Showing 36001 words to 39000 words out of 61982 words

Chapter 13 - IG AJEEMAL book1 Hausa Novel

03 Sep 2025

1546

nan tashiga makota salma tafadi tana murmushi dan tagane bawai gaisuwar ummynne yadametaba ganin mb tareda kamal yasa tafake da wani batun gaisuwa, dan tsuke baki Nisha tayi still tana tsaye bata zaunaba,"

kode zuwana tareda abokinane zai takuraki mb yafadi yana kallon Nisha yana yar dariya, sorry yanxu zamutafi mubaki space ma karmu takuraki, munzo tareda abokinane saboda mubaku hakuri bisa a
kuskure da yafaru jiya ,"

kuskure ko sakaci da rashin kula,? Nisha tafadi yayinda take kokarin neman guri tazauna, munsani shiyasa mukazo mubada hakuri akuma gafar cemu, kinga abokina bashi bane da laifi bro dinsa ne but karkiga yanda ya damu se munzo tare yabaku hakuri gameda abunda dan uwansa yayi, "

aigwara dakukazo kudin don da wancan zauceccen kukazo bazamuma saurare kuba, kamal duk yana jin abokinsa tareda yarinyar but baitaba ganin yarinyar mai tsiwar tsiya irin yarinyar nan ba, dagowa yayi yana kallon yarinyar yayinda suke magana da mb, Allah yama ta kyau ta hada komai allah yabata sede masi faffiyace,

amma de shi yasan tun haduwarsu jiya yarinyar tasuma burgesa kasancewarta mara tsuro komai kai tsaye take ba boye boye bare shakka, "muna mai neman afuwa nida dan uwana akan abunda yafaru munsan munyi kuskure da sakaci da rashin kula kamar yadda kikace, munyi laifi amana afuwa kamal ya tsinci kansa da bada hakuri tareda hade hand dinsa guri guda asha gwabe yana kallon Nisha,

daga mb harsu Nisha kallonsa sukayi yanda yawani marai raice fiska, kasancewan kamal mai barkwanci ne wani sa'in salma da mb fashewa sukayi da dariya mb yashiga zungurin kan kamal yana fadin,"

kai meye hakan? shiru kamal yayi yana kallon Nisha yana kuma sake hada hand dinsa yana fadin," please yana wani sunnar da kai kasa, basu salma bama hatta ita Nisha seda takusa barkewa da dariya but seta matse ta dan turo baki tana fadin," nifa ba ni akayiwa laifi ba kawata ce intayafe to nima nayafe inkuma bata lamunceba to nima fa... bata karisa maganar ba taji salma nafadin," nikam nayafe allah ya kiyaye nagaba, sake baki Nisha tayi tana fadin," da wuri haka kamar wacce kike jira , "

ato mai zata jira kinsanmu bama rike abu, daga anyi muke yafewa mb yafadi yana kallon salma koya kikace, gyada kai salma tayi tana kallon Nisha tana murmushi,

dariya dukansu sukayi daganan fa hira ta barke tsaka ninsu sunyi hira sosae har guraren azahar daga bisani su kamal suka mike tareda ajiye kayan dubiya dasukazo dashi sukai wasu Nisha sallama suka wuce,

bayan tafiyar su Nisha kamar jira take tashiga tambayar salma," ke ina kuma mb yasamu wannan mutumin aina yasanshi,?

friends ne tun american tare sukayi karatu still kuma yanzuma tare suke abokaine sosai mb yafada min muna cikin hirannema kika shigo salma tafadi,

dan jinjina kai Nisha tayi dan bawai ta gamsu bane, sotake takuma wani tambayar but seta fasa ta ajiye se wani ranar idan time yabata dama,

mikewa Nisha tayi tana fadin," bari naje gd nabar umma ita kadae gakuma aiyuka da nabari, zaki tafi baki taba kayan makulashen da aka kawo ba, gashi ummyn bata dawoba, waifa sbd bello tagudu makota salma tafadi tana tabe baki,"

dariya Nisha tayi tana fadin," ba damuwa kigai sheta intazo, oh na mance umma tace agaisheki da jiki zatazo ta dubaki intaji sauki dan bata jin dadi jikinta sosae, "

Allah sarki umma har yanzu jikinne allahde ya bata lapia salma tafadi, ameen bari naje se wani lokacin Nisha tafadi tareda yiwa salma sallama tafice,

Nisha na komawa gd ta tsinci umma bisa sallaya ta kishingida da alamun bacci ya suma daukarta, dan haka batabi takantaba bare ta takura mata, bedroom dinsu tashige tanufi toilet tayi alwala tafito tayi sallah tanufo tsakar gdn tashiga daura musu sanwan rana dan tasan umma bata dauraba because lapia bai wadaci jikinta ba, gashi abubuwan cefanen nasu da kudin dake hanunsu na dab da karewa,

gashi kuma haryanzu abba bai lekosuba balle yasan halinda suke ciki,ga rashin lapiyan umma ya tafi ya dawo, gaba daya abun dunya ya gama isarsu,

Aban garan kamal kuwa tunda suka bar gurinsu Nisha yake son sake sa yarinyar aidonsa, dan shi jiyake gaba daya yarinyar tasuma taba masa heart dinsa, duk Wani juyi da mutsinda zaiyi ita yake tunawa,

da alama son yarinyar ne yafara addabar zuciyar sa, yasa mb ya nema masa numbern yarinyar gurin kwata salma but amma yakasa kiranta, because baisan mai zaice mataba

kamar kullum da yasaba zuwa gdn masaukin daddy shida abokansa wani sa'in kuma shi kadai yake kasan cewa because shi bai cika zama gd ba, yawanci gdn masaukin daddy yake tattaro yazo ya kadaice kansa, ya gama hutawarsa indare yayi ya nemi hanyar gd,

yamade kamar kullum yana kwance saman sofa yarintsa ido kamar mai bacci, jin kiciniyar shigowa yasa yamaida kallonsa ga kofa dan ganin mai shigowa, kb ne tafe yashigo cikin dressed dinsa da yasaba kamar na yan isaka, gashi kan nan acukurkude bakin gashi kareshi amma saboda dunyanci yarinata takoma ruwan kasa, hanusa dauke da shesha,

kamal na kallonsa har yakarisu ya zauna," yade boss bacci kakeyine,? kb ya tambayi kamal, "

No kawai ina kwancene kamal yabashi amsa, ,"

Saboda rashin abunyi,? kb yakuma tambaya",

eh to kusan haka kamal yafadi tareda kokarin tashi yazauna, "

to ga abunyi na kwawo maka kasan mu ba arasa nono ariga kb yafadi hade da ajiye tukunyar shishan saman capet yamikawa kamal daya igiyar shima yaja dayan yasuma zuka yana furzar da hayaki,

kamar zukar shishan yake but yakasa gane meyakeji daya, kamar wani yau yasuma Shanta,"

Ammade akwai abunda yake damunka koh yau naganka kamar wani mace bana mijiba, se wani abu kake sanyi sanyi meyake faruwane,? Kb ya watsuwa kamal tambaya,

Kamal dakatar da abunda yake yayi tareda kallon kb yana fadin,"

inba na mantaba kamar na baka labarin naje gdnsu yarinyar da muka buge da mota tareda kawarta, kasan na sanar dake munje tareda mb,"

Eh kafada kunzame kunje ba da saninaba gudun karna bata muku shiri kb yafadi yana tabe baki,"

Aa ba haka bane ganin nayi kana fusace da marin da tamaka gashi kai ba hakuri garekaba, ita kuma tanada fada da masifa ba barinka zatayi ba, kaga garin gyaran gira se arasa ido, shiyasa mukaje tareda mb,"

hmm to meye kaketa kawo wadan nan zantukan kb yafadi azafafe because ransa yasuma baci ya tunu da marin da yasha gurin Nisha,"

bakomai ji nake kamar na kamu da sonta cikin heart dina, "

What so,? Kb yafadi tareda zaro ido,"

Eh ina expecting haka, ko kamai kana muradintane naga kawani zaro ido kamar katsorata, kamal ya fadi yana kallon kb, "

mtsww allah yakiyaye, kaiko mai zakayi da wannan crazy girl din kb
ya tambaya, kamal hararo kb yayi yana fadin,"

waye kake kira da crazy kodan kasha marin crazy girl ne,shiyasa ,? Kb jiyayi yafara kubula rainshi yasuma baci dama yasan za arina tunda yasha mari gaban kamal yasan ya dinga goranta masa kenan,"

mikewa kb yayi yana fadin," thanks agabana kake fadin kakamu da son wata bayan baikon yar uwata dake kanka yayi kyau, kb yafadi yana huci,"

Nifa bawai nace ina sonta bane alama nakeji nace, nasan yarinyarn ma ba lallai ta amince daniba shiyasama ko nuna alama banyiba, kamal yafadi yana mikewa shima,"

dan kada kai kb yayi yana fadin," hmm naji yanzude ba jin wannan wakokin nazuyiba, please key din gdn nan nake bukata inkatashi tafiya gd, wani harara kamal ya watsawa kb tareda fadin,"

mezakayi da key din,?

baby nice zata ziyarceni zamu dan tattauna kb yafadi atakaice,"

ba anan ba, dan nan gdn bana kawo mata bane ana tattunawa dasu ko kataba ganin nakawo mace gd nan,?kamal ya tambayi kb, "

toni ina zan sani tunda ba kullum muke tareba yau da gobe zaka iya kawowa kaima wazaisan anyi kb yafadi,"

hmm allah ya kiyaye ni da bata yar wani masuyima allah ya shiryasu, wannan hanyar da kadaurani kai addu'a nake allah yabani daman sauka daga kanta, kamal yafadi tareda shigewa cikin bedroom yabar kb tsaye tana binshi da kallo har yashige bedroom,

Lallai fa ni kamal yake shirin wula kantawa haka, har wani hanunka mai sanda yakemin ina bata yar wasu, bakomai hanyar da kake neman tsari dashi, shidin zaka tsinci kanka wata rana, kuma akan wacce kake magana yanzu,

da ninaso na gyara mata zama da kaina domin tagane irin mazan da zatasa hanu tamaresu ba irina bane, but amma yanzu na hakura kaida kanka zakamin ramuwa, wani dariyan mugunta kb yasake tareda kada kai yafice yana kuma bushewa da dariya,

yau one week kenan, salma tafara jin saukin sosai Nisha kusan kullum setazo ta duba jikin kawarta because salma kawace tagari shiyasa Nisha ke ji da ita,

yamma lis umma zaune bisa taburma hanunta rike da carbi tanaja, zuciyar ta kuwa fal tunanin mijinta da sun ganinshi ko ba dan yabasu wani abuba dan kawai tasashi idonta, kullum addu'arta allah ya karkatu hankalisa da tunanin sa kansu, kafin mai duka yayi aikinsa, dan bata tunanin yanda takeji ciyon nan bazatayi wani tsawon rai ba,

Yo banda abun umma mai rai ai baya yanke tsammanin kuma cuta ba mutuwa bace,

haka itama Nisha tana can bedroom tana sakawa da kuncewa, tunanin rashin ganin abba dakuma rashin sanin wani hali yake ciki, kullum intaje gun mami nemansa se tace baya nan, inta tambayi ina yaje ko ina yakezuwa ba asamun shi , se tace," itama ba tasaniba, to ina yashiga ko saceshi,
akayi ?


wannan tambayar kullum Nisha kewa kanta but kuma ba amsa, allah shiyasa sirrin ciki da na boye, tana cikin wadan nan tunanin karan shigowar message wayanta yasa tamike tazauna tadauki wayar tashiga dubawa,"

kusan kullum se anturo mata text awayarta da wani bakuwar number wacce itama batasan ta wayeba, kuma Tex ne zafafan kalaman soyayya , wanda ya turo yake bai yayyana mata tsantsan so da kuma kauna dayake mata, yakuma kasa fitowa ya baiyana mata gudun kartaki amsar soyayyarsa,

Nisha tun bata kulawa da text din tana sharewa because atunanin ta bazai wuce mutane masu hada numbern yan mata suna shirmeba, but yanzu tagane har sashenta ba daidai bane,

Saboda wanda ke turo text din yanuna yasanta , hakan yasa tasuma bawa sakon mahimmanci, wajan karantawa, sede yau sakon yasha ban ban da sauran,"

Nagaji da boye kaina agareki, yau zan baiyana kaina kisan ko ni waye da kuma so da kaunar da nake miki, zuciyata zata buga saboda tsantsan so da take yimaki,

zanzo yau bayan sallahn magarib domin gd susan dani, kishirya tar ban babban bako kuma mai kaunar ki maisun farin cikinki akoda yaushe, kihuta lapia

Nisha mikewa tayi ta tsam tsakiyar gado tana sake bin sakon da allah, da sauri tashiga tasuma kiran numbern but amma yaki shiga, nan tacigaba dakira ko zai shiga amma sam abu daya takeji,..

Khaleeseart Raeys ✍️🌴🌴 AJEEMAL 🌴🌴
Story and writing by Oum AmReesh ♥️

Daga ALKALAMIN khaleeseart Raeys ✍️

Free book,

Ya Allah yanda nafara rubutun littafin nan lapia kasa na gamashi lapia,

Page 25, tana tsaka dakira still tasakejin wani sabon sako yashigo wayar, "

I'm sorry banida butar takura miki ko saki cikin wani damuwa, akwai option ra ayin ganina zan iya hakura najiraki har se lokacinda kika bukaci ganina ahuta lapia,

Dan zamikewa Nisha tayi bisa gadon tazauna tashiga maida ajiyar zuciya, tareda sharce zufar dake tsats tsafowa goshinta, ita tarasa waye wannan dake bibiyar rayuwata da wani batun soyayya,

Allah yagani ita kwata kwata ba wani babin soyayya cikin rayuwarta, ko akasin haka, ita karatu tasa gaba tareda rayuwa da mahaifanta yafi mata komai dadi, shiyasama ko gender aure babu alamarinta balle wata soyayya ayanzu,

Kwana biyu da faruwan hakan, nisha na kitchen ta daura musu abincin dare because yamma tayi, tana tsaka da aikace aikacen taji wayarta tashiga ruri,

cikin hanzari ta dauki wayar domin taga mai kira, wannan numbern da ake turo mata sako dashi again yau shiya kirata, tsayawa tayi tana kallon call din har kiran ya yanke,

ajiye wayar tayi tacigaba da aikin dake gabanta, still aka kuma kiranta, jin yanda aka damu da kiran yasa ta dauki wayar tareda karawa akunne ba tareda tayi maganaba,

wani sallallami taji anfara jeruwa daga bisani aka suma magana," asslamu alaikum cikin wata rudadden murya da batasan ta wayeba batasan kuma tawayeba da alama mai maganar ahanzarce yake,

Amsa sallamar Nisha tayi batare da tace wani abuba, " baiwar allah kece nisha aka tambaya, cikin natsuwa gami da gyara tsayuwa Nisha tace,"

eh nice,

kina sane dacewa wani bawan allah yana dab da rasa rayuwarshi ta dalilinki? yanzu haka yana kwance baisan inda yakeba yanata ambatu sunanki, da alama kafin zuwarki rai zai iya halinsa, "

subhanallah please malam kai din wayene,? kuma ni wanda kake magana akai bansanshiba, Nisha tafadi adan tsurace,

ni friend dinsa ne but tsayawa wani bayani bata lokacine zaifi kyau kizo kiga halinda bawan allahn nan ke cikin domin banda Nisha ba abunda yake furtawa kuma ko yanzu aka samu akasi yamutu da sunanki abakinshi munriga munsan kece sila,

dan haka yanzu zan turo miki da address kizo ki tai maki rayuwar bawan allah, ko kuma inyamutu munemi gdn ku mukawo miki gawarsa, ana gama fadin haka akashe wayar,

tashin ankali, Nisha aza hanu tayi aka kamar mai shirin kurma ihu kiris yarage kuka ya subuce mata tayi saurin tushe baki gudun kar umma tajiyu ta,

har kullum tunani take waye yake kokarin shiga rayuwarta bada yar dartaba,? kuma bakuma ita ta gaiyyato shiba, ,? da ahar yake kokarin rasa rayuwarshi ta dalilinta,

cikin hanzari Nisha tafito daga kitchen din zufa ya gama wanke mata fiska, fitowar umma daga daki ta hadu da nisha tsakiyar parlour tana tsaye tayi zuru, "

Ke Nisha yadai umma ta tambaya, cikin hanzari da kirkiro murmushi nisha tace,"

bakomai tareda barin parlourn tanufi bedroom, umma de bayan Nisha tayi da kallon gami da karisawa kitchen din dan ganin maike tafiya, umma na zuwa ta tararda komai Nisha ta kammala se dan wasu aiyuka da bata samu daman karisawaba,

hakan yasa umma tashiga jarisa aikace aikacen, nisha kuwa tana shiga daki ta tazauna tana tunanin iri iri, shigowar sako wayarta yasa cikin sanyin jiki tadau wayar tashiga dubawa, address aka turo mata hakan yasa tashega wasi wasi, because allah ya gani bazata iya daukar kafa taje gurin Wani saurayiba, wannan ma ai se duniya ta tsine mata,

Kuma umma bazata yafe mataba, saurayi yazo guntama bazata lamunci hakaba balle kuma ita tadau kafa taje,

ta wani fannin kuma tsoro take kar akawo mata gawar sauri kamar yanda mutumin dazu ya sheda mata , dan haka gwara ita taje ayi mai yiyuwa tayiwa tufkar hanci,

tashi tayi tashiga kimtsa jikinta, tareda sauya kaya ta nemi hijab tasaka tareda nufo parlour cikin sauri yayi daidai da fitowar umma daga kitchen,"

Ina kuma kike saurin fita kije,? umma ta tambaya tana kallon Nisha dake ta fidda ido, "

Gdnsu salma zani because na kwana 2 banje naduba jikintaba,"

to adawo lapia ki gaishesu abunda umma kawai tace nisha tasa kai tafice,

tunda tafito take ta tafiya tareda tunanin wannan saurayi da ya tacewa rayuwarta haryake tunanin salwantar da rayuwarsa akanta, inko harda gskne shiko wani irin sone haka,?

Nisha tafiya tayi sosai seda tabar arean anguwar tahau titi, sannan ta tsaya ta tsaida mai daidaita tanuna masa address inda zai kaita daga bisani tashiga suka dau hanyar tafiya,

bada wani bata lokaciba haya ta kawosu, daidai jikin gdn mai adaidaita ya dire Nisha, daga nan ta sallameshi tasakai dan ma daidaicin gdn, tura kofar tayi tashiga kirjinta se dukan uku uku yake,

Koda isuwarta cikin compound din gdn bakowa gurin shiru yake, to nan din gdnsune ko ina,? but bata ga mutane cikinsaba, ga kofar parlourn abude yake nisha ke tambayar kanta,

jitayi tsoro yagama mamayeta kamar tajuya takoma because taji gaba daya bata yarda da gdnba, jin shiru datayi ba alamar kowa, maybe ma yan yankan kaine ko kidnapping, soke kokarin wasa da hankalinta da sunan soyayyarta na kokarin ilata Wani,

har tajuya zata fice daga gdn wayarta tayi kara, kamar bazata dagaba sekuma ta dauka tareda karawa akunne,"

Na hangoki ta window but naga kamar kokari kike kikoma please ki kariso bawan allahn nan ya ganki ko zai kuma cikin hankalinsa kafin musamu mukaishi hospital,

daga cikin phone din takejin ana ambato sunanta, daga gefe da wace irin raunan niyar murya, ana neman agajinta hakan ya tabbatar mata akwai matsala kuma akwai kamshin gsky alamarin

dan haka takarisa takutsa kai cikin parlourn bakinta dauke da sallama, ga mamakinta parlourn ma shiru yake ba kowa nan ta tsaya tana dan wul wul ga ido tana karisawa tsakiyar parlourn, jin an murda handle din kofa ana kokarin fitowa daga bedroom din yasa ta kurawa kofar ido dan ganin mai fitowa,

turos tayi tana binshi da kallo tana dan gwalo ido, kamal ne yafito daga dakin yana sanye cikin t shirt da gajeran wando, yayi kyau dashi, tsayawa yayi yana kallonta shima da mamakin mai ya kawo yarinyar gdn ,

Rintsa ido yakumayi atunanin shi ko gizo tafara masa, kara bude idon yayi dakyau because yanda yaji sunyi masa Wani nauyi , tabbas itacede ba wataba tayi tsaye kamar sakaguwa, ta gagara motsi daga inda take,

dawata kasa lalliyar murya kamar wanda yasha wani abu kamal yakira sunan ta yana fadin," Nisha kece ,? mekuma ya kawoki nan,? yajero mata tambaya yana mai kokarin karisuwa ciki parlourn,

ita kuwa nisha jin tambayar da kamal ke mata yasa ya tabbatar mata wani ke kokarin rena mata hankali ko kuma shida kansa yake kokarin zargata, dan haka kafin ya kariso tsakiyar parlourn Nisha tayi baya da sauri tana kokarin barin parlourn,

kirif taga anja kofar anrufe daga waje, Nisha kamar ta tsula fitsari awajan aikin tsoro da kidima, nan tasuma bugun kofar da karfi tana fadin," waye agurin please kabudemin natafi gdnmu, dan Allah , tafada cikin sigan kuka, kamar daga sama taji murya daga waje ana fadin,"

Rashin kunyarki ya kwaceki yaude kinshigo hanu yau zanyi maganin rashin kunyarki, ashema bakida wayo harna iya zargaki yau gaki amakomata, bake har Zaki iya daukan hanu kimari wanda bakisan waye shiba, zakiyi bayani

makwat kakeji Nisha ta hade wani yawu, tareda sakin handle din kofar da tarike tamaida kallonta ga kamal dake tsaye yana rike da head dinsa yana rinrintsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login