Showing 3001 words to 6000 words out of 61982 words

Chapter 2 - IG AJEEMAL book1 Hausa Novel

03 Sep 2025

1533

Doctor?,

" Eh zaki iya ganinta but har yanzu bata farfaduba, amma munasa rain kafin gobe da izinin Allah zata iya farkawa kishiga ki dubata, to Nisha tace daga bisani ta dangana room din da umma take kwance,

Ahankali takarisa gadon da umma take kwance zama tayi kusa da ita tareda daukan hanunta ta daura saman nata, cikin kallo da tunanin halinda mahaifiyarta take ciki

" Allah sarki ummana allah yabaki lapia, ke kade kika ragemin aduniyar nan, ke kade nake kalla naji dadi hankalina ya kwanta, bakya bari nazubda kwalla balle har ta kaini ga kuka, amma yau nawuni cikin kuka da hawaye, nayi kukun da bantaba irinsaba, but narasa mai lallashina, yau narasa inda zan shiga naji dadi, kuka ta fashe dashi kasa kasa gwanin ban tausayi, seda tayi kukan ya isheta harta suma jin ciwon kai, sabuluwa tayi daga saman gadon tazauna kujera ta kifa kanta jikin gadon tana maida ajiyar zuciya, tafi mintuna ahaka jin shigowar nurse ne yasa ta daga kai tana bin nurse din da kallo yayinda take karawa mahaifiyarta ruwa, murmushi nurse ɗin tayi tana kallon Nisha tana faɗin,

" yadai sis? ummna zata bude ido tasamu sauki? Nisha ta tsinci kanta da yiwa nurse ɗin tambayar ,

" mai zai hana za ayi aiki tasamu sauki karki damu kanki zata warke takoma garau kamar ma bata taba ciyoba, don't worry barinaje nabarki lapia " nurse ɗin tafaɗi cike dayiwa Nisha murmushi tafice, tabbas maganar da nurse din taimata ya dan kwantar mata da hankali, kiran sallan magarib daya ratsa kunnowan tane yasa ta mike tanufi toilet alwala tayiyo tafito tana yarfe ruwan fiskarta, to damema zanyi sallanne bayan ban dauko komaiba ta tmbayi kanta, kode naje gdnsu salma nayi sallahn na dawone, shiru tayi se kuma tafito daga room din tanufi dakin da ke gefensu sallama tayi hade da tura kofar tashiga,.
. tsayawa tayi tana bin matar da kallo , babbar matace tsuhowa fara tass kalar larabawa tana sanye glass aidonta waya take shiya sanya Nisha tsagai tawa, wai me kuke nufine kunbarni da yaro kuma gashi haryanzu baku lekoba, ku komai naku nasaibi, ganin yarinya tsaye daga gefe shiya sanya hajiyar dakatawa da wayar da take, ta tsaya kallon yarinyar yayinda take kokarin karisuwa,

" sannu Hajiya " Nisha tace yayinda tamaida kallonta ga yaron dake kwance gefenta an daure kafarsa da bandage da alma karayace,

"yauwa sannu " Hajiya ta amsa tana kallon yarinyar,

"ya maijiki"

Nisha takuma faɗi tana kallon kyakykyawar yaron game da tausayawa,

" Alhamdulillah " hajiar ta kuma amsawa daga nan Nisha tashiga tambayar taimakon sallaya zatayi sallah because basu tahu da komaiba,

" lah bakomai gashin nan Hajiya ta dauka ta mika mata cike da fara'a da sakin fiska, cikin hanzari Nisha ta amshi sallayar ta shimfida ta tada sallah, tunda tafara sallahn Hajiyar taketa binta da kallo, yarinyar tashiga ran Hajiyar dagani yarinyar akwai hankali da nutsuwa gata kyakykyawa da ita, hajiar na tsaka da maganar zuci tajiyu sallama, wasu kyawawan yan matanne guda biyu suke tafe da alamu ko jikokintane, hannunsu dauke da basket din abinci daya nabin daya suka shigo suka zauna, sannu Hajiyarmu kinsha zamafa, bata cemusu komaiba, se binsu da kallo da takeyi, bayansu wata matashiyar matace ke tafe da kaganta kaga wayewa da karatu, fiskarta babu annuri ta karisu ta zauna kusa da yaron dake kwance time din ya bude ido,

"Oh my baby boy yajikin naka tafaɗa tana shafa gefen fiskar yaron, ,

" uhm uhm mommy kikiramin papa, dafa shoulder dinshi tayi tana faɗin,"

What happened kake neman papanka kasan baza asameshi Wannan time din ba so what do you want,

"mommy ciyon zafi " yafaɗa cikin sigan kuka,

"oh sorry dear zai dena kajiko, gyada mata kai yayi yana matse ido, so inzuba maka food abunda kakeso nadafa maka,"

" eh " kawai yace nan tasumu zuba masa abincin, kallonta kawai Hajiya keyi tashigo but ko kallon ta batayiba balle sannu ko madallah, hmmm Allah yakauta, muryan nisha nisha sukaji tana fadin,

" Hajiya ga sallayan nagode,

"lah bakomai yata, se yanzu hankalisu ya dawo kan Nisha da tun shigowar su bawai sun lura da ita bane, zuba mata ido sukayi suna kallon ta, itama Nishan kallonsu take tareda gaishesu, yan matan ne suka samu daman amsawa, but ita dayan Nisha ko kallo bata ishetaba balle tasa ran amsa gaisuwan ta, kokarin fita Nisha tasunayi, Hajiya tayi saurin faɗin,

" tsaya ki karba muku abinci mana tunda naji kamar kince baku taho da komaiba,

" lah Hajiya kibarshi kawai nagode zanje na dauko agd" Nisha nafaɗin haka tajuya da sauri tafita daga dakin tanufi dakinsu, waje tasamu tazauna tana tunanin kirki irin na Hajiyar, wata zuciyar cewa tayi

'dama kin tsaya kinkarbi abincin ko kya kori yunwar dake tare dake, amma kikace zakije gd kidauko ko dakin wata uwar zaki dauko oho'

sallama taji anbudu kofa azatunta doctor ne, setaga wayan nan yan matan ne suka shigo daya nabin daya tareda basket din abinci hanunsu, daga gefe suka tsaya suna kallon mahaifiyar Nisha cikin tausayawa , kallon Nisha sukayi suna murmushi tareda tambayar ya mai jikin, Nisha ta amsa musu dacewa

"da sauki "tana kallonsu irin tsan tsar kyau dake tareda yan matan kamar ba yan kasarba,"

"hajiyace tace mubiyoki da abincin nan tunda kinki karba acan "daya daga cikinsu tafaɗi,

"Ayya nagode sosae Nisha tace tana dan murmushi, ajiye mata basket din abincin sukayi tareda kokarin juyawa sufita, dasauri daya daga cikinsu tajiyu tana fadin,

"munyi mantuwa baki fada mana sunan kiba" jiyuwa sukayi gaba dayansu suna kallon Nisha suna jiran amsa,

"sunana Aisha ko kice anisha amma anfi kirana da nisha, wow nice name nikuma,

" fareeda but ana kirana da reeda sisterna kuma fadeela nice to meet you suka Faɗi,

" nima haka " nisha tafaɗi tareda musu godiya, daga nan suka mata sallama suka fita, Nisha najin fitarsu da sauri tadauki plate tafara kokarin zuba abinci, bude food flas din abincin tayi koda budewa wani dadda dan kamshi ya buwayi hancinta, kuskusne yaji hadi gami da kayan lambu anyanka hanta kana na kana na, se zuba kamshi yake yawunta yawunta ba karamin tsinkewa yayiba, dayan kulan kuwa papper chicken ne yaji albasa se zuba kamshi yake shima, nan ta diba tasuma ci, tunda tagara ci take santi saboda dadin abincin, seda taci takore yunwar cikinta daga bisani takai hanu ta tsiyayi sassanyar lemon juice yayi sanyi dadin shaa, tana tsaka dashan lemon ta tsinkaya muryan umma tana fadin," zatasha ruwa, azabure Nisha tamike tayi kan umma,

Nisha tsayawa tayi kan umma dake kwance tana kokarin bude ido, da sauri Nisha tashiga tallafo umma tana faɗin

"Umma kibude idonki kinganni tafada cikin sigana kukan farin ciki,

" ruwa ! umma tasake faɗi karo nabiyu, da sauri Nisha ta tashi tadauki ruban ruwanda su reeda suka hadu mata cikin basket tashiga zubawa cikin cup tanufi umma tareda tallafo ta takai mata setin bakinta jikake makot makot tana shan ruwan, wani dadine ya lullube nisha zuciyar ta nayin wani sanyi, tana kammala bata ruwan tashiga kokarin gyara mata zama tasanya mata filo abayanta yanda zataji dadin zaman, umma bari naje na kira doctor Nisha tafadi tareda ficewa da sauri,

Ba adadeba suka shigo tareda likita, doctor seda ya duba umma sosae yakalli Nisha yana faɗin,"

Masha Allah akwai alamun nasara inshallah, "sede kuma naga bata bude ido ba Nisha ta tambaya,"

"wannan ba wani matsala bane zata bude ahankali," allura yamata yasanar da nisha cewa koda yaushe zata iya farkawa, kuma anemi ruwan zafi kokadanne tasha, wani ruwa yakuma daura mata daga bisani yafice, wayanta ta laluba ta dannawa salma kira, aikuwa kamar jira take carab ta daga,

"Yar duniya tunyaushe nake kiranki kinki picking, ko bakiga miss call dina bn, salma ta tambaya, "

"Ke nagani bana yanayin da zan iya dagawane, nisha tafadi cikin damuwa,

"What happened,? salma takuma tambaya,"

"Ummace ba lapia muna hospital,"

" kai amma bakida mutunci umma ba lapia shine koh labarin, wani asibiti ne yanzu zan gayawa ummy zamuzo ,"

"nan Nisha tafada mata hospital din dasuke daga bisani Nisha ta sanar da salma tana da bukatan ruwan dumi, salma tace ba matsala semunzu,

"inkun iso please you can call me, okay salma tace daga nan ta katse wayar, juyuwar da zatayi suka hada ido da umma, gaban tane yafaɗi yayinda bakinta yayi hanzarin faɗan,

" umma!, hade da fadawa jikinta tasaki wani sabon kuka,

"Nisha aina muke" umma ta tambaya cikin raunin murya na marasa lapia,

"muna hospital ne nisha ta bata amsa tana kallonta,"

Ina mahaifinki, ? daguwa nisha tayi tana kallon mahaifiyar tata, abba kuma,?

"Baizoba baima san awani hali mukeba, kuma ba inda banje nemansaba amma ban sameshiba, umma meye kike nemansa bayan ganinan kusa dake , what do you want tell me nizan miki, kurawa nisha ido umma tayi kafin tace,

"fushi kike da Abban nakine,?" hawaye nisha ta shigayi Shar shar kafin tace

," umma Abba ya dena sanmu yanzu ko inda muke baya son zuwa, tun yaushe rabonmu da musashi a ido, kwata kwata yanzu bai damu da muba balle yasan halinda muke ciki, ayanzu hankalisa ya koma kan mami yafi sonta harma.... kuka ne yaci karfinta nan ta sunkuyarda kai sotake ta sanar da umma abunda ke faruwa mami ta tashesu da gdnsu because acewar ta abbane ya mallaka mata, but se kuma ta fasa saboda halinda umma ke ciki bai kamata ta sanar da ita ba, muryan umma taji tana fadin,

"Ki kwantar da hankalinki, karkiyiwa mahaifinki irin wannan kallon, duk abunda kikaga yanayi bawai cikin hankalinsa yakeba, baisan yanayiba kuma ba laifinsa, ninasan halin mijina, nizan bada labarin abunda zaiyi da kuma abunda bazai aikata ba, inaso kisani ko bayan raina ban yadda kinisan ceshiba, duk duniyar nan bakida wani gata da yawuce shi, haka shima kafa daniyar ba abunda yafiso kamarki, kuma kema shaidane ba karamin abubane zaisa mahaifinki ya nisan cemu lokaci daya ba tareda wani dalili ba, dan haka, kinemesa aduk inda yake kinuwa duniya ke diyarsace, mahaifinki makiyane akewaye dashi duk inda yake suna nan biye dashi, kidinga masa addu'a akoda yaushe, zanyi alfahari dake kobayan raina"kuka nisha tarushe dashi tana faɗin,

"Umma kidena irin wannan maganan " ta gama tsinkawa Nisha zuciyar, hanu Nisha tasa tashare hawayenta hadeda dagowa takalli umma tana fadin,

" naji maganar ki kuma inshallah zan kasance mai biyayyawa maganarki, plate tadauka tashiga zubawa umma abincin tareda dire plate din abinci gabanta tana faɗin,

"Umma kici abincin kafin salma sutaho da ruwan zafin, cikin kosawa da magana umma tace,

"bana bukatan abinci ayanzu" tafaɗi tareda ture plate din gefe, wayan Nisha ne yashiga kara, dan dubawa tayi taga salmace hakan yasa tamike tsaye tana faɗin,

"bari naje na shigo dasu salma, gyada kai kawai umma tayi Nisha tasa kai tafice, bata dadeba suka shigo tareda su salma hanunsu rike da kayan bukatu, waje suka samu suka zauna salmace tasuma magana dacewa,

" sannu umma yajiki,

Jiki alhmdllh salma umma tafaɗi fiskarta daukeda murmushi, daga bisani ummyn salma ta karbi gaisuwan dacewa,

" sannu ashe bakiji dadi ba, ,"

"Wlh kuwa, "

"ayya yajikin,?

"Jiki da sauki allhamdullah,

"to allah ubangiji yakara sauki,

" ameen ya Allah"

Salma zungurin kan Nisha tayi tana fadin," umma ba lapia shine ko kisanar damu kiketa dawainiya ke kadai kirkinki yayi kadan gsky,

"Keyanda nake cikin tashin hankali ina tunanina zaikai nan, bakisan damuwar danashiga yau bane, Nisha tafaɗi tareda daukan cup tashiga hadawa umma tea, nisha nagama hadawa ta mikawa umma cup takarba tasuma shaa, to nisha bari muje munbar gd bakowa ga dare yayi, allah yakara sauki gobe zamu dawo, ummyn salma tafadi tareda mikewa,

" to mungode Allah yasaka umma tafadi yayinda ta dire cup din tea gefe, seda Nisha ta rakasu har bakin geat sannan ta dawo, Nisha na karisa shigo tayi gefe da cup din tea din tasamu daman zama kusa da umma tana kallonta, itama umma kallon Nisha take tana faɗin,

" sallah nakeson nayi, kallon ruwanda aka daurawa umma nisha tayi tana faɗin,

" ruwanma yakusa karewa bari nakira doctor yacire miki inyaso sekiyi sallan, nisha na faɗin haka tajuya tafita, ba adadeba suka shigo tareda likita yacire mata ruwan yana mai tambayan ta ko akwai wani damuwa ko matsala, nan umma ta sheda masa ba wani damuwa,"

"To masha Allah haka akeso inkinyi sallan anjima za azo asake daura miki wani ruwan,"

" to ' kawai umma tace, doctor yafice, Nisha matsowa tayi ta taimakawa umma ta sakko daga gadon ta rakata har toilet, adaddafe umma tayi alwala kasance wa jikin bawani kwari sosae yayiba taurin zuciyane irin na umma, seda takammala alwala tafito Nisha na ganin fitowar ta yasa tashiga taimaka mata wajan fitowar ta maida ta gado tareda sanya mata hijab, azaune tayi sallanta yayinda Nisha kuma ta kura mata ido tana kallonta, tana jin wani dadi yana ziyartar zuciyar ta, bayan umma ta idar da sallah tamaida kallonta ga nisha data tsareta da ido ta fada kogin tunani, murmushi umma tasake ganin yanda nisha ke kallonta, tasuwa nisha tayi tazauna kusa da umma tana murmushi, awannan dare Nisha sunyi hira da umma sosae kamar baza arabuba, haka har bacci barawo yasacesu, can cikin dare nurse tashigo takarawa umma ruwa, kallon su nurse din take gwanin shaawa hannayensu cikin najuna se sharar baccinsu suke hankali kwance, seda ta kammala abunda take tajuya tafita,
__________________________________

wajan 6:30 nisha tafarka tabude ido gari yayi haske hakan yabata daman mikewa tana kallon ruwanda aka daurawa umma , ahankali yake tafiya bayida alamar karewa yanxu, toilet tanufa tayi alwala tafito, tashin fida sallayan da salma takawo musu, ba karamin tai mako salma tayiba da yanzu haka zata sake fita aron sallaya har ace kwadayi ke kaita, gabatar da sallanta tayi, bayan ta idar tacigaba da lazimi tana addu'a, tana kammala wa, ta ninke sallayan tamike tanufi gurin umma tazauna daga gefe, tayi tunani tashin umma tayi sallah se wata zuciyar ta hanata hakan, tsagaita wa tayi taga ko umma zata farka amma shiru babu alamar zata farka, ganin haka yasa Nisha tashiga tashin umma tana fadin,"

Umma! Umma!! Kitashi garifa ya waye, gabantane yafidi ganin ba alamar zata bude ido duk da jijjigata da takeyi, nan tashiga kokarin dagota but seji tayi ta dagota asandare, hanu tasa ta dago na umma, se kuma tasake da sauri tana bin umma da kallo, shigowar nurse din ne yasa Nisha tamike dasauri tanufi nurse din tana faɗin,

" please kidumin umma na ki tabbatar min da hasashena karyane ba gaskiya ba tafada cikin sigan kuka, jin abunda Nisha ke faɗi yasa nurse din tayi saurin matsawa gadon umma tashiga dubata, babu alamar motsi ko numfashi atareda ita idonta kuma dama arufe yake, to itamade bazata iya cewa komai ba seta kira doctor, dan haka ta kalli nisha dake ta sharbar kuka tace,"

I'm sorry..... bata jira mai nurse ɗin zata sake fadɗa ba tasake wani kukan tana faɗin,

"Innalillahi wa'inailaihi raju'un tafadi tareda kokarin fita waje, nurse dince taja hanun ta tana kokarin lallashinta da ta kwantarda hankali amma inaa tafizge hanunta tayi waje da gudu bakinta nafadin,"

Doctor

*****____________'_''''''________________*****

Tafiya yake cikin natsuwa warsa na setin kunnansa da alama amsa kira yake, kyakykyawa matashi maijin kanshi inka soma kalloshi bazaka so dauke ido kanshiba, yana sanye cikin kyakykyawar shire mai daukan hankali, ahankali yake mutsa pink lips dinshi yayin maganar ko wanda ke kusa dashi ba lalle yaji abunda yake faɗi ba, because slowly yake maganar kansa na kasa baiyi auneba gab yaji sunyi karo da mutum, cikin hanzari ya rikota ganin tana kokarin faduwa, hankali ya ware sexy eyes dinshi yasuma bin yarinyar dake rike da ita da kallo, itama waro idonta tayi dasuka kankance sun kumbura saboda kuka, cikin rawar jiki tasuma janye jikinta daga nashi tana kokarin yin baya,

shikuwa jin tana kokarin zamewa yasashi sake rikota da kyau, jitake numfashinta na sama sama zuciyar ta se wani irin bugu take, shi kanshi yana jiyu yanda heart beat dinta ke bugawa da sauri sauri, gani yayi ta bude baki da nufin magana, se kuma yaga tarufe ido ta sake masa nauyin jikinta, alamar da tabashi tabbacin suma tayi, nurse din data biyo bayanta ne takariso da sauri ta suma kokarin tallafo ta, su Hajiya dake ciki suka jiyu ihu yasa suka fito da hanzari dan suga abunda ke faruwa, reedace ta taimakawa nurse din suka ciccibi nisha akayi wani room da ita, suma su hajiyan suka rufa musu baya domin jin ba asin ihunda take,

tsayawa yayi yana ganin ikon Allah danshi atunanin shi yarinyar tabin hankali gareta jin yanda take ihu, kamar mai tabin hankali, duk tabi tacikawa mutane hospital da ihu, wani guntun tsaki yaja yana binsu Hajiya da kallo dasuka rufa musu baya sunata rawar jiki, tabe baki yayi tareda shigewa cikin room din da dansa yake kwance, akwance yaron yake saman cinyar mom dinsa ganin papanshi yasa kokarin mikewa zaune Yana washe baki, karisawa yayi kusa da son din nasa yayi tareda sakin murmushi wacce takarawa face din nasa kyau, yana faɗin,"

My little boss ya jikin naka,? I hope everything is going well ,? gyada kai yaron yayi cike da farin cikin ganin papanshi,

"Alright do you need something? papan nashi yakuma tambayarshii yana kallon dan nasa,

"no papah "


"Okay " abunda yace kenan yamaida kansa ga wayarsa yashiga matsawa, tunda yashigo yazauna suka suma magana da son ɗin nashi baidago kai ya kalletaba kamar baisan da zaman mutu awayan ba, kamar tayi maganaba sekuma tamike tana fadin,

" tunda ka iso bari nasamu natafi gd nayi wanka nawuce office , kazauna dashi kafin wadancan su dawo daga gulmar da suka tafi" wani banzan kallo ya wurgeta dashi yana fadin,"you well not going anywhere
seat down and care him nan kuma yamaida kallonsa ga yaron yana faɗin,

" zan tafi but letter I'm come back gyada masa kai yaron yayi yana faɗin

"To papah" ko kallon ta batayiba yajuya yafita abunsa, itama wani guntun tsaki taja tareda neman seat tazauna, *******Nisha*************

bangaran Nisha suma take tana farfaduwa tana surutai tana kiran sunan umma, su Hajiya kuwa kallonta suke cike da tausayawa, Nisha gaba daya bata cikin hankalinta, cikin asibitin akayiwa umma sitira aka mikata gdnta nagaskiya, Hajiya ce tasa aka shirya komai, kwanan Nisha biyu bata san inda kanta yakeba, se surutai taketa faman yi kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login