Showing 9001 words to 12000 words out of 61982 words

Chapter 4 - IG AJEEMAL book1 Hausa Novel

03 Sep 2025

1544

who.., who are you yafada cikin muryan bacci, Nisha kasa mayarmasa da amsa tayi dan ita kanta ba san mezata ce masa ba, maryan shi tasakeji yana fadin

"Zansha ruwa "

zamuwa tayi daga kujeran da take tasa hanu ta dauki ruwan dake gefensa tareda cup din tashiga tsiyaya masa ruwan ta mika masa , ganin ya miko mata hanun hagu because dayan hanunsa da matsala hakan yasa ta tallafo shi tashiga bashi da hanunta , karba yayi yasuma sha seda ta tabbatar ya koshi ta zame cup din daga bakinsa tareda sakar masa marshi, shima washe mata baki yayi yana fadin,

" thanks you" baki Nisha tabude da nufin magana jin shigowar fadeela ya tahadiye talk dinta, ganin su zaune saman capet sunyi zuru suna kallota hakan yabata daman karisuwa inda suke, murmushi tasakar musu tareda mayar da kallonta,

" my little baby katashine " gyada mata kai yayi yana fadin',

" aunty I'm feeling hungry ,

"okay don't worry zan turo baba Barka tazo tayi feeding dinka kajiko to kawai yace nan tamaida kallonta ga Nisha tareda jan hanunta tana fadin,

" muje muci abinci dama ke nazo kira , sunkuyar dakai nisha tayi tareda cewa,

" bana jin yunwa, cikin hanzari fadeela tace,

" Allah baki isaba taya zakice bakya jin yunwa, dagaske kwata kwata babu yunwa atare dani, kodae bakyason cin abincin damune, mudakefa munriga munzama daya fadeela tafada tareda jan hanun Nisha harsun kai kofa Nisha taja ta tsaya takalli dayayi abun tausayi yana binsu da kallo sekuma takalli fadeela tace,

" please to kikawomin nan semu zauna tareda shi kar abarshi shikadai,

" nafahimci kifi bukatan Zama nan , alright bari na turo muku Barka, " tafada tareda juyawa tafita, murmushi tabi bayan fadeela dashi, gefe kuma tamaida kallonta ga aheel, kumawa tayi tamatsa kusa dashi tazauna, tana maibinsa da murmushi jin yaron take sosae ajikinta, sekace wanda suka fito ciki daya, Nisha uwar yaya tana mutukar son yara dan koda suke gd faruk kanin salma tare suke wuni tana manne dashi darene kawai ke maidashi gdnsu, ita kade Allah yabawa mahaifanta batada yaya ko kani, shiyasa Allah yadaura mata jaraban son yaya, shima aheel din murmushi yaketa zuba mata kamar gonar auduga, yaron akwai fara' a sosae shiyasa yakeda shiga rai,

ba adadeba Barka tashigo hanunta dauke da tiredin abinci zubawa Nisha tayi afilet tamika mata, tuwone miyan egusi yaji kifi da nama kaca kaca , aheel kuwa irish da akwai aka suya mishi nan baba Barka tazana tana kokarin feeding din shi, lah da kimbarshi zan tayaki bashi kije ki huta kema, nisha tafada yayinda take kokarin dakatarda ita, aa yata karki damu bawani hutawan da zanyi aheel mutuminane gwara na sallameshi, daker Nisha ta lallabeta ta tashi tafita, filet din abincinta ta ture gefe ta kamo na aheel tasuma bashi, seda ta tabbatar da yaci sosae ya koshi sannan ta kyaleshi ta tsaya tana kallonshi ko abinci takasa ci, kwata kwata abinci baya ranta, muryan aheel taji yana fadin,

" aunty ke bakici abincin nakiba, am. banajin yunwane, to aunty kici kokadan because baba Barka ta iya abinci kema nasan zai miki Dadi, gyada masa kai tayi yayinda taja filet din abinci gabanta, nan tafara tsikaran abinci tanaci ba dan tana jin dadinsaba, sam bata ma gane dadinsaba, nan tunanin umma yafado mata nanfa hawaye yashiga wanke mata fiska jitake kamar ta fashe da ihu, sunnar da kanta tayi kasa dan kar aheel yagane halinda take ciki, guge hawayen tareda sake kasa da kanta tana cigaba da tsikaran abincin,

," aunty meye sunanki , da guwa tayi tana kallon aheel dayayi mata tambayar, murmushi yasakar masa tana fadin

" NEESHA Aunty nisha? yafada yana kallonta gyada masa kai , ina Zaki zauna damu anan koh kuma baza kitafiba tunda mummy na bata sun zama dani kezaki dinga feeling dina kimin wanka kishiryani cikin uniform natafi school? yafada yana washe baki, yaron akwai surutu balaifi kallonsa take yaro irin wannan da bai wuce 7 year's ba amma se surutai wani radio, a ido inka ganshi bazakace yana da surutu hakaba, koda yake Aunty's din nasama ba bayaba wajan magana, karka damu muna tare duk abunda kakeso zan maka kajiko tafada tareda da ture filet din abincin gefe, tareda yiwa aheel matashi da cinyarta, aheel hira tacigaba da yimata kamar dama can yasanta, kodama can aheel na saurin sabo da mutane, labarin papansa yashiga yimata, irin sonsa da yakeyi da kayan wasan da yake siyo masa , da wajan wasa da yake kaishi,

itadae Nisha kallon yaron take yayinda yaketa zuba makar fanfon da ya lalace, hira yake sekaceba majin yaciba, sam bakinsa bai mutuba, jin motsin shigowarsu hajja mma ne yasa Nisha daguwa suna binsu da kallo yayinda suke karisuwa , fareeda ne takariso wajansu tana fadin,

" yauwa yanata zuba sutun nasa daya saba ko wani labarin yake baki naketa jiyo sautin muryan sa daga waje ,

"lallai baki yabude sauki yasamu, washewa sukayi da dariya dukansu nanfa hira ya farke aka cigaba da tadi, tadi suke sosae wanda sundau tsawon lokaci suna yinsa , yanzu kam Nisha ta dan sake sosae anyi firan da ita, hajja mma data fahimci hakan ba karamin dadi tajiba, Hajiya bata wani dadi sosae ba wajan hiran ta mike taimusu seda safe domin kuwa bakaramin gajiya tayiba zaman asibiti ga ba bacci mai Dadi, gakuma dawainiyar aheel, sallama sukayi ta tafi tayi kwanciyarta, ba adadeba fareeda ma tamike saka makon wayanta dake ringing itama seda safe taimusu ta tafi, sunyi tadi sosai da fadeela sewajan karfe 10:30 lokacin bacci yafara cinye idon fadeela itama mikewa tayi tana fadin,

" Nisha kitashi muje mukwanta wlh bacci nakeji sosae, aheel baiyi bacci ba karmutafi mubarshi shikadai, rabu dashi papanshi zezo ya daukeshi ae ,

" aa kije kawai zan biyoki dan nima banajin baccin yanzu zamu danyi hira kadan, murmushi fadeela tayi tana fadin,

"naga kamar zama da aheel yana miki Dadi koh,

"hmm zaki gajima inde yaron nane surutain sama kadae ya isheki,

"aa nikam bawani isata dazaiyi, alright se kinshigo to, tafada tareda juyawa tafita, maida kallonta ga aheel tayi da ya tsura mata ido dan bayason ta tafi tabarshi,

"Aunty zanyi fitsari kikaini toilet , taimaka mishi tayi takaishi yayi fitsarin, ta dawo dashi tagyara masa kwanciyar tamasa matashi da cinyarta, suka cigaba da hirarsu wajen karfe 11: lokacin sunyi laushi daga shi har Nishan, domin kuwa bacci yafara cinye idon su, tuni aheel yasuma baccinsa nanfa itama tafara gyan gyadawa,

Motarsace ta kunno kai gdn , jin hon yasa mai gadi yaye geat din gdn, nan ya tako motar ya kariso haraban gdn yayinda yayi parking, mitowa yayi yayi da mai gadi yakarisu da hanzari yana mai kwasan gaisuwa, amsawa yayi tareda tafiya yakarisa ga part dinsa , nan yatura kofar yashiga back din hanusa yacillar kan kujeran, direct bedroom dinshi yanufa kokarin cire kayan jikinsa yasuma yi seda yacire yarege daga shi se dan short dress daga bisani ya dauke lallausan towel dinsa yanufi toilet, wanka yashiga yi sosae dan yau ba karamin gajiya yayiba , fitowa yayi jikinsa daure da towel iya gwiwa, kallon inda mai yake bai kalleba because wani kasala yakeji gakuma gajiya gaba daya yagama yin laushi, jallabiyarsa yazura tareda fitowa yanufi kitchen tareda hadu coffee yasamu gu daga dining yasamu waje yazauna yana sha, seda ya kammala yamike ya koma bedroom domin kwanciya ya hutawa ransa, kashe wutan dakin yayi tareda kwanciya saman bed din hade da janyo blanket yarufu, wayarsace tayi kara hakan yabashi daman lalubu phone din dan yaga waye meshirin shiga hakinsa acikin night haka, dago phone din yayi yana kallon screen din wayan , matarsace raheela ke tafaman kiransa komai zatace masa oho, wani tsaki yaja da kamar bai daukaba sekuma ya daga batareda yace komai ba,

" hey my baby yau nayi dare sosae gashi but ina ta missing dinka gakuma wani accident din da aka kawo yanzu, so bazan samu dawowa ba se zuwa tommorow, baijira takarisa maganar ba yakatse wayar tareda cillata gefe namaijan tsaki,

" stupid dama yau kika saba kwana hospital koba wani issue zakice akwai meye problem dina da hakan yafada tareda sake lullube jikinsa hade da rufe ido yana maida numfashi slowly, firgit yatashi yazauna se yanzu ya tunada aheel, gaba daya gajiya tasa ya mata dashi, da sauri yatashi yanufi hanyar waje, bangaran Hajiya yanufa tareda murda handle din kofar yajita abude take yakutsa kai, dauke da sallama, turus yayi yayinda yakarisa shigowa ciki, binsu yayi da kallo duk sunyi bacci Nisha ma baccin barawo yasaceta, kan aheel na cinyar ta , itakuwa ta jingina bayanta da jikin kujera, tanata sheka bacci, haunsu cikin najuna, Nisha tareke hanunshi gam, wani abu yaji yatukare masa makoshi , gaba daya haushin yarinyar yagama kamashi , datasan haushita dayakeji bata fara gigin kusantu dansaba, matsawa yayi ahankali yafara kokarin jan hanun aheel tareda cire hanunsa acikin na Nisha,

cikin bacci Nisha taji aheel na kokarin zare hanunsa hakan yasa takara rike hanun gam , kamar wani zai kwaceshi, gaba daya jiyayi ransa yafara bacci gani irin rikon da tayiwa dansa, hunsa yasa akan na Nisha yana yamutsa fiska, daya hanun kuma ana aheel yana kokarin raba han nayensu, jin tarike gam yasa afusace yafincike da karfi wanda yasa aheel mutsawa yana fadin,

" ah. Aunty hanuna yafada cikin nan nauyan bacci, yacigaba da bacci yana surutai, itakuwa jin aheel ya janya hanunsa yasa tasake jayo hanunsa ta rungume akirji, waro ido yayi yana bin hanusa da takamu takai kirji tanamai cigaba da baccinta, nanfa yafara kokarin jaye hanunsa jin haka yasa Nisha kokarin bude ido dayan hanunta tasa tana murza idonta, karfa idonta ya sauka akansa dake kokarin kwace hanusa daga nata kyansa ta zubawa ido wanda ta gagara dauke idon akansa, lumshe ido tayi tabude still tana rike da hand dinsa taki sakewa, ,

" hey madam samu dama kisakarmin hand na dauki dana yafada tareda hade gira, cikin hanzari takalli hand dinshi da tarike Gam sakuma tasake dasauri tana fadin,

" I'm sorry ta fad'i tareda mikewa tsaye , kauda kai yayi tareda daukan aheel yadaurashi saman shoulder dinsa suka nufi part dinsu, bayansa tabi da kallo jikinta se mazari yake sekace wanda taga wani dodo, cikin hantsari tabi bayanshi ta nufi bangaran su itama, tana shiga ta samu su fareeda duk sunyi nisa da bacci itama samun waje tayi takwanta dan idonta tuni yamata nauyi,**********

washe gari da asuba suka tashi sukayi sallah su farida suka koma bacci abunsu, qur'an Nisha ta dauka tasuma karatu kasa kasa take gudun karta shiga hakkinsu suna bacci ta dade tana karatu daga bisani ta dakata, addu'a tashigayi wa mahaifanta ita kanta sannan tashafa takoma tayi kwanciyar ta,

,sewajan karfe9:40 Nisha tafarka ganin babu kowa ita kade aka bari tanata sharar baccinta hakan yasa ta sakko daga bed din ahankali takarisa sakkowa, itama waje tanufa a parlour ta iskesu suna zaune, ahankali takarisa inda hajja mma take hadeda gaisheta amsawa tayi cike da fara'a tana fadin ,

"anishatu harkin koshi da baccinne tafada tareda kokarin dagata daga durkusawan datayi , cikin tsukuna fareeda tace,

" oh mubaza akulamuba hajja mma kawai aka sani, bude baki tayi daniyar magana nanfa hajja mma tace da ala kyalesu zumuje muci abinci ke muke jira daman tafada tareda jan hanun Nisha suka nufi dining table, time din baba Barka takammala komai ta ajiye inda yadace, fareeda ne ta bude abincin tashiga zubamusu, seda ta zubawa ko sannan ta koma tazauna domin fara ci, kuwa yashiga cin nasa banda Nisha datasa plate agaba tana juya spoon, tanason sake sa aheel aidonta, hajja mma duk tana duk tana kallon abunda take, yade nisha tunanin mekike,? cikin hanzari Nisha tadagu tana fadin,

" bakomai tana fadan haka tashiga tsikaran abincin tana ci, wayan fareeda ne yayi kara ta dauka cikin hanzari ganin mekiran , karawa tayi akunne tareda fadin,

" hello ammi ina kwana, daga daya ban garan ammi ta amsa da lapia, ya gd yasu Hajiya, qlu suke sede gd ba dadi muna miss dinki gsky fareeda tafada cike da shagwaba, fisge wayar fadeela tayi takara akunne tana fadin,


" ammi yaushe zaku dawo , ina daddy ,? kibashi wayan , daddyn ku baya kusa don't worry nanda 2 days zamu dawo, ammi tafa cikin sigan lallashi, yau to kuyi suri kidawo kiga new baby girl da muka miki fareeda ne ta kwace wayar dacewa,


" kuma ammi so beautiful inkika ganta zakiyi happy, ammi batayi mamakin maganar suba domin ta dade da jin labarin gurin Hajiya daga ita har Daddy sunsan zancen, to shikenan se mundawo din, daga Nisha har hajja mma kallonsu suke suna murmushi, sunyi fira sosai da amminsu daga bisani sukayi sallama yakatse wayar farin ciki fal zuciyoyinsu, suna kammala cin abincin suka koma cikin parlourn suka cigaba da firansu, sundau time suna hirarn daga bisani hajja mma takatse kiran dacewa,

" kun fasa fita shopping dine ko se rana tayi? cikin hanzari fadeela tace,"lah mun mance fira tayi dadi, lallai kam hira tayi dadi kutashi muje mushirya mutafi cewar fareeda duk suka mike, ganin ba alamar mikewar nisha yasa reeda taja hanunta tana fadin,


" dake zamu ae tashi mutafi tafada tareda jan hanunta izuwa ciki, hajja mma kam kallo kawai tabi bayansu dashi tareda mikewa tanufi bangaran ta , ba adadeba suka fito cikin shirinsu mekyau but koda suka fito basu tararda hajja mma a parlourn ba, hakan yasa suka bi bayanta domin yimata sallama, Nisha kam bata samu daman bin bayansuba daga waje tatsaya tana bin part din dataga AJEEMAL ya nufa da aheel tana karewa benen kallo , juyawa tayi danufin shiga part din Hajiya jin muryan aheel yasata dakatawa, da sauri ta daga kai takalli inda take jiyo muryan aheel, daga saman benan yake kwala mata Kira, Aunty see me yafada yayinda yake dago mata hanu yana dariya, washe masa baki tashigayi yayinda take daga masa nata hand din, daga sama take jiyoshi yana fadin,

" Aunty ina zakije,? kizu muyi tadi irin najiya yafada yana washe baki kamar gunar auduga, bata kaiga bashi amsaba su fareeda suka fito bada wani bata lokaciba fadeela taja hanun Nisha tana kokarin kutsata mota ganin haka yasa Nisha tayi hanzarin dagawa aheel hand batareda kowa ya luraba, shima hanun ya dagamata har suka bar harabar gdn aheel yna yiwa motar bye bye har seda mai gadi ya maida geat yarufe sannan ya tsagai ta, tafiya suke suna dan hiransu har suka su deden wani big plaza, shiga sukayi suka suma siyayyansu, nan sukashiga zagayawa domin zaban abunda yamusu tareda fadawa Nisha itama tashiga ta duba abunda yamata, amma sam itakam duk inda sukayi nan takeyi, ganin haka yasa suka shiga dauka mata duk wani abunda yadace na bukata, kama daga kayan sawa manya da kana , mayuka turare masu kamshi hada da kayan kwalliya shoes da sauransu, suyi shopping abubuwa da yawa reeda tabiya kudin suka tafi, kan hanyarsu na kumawa gd, Nisha ta sanar dasu akwai wasu kayanta datake da mukatan daukosu agdn da tabari, dake reedace driving dinsu tana tajiya kana motar Nisha tafada musu anguwar tareda bayani inda zatayi hanya yabulle dasu, ba dau time ba hanya takawosu anguwar,


nan sukayi parking daga gefe tareda fituwa daga motar suka nufi cikin gdn, azaune suka samu matar kusa da kofar dakinta tana tsintar shinkafa, dukawa sukayi tareda gaisheta cike da ladabi, amsawa tayi tana binsu da kallo dan ba wanda tasani acikinsu, se Nisha kadae, kallonsu tashiga yi daya bayan daya sannan ta sauke kanta akan Nisha tana fadin,


" Nisha kece, murmushi nisha tayi tana fadin," maman husna, ayya yakike ya karin hakuri kuma narashinda mukayi tunda samau labarin gurin ummyn salma ba karamin alhini muka shigaba, allahde yajikan Hajiya Zainab, ameen Nisha tafada tana maijin wani irin azuciyarta, nan Nisha tashiga zaiyanu mata dalilin zuwansu, bada wani bata lokaciba maman husna tamike suka nufi dakin da aka kallace kayan, nisha tashiga duba abuwanda yakeda bukata dakuma na ummanta wayanada zatana gani tana tunawa da ita, sanan Nisha ta fadawa maman husna data dauki sauran kayan intanada bukata tabar mata because batada ra' ayin, ba karamin murna tayi ba sbd taji dadi sosae, tashiga zubawa Nisha godiya hade da rakasu bakin kofa tajiyo,


nan sukuma suka shiga mota suka dauki hanyar gd, suna isowa mai gadi yaye geat din gdn suka shigo da motar sukayi parking, suka fito tareda kokarin shaga parlourn, tunda ga door din parlourn suka fahimci, sunyi bako, suna shiga ciki wa Nisha zata gani, Salam ce zaune bisa kujera tana sakar mata murmushi gefe kuwa hajja mama ce zaune tana kallon shigowar su, ledar hanunta tasake cikin murna tayi kana salma dagu tafada cikinta, nanda nan tafashe da kuka, cikin hanzari salma ta dagata nata fadin,

"uhm za afara sanar koh ? Wlh yanzu zakisa natashi natafi inda nafito dan ni banzu dan naji kukankiba, ciki hanzari Nisha tadago takallita hadeda bugeta kadan tana fadin,

" sorry bansan sanda kukan yazu bane tafada tana kokarin goge hawayenta tana tura baki kamar wata baby, dariya salma tayi tareda maida kallonta gasu fadeela da suke ta washe mata baki,

" ina kukaje haka naketa jiranku? Reeda tace wani dan shopping mukaje, to allah yasa anhadu da nawa shopping salma tafada tana dariya,

" tashi muje kigani, nan suka tashi suka bedroom dukansu sukabar hajja mma tana ta binsu da kallo gwanin shaawa, suna shiga dakin saman bed suka shigayi dad daya da kayan dasuka siyo suna nunawa salma,

" masha Allah kaya sunyi kyau sosai ga tsada, hakalin salma ba karamin kwantawa yayiba ganin Nisha tashiga hanun mutane kirki masu son mutane ba kyama balle girman kai, nan tashiga karewa dakin kallo gsky Nisha ba karamin sa' a tayiba ba karamin taya Nisha Happ tayiba ko bakomai damuwarta na rashin umma zai dan ragu,

salma kiga wata riga da aunty fareeda tazabamin, salma bin rigar tayi da kallo duguwar riga ce ash colour da rintsin baki baki, rigan ba karamin haduwa tayiba dagani zatayi tsada, gsky tayi kyau sosai fadan salma, reeda ne tayi yaddariya tace,

" ae dama ni na iya zaban abun mai kyau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login