Showing 6001 words to 9000 words out of 61982 words

Chapter 3 - IG AJEEMAL book1 Hausa Novel

03 Sep 2025

1536

wacce tayi karamin hauka, tunda doctor yashigo yamata allura bata sake tashiba se washe, se gurin yamma tasuma kokarin bude ido, ahankali take bude idon harta budeshi tar bin kowannesu da kallo Nisha keyi tana dan zazzare ido tana kuma maibin dakin da kallo, jitake kamar abun a mafarki, wai dagaske umma tafiya tayi tabarni, ? ido suka zuba mata cikin tausayawa jin sun batunda take, salmace takarisu tarike hannayenta tana faɗin

"kiyi hakuri Nisha duk mairai mamacine muma wata rana bama raye addu'a take bukata agareki ba kuka ba, please kiyi hakuri" Nisha binta tayi daga kallo sekuma tafashe da kuka tareda fadawa saman cinyar salma tana faɗin,

"salma wai dagaske umma rasuwa tayi salma jiyafa kwana mukayi da umma muna fira, yanzu awayi gari babu ita, salma kikaini gurin umma doctor yasake dubata bata mutuba nasan umma bazata tafi tabarni ba" tafaɗa cikin sigan kuka maiban tausayi, kokarin turo kofar da akayine yasa Nisha tamike dasauri tanufi kofar tana fadin,

" doctor um.ma . , sekuma tabi ta tsaya cak kafarta yadau bari kamar mazari, tana neman faduwa, ganin haka yasa hajiya tamike da kanta ta janyo Nisha jikinta takwantar, bin yarinyar yayi da kallo da bakaramin kuluwa yasumayi da yarinyar ba, duk yanda akayi brain dinta da matsala, dan karamin tsaki yaja tareda maida kallonsa ga dansa aheel dake kwance cinyar fareeda ganin yayan nasu yasa tazame aheel daga cinyarta takoma gefe indasu Hajiya suke,

matsawa yayi yamaida aheel nasa cinyar yana mai shafo gashin kansa yayinda yake baccinsa, shawaran Hajiya da tabukaci hada aheel da Nisha room daya because Nisha ba kowa kusa da ita dan haka ahadasu tare kodan susamu daman kula dasu duka,

"Hajiya anbamu sallama so zamu iya tafiya, yafaɗi batareda yakalli indasu keba,"

" eh haka nasani sunake yarinyar nan tadan koma dede inyaso mutafi da ita, kasanfa batada kowa kusa da ita mahaifiyar ta tarasu kar kewa yamata yawa, " sake baki yayi yana kallon karfin hali irin na kakar tasu, daman yasan za arina hakan duba da yanda suke wani shishshige mata,

' basusun yarinyar daga ina takeba basusan komai akantaba kuma ace za adauketa akawota cikin family' girgiza kai yayi ba tareda yasa yace komai ba yacigaba da abunda ke gabanshi gamida tabe baki ba tare da daya sake cewa komai ba, maida kallonsa yayi ga ɗan nasa Aheel da haryanzu baccinsa yake, mikewa yayi yasuma kokarin fita daidai lokacin da salma tashigo da Doctor dumin duba nisha cike da tabe baki yawuce yayi gaba abunsa,

Dubata yayi sosae yasanar dasu zata iya farkawa koda yaushe, dan haka za aiya sallamansu bawata matsala, bayan farkawarta kamar yanda doctor yafada suka shiga tattara kayansu dan komawa gd, AJMAL kam tuni yayi gaba da dansa dan haka suma suka shiga shirye shiryen bin bayansu, Nisha kam ba abunda take se kuka, duk inda akayi da ita nan takebi domin kuwa batada inda zata rabe, Hajiyace tarokota tashigarda ita mota, salma nata faman bata baki da tabar kukan haka tayi hakuri tabar komai agurin Allah, tamika lamurnta gareshi, sai da ta tabbatarda tarage kukan sannan sukayi sallama tareda alkawarta mata gobe zatazo inda take, sunyi musayar number da fareeda zata kirata,

Wani kuka Nisha tashiga yi ahaka suka rabu da salma, gaba daya jikin salma yayi sanyi duk taji babu dadi allah sarki umma mutuwa meraba tsakanin da da uwa, tafiya suke yayinda Hajiya tareke Nisha tsam ajikinta yarinyar tashiga ranta ga tausayi na rashin uwa, tabbas karasa duk wata madafa arayuwa, tanajin yarinyar kwarai ajikinta ba ita kadaibama hattasu reeda domin kuwa Nisha yarinyace maishiga zuciya, motarsuce ta kunna kai cikin wani gd na alfarma, nagani Nafada, hon dinda akayine yasa mai gadi yaye geat din gdn, shiga sukayi tareda yin parking ainda ake adana motocin, fito da ita Hajiya tayi ta dangana da ita izuwa cikin gdn, tunda suka shigo nisha taketa karewa gdn kallo masha Allah gdn ya hadu sosae gawasu shuke shuke masu daukan ido da jan hankali 😌 kaida kaga gdn kasan ba irin tsarin gdnmu na nigeria bane, gaba daya kirjinta sewani irin bugu yake, murmushi Hajiyan ke bin Nisha dashi yayinda take karewa gdn kallo, parlour suka nufa yayinda su fareeda ke biye dasu, wani lallausan capet data taka yasata lumshe ido hadeda bin parlourn da kallo, ya Salam aljanar duniya parlourn ya hadu iya hadu kuma ya tsaro, gaskiya an narkawa gdn kudi sosai ba karya , zaunar da ita tayi a lallausar kujeran sannan ta kallisu fadeela tace,

" kukaita bedroom ta watsa ruwa ta huta, basu jira takarisa maganar ba kamar jira suke fareeda taja hanunta sukayi ciki, toilet ta nuna mata hade da mika mata towel nan ta karba tareda shigewa tamaida kofar tarufe, kallon toilet din tafarayi tana bin ko ina da kallo, toilet ma kaide aka barka dashi abun kallone, to ni yanxu ta ina nasan zan fara, wasu ma dannai kurawa wajan ido tayi sekuma tasa hanu ta danna daya daga cikin madannin , shaa kaji ruwa me bala'in sanyi yazubu mata, bakaramin kidima da tsoro tayiba, hakan yasa tafito dagudu tana salati, juyowa sukayi gaba dayansu suna kallonta, jikinta se rawa yake ruwa se diga yake daga fiskarta, reeda ne tamatso tana tambayanta lapia kuwa,? shiru Nisha taimata , jin karan ruwa nazuba hakan yabawa reeda daman lekawa toilet din tagani, shower ta kuna ga power ruwa se zuba yake, sekuma tamaida kallonta ga nisha taketa wutsi wutsi da eyes cike da kunya, murmushi reeda tayi tareda jan hanun Nisha , nuna mata tayi duk yanda abubuwan toilet dinsuke da yanda zatayi amfani dasu,

" nagode" abunda Nisha tace kenan, fitowa tayi domin bawa Nisha waje tayi wankan, wanka tayi sosae taji dadin jikinta tana jin wani nutsuwa na ziyartar ta wanka rahamane, fitowa tayi daga toilet din ga mamakinta bata gakowa adakinba alaman sunfita daga dakin kenan, wani duguwar riga tagani asaman bed din da alamar ita aka ajiyewa dan tasan batazo da wani kaya in gantacceba, dan haka ko inda mai yake bata nemaba tashiga sa kayan, ya zauna damas ajikinta sede dan matseta da yayi kadan kasan cewan tadan fisu jiki kadan , kallon kanta tayi amadubi kayan ya amshi jikinta yayi mata kyau sosai abunka da kyakykyawar mace, waje tasamu daga bakin gadon tana karewa dakin kallo, shiru tadanyi na wani lokaci se kuma tunanin umma ya fado mata , kuka tafashe shi tareda nitsa kanta afilo tana kuka tana fadin," ina ma ace marki take duk abubuwan dasuke faruwa ayanzu mafarkine ba gaskiya ba,

***** Wacece Nisha da kuma labarinta*******

Aishatu Hashim yarima
Yace ga Alh Hashim yan asalin kasar sudan mahaifinta da mahaifiyar ta tushensu kenan, kasuwanci ya kawoshi nigeria yankin adamawa, cikin garin adamawa aka haifi Nisha, ita kadai Allah ya mallaka musu matsayin ya, dan haka suka dauki son duniya suka daura mata, sunsata makaranta mai inganci boko da arabic, suna kulawa da ita sosae ba abunda ta nema tarasa, duk abunda takeso shi akeyi, har Allah yasa kasuwancinsa yakara bun kasa yazama babban dan kasuwa, yazama babban mutum Allah yarufa masa asiri ya daukakashi, kasan cewan shikaru gaba suke girma na kara bayyana, Alh Hashim ya damu da rashin haihuwar matarshi Hajiya Zainab mahaifiyar nisha da batayiba, tun haihuwar Nisha bata sake ku bariba, tabbas ba abunda yafi bukata ayanzu da yawuce haihuwa, kuma da namiji atunanishi yasamu magaji wajan kasuwanci, saboda kullum shekaru ja suke girma na karuwa,

Alh Hashim mutumne maison tara zuri'a sunyi addu'a sunyi magani gd da asibiti amma shiru ku alaman batan wata babu, shikuwa kullum maganar da bata wuce na haihuwa, abun harya fara bawa Hajiya Zainab haushi da ita take bawa kanta haihuwa da tabasu, gdnsu se yacika da yara amma abun na allahne ba yadda zasuyi, nanfa yafara neman shawaran abokan arziki to abunka da shawaran namiji bai wuce aureba, tabbas baiyi niyan kara aureba kuma bayida ra ayin karawa to amma ba yanda zaiyi tunda yana da bukatan yara, koda aka bashi shawaran kara auran ya kasa tin karar matar sa da maganar, to abunka da mace mai tunani tuni tagane inda yadosa, dan haka tasamishi da maganar dacewa,

" idanaure yakeson yi ya sanar da ita ba hanashi zatayiba, allah yabashi ikon auran mata 4 ita bata isa ta hanshi abunda allah ya halasta masa, yadena wani buye buye, amma abunda takeso ya fahimta shine karin auransa bashine zaisa yasamu abunda yake bukata ikon Allah ne, inda ya daya rubuta zamu rayu tofa wanda ya isa yacanza hakan"

Tudae Alh Hashim yayi auransa kamar yanda tabashi dama, ya auri Hajiya Fatima zan kadedeyar bazawa gogagiya mai idanu atsakarka, bazama yakawotaba zaman jiri taxoyi kamar yadda tasaba ga sauran gdn da tafito, da zaran tasamu abunda takeso zata cikawa rigarta iska, to dan haka ba kansa farauba balle takare kansa, yanzu shekaransu wajan biyu knn, amma babu alamar ciki, itadae inbanda cin kudi ba abunda tasa gaba domin Alh Hashim bakaramin sake mata bakin aljuhu yayiba domin shi mutumne da hanunsa asake yake, amma ganin Hajiya Fatima babu alamar ciki atareda ita nanfa yafara mitarsa yanda yasaba akan haihuwa, tana jinsa zai karaci surutun sa bazata tamka masaba, dan ita tasan zamanda take dan ita tariga da tasan bazata sake haihuwa ba, ma haifartama ba aiki takeba, ita atunanin ta arziki tazuci ba haihuwa ba, dan haka yafara sheda mata shi aure zai kara tunda ita bata haihuwa,

Tunda taga haka tasawa ranta ba wacce zatazo ta tayata cin dukiyar nan , matarsa tafarkoma bayanda ta iya tazu ta sametane, amma itama tasan yanda zatayi da ita , da kafar Alh Hashim akace yaje gdn matarsa Zainab bazai iyaba, kawarta takira ta sanar da ita abunda yake wakana, tace mata karta damu zatazo akwai inda zasuje inda bukatansu zata biya, tana zuwa ta dauketa ba inda ta zame da ita se wajan boka wanda itama Hajiya Fatima bokan ba wani bako bane agurinta,

"me kukeso amuku dan nasan abunda ke tafe daku kafin zuwanku naji bayanin komai kasheta kukeson ayi,?

"Aa boka kawai sunake su wulakanta ma ana banaso Alh Hashim yakara tuna yanda wata mata kowata ya aduniyar nan, nikawai nakeso yagani nazama abar tunawarsa, duk duniya yaji baya son wata mace inbaniba, kuma wannan zance na aure yafita abakinsa ya manta maganar,"

"Angama bukatarki tabiya, duk wasu kasuwanci dayake da wasu kadaruri duk zasu koma hanunki, seyanda kikayi dashi, mai kikace yayi darawar jiki zai mikishi, "

"godiya nake boka,"

" to ammafa kafin aiki yacika zaki kawo gurguwar sauro da jan taure,"

" kai boka ina zamu samu wayan nan kuma"

"Sai ku ka wo kudi boka dan kundalo zaisiyo se ayi aikin, "

kudi masu kauri Hajiya Fatima tabayar suka tafi,
Dan adam da saurin yadda tabbas abunda sukayi yayi tasiri dan tundaga wannan ranar Alh Hashim bai kara taka indasu Nisha sukeba, baya zuwa balle ya aiko muda wani abu, mami dadi kamar matsata mutuba, duk abunda ya mallaka aduniya seda tasa ya mallaka mata shi, rashin zuwan Alh Hashim tun baya damun Hajiya Zainab harya fara damunta, dan haka seta fara tura Nisha gdn mami tadubu matashi, amma kullum Nisha taje se ace mata baya nan, shirun yayi yawa dan haka tasa Nisha agaba har gdn mami amma abunda tacewa Nisha shita sake maimaitawa Hajiya Zainab, to wai ina yake zuwane ko lekomu bayayi umma ta tambaya, mami hararo Zainab tayi tana fadin

," to ni ina zan sani, ki nemeshi kitan bayeshi mana , koku tsaya kujira yadawo, " mami tafada tareda juyawa tayi daki tabarsu awajen suna tsaye, daga cikin dakin suka jiyu muryanta tana fadin,

" in kungaji da tsayuwar se ku seta hanya kuma karku sake kutafi kubarmin kofa ashigo amin barna," komawa gda sukayi kowa jiki babu dadi, tundaga wannan ranar umma ta kwanta ciyo da kuma tunanin mijinta, haka umma ke kwance yau da lapia gobe babu, duk wani kayan abincinsu seda ya kare, wani lokacin salma ke kawo musu abinci daga gdnsu, ga rashin lapia kullum gaba yake, ta dau tsawon lokaci tana ciyo Amma wannan karan ciyon baizuwa umma da wasaba balle susa ran samun sauki, Nisha ba yanda batayiba da umma batun zuwa asibiti tunda kullum ciyon gaba gaba yake har yaci karfinta amma inaa umma taki itade damuwarta tasa mijinta aidonta, dan haka kallum maganar umma Nisha ta nemu mata abba,

"yauma kamar kullum sassafe Nisha tayi gdn mami dan ganin abbanta, azatunta zata sameshi tunda yau tayi sammako, amma sam yauma batayi sa'a ba, dan kuwa bata sameshiba,

"to waini ina abba ke zuwane kullum baya nan Nisha ke tambayar mami, cikida fusata mami tace,

" to ko zaki matse baki nane inyaso sena fada miki inda yake zuwa,"

" Allah yabaki hkr ummace ba lapia inaso nakaita asibiti, kuma ba komai ahanunmu yanxu, "

"to shine meye kina fadaminne koni zan bata lapia,? ko alhakin kaita asibiti awuyana yake,"

" Aa abba nake nema infada masa abunda yake faruwa, "

""to sekije kinemesa aduniya",

"zan zauna na jirasa komai dare zai dawo ae" Nisha tafada tareda neman guri daga gefe ta zuguna,

" mara kunyar yarinya seki zauna kijirashi ae iskane yake wahalarda mai kayan kara, "Nisha binta tayi da kallo yayinda mamin ke shiga daki tana mai bushewa da dariya , tana shiga dakin tazari phone dinta tanufi toilet can ciki tashiga tadanna layin kawarta takira, dagawa tayi tana fadin,

" yade Hajiya fty shekewa da dariya mami tayi tana fadin,

" gsky aikin boka na kyaufa",

"aidama nafada miki boka baya wasa, meyafaru najiki cikin farin cikine,"

" ke yanzu Nisha tazu tana neman mahaifinta wai ummanta ba lapia," cikin shekewa da dariyan mugunta tace

"yanxu haka tana cikin tsakanin rayuwa da mutuwa ," dariya kawar ta fashe dashi tana fadin,

"haka akeso ae suta mutuwa suna bamu waje, to yanzu ba tsayawa zakiyiba, buriki bai gama cigaba, kinsanfa Alh Hashim ya mallaka miki gdnsu dasuke zaune, dan haka kiyi gaggawan karban gdnki, kafin su saida kayan ciki suyi kudin magani",

"kumafa hakane kawata kin kawo shawara mami tafada tana jimami, shiyasa nakeyinki bakya wasa,"

" ato tsaya kallon ruwa kwado yamiki kafa, to yanzu ina Nishan take, "cikin yamutsa fiska mami tace,

" gatacan wai tana jiran abbanta yadawo,"

" aiko bazata ganshiba kibarta kawai inta gaji zata tafi dan kanta, dan bazata taba hada ido dashi ba, har abada, kuma kema karki sake da haka kinsan abunda boka yafada," cikin jan numfashi mami tace

"hakanefa ai bazan taba barin hakan tafaruba, to yanzu kibari inta tafi kibi bayanta kiyi hayan kartan maza kuje dasu ku kwashe kayansu tas ku cillasu titi, susan inda dare yamusu, "

"kai haka za aiyi kawata nagode sosae," da haka sukayi sallama farin ciki fal Hajiya fty,

**Nisha
tun safe haryanzu yamma lis amma sam babu alamar zaidawo, ga tunanin umma wani hali take ciki, gawani hadari da ya lullube garin har ansuma yayyafi, dan haka ta tashi tafita, daga window mami tabi bayan Nisha da kallo tana dariya, mtswww yan wahala zaku gaji kubari, to atakaice dai wannan ciyo da yamatsan tawa umma da rashin ganin mijinta shiya kaita ga kwanciya asibiti har Allah yakarbi rayuwarta, wannan kenan

Cigaban labarin, seda tayi kukan ya isheta sannan ta mike ta wanko fiskarta, fitowa parlourn tayi itama nanma ba kowa parlourn kallon parlourn take gwanin shaawa, jin motsi cikin parlourn yasa tajuya inda taji motsin, wata matace dagani tadan manyanta tafito daga kitchen hanunta dauke da filet din abinci tana jeresu a dining table ganin Nisha yasa matan tasaki murmushi tareda karisowa inda Nisha ke tsaye, tana fadin," yade yata akwai abunda kikesone,? cikin tsoro Nisha tace," am ., banga kowa a parlourn bane, ko su fadeela kike nema,? cikin hanzari Nisha tace,"eh , suna part din Hajiya muje innuna miki inda suke, har bangaran Hajiyar ta rakata tabude mata kofar sannan tajuya, shiga Nisha tayi hade da sallama, fadeela ne ta taso tana fadin," lah mundauka bacci zakiyi da kikayi wankan shiyasa muka fito muka baki guri kihuta, cikin wani irin murmushi nisha tace," nakwanta baccinne baizoba, murmushi Hajiya tayi tana adin," matsunan kizauna kusa dani yaranne se ahankali suntafi sunbarki kikade

murmushi nisha tayi tareda da matsawa inda Hajiya tamata nuni, hira suka cigaba da yayi suna janta da tadi amma sam bata wani sake sosae ba, hjy duk tana kula da yanayinta ba karamin tausayin yarinyar takeba, yarinyar irin wannan da rashin uwa bawani makusanci kusa da ita, itadae Nisha gaba daya hankalinta ya tattara ga aheel dake kwance yana bacci, kyakykyawa kamar bababsa haka kawai takejin yaron cikin ranta, kiran sallan magarib ne ya dakatar dasu daga firan dasuke, duk suka mike toilet din hajja mama kowannesu ya nufa yayi alwala, itama tashi tayi tanufi toilet din tayi alwalan koda tafito bataga su fareedan ba, da alamu sun nufi part dinsu sallah, .

hajja mama ce daga gefe kan sallaya tana gabatar da sallah hakan yabawa Nisha daman matsawa inda taga an ajiye mata lufaya da sallaya, gefe da hajja mama nisha ta shimfida sallayan tashiga gabatar da nata sallan, bayan kammalawar hajja mama tashiga lazimi tana jan jarbi, yayinda idonta kekan Nisha dake gabatar da sallah cikeda nitsuwa murmushi Hajiya tayi yayinda tamai hankalinta ga abunda takeyi, bayan idarwa nisha tajima tanayiwa umma addu'a da ftn alkhari da samun rahama ga ubangijinta, tareda mahaifin nata dan shima ako ina yake yana bukatar addu'an ta gareshi, tana kammalawa tamike tareda ninke sallayan , mike hajja mma tayi daga zaman da take tana fadin,

" bari naje na dubo baba Barka ko ta kammala dinner dan yuwa nakeji sosae gyada mata kai kawai Nisha tayi hakan yabawa hajja mma Daman ficewa, aheel dake kwance saman capet anmasa matashi da pillow Nisha takurawa ido tana kallonsa, sam bata gajiya da kallonsa, yaro so beautiful wani dan larabawa, gsky family din Allah yabasu kyau masha Allah, murza idonshi yashigayi alamar farkawa daga bisani yabude idon gaba 2 , ya saukeshi akan Nisha da ta kura masa ido kamar zata hadiyeshi, kallon rashin sani yafara mata, cikin wara ido da tsoro yake fadin,'

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login