Showing 48001 words to 51000 words out of 61982 words
lapiyarki nazo naji bye , yana fadin haka yajuya yafice nan yashiga motarsa mai gadi naganin fitowarsa yashiga mota yabude masa get tareda daga masa hanu ajmal yafice,
heelah shiru tayi da mamakin tureta dayayi dukda ba sabon abu bane wani lokacin haka yake yaita tureta kamar ba namijiba wani time din kuma yanajinta tana kissing dinshi tareda tabashi yanda takeso bazaice mata kalaba wani lokacin ma har biyeta yake, to kode turarenda tasane bai masaba, inba hakaba kodan kewarsa da tayi yakamata ya saurareta,
Nan heelah tashiga shun shuna humran jikinta ko zataji wani aibu amma sam bawata aibu maybe halinne ya motsa kawai
🌴🌴IG AJEEMAL🌴🌴
Story by oum amreesh❤
(Khaleeseart Raeeys)
Page38
Mikewa tayi fiska ba annuri tanufi upstairs Tana surutai,
______Nisha____________
karfe 9:30 nadare bayan kammala dinner kamar kullum kowa ya halarci turakarsa, Nisha na kwance bisa gado Tana kallo cikin wayarta se aheel dake kwance gefenta daya gama rikecinsa har bacci ya daukeshi duk da bacci yaci idonta sosai amma takasa ajiye kallon da take takwanta ,
gefenta reeda ce zaune Tana amsa waya da alamar habibintane akan layi , se fadeelah dake baje saman carpet tana karatun exam dan tuni suka suma jarabawa da alamar tayi nisa cikin karatun, kowanne da aikin da yakeyi
sannu ahankali har bacci barawo yayi nasaran cinye idanuwansu fadeela na kasa tana karatu bacci ya dinke idonta kowacce bacci mai nauyi tashiga yi cikin kwanciyar hankali, guraren 11 aheel yasuma motsawa yana lalubar Nisha dake gefensa yana fadin "
papa, jin surutun da aheel keyi cikin bacci yasa nisha mutsu mutsun bude idonta ahankali, cikin muryan bacci nisha tace "
Aheel what happened fitsari zakayine domin kuwa tasanshi wani time tashi yake yace mata zaiyi fitsari,"
Uhm uhm papana kikaini gurinshi please , Nisha tatsinci muryan aheel yana fadin haka cikin sigan kuka , tarr nisha tabude ido ta tashi zaune tareda kunna wutar gefenta takai hanu ta lalubi wayarta tashiga duba time 11 yawuce , dan waro ido tayi tareda sake kai hanu tadago aheel tajanyushi jikinta tana fadin "
Sorry aheel bazan iya kaika gun papankaba dare yayi sosai ina tsoron fita kar dodo yakamamu gobe zan kaika dasafe kaji! nisha tafadi cikin sigan rarrashi tana dan bubbuga bayanshi, ga mamakinta yaro yasaki kuka mai sauti wanda yanya reeda dake gefensu motsawa ta gyara kwanciya batareda tabude idoba balle tasan rigimar da aheel keyi ,
inba kai yaron nan tayi gurin mahai finshiba da alamar se yarikita kowa nacikin gdn ya ta shesu dan aheel inyatashi rigimarsa baya jin lallashi, tsam nisha tamike tsaye jikinta sanye da gown ta bacci ahanzarce tadauki mayafinta tareda kai hanu tasun kuci aheel tarabashi bisa gafadanta sukayi yuyo parlour
Ahankali take tafiya tamkar wata barauniya kirjinta se bugawa yake tsabar tsoro , tunda suka fitu bakinta keta kwararu addu'a duk addu' ar datazu bakinta yitake tana zare idanuwa ,
Kowa yayi bacci hatta securitys din dake zagaye gdn sunyi bacci gari yayi shiru , seda suka karisa part din tasa hanu tamurda handle din door din taji abude yake hakan yabata daman bude kofar suka shiga ,
Parlour shiru yake nan tasauke aheel tana fadin,"
To gashi nakawoka kakarisa bedroom din papan naka nibari natafi ,
nanfa aheel yanuke yakawo kuka yasaka yana kiran sunan papa shisam sede takaishi bedroom din papansa
duk wannan bidirin da aheel keyi ajmal na kallonsu tasama domin yana parlourn sama saman sofa yana danna system jin motsin shigowarsu da jin sautin aheel yasashi tasowa ya tsaya yana kallonsu,
sanya hanu yayi cikin aljuhun jallabiyarsa yanufi downstairs ahankali yake tafiyan jin motsin ansakkowa aheel da nisha yasa hankalisu ya karkato zuwaga reshi aheel ganin papansa da yayi baijira kariso warsaba yajanye hand dinshi daga na Nisha yayi gurin mahaifinshi da gudu yana washe baki ya fada jikinsa,
zuro Nisha tayi yayinda tabi bayan aheel dakallo yayinda ya karisa ga papansa , kamar ce mata akayi ta tsaya karta tafi haka takebin papan aheel da kallo gwanin shaawa kullum kyansa sake karuwa yake wato ko namiji dan uwansa inya kalleshi dole yasake daga ido ya kalleshi biyu zuwa uku balle kuma macce bataki tasashi agaba taita kallo kamar TV ba
shi kanshi ajmal kallon yarinyar yashigayi da mamaki uwar maita tsaya jira datakasa tafiya se kallonshi take kamar wata mayya duk da yasan ba abun mamaki bane bazai wuce kyawu na face din da Allah yamishi take dubaba , sauda dama inyafita ko ina yashiga andinga kallonsa anasakewa shiyasa yake yawan amfani da face mask dukda wani lokacin yana damunsa saboda matsalar numfashi (asthma)"
Aunty bye seda safe aheel yafadi yana daguwa Nisha hand , seyanzu ahankalin nisha ya dawo jikinta, dakyar ta kirkiro murmushi tare da dagawa aheel hand tajuya jiki asanyaye sidib! sidib!! tafice ,
Ajmal kallon aheel yayi Wanda ya manne masa ajiki ya dagusa tareda azasa bisa shoulder dinsa yakarisa dashi bedroom ya kwantar dashi, yana fadin"
I'm coming , yana fadin haka yajuya yafice daga bedroom din yanufi inda system dinsa yake yakasheta yakuma bedroom gurin aheel yakwanta daga bisani yakalli aheel yana fadin, "
sleep good night lumshe ido aheel yayi yana fadin, "
Good nights papa, nan ajmal ya kashe musu wuta tareda yajanyo blanket yarufesu, bajimawa bacci ya daukeso ,
haka itama Nisha tunda tafito daga part dinsu aheel take ta banka sauri tana waige waige harta karisa sashinsu ta isa bedroom dinsu tanemigu ta kwanta tanamaida ajiyar zuciya , idonta yabude gaba daya jitayi bacci ya kauracewa idonta haka taita juyi daker tasamu baccin ya dauketa ,
Washe gari da misalin 8am ajmal zaune bisa kujera yana sanyawa aheel school shoes ya gama shiryar yashi tsaf domin kai aheel makaranta , murda kofarda akayi ana kokarin shigowa yasa aheel da papanshi suka maida ankalinsu ga kofar
Washe baki aheel yayi tareda zurawa da gudu yayi gunta ya rungumeta yana fadin, "
Good morning murmushi Nisha yayi kana tace ,"
Morning my little baby katashi lapia ?
Lapia qlu aunty aheel yafadi yana murmushi , daga ido Nisha tayi takalli papan aheel time din harya mike yana kokarin barin gurin , muryan Nisha yaji tana daga masa gaisuwa,"
Ina kwana antashi lapia, kamar bazai amsaba sekuma taji yace,"
Lapia! yacigaba da tafiyarsa yabar gurin tabe baki Nisha tayi kafin takalli aheel tareda mika masa school back dinsa data tahu masa dashi , nan aheel ya karba yasanya jakan bisa bayansa sannan ta mika masa lunching box dinsa tana fadin "
gashi special food nayi maka zakaji dadinta sosai, cike da zumudi aheel ya karba yana fadin ,"
Thanks
banda wasa a school yayin karatu , gyada mata kai yayi yana washe baki kamar gonar auduga , suna cikin haka ajmal yafito hand dinsa dauke da key din mota tareda phone dinshi , Nisha naganin haka tasuma kokarin barin parlour, "
Aunty yau bazaki rakani school bane , aheel yafadi yana kallon Nisha da harta bude kofa zatafita , ahanzarce tajuyo tana fadin,"
Sewani lokacin , kafin tafice dasauri tabar parlour, Sam. aheel baiji dadiba yau Auntynsa bazata rakashi school ba , kamar yanda tasaba yan kwanaki , tabbas itama taso rakashi kamar yanda tasaba dan bata gajiya da kallon school dinsu aheel, makarantar burgeta take gwanin shaawa, especially wajan wasanninsu , to amma tareda papanshi zasuje bazaiyiyo tabisuba,
Nan aheel da papansa suka nufi mota suka shiga mai gadi yabude get ajmal yaja mota suka tafi, ,
Nisha na karsawa cikin parlour taci karo da ammi cikin shirinta nazuwa office da alamar cikin sauri take da sauri Nisha ta dagawa ammi gaisuwa,"
barka da safiya ammi antashi lapai, cikin hanzari ammi ta amsa da
lapia qlu, dama bedroom dinku zanje tasuke , aikin lada zansaki idan bakida uzuri nayiwa ajmal breakfast nasa barka tashiryamin ta ajiye a dining table, so kuma ina sauri akwai wani azuri da yataso min office kidauki breakfast dinshi kikai masa part dinsa ,
shiru Nisha tadanyi kafin tagyada kai tana murmushin da baikai zuciba tashiga fadin ,"
Bakomai zan kai mashi sekin dawowa , yauwa kuma kidan tattare masa bedroom din kisan abunka da gwauro ba mace kusa dashi nasan ba abunda zai tabuka, ammi tafadi tana murmushi yayinda take kallon baby face din Nisha, "
To Nisha tafadi ahankali, ammi shafa gefen face din Nisha tayi tana murmushi tana fadin "
Allah yamiki albarka bari naje , murmushi Nisha tasake wanda yasanya dimpul dinta lutsawa because ba karmin dadi tajiba jin albarka da ammi ta Samata , daga haka sukayi sallama da ammi tawuce tafita, ita kuwa nisha tanufi bedroom dinsu,
tana shiga bedroom din tasamu su fareeda sun shirya tsaf zasu wuce school suma because karfe 9 zasushiga paper tuni sunyi breakfast dinsu shape shape dukayiwa nisha sallama suma suka fice, ,
Kwanciya Nisha tayi idanuwanta na kallonsama ta tsunduma kogin tunani amma gani tayi zama cikin tunanin ba amfanin da zai mata zaifi kyau tamike taje tayi abunda ammi tasata kafin yadawo ya taddata cikin sashinsa baisan dashigartaba yazo yanemi lika mata wani sharrin, gwara tayi tagama baisan tashigaba,
mikewa tayi ahankali tanufi parlour tareda wucewa dining table barka tagama shirya komai dan haka ta kinkimi try din abinci tafice tanufi sashin papan aheel, tana shiga parlourn tanufi inda dining area ta dire tr din abincin , sannan tasuma waige waige da tunanin inane bedroom din nasa yake , kallon parlourn tayi bawani dauda yayiba kaikace ba masu rayuwama aciki , sede parlour yana dan bukatan atattareshi abunda yake ba daidaiba amaidashi mazauninsa ,
nan tasuma kokarin haurawa sama inda taga yasakko jiya , seda ta karisa haurawa taci karo da kofar wani bedroom nan tabude tashiga da tunanin shine bedroom dinsa, "
Wow abunda nisha tafurta ahankali yayinda take karewa dakin kallo , bedroom din yayi kyau sosai , komai naciki white and maroon ne , dakin yayi matukar yimata kyau, ga kaya na alfarma komai qlu ba abunda yasamu dakin , dib annashuwar dake face din Nisha yakau saka makon idanunta daya kai wajan mirror ta hangi hoton heelah arantabe agurin ahankali takarisa gaban wajan tadauki hoton tana kallah , dasauri ta ajiye hoton tafito daga bedroom din da alamar dakin matarsace banashiba ,
Gefen damanta da takarisa wani katafaren parlour ne ya hadu ya fasaltu again aciki akwai kofofin bedroom guda biyu dasuke kallon junasu white and pik color dan haka takarisa daya daga ciki inda take tuna nin cikinsu baza arasa bedroom dinsaba,
murda handle tayi tashiga ,"
Ya salam aljanar duniya wannande ko ba afada mataba tasan bedroom dinsa dan bedroom din duk kamshin turarensa kakeji ya gauraye ko ina, komai yaji yayi das dashi alhamdulilah masha Allah kawai za ace dan tsayawa fadin irin kyan dakin bata time ne , komai nadakin back and white color ne because ajmal yanason wadannan color's din su hade guri guda,
ahankali Nisha ke karisawa ciki tana juye juye kamar dan kauye yashigo birni, yanayin tsarin da kwalliyar da akayiwa dakin ba karamin kawata mai kallo zaiyiba , sede dakin yana bukatan gyara because komai nacikinsa ya cukurkude,
Kamadaga bedsheets pillows dindake watse kasa , saman coffee table shima kaca kaca , haka saman mirror dinsa duk ya hargitse , nan Nisha tashiga fara aikinta gadan gadan , duk ta dauke cups dindake saman table din da duk shirgin dake gun tafita dasu kowanne takaishi inda ya dace , koda tanufo kitchen da nufin kai cup's da plate din dayayi amfani dasu , seta tarar da sauran shirgin wanke wanke da ya hada duk da ammi jiya bayan fitarshi tasa baba barka takwaso duk wani shirgin wanke wanke adauraye masa amaida masa "
Hmm lallaifa da aiki nisha tafadi afili kafin tasunce mayafin kanta tadaure jikin kugunta tasuma wanke duk wani abunda akayi amfani dashi tamaidashi mazauninshi,
Atakaice de Nisha yau ta mutsa jiki duminko ta aikato balaifi, tagyara koamai ta kimtsa komai komai yayi tas dashi , nan tafito parlourn sama ta kishingida tana hutawa dan takaji sosai, sassanyar iskar Ac haka yake ratsa jikinta tana wani lumshe ido tana budewa wan dadi se ratsata yake, gaba daya jikinta seya mutu harwani bacci tasumaji,
Nanfa tasake baki tasuma gyangyadawa tanayi tana bude ido , jin hon ana kiciniyar bude get yasa tabude ido da sauri tamike tanufi window, tana daga labule idonta ya hango motar ajmal nashigowa haraban gdn ,
cikin hanzari tanufi downstair sekuma ta tuna da phone dinta dake ajiye saman mirror a bedroom din ajmal marmaza takuma dakin tasun kuci wayarta da sauri har tana tuntube tanufi kasa gudu gudu sauri sauri haka take sakkowa , shikuwa ajmal tuni yakarisu kofar parlour ya murda handle zaishigo, kankace me kafar Nisha daya yashiga cikin daya kafarta ya harde tafadi daga tsakiyar stairs nan tasa ihu arazane , ajmal tsurawa wajanda yaji ihu ido yayi seganin Nisha yayi tana zamuwa daga kwance tana ihu seda takariso harkasa ajmal yashiga binta da kallo yana kuma kallon sama inda tazamu da mamakin mai yakaita saman
🌴🌴IG AJEEMAL🌴🌴
💦Story and writing by oum amreesh💦
DAGA ALKALAMIN✍🏼
🦚Khaleeseart Raeeys🦚
_________________________
FREE BOOK
Ya Allah yanda nafara rubuta wannan littafin kasa naga karshensa lapia, kabani ikon rubuta abunda zai ilimantar ya nishadantar ameen********************page 39
Ahankali Nisha ta Mike tana mis mis da ido tana dan cizon lips din ta kamar maishirin kuka, because jikinta yabugu sosai, yafinta data daure saman waist dinta tasunce tamaidashi saman kanta tasuma kokarin takawa,
slowly take dingisa kafar tana tahowa shide ajmal haryanzu kallonta yake hartakariso gefensa ta tsaya yayinda tasun kuyar dakai kasa baki nabari tasuma fadin, "
Uhm ammice tace nazo nakawo maka breakfast sena gyara maka bedroom dinka idan da wani abunma kafadi zanma, jin shiru bai amsataba yasa ta daga ido ta kalleshi still idonsa nakanta but baice komai, ganin haka yasa ta dan hadiye miyau tazame jiki tasuma kokarin barin parlourn, "
Hee you! cak Nisha ta dakata da tafiyar da take jin muryan ajmal akaushashe yana magana nan tajiyu tana kallonsa suna fiskantar juna, daga inda yake yatako yakariso kusa da inda take tsaye, seda yagama kallonta tsaf sannan yace,"
As from now karna sake ganin kafarki cikin side dina if not zan karya wadannan sirarun kafar takin , I hope kinfahimci point dina , ajmal yafadi yana kallon Nisha da hawaye suka wanke face din kanta asunkuye tana sauraron abunda yake fadi,
Oh allah wannan wace iriyan bakin haline ga mutumin nan duk wahalar da tasha wajan gyara masa muhalli da maganganun da zaisaka mata dashi kenan gaskiya tayi danasani duk da ba ita tasa kantaba ammine tasata kuma dan ita tayi ,
Kikoma kidauki breakfast dinda kika shigo dashi kifitarmin daga side bana bukata, ajmal yakuma fadi karo na biyu, share hawaye Nisha tayi tareda takawa ta isa zuwaga dining table inda ta ajiye abincin da tashigo dashi tasa hanu ta dauki tr din tanufi hanyar fita, ajmal yana kallonta yanda take taka kafar dakyar hartafice tabar side din daga bisani ajmal yaja wani siririn tsaki yacilla phone dinsa tareda key din motarsa saman sofa yanufi upstairs,
Tunda yashiga bedroom din yayaba da gyaranda akayiwa dakin domin ko bakomai bedroom din yayi bakon gyara komai yashiryu yayitas dashi komai yazauna inda yadace gyanin kyau gwani burgewa , dan zamewa ajmal yayi yazauna bakin bed yana maida ajiyar zuciya, yadade ahaka natsawun wasu mintuna daga bisani yashiga sabule kayan jikinsa wanda yarage dagashi sedan short yanufi toilet domin wanke jikinsa,
ya dade yana wankar daga bisani yafito ya kimtsa jikinshi yashirya cikin yanayi mai kyau da daukan hankali yasanya turaren sannan mai kamshi dadi mai wuyar barin jiki yanufo downstairs,
inda ya cilla key tare da phone dinsa yanufa wanda tunkan yakariso wajan yakejin karan ringing phone dinsa yana tashi alamar kira but kafin yakariso takatse,
Nan yashiga duba wayar yaci karo da miss call din doctor fu' ad kaca kaca ahanzarce yafice daga parlourn yafito yanufi motarsa yashiga mai gadi yabude masa gate yafice,
aban garan nisha kuwa tunda tabar side din IG tanufi sashinsu idonta sefidda kwallah yake , tana shiga parlour tanufi kitchen tare da ajiye tr din abincin bisa table din kitchen din tafice da sauri tana shashshekar kuka, barka dake tsaka da aiki jin motsin shigowar nisha ta ajiye tr tafita tana kuka hakan yasa barka ta tsagaita da abunda take tabi bayan nisha cikin bedroom din su,
koda barka tashi akwance tasamu nisha tayi rubda ciki tanitsa kanta cikin pillow kuka mara sauti ahankali barka ta matsa kusa da bed din tana fadin,"
yar nan lapia kuwa kike kuka? dib Nisha ta tsaya dakukan jin muryan barka tana tambayarta, mikewa nisha tayi daga kwanciyar datayi tazauna tanamai share hawaye tana fadin,"
Ba komai, "
Aa yarinya yazakice ba komai bayan gashi kuka nazo natadda kinayi , wani abun aka miki, kinzo kin ajiye tr kintafi kina kuka , kuma nasan daga sashin ajmal kike wani abun ne yafaru,
barka takuma tambaya tana kallon baby face din Nisha dayayi jawur bawani bata time nisha tashiga labartawa barka abunda ya wakana takarishe zancen da kuka tana fadin,"
sam papan aheel bayida ahali irin na yayan gdn nan halinsa ya banbanta danasu , kowa dake cikin gdn nan ya karbeni hanu biyu bawanda ya kyamaceni, amma shikuma gaba bayason ganina daga shi har matarshi ko alakata da dansa baso yakeba kwata kwata bayason narabeshi bansan dalili ba,
Nikuma tunda Allah yayi zuwana gdn nan Allah ya hada jinina da na dansa , Allah yadauramin son da kaunar aheel cikin zuciyata jinake tamkar ciki daya muka fito , ko wuni nayi bansa aheel aidonaba banajin dadi, gashi yau yamin iyaka da inda suke balle nasake haduwa dashi, waishin wani irin hali gareshi haka? Nisha tafadi gamida sunkuyar dakai kasa tanamai matsa kwallan da suka cika idonta,
dan numfasawa barka tayi tareda matsowa kusa da nisha tadafo shoulder dinta tana fadin,"
kiyi hakuri yar nan dama ita rayuwa haka take akwai mutane iri da kallah , amma sam wannan abunda yafaru ya dameki ko yadaga miki hankali , ajmal ahaka yake bayida saurin