Showing 21001 words to 24000 words out of 61982 words

Chapter 8 - IG AJEEMAL book1 Hausa Novel

03 Sep 2025

1541

kawai Nisha tace daga bisani suka kayi sallama, salma takatse wayan, zama nisha tayi abakin gadon tareda zamewa ta kwanta farin ciki fal zuciyar ta, jitake kamar ta bace ta tafi gdnsu salma,

aheel ne yashigo dagudu dakin tareda hawa bed yafada jikin nisha Yana washe baki yana fadin," Aunty

ta tsorata sosae ganin bata san da shigowar shiba, cikin tsoro tana zaro ido ta dago aheel tana fadin," amma kai wannan yaro koh tafada tareda jan kumatun sa , gabani tsorofa,

washe mata baki yayi yana fadin, "Aunty wai tsorita kikayi, eh mn, waima mai ya hanaka zuwa school yau, Nisha ke tambayan sa,

lah yaufa weekend kin manta ba school , oh haka na manta , suna cikin hiran tasu su fareeda suka shigo daya nabin daya, suka karisu suka zauna, hanun fadeela dauke da chocolate suna sha, fadeela ne ta ajiyewa Nisha ledar acinyarta tana fadin," ga chocolate kisha, nan sha ta bude ledar tadauki daya tabare tasuma sha har wani lumshe ido take aikin dadi, nisha na kaunar chocolate sosai,

Nan Nisha takalli aheel dake kallonta shima tana fadin," kaima kadauka kasha mana, nan yakai hanu zai dauka reeda tabuge hanunsa tana fadin," mai zakayi, Aunty nima sha zanyi yafada tareda marairaice fiska, fadeela ne ta amshi maganar da cewa" saboda kaine mai bakin kwadayi koh,? to muma ya kml ne yasammana kaima kaje yabaka yanadashi dayawa,

cikin hanzari aheel kuwa yazame daga bed din yana fadin," nima bari naje yabani, yafada tareda yin waje dagudu,

Da kinbarshi muma ba iya shanyewa zamuyiba, Nisha tafada tana kallon su reeda, ke kyaleshi yaje zamu iya shanyewa tunda muka dibo, Nisha bata kuma cewa komaiba sukaci gaba da hirarsu, wunin yau kam yamata dadi sosae because abokan hiran suna nan,

sede damuwarta dayane shine sanar da ammi batun fita, dan haka da batun takwana aranta,

Washe gari da suba suka tashi sukayi wanka tareda alwala suka yi sallah kamar yanda suka saba, su fareeda suka suma shirye shiryen tafiya skull domin kuwa 7 a mkrnt yake musu, dan haka basu tsaya wani dugun breakfast ba coffee kawai sukasha suka wuce,

nisha kuwa tana kammala karatun Qur'an da tasaba ta koma takwanta, batayi wani wacci mai tsayiba sbd atunanin ta ammi 10 ma baya mata a gd,

wajan 8:45 Nisha tasamu daman farkawa, dan haka ta sakko daga gadon tanufi hanyar parlour takoyi sa'a can dining ta hangi ammi na break dan haka tasamu daman karisawa dan su gaisa,

cikin fara'a da nuna kulawa ammi ke kallon nisha tana fadin,"har kin tashi, cikin murmushi nisha tace,"eh ammi natashi, ae na dauka se 10 kamar yanda kuka saba ammi tafadi tana dariya, murmushi nisha tayi batare da tace komaiba,

to maza kizauna kiyi break ammi tafadi tareda turawa Nisha kan abinci gabanta, hanu Nisha takai ta hada tea tafara sha, daga bisani tadauki pancake tana ci tana mai satar kallon ammi yayinda take karyawa,

bari natashi nashirya karna makara ammi tafada yayinda take mikewa ta haura sama tanufi bedroom dinta,

Seda nisha tagama karyawa sannan ta tashi tareda komawa parlour tazauna tana jiran sakkowan ammi, ba a wani dade ba , ammi ta sakko cikin shirinta mai kyau gwanin shaawa,

ido Nisha ta tsurawa ammi yayinda bakinta me bari tana kokarin cewa wani abu, ganin kallon da Nisha ta tsare ammi dashi yasa ammi fadin," lapia kuwa Nisha akwai abunda kikeson cewane ammi tafa yayinda take shafo gefen fiskar nisha,

kifadamin inkinda bukatan wani abu tafada cikin yanayi na kwarin gwiwa, dama kawata salma aka kawo kayan aure shine nakeson naje nagani nisha tafadi tareda sunnar da kanta kasa tana wasa da yan yaysunta,

murmushi ammi tayi na Fadi,"shine kuma baki fada tun jiyaba, gashi ina sauri da na ajiyeki, amma bakomai yanzu kiyi sauri kije kishirya sena saukeki, ammi bazansa ki makaraba, tafada tana kallo ammi, a no ba damuwa da sauran time, kije kishirya ammafa karki bata lokaci ammi ta fada yayinda tasamu gu tazauna,

cikin rawar jiki da murna Nisha tashiga daki dan shir yawa, kamal ne yashigo parlourn ya tarar da ammi zaune bisa kujera yayinda hanunta ke latsa wayarta, sallma yayi tareda kokarin karisuwa kusa da ita,

nan ya zauna ya gaisheta ta amsa fiskarta daukeda murmushi, kallonsa tayi tana fadin," lapia kuwa naganka cikin jallabiya, ina shirin office din, ,? dan wani guntun tsaki yaja yana fadin," kai nifa ammi yau banajin zuwa office dinnan, why ammi ta tambaya, yau banajin dadin jikinane sosae shiyasa,

maganar ammi keda wuya Nisha tafito cikin shirnta mai kyau, fiskarta daukeda murmushi, amma ganin kamal murmushi da annashuwar dake fiskarta dip yadauke, gani fitowar nisha yasa ammi tana fadin," yauwa kin fito ko to semu samu mutafi dan nakusa makara, ahankali neesha take daga kafarta sbd yanda taji kafarta yamata nauyi,

yayinda idon kamal kuwa ke kanta, ammi ina kuma zakuje nazaci office Zaki, kokema yau zaki hutane, kamal ya tambaya, no yanzu zan wuce nisha nakeso nasauke gdnsu friend dinta salma, cikin tare ammi da magana kamal yace,"

haba ammi keda zakitafi office maizai kaiki da wani biye biye, aiseki makara kisa driver yakaita mana, ko kibari nina sauketa, yafada yana satan kallon Nisha,

wow da kate makeni domin kuwa nakusa makaran please ka tai maka kasauke min ita , ni bari na wuce tana fadin haka tayiwa nisha sallama tayi fice warta,

Nisha kam kamar wacce aka dasa agun batayi gaba ba batayi bayaba, jitayi kamar tafasa fitan, har kamal yafita yakoma dakinsa yacanza kaya ya dawo Nisha na tsaye inda yabarta,

jin inuwar mutum kusa da ita yasa tadago takalleshi tareda dan zaro ido waje, kallonshi take sosae cikin shiri maikyau, yayi kyau dashi kamar kasaceshi kagudu, kamarsu ya kara fitowa sosai da brothern shi AJMAL, sedan haske da AJMAL yafishi danshi yaynsu ba inda yabar mahaifinsu, mujeko abunda kamal yace kenan yana dan murmusawa juyawa yayi yafice, itama bayanshi tabi .

ahankali take tafiyan kamar wacce kwai yafashewa aciki har ta karisu jikin motar, kamal duk yana kula da yanayinta, bude mata motar yayi ganin tashiga yasashi maida kofar motar yarufe, nan shima ya zagaya yashiga motar tareda sawa motar key,

tunda suka hau titi suka suma tafiya bawanda yacewa da uwansa kala, kamalne ke sauraren sautin wakanda yakunna yana mai bin mamin din wakar, yana satar kallon Nisha wacce kanta ke gefe tana kallon hanya,

baki fadamin inda zakijeba, ko mucigaba datafiya se inda mai dinmu yakare, kamal ya watsawa Nisha tambaya, dan jiyuwa nisha tayi tana fadin," nasarawa, bansan wajanba kamal yafada yana mai cigaba da kallon titi, zuro taimasa da ido ganin cewa komaiba still kuma tacigaba da tuki, tama kauda kai gefe tayi tana mai maganar zuci,"

dama kaida ba dan gariba taya zatasan gari, shiru tayi tareda zubawa sarautar allah ido, amma ga mamakinta segasu a anguwar, yana tsaka da tukin ya dan jiyu yakalleta yana Fadin," sekuma ina zamuyi,

yo kuma kace bakasan unguwar ba yanzu waya kawomu ,?Nisha tafada cikin zuciyarta, kinyi shiru kamal yafada yana mai kokarin tsaida motar,

dan tsuke fiska Nisha tayi daga bisani tashiga masa kwancen ida zasuyi har suka karisu kofar gdnsu salma,

daga gefe ya tsaida motar yayi parking, hakan yabawa Nisha daman fitowa daga motar, tafara kokarin maida kofar tarufe, jin muryan kamal nafadin," karki bata time yasa taja tatsaya tana fadin," nifa zan kai yamma, aina kenan kamal ya tambaya, nan Nisha tafada tana mai tura baki,

ina tunanin baki da labarin gdn ALH ABUBAKAR MODIBBO BATURE ba afita yawo balle asa ran za awuni kuma kema yanzu kina daya daga cikinmu, dan haka ki hanzarta inajira yafada tareda maida kansa ga wayarsa,

jiki ba kwari tamaida kofar motar tarufe tajuya tashiga gdnsu salma, da sallama tashiga cikin gdn tana dan wul wul ga ido,

salma ce tafito daga dakin, ganin Nisha tsaye cikin gdnsu yasa tazura da gudu tayi kan Nisha ta rungume ta, cike da murna da zumudi, yar halak ashe kina tafe, tafada tana washe baki,

bakowa gdnne ina ummyn naji gidan shiru, ummy bata nan faruk kuma yana makaranta tareda tareda jan hanun Nisha suka shiga ciki,

daga nakin gadon salma nisha tasamu tazauna tana kallon salma wacce itama Nisha take kallo, kawata kinga yanda kika kara kyau kike glowing har wani kumatu kikayifa, salma tafada tana jan kumatun nisha

Murmushi nisha keyi yayinda take kallon salma tana fadin," amaryanmuba mrs bello to akawomin lefen nima nabawa idona abinci, ko anrufe gani, Nisha tafada cikin tsokana, yo ko anrufe gani dole abude kigani tafada tareda jan hanun Nisha suka fita daga dakin,

dakin ummynsu takai nisha domin adakin ummy kan suke, nan salma tashiga nunawa nisha kayan arzikin da abun kaunar ta, ya aiko mata, masha Allah kawata kaya sunyi kyau sosai kawata tayi gishi nisha tafa tana zungorin goshin salma,

to yaushene bikin ko ba asa ranaba nisha ta tambaya, ba asa ranaba tukun kin kin matsu akaini koh, gsky kam namatsu shima kansa uban gayyan amatse yake Nisha tafada tana tabe baki, salma ce takaiwa nisha bugu tana fadin," kefa bakida m to karya akayine nisha tafada tana dariya,
.
sun dau dugun lokaci suna fira daga bisani Nisha tamike tsulum tana dan zazzare ido, sam ta manta da kamal dake jiranta awaje, salma bari naje gd ba kowa muku ana jirana awaje, salma tace," dawuri hk nadauka wuni zamuyi, zan sake dawowa nisha tafada cikin hanzari,

to bari na tattara kayan nan nazo na rakaki, to kawai Nisha tace tashiga tayata suka maida kayan, mayafi salma tadauka suka nufi hanyar fita,

fitowar su keda wuya gaban Nisha yafadi, ganin ba motar akofar gdn, wul wul ga ido tashigayi nan ta hangi motan daga can gefe yayi parking,

nanfa Nisha taja wani goron numfashi tareda kokarin yiwa salma sallama, to to ina motar da take jiran nakin salma ta tambaya, da hannu Nisha tayiwa salma nunin inda motar take a pake, yo inbanda abun driver meyena kai motar can kuma salon yasaki tafiya, dariya Nisha tayi tana fadin,"

maybe ya gyara parkine bari naje se munyi waya, to kawata nagode kigaida su Hajiya dasu reeda nima zanzo inna samu time insha allahu, to shikenan senaganki nan sukayi sallama sannan salma tajuya tashiga gdnsu, hakan yabawa Nisha daman barin kofar gdnsu salma tanufi inda ta hangi motan kamal,

tana karisawa tasa hanu tabude murfin kofar tashiga tamaida kofar yarufe, akife ta sameshi ya kife kansa kan siterin motar da alama bacci yafara daukansa,

jin motsin shigowarta Nisha yasashi daga kai yana binta da kallo da rinannun idanunsa da sukayi jawur dasu, harara ya watsa mata yana mai hade gira wanda yasa Nisha sunkuyar da kai kasa,

baicemata Kala ba yaja motar da wani irin gudu kamar mai shirin tashi sama, wanda hakan bakaramin bawa Nisha tsoro yayiba,✍️

🥀🥀 IG AJEEMAL 🥀🥀

Story and writing by Oum AmReesh ♥️

tunda suka hau titi suka suma tafiya bawanda yacewa da dan uwansa kala, har Allah yabasu da man karisowa gdn, jin karan hon kamar zai daga gdn yasa mai gadi yaye geat din gdn, nanfa yataka motar ya isa inda sauran motocin suke yayi parking,

nan Nisha tafada kokarin bude murfin kofar tafito, kicewa barka ta kawo min food, abunda kawai yace kenan, yafita daga motar cike da kasala kamar ka karba masa tafir yanda yake tafiyan kamar mara laka, itama fitowa tayi tanufi bangaran su,

bedroom dinsu tanufa tanemi gu ta kwanta, tana maida ajiyar zuciya, wani kewa taji yana ziyartar ta, duba da basu fadeela ba aheel abokin surutun nata, se Hajiya kawai,

hakan yabata daman mikewa tanufi hanyar kitchen tasanar da baba Barka sakon kamal, nan tajuya ta koma dakinsu,

tube kayan jikinta tayi tareda daukan towel tanufi toilet, wanka tayi tafito tana goge jikinta dawani karamin towel din, komai bata nemaba tanemi yar duguwar riga red color wanda su fadeela suka zaba mata lokacin da sukaje shopping,

rigar tayi matukar yimata kyau sosai, hula tasa akanta tanufi hanyar waje, bangaran Hajiya tanufa, tana zuwa ta tura kofar hadeda sallma abakinta, duguwar kujera ta hangi hajiya ta kishinfida da alman bacci tadumayi, jin motsin shigowar Nisha yasa tamike daga kwanciyar da take tana sakar mata murmushi,

Nisha karisowa tayi tareda samun guri ta zauna tana fadin," Hajiya sannu da hutawa, yauwa sannu Nisha, kindawo dazu nashiga ae natayaki fira Barka tace kunfita da kamal,

Eh gdnsu salma naje kallon lefen ta, ayya masha Allah kice salma kaya ya iso, kai Allah de ya sanya alkhari Hajiya tafadi, ameen Nisha tace, tanan suka shiga hiransu har wajan la'asar, daga bisani Nisha tamike tanufi sashinsu domin gudanar da sallah,


Hajiya ma tanufi bedroom dinta, Nisha tana shiga bedroom din toilet tanufa tayi alwala tafito tayi sallah , bayan idar wanta kamar kullum tashiga yiwa umma da abbanta addu'a da fatan alkhari,

tana kammala tamike tareda samun guri daga bakin gadon tazauna yunwa takeji sosae because tunsafe rabonta da tasawa cikinta wani abu kuma bata san cin abinci ita kade, tasaba ci tareda su fadeela, dan haka tazauna zaman jiransu,


jin hon din mota tashigo haraban gdn yasa Nisha mikewa, tanufi window domin lekawa taga waye, ganin cewa su fareeda suka dawo tasaki wani murmushi jin dadi, Allah kadai yasan miss dinsu datayi agdn yau,

nan takoma tazauna tana jiran shigowar su, ba adadeba sekasu sunshigo kamar yanda aka jefosu daya nabin daya,

washewa Nisha baki suka shiga yi yayinda suke karisa shigowa, reeda ce tasuma magana tana cewa," sannu da gd sis da alamar yau gdn nan bai miki nice ba, fareeda ne takarbi maganar dacewa,"

inafa zai mata dadi bama nan tafara cike da zulaya, don't worry kinkusa dena missing kema yayinda tamike saman bed tana sauke gajiya,

I'm feeling hungry wlh reeda ta fada tana shafa cikinta, nima yunwan nakeji fadeela tafada tareda mikewa tana kallon Nisha daketa faman zuba musu murmushi,

Ke kinci abincinne ko bakijin yunwane , aa dama kunake jira banajin dadinci nikadai, alright bari naje na kawo mana abincin, fadeela tafada yayinda tanufi hanyar waje,

tana zuwa kitchen tasamu baba Barka ta tsaka da aiki, ganin fadeela ne yasa ta tsagaita da aikin datake, tashiga washe fadeela baki tana fadin," yan matan daddy andawo, " wlh baba Barka kuma gashi yau mun dawo da yunwa,

shine nace bari nazo na daukar mana abincin, lah ae ai dakin koma abunki yanzun nan zan kawo muku, a no karki damu, bari nadauka dakaina, tana fadin haka takai hanu ta dauki food flas din abincin tareda plate din abinci, tafita tareda komawa bedroom dinsu, tana shiga ta baje musu kayan abincin saman capet,

nan ta tadauki plate tashiga saka musu abincin nan suka sakko daga bed din suka suma cin abincin, sunci suna dan hiransu , seda suka kammala Nisha da reeda suka shiga tattara kayan da sukayi amfani dasu suka maida kitchen,

bikin kml yanata kara matsuwa yau saura 2 weeks, yau gd yayi baban bakowa Hajiya rabi,

kamar kullum dasuka saba banyan gama breakfast dinsu sukan dawo parlour suzauna su dan taba hira, ammi yau bata fita office ba kasan cewa weekend ne ba aiki, Hajiya sesu fadeela, Nisha yau bata jin dadi maranta naciyo saka makon bakunta na wata,

ammi ta bata magani tasha sannan tasheda mata da ta kwanta tayi baccin ta tahuta, hira suke sosae cikin nisha di, jin sallmar da ake yasa suka zubawa kofar parlourn ido dan ganin mai shigowa,

gaggo rabice kanwar dadinsu ketafe hanunta dake da jakarta, cikin shirinta mekyau fiskarta ta dauke da murmushi yayinda take karisuwa ciki, bayanta dauke da mai gadi yana tafe da akwatin kayanta,

su fadeela ne suka tashi dasuri sukayi kanta suna fadin," oyo oyo gaggo sannu da zuwa, cikin farin ciki ta rungume yayan nata tana fadin," my daughter's kune kuka kara girma haka masha allah ashe nakusa na auradda yayan nawa mekukeci haka gaba daya kun dawo wasu broilers daku, tafada cikeda zulaya tana dariya,

cikin sunnar da kai alamar kunya suka shiga yimata dariya tareda kokarin karbar jakar hanunta, karisuwa tayi kusa da Hajj mama tazauna tana sakar musu murmushi,


Mutan kd irin wannan zuwan bazata haka, ammi tafadi tana kama haba, dariya goggo rabi tayi tana fadin," wlh kuwa dama cewa nayi zuwan bazata zan muku, Daddy ne kadai yasan da zuwana shima kuma na kwabeshi nace kar ya sanar daku,


carab Hajj mama takarbi zancen da cewa," a lallai kin sham macemu, ina mutumin nawa shima kwana biyu shiru kamar baya nan ku leko mutane bayayi,

dariya goggo rabi tayi tana fadin," muhaiseem wai , shifa Hajiya tafadi, yana uganda, yakusa dawowa ae shima zai zo bikin kml goggo, hmm Allah yasa nasan halin mutumin da kalula,

dariya sukayi daga bisani ammi tace," Allah yasa hutun da yawa akazo amana, dan kema kin dade rabunki danan,

kede bari ae yanzu se kungaji da ganin, dan har bayan auran kamal ina nan kusuda uwata dan tayi kewanta so much, tafada tareda kwanciya shouldern Hajj mama,

dariya sukayi Hajj mama nafadin," kede rabi bansan yaushe zaki girmaba har yanzu wani abu kike kamar yarinya , yo ba dole ba yar uwatan Hajiya guda ammi ta fada na dariya, ato nima shi nagani goggo rabi tafadi tana wani sake nukewa,

lah namance bamu gaisaba natsaya surutu tafadi tana dariya, nan tashiga gaishesu suka amsa cikin fara'a da muna suna tambayar ta ya hanya tace alhmdllh,

nan suka cigaba da hiransu cikin raha da nishadi, kiran sallan azaharne ya dakatar dasu daga hiran, daga bisani goggo rabi takalli su fareeda tace,yayan nan muje kutayani daukan kayana mukai dakin Hajiya, yo kaji matar nan ga dakuna da yawa agdn nan bazaki bari nasa baba Barka ta gyara miki inda kikeso kishigaba fadar ammi tana kallon, rabi ,

aa nikam yau ina kusa da Hajiya ta dakinta zan sauka because nayi kewarta, tafa tana kallo Hajj mama tana dariya,

shikenan to autar Hajiya se kudau kayan ku isa mata dashi, ammi tafadi yayinda take kallon su reeda, nan suka dauki akwatin kasan cewa akwatin biyun suka raba kowa yadauki dada suka fita, yayinda rabi da Hajiya suka rufa musu baya, banda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login