Showing 12001 words to 15000 words out of 61982 words

Chapter 5 - IG AJEEMAL book1 Hausa Novel

03 Sep 2025

1537

ba irin fadeela mezaben shirmeba tafada cike da tsukana, kallon fadeela sukayi da ta tura baki gaba tana kallon reeda yayinda take maganar dariya suka shiga mata, Salma tace,

" lallai kin iya kam dan gsky rigan tayi kyau sosai , thanks reeda tace tana fari da ido, sunyi fira sosai, kiran sallan azaharne ya dakatar dasu daga hiran kowannesu ya nufi toilet yin alwala, nan suka shinfida sallaya sukayi sallah, bayan sun idar , fadeela taja hanun Nisha suka nufi kitchen suna zuwa suka sami baba Barka takammala komai dan kwata kwata batar bata da ganda ga sauri wajan aiki nan da nan, fadeela ne tashiga shirya musu abincin seda ta kammala ta kalli baba Barka tace,

" yau a bedroom dinmu zamuyi lunch dan haka ki kaiwa Hajiya nata sa shinta, cikin hanzari baba Barka tace,

" to shikenan za akai mata, muje fadeela tafada tana kallon Nisha, itama Nisha kallonta tayi tana fadin, kije zanzo , gyada mata kai fadeela tayi tareda ficewa ta tafi, kallon Barka Nisha tayi tace ,

" ki hadamin abinci Hajiya nakai mata, " lah yata da kin bari yanzun nan zan hada nakai mata bada wani bata lokaciba, aa karki damu inaso nakai mata ne da kaina, bata mata wani musuba tashiga shirya mata abincin tareda mika mata, amsa Nisha tayi tajuya tafita, bangaran Hajiya tanufi ta murda handle din kofar tashiga, bata tarar da ita a parlour ba hakan ya tabbatar mata tana bedroom dinta, dire abincin tayi a table din dake parlourn, tanufi hanya dakin, murda handle din door din tayi hade da sallama kasa kasa, jin shiru yasa talekawa ahankali ta hango ta kwance saman sallaya hanunta rikeda carbi, da alama bacci ta sumayi, kamar ta ta suta sekuma tafasa tareda maida door din tarufe tanufi hanyar fita, tana fitowa harta nufi hanyar part dinsu, karaf ta hangi AJEEMAL dake kokarin fita jikinsa sayi da kana nan kaya sun amshi jikinsa sosai, ganin yanufi hayar geat mai gadi yabude masa yafita, wani hamdala tayi dan yau da son ganin yaron ta tashi duk da tasan cewa papansa ba nisa yayiba ganin bai dauki motaba, hakan yabata daman sidadewa bangaransa, takunna kaiciki, da sallama kasa kasa takarisa shiga ciki tana dan zazzare ido,

akujera ta hango aheel na zaune ya tusa tv agaba yana kallo abincine gabansa amma wasa yake dashi hankalisa nakan kallon cartoon, yana ganinta yashiga washe mata baki yana kokarin tashi, karisuwa tayi kusa da kujeran sa ta rungume shi tana murmushi tareda sauke ajiyar zuciya, daguwa yayi yana kallonta ciki da dariya yana fadin," Aunty dazu ina kukaje kedasu Aunty farida, aheel shopping mugaje, papana yaganku ae, gabantane yadan fadi , hakan yasata mikewa tana fadin," bari natafi su fadeela suna jirana, letter are well come back, ga mamakinta yaro yasuma kokarin kuka yana make shoulder yana fadin," karta tafi tabarshi, ita kuma tsonta kar papanshi yashigo ya tarar da ita dan ta fahimci ba nisa yayi ba, jin kukan yake da gsk yasata matsawa tazauna tana fadin,

" shikenan bazan tafiba, nan tasuma bashi abincin abaki hanunta se bari yake, kallon shi tayi tana fadin," ina mom dinka, dazu mummy na tafita kuma bazata dawo ba se dare time din nayi bacci, cin shagwaba irin na yara yace,"Aunty mummy na bata son zama gd kusa dani, papa nane yake son zama dani har office dinsa yana zuwa dani, bakaramin tausayi yaron yaba Nisha ba , rashin kulawar mom disa atareda shi, da alama bata wani damu dashiba, muryan aheel taji yana fadin," papane yakemin wanka ya samin kaya yadafamin abinci, kallonsa kawai take yayinda yake zuba surutu, to kayi shiru ya isa haka ka karisa cin abincin, yanzu papanka zai dawo nima kuma ana jirana bari naje nan ta lallabe shi tafada tareda mikewa tayi tanufi hanyar fita, yayi daidai da time din da AJEEMAL ya kunno kai yana kokarin tura door din,

idonsane ya sauka akan na Nisha hakan yasashi dakatawa yana binta da wani kallo, itama ganinshi datayi tsaye yasa taji kamar tasake fitsari awajan, tsabar tsorita, wani kallo yadinga binta dashi wanda yasa duk ilahirin jikinta ke bari, shikuwa bawata kallo bace da tawuce nacinda takewa dansa da shishshige masa datake wanda ba kaunar hakan yakeba, takaicine duk ya isheshi yarasama bakin magana, ita kuwa tarasa meyasa inta ganshi take nuna masa tsoronta afili kamar mara gsky, duk yanda takaiga danne tsoronta indan taganshi but takasa, because wani irin kwarjin yake mata, dukansu kowa ya gagara bawa dan uwansa hanya yashige, ita tana bakin door din shima haka, Nishane jitayi kafarta yamata nauyi tagagara ko mutsawa , muryan aheel ta tsin kaya dacewa,

" papa yace zaikaini wasa anjima zamuje tareko zaki rakamu.,? jiyowa tayi tana kallonsa tagagara basa amsa sedariyan yakenda bata san tana yinsaba maida kallonta ga AJMAL tayi da haryanzu wannan kallon yake binta dashi, still kuma yaki bata hanya tashige, daker ta iya matsawa baya kadan kanta sunkuye, wani harara ya wurga mata tareda jan karamin tsaki , shima tsayawar da yayi soyake yaga karshen rashin kunyarta na rashin kauce masa daga hanya da batayiba, ganin yashiga yasa tasamu damana fita cikin hanzari, aheel bin mahaifin tashi yayi da kallo, yanda ya hade gira yabata fiska, AJEEMAL kokarin shige aheel yayi daniyar shiga bedroom muryan dansane yatseshi dacewa,

" papa nagama cin abincin yafada yana kallon mahaifin nasa, cikin hanzari tajiyo batareda ya cemasa koamiba ya dauke plate din yakai kitchen yadawo yakalli aheel yana fadin,

" zanje nakwanta akwai abunda kakeso,? yafada cikin tsare gd, papa nima zanyi bacci kusa dakai, kamar zai daukeshi sekuma yafasa, yajawo hanun dan nasa yasauko daga kujeran , ahankali yake dingisa kafar hasuka isa bedroom, kwantar dashi yayi shima ya kwanta, domin yasamawa kansa saukin bacin randa yakeji, allah yagani kwata kwata bayaso Nisha ta kusanci aheel, gaba daya ransa baci yake inya gansu tare, gashi allah yayi dansa mai bala'in wayo da surutu allah kadae yasan mai yake gayamata insuna tare, gaba daya bakin aheel ba ba control, maida kallonsa yayi ga aheel daya tsura masa ido yana kallonsa, yaron magana yakesonyi but ganin mahaifinsa fiskarshi babu annuri yasa shi yin shuru, shikuwa AJEEMAL kallonda aheel yake masane yasa yace,


" bazakayi baccin bane kake kallona, lumshe ido aheel yayi daga bisani papansa yaja musu blanket yarufasu,
Nisha kuwa tana shiga part dinsu tasamu ita suke jira dan haka tasamu gu tazauna sukashiga fara cin abincin suna dan hiransu cikin nishadi, bayan la'asar salma tafara kokarin shirn tafiya gd, nan fareeda tasanar da ita wani birthday party dazasuje nawata friend dinsu , dan haka ta tsaya sutafi tare daga bisani sesu sauketa agd, haka kuwa akayi nan suka shiga shiri cikin riga da wando saman kuwa suka daura bakar riga, itama Nisha hakan suka sata tayi, fareeda taimata light makeup tafito tas da ita tayi kyau sosai, salma se kallonsu take yanda sukayi kyau dasu musamman Nisha kamar ba itaba, da itama kamar zatasa duguwar riganda reeda taba sekuma tafasa because seta nunawa ummynta, part din Hajiya suka nufa domin mata sallama, a parlour suka sameta zaune tanacin abincin da Nisha tazo ta ajiye mata, binso tayi da kallo daya bayan daya tana kare musu kallo, yan matan daddy sunyi kyau sosai, too wannan kwalliyarfa se ina, waje suka samu suka zauna suna kallonta , ina tambayar ku se ina, sun kuyar da kai nisha tayi tana jiran taji mai zasuce, cikin susa kai reeda tace

" am gdnsu fauziyya zamu yau take birthday, ba ranar munfada miki zatayi birthday ba ko kin mantane, aa ban saniba amma kusantu dazu kunfita da safe , AJMAL yanajin fitarku agdn nan haka yazo yasamene yana fadin fitarku yayi yawa kuncika yawo duk inda kukace zaku ninake barinku su ammi basusan shiga da fitar kuba, to kunga atakaice dai ninake daure muku gindi kenan ko,? to tunkafin ku saka ranku afitar nan gwara ku hakuri shi zaifi dan nasan zaku iya gamuwa dashi, kuma ba wanda zaije yayi mitar seni gwara ahakura da kitarnan kawai, parlourn ne yadau shiro kamar bakowa daga bisani fadeela tace,


" amma ko fauzee bazataji dadiba fareeda tace gskykam tafada tana kallon Hajj mama, kuma ae fitanda mukayi dazu ammi ne ta turo da kudi tace muje muyiwa Nisha shopping, to komade mainene kukirata kubata hakuri baza kusami zuwaba , kai bazai yiyuba shi waya takura masa haka damu zai takuramu reeda tafada tareda mikewa tsaye, cikin hanzari hajja mma tace,


" to rashin kunya zakimin, ko zaki ketare abunda tacene iyye, sbd kin isa ko shakararriya, jitayi kamar tayi kuka because sunsa ransu zuwa party nan, part dinsu tanufa suma suka rufa mata baya, yau murna ya komaciki, gaba dayansu samun waje sukayi suka zauna bawanda ya iya cewa da dan uwansa kala, salma kadan yarage dariya ta kubcemata, yanda take kallonsu fadeela bakinsu kamar zai taba bango, jin ana kokarin bude geat fareeda tamike cikin hanzari yayi labuleh window tana lekawa, AJEEMAL ne yafito hand dinsa cikin na aheel suka shiga mota mai gadi yamude masa geat yafita, wani wawan tsalle reeda tabuga cikeda murna tace,

" kaikuzu mutafi yanzu ya AJEEMAL yafita, part din Hajiya suka koma suka sanar da ita yayansu yafita hutawa dan Allah suma tabarsu suje su shakata, ganin yanda suka damu da fitar yasa ta kyalesu, da sharadin lallai su dawo kafin dawowarsa in har yadawo yafahimci basa nan tofa ba ruwanta, dan sunfita sanin koshi waye kuma sunsan halinsa, cin yanayi na murna da nisha di sukace inshallah allahu ma zai dawo ya tarar dasu agd, nan suka mata sallama sukayi gaba, tafiya suke suna hiransu cikeda nishadi, tsayawa sukayi daidai wani katon plaza suka shiga suka siya mata wani birthday cake mai hawa uku cake din yayi kyau sosai gwanin shaawa, suka hada mata da wani turare na kwali mekyau da kamshi ga kuma tsada, suka shige mata dashi,
koda suka iso wajen sukayi parking motarsu a compound din wajan, tundaga arian wajan kakejin sautin kifa natashi koda suka karisa shiga Hall din, salma da Nisha suke karewa wajan kallo wajan ba karamin haduwa yayiba kaikace biki ake, ganin su farida da fauzee tayi yasa tayi kansu da gudu ta rungume su, ta mikawa salma da Nisha hand suka gaisa, ga fara'a ga kyau yarinyar balaifi, aina dauka baza kuzuba danaga time yaja da harnayi fushi, fauzee tafada tana kallonsu, kema kinsan ba abunda zai hanamu zuwa ae suka fada suna dariya, waje ta sama musu suka zauna daga bisani suka mika mata gift dinda suka taho mata dashi cikin murna da farin ciki ta karba tana fadin,

" thanks, kowani table ankewaye da kayan ciye ciye da makulashe, mazansu da matansu se shashewa ake ganin haka yasa fadeela da reeda suka mike suka shiga cikin yan rawar because yawanci classmates dinsune awajan, can Nisha taji bazata iya jure zama wajanba, ga wasu maza da suka zuba musu ido suna kallonsu musamman Nisha, ganin haka yasa Nisha tamike tana kokarin fita , yanaga kin mike salma tafada tana kallon Nisha, nagaji da zaman nan dinne ga kuma karan balonda yake fashewa, jirani nima salma tafada tareda rufa mata baya, su reeda kam basuma kula da fitansuba, hankalinsu yayi gaba, waje suka samu daga gefen Hall din suka zauna, suna ganin masu shiga da fita na wajan , ke dama inaso na tambayeki dama haka ya AJEEMAL din nasu yake, mekike ganin Nisha ta tambaya, yanada miskilanci kuma masifaffene, dariya Nisha ta tintsire da dariya tana fadin,

" gsky baki fahimce shiba mutumne da yatsa akasa masa abaki bazai cizaba, yanda kikasan kurmafa haka yake gsky banaje yacika surutu bama balle masifa dakikace, baeshida miskilanci de, amma de bansan mekika ganiba kikace hakan, to nide abunda idona yagani kenan kuma yayi agabana nagani, domin dazu danazo ban samekuba kunfita muna zaune da Hajiya yashigo yana surfa bala'in, wai ina kukaje, wlh mutumin nan kamar bazai amsaba nina daukama bai jinibane ashe yaji se masifa yake nida farkoma na dauka ko baban sune amma yanda nagansu zankada zankadan yan mata nace kai wannan bai kai ya haifesuba, allah seda nayi nadamar gaisheshi, dariya Nisha tashigayi tana fadin,

"tab waneshi ya haifi kamar wadan nan, boy dinsa daya aheel shima daya yakare dashi, nimade shinagani ganin masifar tayi yawane shiyasa nayi tunanin hakan salma tafada tareda sake fadin,

" ke tashi mukoma ciki kar su nememu surasa, mtswww wlh banason komawa cikin nan bare barensu yayi yawa Nisha tafara tana tsuke baki, daurewa zakiyi ae munkusa tafiya salma tafadi, harsun tashi zasu shiga me idonta rahila da wani matashin saurayi sunfito daga mota suna kokarin shiga cikin hotel din, idonta tarufe takuma budewa da sauri tareda murza idon da kyau tana binsu da kallo, salma ce ta dan bugeta kadan tana fadin,

" ke lafiyanki kuwa meye hakan,? kinta bin bayin allah da kallo kinsansune dakike kallonsu hk, ke nasanta mummyn aheel cefa dawani sekuma tayi shiru ko ba ita bace kam Nisha ke tambayan kanta, to mema zai kawota nan ita da take gun aiki, inga kamane ko nasaba gani, gsky kam kinsaba gani kam dan banga mezai kawo matar aure nanba, to meye ma naki aciki in itace mutafi muyi abunda ke gabanmu salma ta Fadi, tabbas abun yabawa Nisha mamaki dama ace batasan rahila bace se ace kama tagani ko kuskusne ganine, dan haka bawani batun kama itance,.

"kukuma mekukeyi anan munata nemanku aciki, please kudawo ciki fareeda tafada tareda juyawa, rufa mata baya Nisha da salma sumayi suka shiga ciki, , anci ansha yanda yakamata anyi rawa sosae gari yarufa magarib ya gabato kai, yanda suke ciki bawanda zaiyi tunanin magrib yayi, kowa dake wajan seda fauziyya ta taimasa kyauta mai kauri daga bisani akashiga watsewa, fituwar su fareeda keda wuya, sukaga gari yayi duhu, lokacin fadeela takalli agogon hanunta karfe 6:45 , ga miss call din hajja mma kaca kaca, nan suka shiga mota suka nufi hanyar gd , seda suka suke salma agd sukayi sallama, sannan suka wuce suma, reeda ta dannawa mai gadi hon, yabude musu suka shigo, tundaga nisa suka hango motar yayansu, dan haka sukayi parking motar suka fito, kota kan Hajiya basuyiba suka wuce part dinsu asukwane, kowannesu ahankali atashe banda Nisha da ahankali ta akwance yake, dan haka tanufi toilet tayi alwala tafito tayi sallah abunta, ganin haka yasa suma suka tashi sukayiyo alwalan sukayi sallah, bayan idar wansu kowa yasamu gu yazauna , kowannesu da abunda yake sakawa cikin ranshi, tunda suke basu taba kai dare awani wajeba se yau, duk fitanda suke arayuwar su, da zaran yamma tayi zasu nemi hanyar gd, sede infita yakama na family to shine ahankalinsu kwance, gashi yau sanadin fauziyya sunyi dare,

Nisha kam yau gaba daya abun kallo su reeda suka dawo mata, duk yanda suke da surutu amma yau shiru kamar basuba, ko wacce se zare ido take kamar tayi karya, jin ana turo door yasa suka kurawa kofar ido a tunanin su Hajiya kokuma yayansu, ganin Barka ce yasasu sauke wani goron numfashi, kufito kuci abinci anshirya komai baba Barka tafadi, dukansu bamaijin yunwa, dan ba karamin ciye ciye sukayiba awajan partyn, duk da nisha bawani cin abu tayi sosaeba, itama ba yunwar atareda ita, nan suka sanar mata ba maijin yunwa acikinsu ma'ana yau baza sufito cin abinci ba, bata tambayi daliliba tajuya tafita daga dakin, itama Hajj mama cewa tayi takai takai mata nata bangaran ta, sunayi Isha kowa tanemigu ta kwanta yau bawani Hira, juyi suka dingayi dake suka samu bacci ya daukesu, da suba Nisha ne ta tashesu sukayi sallah daganan suka nemi guri suka kwanta, Nisha kuwa seda ta dan taba karatun Qur'an data saba, sannan ta kuma ta kwanta itama,

se wajan karfe 10:30 , Barka tazu ta tashesu tasanar dasu ana jiransu a parlour, wanke bakinsu sukayi sannan suka fito, angama shirya komai kan table Hajj mama zaune harta fara cin abincin ta, karisowa dining din sukayi suka shiga daga mata gaisuwa bata kallesuba tamaida kallonta ga nisha tareda amsa nata gaisuwan, ganin haka yasa suka sake gaisheta karo nabiyu , murya can ciki ta amsa musu, sannan suka nemigu suka zauna tareda diban abinci suka suma ci, suna tsaka daci, AJEEMAL ya kunno parlourn hade da sallama jikinsa sanye da kana nan kaya wayanda suka amshi jikinsa , abunka da kyakykyawar namiji sede ace shiyayiwa kayan kyau, hand dinsa daukeda na aheel, fiska ba yabo ba fallasa, ya nemigu daga parlourn yazauna remote ya dauka ya kunawa aheel cartoon amma sam aheel hankalisa baya gun, yana kan Auntyn sa se washe mata baki yake yana kokarin tashi yaje gunta ganin yanda papansa yarike hand dinsa gam yasa yakalli papan nashi , koda yaga hankalisa nakan wayarshi yasa shi dole yakura yakoma ya zauna,

Nisha duk tana ganin abunda AJEEMAL keyi wato bayason aheel yazu gunta shiyasa ya hanashi tashi, su reeda kam tunda yayansu yashigo suka dakata da cin abincin kirjinsu se dukan uku uku yake, Hajj mama mikewa tayi tareda riko hand din nisha suka nufo parlour, ganin Hajiya ta tasu yasashi zamewa daga zamar da yake still yana rikeda hanun aheel, gaisheta yayi ta amsa da fara'a tareda neman guri tazauna, shima kujeran ya koma tazauna yashiga latsa wayarsa , Nisha kamar bazata gaishe shiba, sekuma tace,

" ina kwana, shima shiri yayi kamar baijiba, sekuma yace lapia, tareda maida kansa ga wayarsa, jin muryan aheel yakira sunan Auntyn sa yasashi AJEEMAL saurin kallonsa sekuma yamaida kallonsa ga Nisha da tamikowa aheel ahannu alamar yazu, ganin Hajiya na kallonsu yasa AJEEMAL yasaki hand din aheel fiska murtuke yakebin aheel da kallo ganin irin tacinsa dashi da Auntyn tasa dayake Fadi, ahankali aheel ya dingisa yakarisa gun Nisha tareda fadawa cinyarta yana dari itama Nisha dariyar take tana fadin,


" my baby yakake, I'm fine aheel yafada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login