Hajiya tafi tana murmushi, kai irin wannan kyakykyawar flower gaskiya nayiwa muhaiseen dina kamu goggo rabi tafadi tana dariya hade da sake kallon Nisha, to seki fada masa yashirya dakyau ban tsan manin zai sami nisha abagas dan haka kema se kitayashi shiryawa, Hajiya tafadi tana yar dariyan itama,

Nisha ma dariyan take kasa kasa hade da sake kasa dakanta tana wasa da yan yatsunta, duban Nisha goggo rabi tayi na fadin," baki sanniba koh, gyada kai nisha tayi alamar eh, ni goggonsu fadeela ne , kanwar Daddy, but as from now kuma nazamo cikin jerin sirikar gdn nan domin nayiwa dana kamu kafin ace wani yarigamu goggo rabi tafadi cikin zolaya, dariya sukayi yi dukansu, lokaci AJMAL ya kunno kai cikin parlourn hadeda sallma,

Karisuwa yayi yazauna ganinshi da goggo rabi tayi tashiga suma masa tsiya tana fadin,"

yanzu MODIBBO yau kwana daya a gdn nan amma ko lekoni bakayiba konayi laifine ansakani cikin magarkama baza azu inda nakeba, halama bakasan da zuwanaba, tafadi cike da zolaya,

dan murmusawa yayi wanda hakan yakara kawata fiskarta shi kyansa yakara baiyana, yana fadin," nasani but bana jin dadine kaina kedan ciyo tunjiyan shiyasa ban lekoba, ayya sorry yajikin rabi tafadi, alhmdllh yafada atakaice, nan yashiga gaishesu, seda suka gaisa sosae daga bisani yamike yana kokarin fita,

murya Nisha yatsinkaya tana gaishesa wacce dama jiratake sugama gaisawa dasu goggo rabi seta daga masa nata gaisuwan, amsa mata kasa kasa yayi daga bisani yasa kai yafice,

Nisha tabe baki tayi dama tunshigowarsa bawai tayi niyar daga nasa gaisuwa bane sa a kawai yaci because abunda yafaru jiya da magan ganu dasharri da kokarin maidata shasha da yasuyi, yanzu tsoransa datakeji ya ragu sema dan hashi daya fara bata because taga kamar bakin hali gareshi ba kamar kamal ba shiyada dan sakin fiska da magana mai Dadi,

"Oh ni rabi haryanzu MODIBBO yana nan da wannan miskilanci nasa goggo rabi tafadi tana kallon Hajiya tareda kama haba,

"ke kinsan mutumin naki tun yarintarsa haka yake yanzukam ma se abunda ya karo Hajiya tafadi tana yar dariya,

aini nadauka yanxu miskilancin yaragu because yanzu ga mata ga da ashe abun sake girmama yayi, kodayake itama matar tasa miskilarce but itakam ma ya hadu mata da bakin hali da rashin kunyar tsiya Kai Allah de yakyauta goggo rabi tafadi tana tabe baki, ameen Hajiya tafadi,

Nisha kam shiru tayi batace komai ba tana sauraron su ,

sunyi hira sosae awannan ranar Nisha tasake da goggo rabi kai kace dama can suntaba sanin juna, kasan cewa goggo rabi macece mai wasa da kuma barkwanci dason mutane dakuma sakewa dasu, musamman Nisha data kwanta mata arai,

yau Wednesday anshiga satin bikin kml su fadeela suka shirn fita wanke kai, Nisha tanajin su, sunayiwa kamal tsiya suna fadin yau tareda ango zasu fita,

sun shirya tsaf daga bisani suka fito waje tareda nufar sashin kamal,

Nisha batabi bayansuba tsaya tayi daga bakin kofar parlourn tana jirasu suje su dawo daga nemo maganar dasuka tafi,

part din su aheel Nisha tabi da kallo tanajin kewar aheel aranta , tayi kewar aheel sosai, sauda dama setayi tunanin tashiga bangaran su ko asace domin taganshi setaji tana tsoro bazata iyaba,

duk da tayi alkawarin bazata sake ko kallon inda sashensu yakeba because papansa yaso yamai data shasha yana mata kallon mai halin bera,

tunda take ba wani mahalukin da yataba kwatanta yimata irin wannan kallon , har tambayar ta wani aiki tayi aka bata kudin, to meyake nufi watoma ni yar iskace komai yakeso Fadi ,?

ganin ranta yasuma baci yasa takauda wannan tunanin aranta, nan tafara kokarin nufa sashen Hajiya domin su dan taba hira irin na wancan ranar,

dan bakaramin jin dadin hira da goggo rabi takeba, karab idonta ya hango mata raheela dake tafe tana tin karota, ganin haka yasa Nisha hanzarin kokarin shiga sashin Hajiya,
.
hey you, where are going , jin haka yasa Nisha tayi kokarin jinkirta tafiyar datake,

ina kuma zakije naga kina kokarin guduwa, raheela tafadi tareda da hararo Nisha

magana nakeson nayi dake kuma ba komai tsawo bace, kallon up and down heela tashiga yiwa Nisha tareda sannan ta tabe baki tana fadin,"

nadade ina bukatar ganinki but time bai bani daman hakanba amma yau nakashe duk wani uzuri dake gabana domin na gargadeki nakuma miki kashedi naja kunnenki,

this is the first and last da zan gargadeki akan aheel daga yau inaso kifita aharkansa ko inuwa daya banason kusake hadawa, domin nagane take takenki dakuma inda kika dosa,

tunda kinsamu shiga zuciyar aheel shiga zuciyar mijina baizai baki wahala ba because kinga yanason danshi sosai, to kisani IG ba irin mazan da ake saye zuciyarsu da sauki bane,

let me tell you something inma turoki akayi domin shiga Wannan ahalin gdn nan to kitsaya iyaka bangaransu but karkishiga hurumina,

domin kuwa wani gigi yadebeki kika kuskure to ina mai tabbatar miki.... ganin su fadeela sunfito daga part din kamal yasa ta tsagaita da abunda takeson Fadi dan haka seta saki wani shuumim murmushi hadeda dan jan kumatun nisha tana fadin,"

be careful your self se anjima tana fadin haka tajuya takoma part dinsu

Nisha kam shiru tayi gaba daya abun yagama bata mamaki tabbas se hali yazo daya ake abota daga shi har matar tasa kusan daya suke, gaba daya jitake magan ganu heelah suna mata yawa cikin kanta,

jitake kamar ta tattara ta gudu daga gdn takeji wanna wani irin rayuwace daga wancan se wannan,

toma inbanda abunta maima zatayi da mijinta wannan shugaban yan bakin halin itade gani take ko kyauta akabata shi bakarba zatayiba dan wannan miskilanci nasa se itan,

Nikuwa nace,( ajura zuwa rafi domin kuwa IG nada banne baki fahimci mutumin bane kuma bakowa yake iya fahimar saba,)

what is going on,? mai wannan rasa kuyan take fadamiki, reeda tafadi tareda dafa shouldern Nisha wanda yayi saurin dawo daga ita daga dunyar tunani data wulla,

kirkiro murmushi nisha tayi tana fadin,"bakomai, gwara kifa dan san ba alkhari yakawotaba fadeela tafadi tana kallon Nisha,

dariyanda baije zuciba nasha tasake tana fadin," aa nikam ba abunda tafadamin,

Alright mukarisa part din Hajiya mujirashi ya kamal din reeda tafadi tareda shigewa suma suka rufa mata baya ,

da sallama suka shiga dakin suka tarar dasu suna tsaka dan hiransu, karisa shigowa sukayi tareda neman guri suka zauna, Hajiya ce ta kallesu tana fadin," dama bakutafiba har yanzu , eh Hajiya kamal muke jira shizai kaimu,

goggo rabi ce takarbi maganar dacewa," kai amma ya'yan nan da neman magana kuke, yo ga driver agd amma se kun gajiyar da angon namu tun yanzu,

To ai daga yaune gabama ba ganinsa zamuyiba balle muce yakaimuba koya fadeela tafadi tana kallon reeda, eh mana shidama ba zama yake akasarba

daga andaura aure zai dauke matar shi suwuce canada Allah sarki lovely bro zamuyi miss dinshi tafada tareda yin raurau da ido kamar mai shirin yin kuka ,

jin maganar da reeda tayi ba karamin sanyi jikin Nisha yayiba jin kamal bayan daura aure zasutafi, jitayi kamar itama ta taya reeda kukan suyi tare

yo da allah kujimin yarinyar nan, insun tafi tabbata zasuyi acan, goggo rabi tafadi tareda kama haba tana kallon Hajiya,

Dariya dukansu suka bushe dashi, shigowar kamalne ya dakatar dasu daga nishadin dasuke ciki, karisuwa wa yayi yasamugu shima yazauna, nan yashiga gaisawa dasu Hajiya daga bisani goggo rabi tabige da tsokanar shi tana fadin,"

ikon allah kai yanaga angon jibin namu sewani fresh yake kara yine, meye sirrine ,kaiba amaryanba ,

inbanda abun ki shimafa angone dole kika canji Hajiya tafadi tana yar dariya, okay ashefa hakane sede naga kamar angon baya wani Happy sosae goggo rabi tasake fadi cikin tsokana,

shiru kamal yayi se dan murmusawa dayake Allah ne kade yansan abunda yake juyawa cikin ransa,

mikewa yayi yana fadin," mukam bari muje, kutashi muje kamal yafada yana kallon su fadeela, dukansu mikewa sukayi tareda yiwa su hajja mma sallma,

harsun kai bakin kofar parlourn suka tsinkayi muryan goggo rabi da fadin," afayiwa sirkata wankin kai yafi nakowa kyau harna amaryanma, tafadi tana dariya,


Kamal ne yajiyo ahanzarce yana kallon goggo rabi yana fadin," waye kuma sirkarki,? gatanan kana ganinta tanuna nisha da tasunkuyar da kai tana murmushi dan tasan halin goggo rabi da zolaya,

dan murmushin yake yayi kasan cewa yadan ji wani abu aransa duk da san fada kawai take,

dariya fadeela tayi tana kallon reeda data dan gimtse fiska fareeda iyayen kishi , sekuwa tasake fashewa da dariya because goggo rabi tasani sarai reedace sirkarta kawai tsokanace,


Fadeela ne tayiwa goggo rabi ido alamar takalli reeda daga Hajiya har goggo rabi kallon reeda suke suna dariya, reeda ganewar datayi da ita suke wannan dariyan yasa tafice da sauri tabar parlourn , Nisha ma tabi bayanta, ganin haka yasa kamal da fadeela suka rufa musu baya suka fice,

Goggo rabi takalli Hajiya tana fadin," ni naga gaba daya kamal ya canzamin, but senaga kamar baya happy da auranda zaiyi, sekace wanda za amasa dole,

Eh to kusan dolen za ace tunda bason auran yakeba, amma ai yanasun nabeela sede yan yanzune yake kokarin sauya ra ayi, kokuma auranne baya bukata yanzu,

tokumade mainene bakin alkalami yabushe , yanzu kamar kamal inbeyi aure yanzuba se yaushe,? Hajj mama ta tambaya tana kallon goggo Rabi, gsky de kama to allah de yazaba mana abunda yafi alkhari ya kuma basu zaman lpy, amin ya Allah Hajiya tafadi,

compound din gdn suka nufa inda akayi parking motorcin, kamal ne yasa key yabude motar yashiga, nan suma suka bude suka shiga, reeda na gdn gaba su fadeela da nisha suka nufi gdn baya,

mai gadi yana ganin shigarsu mota yaje yaye musu geat suka fice, tafe suke akan hanya suna ta zuba surutu, banda kamal dake tuki yana satan kallon nisha ta glass,

Tun Nisha bata kula da abunda yakeyi harta kamashi dumu dumu yana satan kallonta, murmushi kawai take tana dan girgiza kai, batareda su reeda sunsan wainar da ake toyawaba,

karo nakarshe da yadago suka hada ido Nisha ta tsinci kanta da sake masa wani kayaceccen murmushi wanda yasa kyakykyawar dimpul dinta baiyana, wanda yasa kamal rasa nitsuwarahi,

yafara kokarin sake hanyar daya kama, kiris yarage subugu da wata motar allah yatsare kamal yayi saurin kaucewa motar,

daga nisha harsu fadeela seda abun yabasu tsoro ganin abunda kekokarin faruwa dasu, oh my God bro what happened baka ganin kakusa buguwa wancan mai motar nagama kamar hankalinka baya kana driving din,


baki ganin shiya yasake hanyarsa ya kama hanyar da batasaba kamal yafadi yana dan hade gira, gefe kuma yamaida kallonsa ga glass yana kallon Nisha datake wuli wuli da ido,

murmushi yasake lokaci daya kuma yadan hade rai yana maijin wani iri aransa, inama ace da nisha zasu kasance matsayin ma aurata ba wataba, shikade yadinga sakawa da kunce cikin zuciyarsa allah ya isu dasu wajan saloon d'in
yanayin parking wayansa tashiga kara, nabeela ya baiyana screen phone din, fiska bayabo ba fallasa ya dauka ya kara akunne hade da sallama

Magana suka danyi daga bisani tasake tunasar dashi tana jiransa, because tunjiya da sukayi waya sunyi dashi zasu hadu yau, nan yasheda mata yana zuwa daga bisani sukayi sallma yakatse wayar,

reeda yakalla da tunda yafara wayar sukayi tsit suna tsauraron abunda ake cewa awayar," bari natafi inkun kammala komai you can call me

amarya tayi kira kenan to bari mu hanzarta muje se kadawo din reeda tafadi tareda kokarin bude kofar tafita , suma su Nisha fitan sukayi yayinda kamal yaja motar shi yatafi,


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D8AO9ndEkrVIe0gZ1Q9GcP

🥀🥀 IG AJEEMAL 🥀 🥀
Story and writing by Oum AmReesh ♥️ (khaleeseart Raeys)

Free book 🥰

Page 20

Nan suka karisa shiga cikin shagon salon din, ba mutane aciki daga mata mai saloon din se ma aikatan ta guda biyu , se wata babban mata matashiya da ake yiwa wankin kai,

sallma suakayi tareda kokarin neman guri suka zauna, cike da fara'a mata mai saloon din ta tarbesu da alama ta dade da wayansu, gurin ba bakonsu bane,

gaisuwa suka shiga yida mutane gurin daga bisani su reeda suka shiga fadin suzo ayimusu gyaran gashi mai kyau da kunshi mai daukar ido, because bikin yaynsu da za'ayi,

nan matar tasheda musu basuda matsala, batareda bata lokaciba ita dakanta ta tashi tana fadin cinsu wata tazo tasuma mata,

Nisha suka tura afara mata, ahankali Nisha tamike tazo aka suma da ita, sede gaba daya han kalinta yaki kwanciya da gurin,

because tun shigowar su wajan wacce suka samu anayiwa wankin kai take ta binta da kallo duk daguwar da nisha zatayi idon matar nakanta,

duk da batasan wani irin kallo take mataba, dan itade Nisha tasan ba sanin matar tayiba balle ace ko kallon sani take mata, to allah de masani,

seda aka kammala wa matar sannan tamike tasanya mayafinta tareda ciru kudi ajakar tamikawa matar tana fadin," to Aunty sofy gashi nagode nibari nawuce still hankalinta nakan Nisha,

okay Hajiya zulai nine da godiya se anjima kigaida gd Aunty sofyn tafadi, to gd yaji daganan hajiyar tajuya tafice,

bada wani bata lokaciba aka samu daman farayiwa su fadeela, emergency abunka da kwararro basu wani jima sosai shagon salon din ba, nan da nan aka kammala komai,

gyaran kai da kunshin da aka musu yayi kyau sosai especially Nisha yanda kunshin hanunta dana kafarta sukayi mata kyau kai kace itace maryan,

bugu da kari yanda gyaran gashin nan yayi kyau yasake black dashi se wani walwali yake yana daukan eyes,

ita kanta kallon kanta take tacikin mirror tana sakin murmushi yanda gashin kanta yasake kyau dashi ya zubu har bayanta kamar wata kyakykyawar ba india,

hasali ita kanta matar shagon tayaba da kyan yarinyar dakuma sumar da Allah yamata,

haka su fareeda suka komai yayi yaji allhamdullah because suma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login