Showing 24001 words to 27000 words out of 61982 words

Chapter 9 - IG AJEEMAL book1 Hausa Novel

03 Sep 2025

1540

ammi da ta nufi kitchen dan duba halin da baba Barka take ciki,

tana zuwa tasamu baba Barka takammala komai, nan ta tayata suka jera komai inda ya dace, daga bisani ammi tanufi bedroom dinta sallah, tana shiga tayi alwala tayi sallah tanufo kasa,

direct bedroom dinsu Nisha tanufa domin dubata taga awani hali takeciki, tana zuwa tasameta kwance tana bacci da almun baccin nata yayi nisa sosae, dafa koshinta tayi wanda yayi sanyi qlau da alamar zazzabin da takeji ya sauka, ganin tana zufa yasa ta dauki remote din AC ta kuna mata takuma rage fawanshi kadan, ahankali sanyi mai dadi dasa kwanciyar hankali ya lullube dakin nan taja mata kofar tafito,

akokarinta nafita su fadeela suka kunno kai zasu nufi bedroom dinsu, kukuma fa ammi ta tambaya, sallah zamuyi sukaba amsa atakaice, to kadde kutashi yarinyar nan , to shikenan karki damu baza mu tashe miki babynkiba suka cikin zolaya suna dariya suka she dakin nasu,

ammi ban garan Hajiya tanufa tasanar dasu abinci ya kammala sufito suyi lunch, rabi tashiga wanka bari inta kammala se mutafi gaba daya Hajj mama tafadi , okay ammi tace tareda da neman guri tazauna sukashiga hiransu,

bada wani bata lokaciba goggo rabi tafito cikin wani shiri maikyau shin riga da siket na atamfa tamata kyau kamar su yakara fito da dan uwanta wato daddy , rabi duguwar ce fara mai diri maikyau ga manyan idanu kasan cewa ba inda taba mamanta wato Hajiya,

duk da ta manyanta ga wanda bai santaba in aka fadi she karunta bai ce tayi wannan shekaruba, murmushi yasakar musu yayinda take karisuwa tazauna,

dama ke muke jiran fitowar ki, the food is ready, ammi tafadi yayinda take kokarin mikewa daga zaman datayi, suma mikewa sukayi tareda rufawa ammi baya suka wuce babban parlourn, domin cin abincin,

suna zuwa suka tarar da su fareeda suna zaune a dining table din suna jiransu, lallai fa har kun rigamu zuwa da alama yunwace takoroku, goggo rabi tafadi tana dariya, suma dariyan su fadeela suka kayi batareda sunce komai ba,

dukansu zama sukayi suka suma cin abincin sunci suna dan hiransu har suka kammala, nan rabi take tambayar Daddy a tunanin ta yau weekend ba aiki, ammi ta sheda mata yafita dan yasanar da ita yana da tattaunawa da wasu abokan hurdansu, but kafin dare zai iya da wowa,

yinin ranar bakaramin dadi yamusuba because goggo rabi tasamu kawo musu ziyara , kasan cewa rabi tana da barkwanci bata da matsala kokadan shiyasa suke kaunar zama da ita,

aban garan Nisha kuwa tayi bacci sosae yanda yakamata itace batasamu farkawaba se kusan goshin magarib, bude ido tayi amma takasa mutsawa ta tashi gaba daya jikinta amace yake, rinza ido tayi kamar wacce takoma bacci amma azahiri idonta biyu,

hanunta nakan maranta dayake dan murda mata da because dama dan baccin da tayine yasa tadan rage jin zogin, ta dauke dugun lokaci ahaka tana kwance idonta narufe, harsu fadeela suka shigo sukayi sallah suka sake fita duk akunneta tana jinsu ,

ganin kwanciyar kamar shike kara mata radidin datakeji yasa tamike har wani jiri jiri takeji, gaba daya tagama laushi, ahankali tasuma cire kayan jikinta, tareda samun towel ta daura tanufi toilet, wanka tayi sosae, daga bisani tafito tanemi kaya tasa,

ahankali ta taddafa tanufo parlourn ganin shiru ba alamar kowa aciki yasa tanufi inda tan suka saba zuwa, akokarinta nabarin parlourn, taci garo da AJEEMAL dake kokarin shigowa parlourn , kallon kallo sukashigayi, yana kallonta tana kallonsa da rinannun idanuwanta da suka canza launi,

dan jabaya yayi kadan yana sake dubanta kadan kamar wacce yau yataba ganinta, ita kuwa jiki se bari yake ganin irin kallon da papan aheel ke mata wacce itama batasan wani irin kallo bane wannan,

," follow me abunda yace kenan yafara kokarin juyawa, ganin batayi mutsiba yasa yajuya tareda cilla mata wani irin harara," ko bakiji abunda nace bane yafada cikin wata irin murya, " naji Nisha tace bakinta nabari, juyawa yayi itama tarufa masa baya,

tafiya take ahankali yayinda takejin zuciyar ta kamar zata faso heat dinta, tsabar tsoro,

part disa yanufa yatura kofar yashiga, nan ya tsaya tsakiyar parlourn yana jiran shigowar ta,

Nisha kuwa tsawa tayi a kofar parlourn takasa shigowa, tsoronta mai zai fada mata, "baza kishigo bane, nisha ta tsinkayi murya AJEEMAL yana tambayar ta, shigowa tayi ahankali tareda sake bude kofar dakyau because in abun yatashi naguduwa ne basetasha wahalar bude kofar ba, sede tafita da gudu, close the door and seat down here, yanuna mata saman capet, yana tsaye yana kallonta tamatsu ahankali ta tsuguna inda yanuna mata jikinta se bari yake kanta na sukuye kamar wacce ta aikata ba dai ba,

ganin tasamugu tazauna hakan yabashi daman karisuwa bedroom dinsa, still kan Nisha nakasa, har yaje yadawo yasamu kujera nisa da ita yazauna tareda daura kafarsa daya kan daya, yana karewa Nisha kallo wacce kanta ke kasa cikin kakkausar murya yace," ke? cikin hanzari Nisha tadago takalleshi jiki nabari, hanu yamata almar ta kariso,

ahankali Nisha tashiga jan gwiwarta tana kokarin karisawa, seda ta iso dabda kujaran da yake zaune sannan tagyara zamanta saman capet hadeda sunkuyar da kai domin sauraron abuda zaice,

cikin natsuwa yake binta da kallo daga bisani yasa hanu ya dauke black back din dake gefensa yadaura bisa cinyarta yana fadin,"

take this and opened,
ahankali Nisha take bin jakar da kallo, hanu na bari tasa hanu taja zip din jakar tabude makudan kudadene aciki da alamar kudin bata kasar mu, nigeria bane,

I hope kin gane jakar kudinki? AJEEMAL yafadi yana dubanta, gabantane yafidi tadago tana kallonsa tana son jin karin bayani dan kwata kwata ba abunda yazo mata arai,

girgiza masa kai tashiga yi alamar aa tana kuma sake kallon jakar dake gabanta,

bana so na tambayi abu amin karya nakanyi hukunci, hukunci kuma mai tsawari , yana fadin haka yakuma yajin gina kansa da jikin kujera, "

doctor fu' ad shiya bani jakar nan kuma ya shedamin yarinyar da take gdnmu ita takai kudi domin ayiwa mahaifiyar ta aiki, kafin aimata aikin, allah yamata rasuwa,

tambayar da zan miki anan shine, ina kika sami wadannan kudaden, doctor fu'ad ya fada min cewa lokacin aka bukaci kudin ayinin ranar kika kawo, kuma yasheda mun kubamasu karfi bane kuma bakuda hanyar samun kudin da akeda bukata,,

Badole bane na bukaci nasan inda kika samu wannan kudaden ba, but yanzu kin kusanci familyna har kinsamu nasaran shiga zuciyar su, bugu da kari kinsa soyayyarki acikin zuciyar dana dana family,

dan haka bazan zuba ido wani abu yakawo mana shakko acikin family ba,

zan sake tambaya ki karo nabiyu, karkuma kimin karya hakan shi zai baki daman kwanciyar hankali gdn nan,"

so tell me wakika daukarwa kudi,? nina miki alkawari zansa a mayarwa maishi batareda kowa yajiba, yafa yana kallonta,

Nisha kam tunda yasoma mgn hawaye suka shiga wanke mata fiska, tarasa mai yake mata dadi, tabbas wannan kundin da kamal yabatane ,

to amma Allah yagani bazata iya sanar da AJEEMAL cewa kamal ne yabataba, bakiji mai nace bane AJEEMAL yafada atsawace,

cikin hanzari da rudu Nisha tace,"

wlh tallahi ba wanda na daukarwa kudi kuma ni tunda nake banta daukarwa wani kudinsaba bani akayi tafada tana shashshekar kuka,

Gyara zama AJEEMAL yayi tareda fadin," okay who are given ,? kuma wani aiki kika masa yabaki, cikin hanzari Nisha tadago tana dubansa because takasa fahimtar inda zancensa ya dosa, wani kuka tarushe dashi jin zarginda yakeso yalika mata,

wani guntun tsaki yaja yana fadin," nifa ba kuka nakiraki kiminba tambayar ki nake kuma amsa nake bukata, ganin bata da alamar amsa tambaya shi, yasashi tsagaitawa yana sauraron kukanda take rerawa,

ganin zasu batawa juna lokaci yasashi cema ta tashi tabashi guri daga ita har jakar kudin nata, jin haka yasa Nisha tamike dasauri daga ita har jakar fuuuu tayi waje da gudu tana kuka,

AJEEMAL bin bayanta yayi da wani harara hadeda guntun tsaki gaba daya yasakejin tsanar yarinyar acikin zuciyar sa, kalleta is too young amma tana kokarin bata rayuwar ta akan wani dalili,


jin aheel yafado cinyarsa yasashi dawowa daga tunanin da yatafi, dagoshi aheel AJEEMAL yayi yana kallonsa yana fadin," katshi, eh papa, aheel yafada yana duban mahaifin nasa,"

papa mai kayiwa aunty naga tafita tana kuka, AJEEMAL bin yaro yayi da kallo wato da alamar yaga abunda yafaru kenan, bakomai AJEEMAL yafadi tareda mikewa yamaida aheel kujara ya zaunar dashi, jirani anan bari naje nayi sallah na dawo,

aban garan Nisha kuwa tunda tabar daki tafi waje, tasamu daga gefe talafe tana share hawayenta , seda tabbatar bakowa haraba gdn hakan yabata daman shiga parlourn ahankali, duba da cewa bakowa parlourn yasa tazura dagu tayi dakinsu, waje tasamu daga bakin gado tashiga rera kuka mai cin rai, tana tuna kalaman AJMAL dayayi akanta, jakar hanunta takalla tana fadin," dole namaidawa da kamal kundinsa , yanzu damuwarta daya, ina zata ajiye Wannan jakar kafin haduwan su da kamal, dan tabbas a deran yau takesun tamai da masa, kuma batada bukatar kowa yasan da kudin har ta maida masa, because bataso kowa yasan tasan kamal tunkan zuwanta gdn

jin muryoyinsu fadeela da alamun sunshigo parlourn yasa tayi saurin sunkoyawa kasan gado ta tura jakar kudin tareda mikewa tanufi saman bed takwanta ta lumshe ido tamkar mai bacci,

su fadeela suka shigo bedroom din daya nabin daya suka karisu tareda haura saman suna fadin,"haba wakiup mn, tundazu se bacci kike ko abinci bakiciba,

bude ido nisha tayi ahankali da idonta ya kubura tsabar kukan da tasha, ganin haka yasa reeda tace,"what happened Nisha, naga idonki ya kubura kamar wacce kikayi kuka,

ko cikin nakine bai daina ciyoba haryanzu fadeela tafadi tana kallonta cike da tausayawa, mikewa Nisha tayi tazauna tareda kallonsu tana fadin," ciyon cikin nan ya matsamin dayawa, haryanzu bai dena ciyoba,

okay to yanzu kitashi kizo muje muci abincin daga bisani sekisha kikara shan magani ki kwanta reeda tafadi tana kallonta,

banjin yunwa bazan iyacin komaiba yanzu, bayadda basuba dan ta bisu suci abincin amma sam taki, ganin haka yasa suka fita daga dakin, suka nufi parlour,

a dining ta tarar dasu ammi dasu Hajiya da goggo rabi suna zaune suna jiransu, karisuwa sukayi suna kokarin zama ammi ta tambaya ina sukabar Nisha nan suka shiga zaiyanu mata yanda sukayi,

amma ae bai kamata mara lapia yazauna da yunwa musamman da kukace tun breakfast bata sakecin komaiba, fadin goggo rabi because already dama su Hajiya sunbata labarin Nisha ahiransu na dazu sun sanar da ita komai,

bari mu kammala zanje nasameta dakaina ammi tafada, daga bisani suka shiga fara cin abincin su, suna dan hiransu , seda suka kammala , ammi takai hanu tazubawa Nisha zazzafan pepper soup na kayan ciki da jalop din kuskus yaji salad tadaura akan try, tanu dakinsu Nisha,

kwance ta sameta, yayinda kanta ke kallon sama tanata sake sake cikin ranta, jin ana kiciniyar shigowa dakin yasa tamaida kallonta ga kofar, ganin ammice tashigo hanunta dauke da try din abinci, hakan yasa Nisha tamike daga kwanciyar datake tazauna tana kokarin kirkiro murmushi,

zama ammi tayi kusa da Nisha tana fadin," yajikin , tareda kokarin ajiye try din abincin saman capet,

hand dinta takai gefen fiskar nisha tana fadin," ahar yanzu cikin naki naciyo ne, gyada mata kai Nisha tayi hawaye na kokarin gangaro mata,

sorry gashi kuma bakisa komai acikin kiba tun safe shiyasa , yakamata kici wani abu maybe ma harda yunwar take kara miki ciyon cikin, tafada yayinda ta dire mata plate din abinci gabanta,

maza kici kidaure kitaba kokadanne, ammi tafada yayinda takai mata 1 spoon bakinta, karban spoon din tayi tasuma ci ahankali, yauwa inkingama ga plate din pepper soup ma yana jira acinyemin shi tass,

hakade nisha ta dan ci abincin, tanaci ammi na tsokanarta, seda ta tabbatar taci sosae takyaleta, ta dauki try din abincin tana fadin," bari naje nadawo, bayan ammi Nisha tabi da kallo nan da nan tafashe da kuka, because yanda taga ammi na kula da ita sekace daga cikinta tafito,

tadauketa kamar yarda ta haifa, kular da take bata kosu fadeela batabawa, jin shigowar ammi yasa tayi saurin hadiye kukan da takeyi tashiga mis mis da ido,

ammi magani tabude tabawa Nisha hade da ruwa, nan nisha ta karba tasha, daga bisani ammi tace mata takwanta tayi bacci,nan tai mata seda safe tayi ficewarta,

parlourn ammi takoma tazauna aka cigaba da hiran da ita, " oo yau kama ganin Daddy yamin wuya bacci nakeji but kuma inaso naga dawowar daddy, yau tunda nazu daga MODIBBO har kamal bawanda nasa aido, shima daddyn shiru haryanzu goggo rabi tafadi cikin jimami,

da kinyi hakuri ma ibaki gansu yauba zaki gansu gobe, Hajj mama tafadi,

dariya ammi tayi tana fadin," wlh kam dan seta gaji da ganinsu, nan suka cigaba da hiransu har wajan karfe 9:30 daga bisani goggo rabi ta mike tana musu seda safe domin kuwa tagaji tana bukatan hutu,

suma mikewar sukayi domin kuwa dare yayi kowa da alamar baccin aidonsa, nan suka shiga yiwa juna seda safe kowa yawatse yanufi turakarsa banda ammi da tazauna zaman jiran shigowar Daddy,

se guraren karfe 10 Daddy da kamal suka samu daman dawowa gd, daddy parlour suka shigo tareda kamal, ganin shigowar su, ammi tashiga musu sannu da dawowa, jakar daddy dake hanun kamal ammi ta karba tana tambayar su, akwai yunwa ko babu domin tasa barka ta kawo musu abinci, nan suka shaida mata ba mai bukatar wani abu yanxu,

nan kamal yamu seda safe yafice daga parlourn yanufi bedroom dinsa, ammi da Daddy suma suka haura upstairs sukanufi nasu dakin, anan ammi take shedawa Daddy zuwan kanwar sa, goggo rabi,

su fareeda tuni sunyi nisa da bacci banda Nisha da tayi lumui kamar mai bacci, sedata tabbatar baccin su yayi nisa hakan yaba taman lallabawa ahankali ta sauka daga bed din,ta sunkuya tareda zaro jakar daga kasan gadon cikin sanda tanufi hanyar waje,

kofar parlourn abude yake hakan yabata daman budewa ahankali ta fita, gida yayi shiru alamar dare yayi sosai, cikin tsoro tanufi sashin kamal, gaba daya tsoro yakaba kamata amma itade sotake jakar kudinnan yabar hanunta,

Knocking tashiga ahankali, badawani bata lokaciba taji anbude kofar, cikinsa saye da jallabiya babu alamar fara bacci atare dashi,

tsayawa yayi yana binta da kallon mamaki me yakawo Nisha ban garnasa awannan time din, ganin yanda jikinta ke rawa hanunta rike da jaka, hakan yabashi daman fadin,"

what happened yafada yana kallonta cike da mamaki, ganin bata bashi amsaba se waiwai take hakan yasa yasake fadin," come in tareda bata hanya tashigo, cikin sauri tashige kamar mara gsky,

daga door din ta tsaya hade da sunkuyarda , bakinta se rawa yake dake ta iya bude baki tana fadin,"

please kamal I'm sorry for the foolish for you nasan ban kyauta ba .

kataimaken lokacinda bamai taimakona daga bisani kuma na mance dakai for now kuma danazo gdnku bun hadu but haduwa dakai yazama aiki agareni,

allah yagani ina matukar kunyar ido dakai, because baza karasa sani jerin masu butulciba,

cikin shashshekar kuka tareda sake kasa dakanta hadeda mika masa back din tana fadin,"

ga jakar kudinka daka bani domin ayiwa mahaifanta aiki allah bai nufaba ya karbi rayuwarta
ba samu damar amfani dashiba nagode,

shiru yayi hade da kallonta cikin tausayawa,shima yasan ba haka banza take gudunsaba, tawani ban gare kuma yayi farinciki kasan cewarsu tare gata gashi, hakan yamasa dadi kuma yaddai dasanin wannan ranar zatazo,

hanu yasa tareda amsar jakar hadeda jan wani goron numfashi, baki yabude da nufin magana ga mamakinsa tajin ya amsa jakar tabude kofar ta kwasa da gudu tafice,

wani cool smile yasake tareda sake rufe door din dakyau batareda yasa key ba because dama bacika sa key a door dinsaba,

komawa yayi yazauna kan sofa dake parlourn tareda daura back din saman table yana sake murmushi,

mikewa yayi kan sofan kamar wani mai Shirin yin bacci , murmushi yadingayi kamar wani zararre because allah yaga zuciyar shi, yana matukar feeling din soyayyar Nisha da kaunarta acikin heart

duk dacewa yasan batama san yanayiba, gefe kuwa inyatuna da bikinsa da nabeela yakusa seyaji duk ransa yabaci dukda yasan aikin gama yariga yagama manya sunshiga cikin lamarin,

wani bangaran kuma tunani yake namiji mijin mace hudune to amma yasan azababben kishi irin na nabilah, but komade mainene yasan yana kaunar Nisha kuma zai sanar da ita ,

Ahaka yaita juyi yana tunani, har bacci barawo yayi awun gaba dashi nan saman sofa,

Aban garan Nisha tunda ta watsa aguje tafita, tana zuwa parlourn cikin sanda tashige bedroom dinsu because kowa yadadai da bacci, ahankali tasamu tanemigu ta kwanta,

Washe gari da suba kamal nakwance kan sofa yana minshari, AJEEMAL ne yashigo domin tashin kamal sutafi masallaci kamar yanda suka saba,


yana sanye cikin jallabiya biya kamar wani balarabe yayi kyau dashi, ganin kamal kwance kan sofa ba bedroom saman bed dinsaba , han yasa yamatsu yashiga tashinsa,


ahankali kamal yafude ido domin ganin waye yakatse masa wannan kyakykyawar markin dayake tareda gimbiyarsa Nisha, dan zunburo baki yayi kamar wani baby, ganin yayansane yazo tashinsa sallahn asuba, hakan yasashi tashi ya mike hade da yin mika, yanufi bedroom domin yin alwala , ganin yashiga bedroom hakan yabawa AJEEMAL daman kokarin juyawa yafita, karba idonsa yasauka kan jakar dake daure saman table,

sosai yakebin jakar da kallo domin harsashinsa na tabbatar masa da wannan jakar da yabawa Nishane jiya, to me jakar takeyi anan kuma AJMAL ya tambayi kansa, hakan nanufin kamal ne yabata koyaya ko kuma ajiya takawo masa yashiga tambayar kansa , abun yayi matukar bawa AJMAL mamaki,

to ko sunsan junane dama,? dan babu abunda zai kawo back din nan wajan kanisa sede dama shi yabata, to komade mainene akwai time din da zai bukaci sanin hakan yafada cikin zuciyarsa,

juyawa yyi yafita abunsa yakoma inda Daddy ke tsaye yana jiransu domin tafiya masallaci, " ina kamal din Daddy ke tambayan AJMAL bekaiga bashi amsaba, kamal yafito hakan yabasu daman wucewa duka,

su Daddy na dawowa duk suka nufi sashin Hajiya domin duba goggo rabi sugaisa because yau Daddy da kamal da wuri zasu wuce office , shikuwa AJEEMAL tuni yawuce part dinsa domin yasanar dasu kansa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login