Showing 18001 words to 21000 words out of 61982 words

Chapter 7 - IG AJEEMAL book1 Hausa Novel

03 Sep 2025

1543

tajita switch off takira yakai sau uku but abu daya ake mai maita mata, ritsa ido tayi cikin zuciyarta tana fadin,

" please kamal ka gafarceni kai ba irin mutumin da za ayi saurin mancewa dashi bane kayi hakuri da wauta irintawa, hawaye tashigayi shar shar gashi bata san yaushe zata sake sashi a ido ba, dama yata fada mata shi bai cika zama kasanar ba, because shi foodbollas ne, gsky baki kyauta wa kankiba, hakade tacigaba da tunane har bacci barawo yasaceta, su ammi sunyi hira sosae, daddy kam tuni yayi gaba yaje yayi kwanciyar shi dan bazai iya dugun hiraba, sukuwa sundau time suna hiran daga bisani wajan karfe 10 itama taimusu seda safe tabi bayan mijinta, suma kuma taimusu umarni dasuje sukwanta, dan haka suka nufi bedroom dinsu, shiguwan sune yatada nisha daga baccinda take, dasuri Nisha tamike tana kallon aheel da yafarka shima yana dan wul wul ga ido, katashine Nisha tafadi, gyada mata kai yayi yana fadin,


" kikaini gun pahpahna, please kikaishi wajan babanshi Nisha tafa tana kallon fadeela, what tab kikaishi de kokuma kisashi ahanya ko kibarshi anan papanshi zaizo ya daukeshi tafada tareda neman guri takwanta, mai yasa baza kikaishiba to Nisha tafada tana bin fadeela da kallo , bama zuwa part dinsa abunda tace kawai taja blanket yarufu, reeda kam tuni tayi kwanciyar ta, tanajin maganar dasuke amma bata kulaba tayi mukus kamar mai bacci, sake baki Nisha tayi tana kallon fadeela, wani irin magana ne wannan mutum da dan uwansa but ace baya zuwa inda yake Nisha tahau maganar zuci, muryan aheel taji yana fadin,


" akaishi papanshi yana shirin kuka, ahankali ta zamu daga bed din tareda jan hanunsa suka fito, har part dinsu ta rakashi ta tura masa kofar tana fadin,"to kashiga seda safe tafada tareda juyawa, gd yayi shiru, se hasken wuta gaba daya Nisha atsorace take, kamar ace mata shiiii tagudu, jiyuwar da zatayi taji aheel nafadin," Aunty tsoro nakeji dakin da duhu bazan iya shigaba, cikin hanzari tamatso tana fadin," duhu kuma, tabbas dakin da duhu da alamar ankashe light din parlourn, gashi bantahu da phone balle na haska maka, ko mukoma can mukwana da safe sena dawo dakai tafada cikin lallashisa, kuka yafara kokarin mata yana fadin," shigurin papansa zeje, jan hanunsa tayi suka kutsa cikin parlourn, cikin sanda, bata san inda makun nan sukeba balle takuna,

jin muryan aheel dake kwadawa papansa kira ciki muryan kuka, bcuz matso rajin duhune bawaso duhu kwata kwata, sede wajan bacci nanma dan yanajiki papansa, AJEEMAL na kwance saman bed yarufu duk da ba bacci yakeba, jin sautin muryan aheel yasashi mikewa tareda lalubar wayansa, sakko wa yayi daga bed jikinsa dagashi se best da dan gajeren wando fari mai laushi, kunna light phone din wayarsa yanufo parlour, yana isa parlourn direct yanufi kuna wutar, nan da nan haske mai kyau da inganci yabai yana, yayinda idon Nisha dana aheel suka sauka kasansa, idon Nisha ne suka fito waje ganin yanayida AJEEMAL yafito, duk ilahirin jikinta yadau bari, amma ta gagara dauke ido akansa, tana karewa kyakykyawan surorinsa kallo, aheel ne yaje da gudu yafada jikinsa, jin aheel yazame hand dinsa daga nata yasa tayi saurin watsawa dagu tabar dakin cikin yanayi natsoro da kidima, daga aheel har babansa binta sukayi da kallo, shi kansa AJEEMAL yaji kunyar ganinsa datayi ahaka but baiyi tsammanin ganinsu a wannan time dinba, muryan aheel yaji yana fadin,


" papa I'm feeling hungry, okay zauna anan kajira AJEEMAL yafada tareda tufan kitchen yadauko cup tareda hada masa tea tareda sandwich and fried chicken a plate yamika masa, nanko aheel yakarba yasuma ci yana shan tea din, seda ya kammala AJEEMAL ya dauki plate da cup din ya daura table daga bisani ya daukesa suka nufi dakinsu, ba ajimaba bacci ya daukesu dagashi har dan nasan, itama Nisha tana isa bedroom dinsu tasamu kowa yayi bacci hakan yasa itama ta kwanta kirjinta se wani bugu yake, da zaran tarufe ido AJEEMAL take tunawa cikin yanayinda taganshi, ahaka tadinga juyi har bacci ya dauke ta, washe gari, washe gari da asuba ammi da kanta tazo ta tashesu dukda bawani sabon abu bane kafin tafiyarsu ita take zuwa ta tashesu, idan itama ta makara Daddy ke tashinta, nan suka tashi sukayi alwala sukayi sallah, suka koma suka kwanta, tun tashin ammi daga tayi sallah bata komaba tashiga kitchen ta kamawa Barka wasu aikin sukayi tare ,

kasan cewan Daddy nada fita office nanda nan suka kammala komai, a takaice de seda ammi ta sallami Daddy itama tayi nata breakfast din takoma takwanta dan tahuta gajiya sosae, 10am, sannan suka nisha suka tashi sukayi wanka tareda wanke bakinsu daga bisani sukashirya suka fito, a dining suka tarar da nasu breakfast din, fareeda ta kwalawa baba Barka Kira, nan da nan ta isu tana tambayar ba asin kiran, ammi bata fito break bane, sunyi nakaiwa Hajiya nata, ammi kuma tare sukayi da mai gdn har tashiga bacci, okay ya kamal reeda tasake tmby, shima nakai masa har yafita gun aiki, alright you can go, fareeda tafada tareda zama bisa kujeran, suma suka zauna suka shiga yin break, seda suka kammala suka tashi gani cewa ammi na bacci yasa suka nufi inda sukafi kauri majalisarsu ban garan Hajiya,,,

Dawowan su ammi yakarawa gdn armashi sosai dan ba karamin sakewa nisha tayiba, ganin yanda ammi takara janta ajiki, duk wani tunanin ko rashin sakewa ya kaurawa Nisha, tasake da gdn sosae hakan ba karamin dadi yayiwa su ammiba, dan haka suka zage dantse wajan kulawa da ita yanda yakamata, duk wani abunda suka san zai kawar mata da damuwa ko tunani shisukeyi, ba abunda Nisha zata nema agdn tarasa, damuwarta daya shine yanda gidan keda tsauri wajan fita, ba ma'abota son fita bane, koda yaushe zaman gd se mkrnt, atuna ninta taya zatasan halinda mahifinta yakeciki, bugu da kari idonta naso tayi tuzali dana kamal, shiyasa take allah allah time din zana jam yayi itama tayi kamar yanda ammi ta sheda mata tasamu allah yabata sa'a taci tafara zuwa makaranta nan kota samu wata dama, ,yau weekend kowa na gd,

tunda sukayi break suka dawo parlour suka yada zango, hira suka shigayi suna kyakyatawa, cikin raha da kwanciyar hankali, suna tsaka da hiran AJEEMAL yashigo bakinsa dauke da sallama, hanusa dauke da na aheel, bayansu kuwa rahilace ketafe cikin isa ita kadanta se yamutsa fiska take, AJEEMAL samun guri yayi kusa da Hajj mama kasan carpet yazauna tareda daura aheel acinyarsa, ita kuwa rahilace waje tasamu daga nesa tazauna tana karewa yan parlourn kallo, AJEEMAL ne yafar isar da gaisuwanshi gasu ammi suka amsa cikin fara'a, su fareeda ma suka gaishe da yayan nasu, batareda sun kalli inda Aunty heelan tasu takeba, bacce ko sun gaisheta tama ba lalle ta amsasuba, murya can kasa ya amsa gaisuwan kannen nasa tareda maida kallonsa ga heela tareda sakar mata wani harara, tsuke baki tayi tareda dan zamewa tana gaishesu, fiska ba yabo ba fallasa suka amsa mata gaisuwar, ammi ne takalli AJEEMAL MUDIBBO kaikam kayi wuyar gani daga kai har matar taka, allah yagani ammice ke kiransa da wannan sunan amma bayaso bade yanda ya iyane itadinma tana kirane dan tsokana dan tasan baya son sunan, Daddy ne yakarbi maganar dacewa,

" banda abunki kinsa hukuma se ahankali basuga ta zamaba, to itama matar tasa jami' ar lapiya ce, bata dawani time yau night gobe morning, se ana musu uzuri, gsky kam se ahankali Hajj mama tafa tana kallon Daddy, itadae ammi batace komaiba, tasan wannan ba hujja bace yade fadane kawai, nan taja bakinta tayi shiru, shima AJEEMAL kansa sunkuye yana wasa da yan yatsun aheel, itama heela hankali ta nakan wayarta, dakinne yadau shiru nawani lokaci, fareeda da fadeela se hararo Auntyn nasu suke, wacce batama san sunayiba, gaba daya tagama fita musu arai, basuki yayansu yasaketaba ko yakaru aure dan kwata kwata batada hali mai kyau, ga isa da gadara shi kuma batada kunya kokadan✍️

Ina Auntyna take bangantana,? Aheel yafada tareda zamewa daga cinyar papansa yanufi su fadeela yana tambayar su,

daga AJEEMAL har rahila su ammi bin aheel sukayi da kallo

Daddyne yakamo hanunsa yana fadin,"bagasu nan kana kallonsuba yafa yana murmushi yana nuna masa su farida , cin hanzari reeda tace,"

Daddy bafa mu yake nufiba, mutumiyar sa, nisha yake tambaya, Daddy ai inkaga aheel yashigo parlourn nan bai tambayi Nisha ba to ae ba lapia,

Gskykam Nisha mutumiyar sace, inbai gantaba ba zaman lapia kaje dazunan tashiga daki , sedefa kar ka dameta da surutu dayawa inkashiga kajiko, Hajj mama tafada tana dariya.

gaba daya dariyan sukayi banda rahila data sake baki tana bin aheel da kallo,"

yau kajimin shermen banza wai Aunty, yanada wani Auntyne bayan wayanda yagani zaune agabansa yana kallonsu,

azahiri kuwa wani guntun tsaki taja wanda yafito fili wanda yasa yan parlourn suka karkatu hankalisu gareta, ganin yanda suka tsura mata ido suna kallonta yasa tamike tana yamutsa fiska tafita,

AJEEMAL naganin fitan ta yatashi shima yabita, ikon Allah ammi tafada tareda bin dan nata da kallo, murmushi Daddy kawai yayi tareda tashi yamu sallama ya haura sama abunsa,

Mtsw dama na fada miki ammi rahila bata da kunya da kike ganinta, fareeda tafada tana tabe baki, sekuma tasake cewa kinma san meyafaru bayan tafiyar ki,..,fuf taji ammi ta buge mata baki,

banason maganar banza da kananun magana, dib reeda tarufe bakinta tana kallon ammin nasu, tana kokarin sake cewa wani abu, ganin ammi ta tashi tahaura sama tabi bayan daddy yasa tayin shiru, zuciyar ta namata wani irin suya,

Kema da kinyi shiru yanzu gashi kinja ta buge miki baki fadeela tafada tana kallon reeda,

To shiru yana da amfanine ae seta dauka ko tsoronta akeji reeda tafada tana tura baki, bawani tsoro inkikaga haka mutum yana abu ana masa shiru to akwai darajan da yakeci ne bawai tsoro ba, Hajj mama tafadi yayinda idonta ke kan reeda da fadeela,

To ae naga daga zuwanta tanaso tashiga tsakanin mu da yayanmu kuma mu bashiga harkanta mukeyiba ita kuma tanaso tashiga namu, reeda tafadi,

to seku kauda kai kuyi kamar baku san tanayiba, kuma ina baku shawara kudinga kauda ido akan duk wani abunda kuka gani kudena yawan magana akwai shine mafi alkhari,

Bakowa yakeso adinga kawo masa kana nun magan ganuba, kekam kinga zahiri ae Hajj mama tafada tana kallo reeda da ta tura baki kamar zai taba bango,

gimtse fiska fareeda tayi tana kallon kakar tasu , jin dariya kasa kasa yasa taimada kallonta ga fadeela dake dariya kasa kasa cikin hanzari reeda takalli Hajj mama tana fadin,"

wlh Hajiya kiyiwa fadeela magana dariya fa takemin, ato gulmarki taja miki Hajiya tafadi,

nan fadeela tasake bushewa da dariya , pillow reeda ta dauka tabugawa fadeela, itama fadeela tadauka tajefa mata, Hajiya kam kallon su take tana dariya,

Aban garan Nisha kuwa tunda tayi breakfast bata zauna adakinba takoma tayi kwanciyar ta
Daga daki takejin hayaniyarsu amma takasa fitowa, saboda kanta dake dan sara mata,

Shigowar aheel ne yasata dole ta tashi tazauna ta saurari shirmensu da yasaba, Aunty gobe Monday zan koma school zakirakani koh Muje kiga school dinmu, school dinmu yanada kyau sosai, Ai nataba baki labarin koh ,

Eh kataba bani lbr yana da kyau nisha tafadi, yau zamuje tare koh , eh tace masa dan yau kwata kwata batajin yanayin surutu,

muryan aheel taji yana sake fadin," yau mummyna tana gd bata fitaba, baki taba ganin mummyna ba koh, nataba mana , cikin zaro ido yana fadin," a ina to, ? murmushi tasakar masa tace," lokacin da kake kwance asibiti,

lah ashe kintaba ganinta yafada yana washe baki, murmushi tamasa batareda tace komaiba, su fareeda dane suka shigo yayinda suka gama hiransu kowa yakama nashi guri, yauwa aku sarkin surutu yana nan yana miki surutun nasa da yasaba koh, fadeela tafa yayinda suke karisuwa ,

kallonsu nisha tayi tana fadin,"har kungama firan , eh mungama anyi bake, cikin sauke numfashi Nisha tace,"to yazanyi naso fitowa ayi hiran dani amma ciyo kan nan ya matsamin , oh sorry kinsha magani kuwa, fareeda ta tambaya," aa base nashaba nasuma jin sauki, aheel ne yazame daga bed din yana fadin," Aunty zanje gurin papana zan dawo anjima , to kawai tace tareda bin bayansa da kallo har yafita,

Wani dugun numfashi tasauke tareda maida kallonta gasu fadeela da suka kwanta suna danna phones dinsu, ahankali tazame daga gadon tanufi hanyar fita, domin kuwa ta gaji da kwanciyar, parlour tanufa tanemi kujera daga gefe ta zauna tvn parlourn akunne yake dan haka tashiga kurawa tv ido,amma hakalin ta kwata kwata baya wajan , da alamar ta lula wani dunyar tunani,

Kamal ne yashigo parlourn hand dinsa daukeda hairbrush yana taje kansa, idonsa ne yasauka kan Nisha dake zaune takurawa tv ido, da alama batama sanda shigowar sa ba,

ahankali yamatsa tsakiyar parlourn yana karewa Nisha kallo da mamaki, kallonta kawai yake bakinsa tagagara furta komai,

ita kuwa jin kamar ana tsaye kanta yasa ta daga idonta kadan, dantaga waye, daram gabanta yafadi kamal tagani tsaye kanta yana kallonta,

azabure tamike tayi baya tana kallon shi cikin zare ido, shima haryanzu kallonta yake," NEESHA kece,?:kml yafadi yana sake dubanta da kyau, ita kuwa baki se bari yake takasa cewa komai, hakan yasa tajuya tareda watsawa da gudu tayi daki,

shikuwa baki bude yake binta da kallo harta shige dakin, abun yayi matukar bashi mamaki meye Nisha taxoyi gdnsu, to kodae gizo tamasa,

kaiwan nan ba gizo bane tabbas nisha ce yabawa kansa amsa, yana cikin wannan tunanin ya tsinkayi muryan ammi dacewa,"

kai kumafa seyanzu, hanzarce ya kalli ammin tasu cikin sosa kai yana fadin," eh wlh , wani irin bacci kake haka, kayi break kuwa ammi ta tambaya, eh nayi Barka takaimin seda nayi ma nakoma baccin, okay to ae shikenan ammi tafada tareda take kokarin juyawa tayi kitchen, cikin hanzari kml yace,"

am bakowa mukayine, cikin tsareshi da ido tace," bakowa kuma aina ammi ta tambaya, eh yanzu naga tashiga bedroom dinsu fadeela, murmushi ammi tayi tana fadin," kodae Nisha kagani,?


Eh to ina ganin ita dince kamal yabata amsa,
baku taba haduba se yau kenan, eh kawai kml yace yayinda yake kallonta yanaso karin bayani, okay yanzu ina dan saurine in nasamu time zan maka explain daga baya kajiko, okay yace batareda yasake cewa komaiba, nan ammi tajuya tashiga kitchen abunta, ganin haka shima yajuya yafita daga parlourn,

Nisha kuwa tunda tashiga daki tanemigu ta kwanta, lokacin ta tarar su reeda duk sunyi bacci, nan ta nitsa kanta cikin pillow tana jin zuciyar ta yanda yake mata dukan uku uku, yanzu ta tabbatar da zarginta dama shine ya kml dinda su fadeela suke fadi, atunanin ta wani kamal dine da ban ashe kamal din da tasanine,

tundaga wannan lokaci Nisha tasumu sara daga sungama breakfast sun koma parlour Hira zata zame tayi daki tayi zamanta because kunyar hada ido da kamal takeji,

dukansu sun lura da hakan atunaninsu rashin sabu dasune wanda kuwa ba haka bane,

haduwa da kamal ne bata sonyi, wani lokaci ahar tunani take akan wace irin kaddarace ta kawota gdnsu kml

inama bata biyusu Hajiya ba tayi wani wajan daban, duniya da fadi ae bazata rasa wajan fakewa ba,

aban garan kml kuwa tunda idanunsa sukayi tuzali dana Nisha yakeson sake ganinta but hakan yakasa samuwa because duk wani hanyar dazaisa su hadu Nisha ta tusheshi ko haraba gdn ta daina fita, balle yazuba ido wajan shiga da fitar ta,

Abunda yasani shine zasu hadu komai daran dadewa tunda gd daya suke dole wani dalili zai hadasu,


yau hutun so fareeda na makaranta yakare komai ya dawo mata sabo kewa yasake dawo mata, domin kuwa su reeda sun koma makaranta,
dama hutu suke yanzu kuma hutu yakare,

shima kuma aheel mutumin ta yakuma school kuma wuni yake acan, gaba kidaya abokan surutun nata basa nan gd yakoma shiru, hatta itama ammin tana zuwa office, dan haka intaji kewan yamata yawa, seta tattara takoma sashin Hajiya tazauna suita hiransu, har yamma kafin su fadeela sudawo,

bikin kml da nabeela se karatuwa yake yau bai wace saura month ba, gd se shirye shiryen biki ake kaikace next week ne bikin, su fadeela har ankai dinki na event din bikin, duk da kamal yasheda musu shiba wani bidi'a zaiyi a bikinba,

atunanin shi wannan bawani bikin da za'ayi wani shagali bane because bikin bawani shiga heat dinsa yayi harcan ba,

nishane kwance bisa gado yayinda idonta ke kallon sama kamar mai nazarin wani abu, phone dinta ne yashiga ringing akwai kamar jira take akirata dama, salmace kan laye, hanunta har bari yake wajan dagawa,

Karawa tayi akunne ta tareda yin sallma, salma bata amsa sallamar taba tashiga watso mata tambaya, " wai nikam qlu kike kuwa, salma tafadi,cikin hanzari Nisha tace," mekika gani meyafaru,? tafada yayinda take kokarin gyara zama, ✍️

Bansan meyake damunkiba, tunda nabar gdnku baki sake daukar waya ki kiraniba, kuma kince zakizo gd shima kuma kin gagara, shine nace bari nakira naji har rayuwa tai miki dadinda zaki manta dani koh,

jikin Nisha ne yayi sanyi dan tasan bata kyauta ba , gaba daya tarasa meke damunta, cikin sanyin murya nisha tace,"

Nama rasa bakin magana amma kiyi hakuri nasan ban keutaba, ke kwata ce kuma aminiyata aduniyar nan banida kawar datakaiki, hasalima in inada wata damuwa nakanzo nasanar dake ko ummata wani damuta bata sani kamar da ke kika sani , salma yanxu haka ina cikin damuwa amma maganar bazaiyiyu awayaba, gashi gdn nan ba afita daga gd se mkrnt, kwata kwata ba afita salma,

naji ba afita amma yanzu dole kisamu hanyar fita domin kuwa ankawo kayan lefena, salma tafada tana tura baki duk da Nisha ba ganinta takeba,

cikin farin ciki nisha ta wantsalo daga gadon tahau rawar murna kaikace ita aka kawo kayan, daga bisani tadan dakata da rawan tana fadin," amma kuma shine baki sanar daniba kafin akawo kayan,

dama nazuba miki idone inga ko zaki kirani, amma baki kiraba kirkinki yayi kadan, gashi nina damu dake nakiraki, kuma na sanar dake, yanxu de sena jiki kuma ina zuba ido, to

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login