Showing 18001 words to 21000 words out of 86876 words
Sauban Yana kan gadon asibity inda tashiga d'aki tarufe dinga rawa da murna tana Addu'ar Allah yasa daga can sai kabari,
A lokacin Da Abdullah ya dawo gida domin bincike sai ta marairaice ta zama kalar tausayi kamar zatayi kuka tashiga tambayarsa Yaya jikin d'anta Sauban?"
Kwantar Mata da hankali yashigayi ganin tana Shirin zubar da hawaye domin ya fahimci yanzun Jamila tana matuk'ar son Sauban,
Yashiga fad'in "kiyi hakuri insha Allah Sauban bazai mutuba zai Sami lafiya da Yardar Allah domin a halin yanzun anyi nasarar ceto numfashinsa ya dawo,
Wanda likitoci sunyi iya bincinsu sungano wani abi yaci a cikin abinci Wanda ansara gane ko meye."
A zubure tace numfashinsa ya dawo kana nufin kace mun Yana motsi kenan?"
Murmushi Abdullah yasaki yace yafara motsi, yanzun binciken da mukeyi waye ya bashi abincin?"
Ta Ina aka zuba Masa abincin?"
Snn menene aka bashi yaci."
Sarki yayi Alk'awarin muddun aka samo Wanda yayi wnn aikin zai fuskanci hukunci Mai tsanani
Hakan Nima ko waye idan asirin sa ya tonu sai yasha mamaki na,
Snn ki kula da SADEEQ da Sageer domin Suma komai zai iya faruwa dasu tinda akayiwa d'an uwansu hakan."
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍
🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴
Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)
*DIDECTED TO Fateemah M Uthman*
*Page 11*
Shuru tayi domin kwatakwata Bataso aka zo Mata da labarin cewar Sauban ya farkaba,
Ta d'auka ganin Abdullah da tayi a dai dai wannan lokacin mutuwar Sauban ce yazo ya fad'a Mata, Amma sai taji sab'anin hakan."
Bata ankaraba tana cikin tinani ta Kuma jin muryar Abdullah Yana fad'in "ki daina tinani insha Allah Sauban zai tashi zai rayu zai Sami lafiya da Yardar Allah,
Ya mik'e tsaye tare da sanya talkaminsa yace "Ni natafi zamuje muci gaba da bincike Allah ya tona marar gaskiya"
Girgiza kai kawai tayi da kyar ta bud'e Baki tace "Allah ya bashi lafiya."
"Ameen yace "yayi ficewarsa."
Tana ganin fitarsa ta mik'e tsaye tashiga safa da Marwan tana tinanin idan bincike yayi bincike asirinta ya tonu, wani irin hali zata shiga idan asirinta ya tuno aka gano cewar itace tabashi magani yaci domin ya mutu,
Wanda itama kanta batasan ko wanne irin magani bane, ita dai , a wurin bokanya jakadiya ta karb'o Mata shi."
Shin wanne irin hukunci ne sarki ya tanadarwa Wanda ya aikatawa jikansa hakan."
Zufa tashiga wanke Mata fuska,
Tana cikin wnn Halin kuyangarta ta shigo ta zube a gabanta tana fad'in "ranki ya dad'e sarkin gida Yana son magana dake."
Gabanta ya yanke ya fad'i ta kalli kuyangar tace "meyafaru me Yake so yacemun?"
"Ranki ya dad'e Nima bansaniba Amma yace "afad'a maki magana zakuyi Mai mahimmamci ."
"Kije kiyi Masa iso ki ajiyeshi a falon saukar Baki kifad'a Masa Ina zuwa."
"To ranki ya dad'e Allah ya k'ara maki lafiya, kuyangar ta mik'e tafita domin ai watar da umurnin uwar d'akin nata."
Sai da aka d'auki kusan minti 15
Bata fitoba sai da ta dai dai ta natsuwarta akan rud'anin da tashiga sannan tafito cikin k'asaita da nuna Isa tanufi inda sarkin gida Yake a zaune a d'akin Baki."
Tana zuwa cikin Isa da nuna mulki ta nemi kujera ta zauna,
Wanda dama sarkin gida Yana zaune a kan cafet,
Sai da ta zauna ta d'auki k'afa d'aya ta d'ora akan d'aya snn ta juyo ta kalli sarkin gida dake durk'ushe a gabanta Yana fad'in "barka da fitowa gimbiya barka da fitowa sarauniyar gobe Kuma fulanin sarki in Allah ya yarda, Allah ya k'ara maki lafiya,
Tsawa ta daka Masa domin tin farko sarkin gida baya cikin tsarinta asalima haushi yake Bata saboda suffar munafukai garesa, don Yana tsananin shiri da Hajjah sannan ta lura Yana matuk'ar son Sauban da kulawa dashi akan yaranta dako kallon banza basu ishesaba."
"Me Yake tafe dakai ta fad'a a tsawace."
Murmushi yasaki domin yasan Bata son ganinsa, yace "ranki ya dad'e zuwa nayi domin na jinjina maki akan namijin k'ok'arin da kikayi hak'ik'a kinyi matuk'ar k'ok'ari wurin samun nasarar Sauban yaci abincin dakika dafa a jiya, saboda Sauban yarone Mai tsananin wayau Kuma bayacin abincin kowa sai na Hajjah."
Zaro Ido tayi cike da firgici,
Ko me tatina a Nan take ta Kuma saita kanta tare da daka Masa tsawa "rufemun Baki mekakeso kace ne?"
Kana nufin nice nazubawa Sauban wani abin a cikin abinci domin yaci ya mutu?"
Ko kana nufin nice nayi yunkurin kashesa?" Lallai kanaso kayi Wasa da rayuwarka,
Binciken da aka turoka kayi mun kenan?"
to bara kaji kada ka manta Kai sarkin gida ne, Ni Kuma gimbiya ce ko yanzun idan naso zan iya cireka daga matsayin da kake nabawa wani snn daga k'arshe idan naso zanyi sanadin barinka gidan gaba d'aya, Dan hakan. Ka tsaya iya matsayinka kada kayi yunkurin shiga hurumin da banaka ba."
Sarkin gida yace "hakan ne gimbiya matar yarima, gskya kina namijin k'ok'ari a cikin gidan Nan."
to Amma Ni abinda bansaniba shine komeye ribarki ta son kikashe Sauban?"
Kina tinanin idan binciken da sarki yakeyi idan ya gano kece sila komeye makomarki?"
Waifa Ina ganin Dubara ta b'ace maki idon ki a rufe Yake shiyasa Kika aikata abinda Kika aikatawa Sauban,
diba kigani."
Ya Ciro wayarsa a Aljihunsa ya kunna video tin lokacin da Sauban yashiga b'angarenta har zuwa lokacin da yafito har fad'uwar da yayi da lokacin da ya fad'i ta lek'a ta gansa yashe a k'asa tasaki dariya ta koma ta rufe k'ofarta."
Murmushin mugunta sarkin gida yasaki yace "mezakice Dan ganne da wnn video snn bashi kad'ai bane na ajiye wani a wuri Mai mahimmaci,
Ya mik'e tsaye yace idan kinshirya magana Dani Zaki iya nemana tin kafin lokaci ya k'ure maki."
Jikin Jamila duk yayi sanyi hankalinta ya tashi zufa sai tsiyaya take Mata a jiki kamar wacce tafito daga wanka takasa bud'e Baki tayi magana
Har sarkin gida ya Kai bak'in k'ofar fita, sannan tamik'e tsaye tace "dakata sarkin gida."
Cak ya tsaya batare da yajuyo ya kalletaba,
Tafiya ta farayi sai da tazo daf dashi ta tsaya tace " nawa kake buk'ata domin ka rufe wnn maganar?"
zan baka duk abinda kake so in har zaka rufe wnn maganar a cikin gidan Nan."
Murmushi sarkin gida yasaki domin anzo wujen dama abinda Yake buk'ata yaji daga bakinta kenan saboda yasan watan arzikinsa ya kama."
Juyowa yayi ya kalleta yasaki murmushi yace "miliyan biyu kawai nakeso daga gareki ba yawa."
"Bani account no naka tace a tak'aice,
Cikin sauri yashiga karanto mata,
Yana Nan a tsaye cikin minti talatin yaji alert din miliyan uku."
Ta dubeshi tace harda k'ari naiyimaka domin bana buk'atar naji makamanciyar wannan maganar
Kafi kowa sani komai zan iya aikatawa Wanda ya zalinceni,
Kasani muddun maganar Nan tafita bayan nabaka kud'ina kasani da Kai da zuri'arka Kuna cikin tsaka Mai wuya mutuwa ko rayuwa."
"Bakida matsala indai wnn ne ai tinda kin biya shikenan,
Ya Kuma zuwa gabanta ya durk'usa yace "kina burgeni ranki ya dad'e kud'i ba matsalarki bane shin me zai Hana kisaki kud'i domin a aika da Sauban lahira."
Murmushi tasaki ta taka zuwa kan kujerarta ta zauna,
shima sarkin gida ya dawo ya zauna a gabanta domin yaga maganarsa tasamu karb'uwa a wurinta."
"Mekake gani za'ayi domin biyan buk'ata ta na ganin sauban ya bar duniya?"
"Ranki ya dad'e ai wnn aikin Mai sauk'i ne abinda za'ayi shine, kisaye likitan dake kula dashi a asibity da kud'i, ya masa allurar guba a Nan take zai mutu wnn shine mafita."
Dariya Jamila tasaki Mai sauti tace "Ashe dama kana da wnn tinanin da hikima tin tini ka gujeni ka nuna k'iyayyata a fili?"
Kiyi hakuri ranki ya dad'e kece tin farko Kika nuna tsana ga gareni, wnn dalilin yasa bana wata alak'a dake sai dasu Hajjah wad'anda babu abinda suka tsinanamun tin iya zamana dasu sai dai nayita masu bauta Ashe ke Alheri ce."
"Ya Isa tace."
"Ta Yaya zanga likitan domin muyi maganar?"
Ranki ya dad'e indai Zaki saki kud'i ganin likita baya da wani wahala Ni da kaina zan d'auko maki shi na kawo makishi har cikin falonki.
Sabida kinsan Hajjah da sarki sun yarda Dani d'ari bisa d'ari."
Murmushin farin ciki Jamila tasaki tace "ka burgeni ban tab'ajin farin ciki irin na yau ba,
Kaje ka d'auko mun likita ko nawane zan bashi in har burina zai cika ganin Sauban ya daina motsi a doron k'asa,
kaima zakayi murmushi domin idan burina ya cika za kayi mamakin abinda zanyi maka."
"Godiya nake ranki ya dad'e bara natafi kada a ga mundade a wuri d'aya a zargi wani abin, ki Sanya idon ganinmu xuwa anjima tare da likitan."
**************
Bincike akeyi sosai a cikin gidan sarautar domin ganin an kamo masu hannu a cikin wad'anda sukayi yunkurin kashe Sauban,
Ba wani abu da aka gano ko wata alama,
Wanda har da Jamila ake binciken wnn yasa ta b'atarwa mutane da hankali akan ayi bincike a kanta."
Saboda tana matuk'ar nuna bakin cikinta Akan abinda ya faru,
Inda Abdullah yake Mata kallon tafi kowa shiga cikin damuwa na faruwan lamarin wani lokacin har lallashinta yakeyi."
***************
Sarkin gida sai zirga zirga yakeyi tsakanin gida da asibity domin Hajjah tayi matuk'ar yarda dashi duk abinda za'a sawo Dan gane da magani ko wani abun to shi ake Bawa kud'i Ya sawo,
Wnn dalilin yasa yasamu damar keb'ewa wuri d'aya dashi da likita ya fad'a Masa cewar gimbiya tana buk'atar ganinsa yau da misalin k'arfe 8 na dare."
Likita bai kawo komai a ransa ba,
domin yaga yanda sarkin gida yake zirga zirga a asibityn sannan ya lura da yanda aka yarda dashi
Ganin anyarda dashi d'ari bisa d'ari yasa baiyi tinanin komaiba ya amsa Masa da to idan yatashi daga asibity idan zai koma gida Yana Nan tafe,
Yashiga tinanin wata k'ila akan maganar ciwon Sauban ne take nemansa."
Misalin k'arfe 8 sarkin gida ya tsaya a can bayan asibity inda ba Wanda zai iya ganinsa yakira likita a waya, cikin minti 5 likita yafito daga asibity dama lokacin tashinsa yayi, ya tarar da sarkin gida ya d'aukeshi a mota ya nufi wurin gimbiya Jamila dashi."
Hak'ik'a Jamila tayi farin cikin ganin likita a gabanta zaune sai murmushi take saki a fuskarta,
Ta kalli likita da kyau tace "barka da zuwa doctor."
"Yawwa hajiya barka da gida Yaya iyali?" inji likita."
Bata amsa Masa ba tace "Yaya jikin Sauban d'in ?"
ta kuma jeho Masa wata tambyar."
"Alhamdulillah sauki yanata shigosa sai dai har yanzun lakkan jikinsa Bata Fara aiki ba domin. Abinda akayi amfani dashi, Yana da k'arfi sosai domin yafi guba masifa a jikin d'an adam Wanda har yanzun mun rasa Gane ko meye."
Murmushi ta saki ta girgiza Kai, tace "likita katab'a rik'a miliyan 20 a matsayin naka na kanka?"
Wata irin zabura tare da Zaro ido sarkin gida yayi Jin Ankira miliyan 20 to Ashe shi da yace abashi miliyan 2 kad'an ya d'iba kenan tab da yasani da yace sai anbashi miliyan goma."
Girgiza Kai likita yayi yace "ranki ya dad'e a Ina zanga miliyan 20 bare har na rik'eta, kinsan aikin namu a k'ark'ashin wani mukeci, sai dai idan wata ya k'are muke k'arb'ar Albashi Wanda bazai wuce dubu 80 ba dashi muke rufawa iyalinmu asiri tare da 'yan uwanmu."
Wani shu'umin murmushi Jamila tasaki tace "kana son ka mallaki miliyan 20 naka nakanka?"
"Kwarai Kuwa likita yace tare da Kuma gyara Zama."
Jamila tace "so nakeyi a matsayinka na likita Wanda kasan sirrin jikin d'an Adam so nake kasan yanda zakayi cikin hikima da dabara irin taku ta likitoci ka kawar mun da Sauban yaron gidan Nan Wanda kake kula dashi, ya bar duniya."
Idan ka kawar dashi to kasani zaka mallaki miliyan 20 Kai har da ma k'ari domin zan K'ara yi maka wata kyautar ta ban mamaki."
Zaro Ido likita yayi gumi ya shiga wanke Masa jiki, ga k'oshi ga kwanan yunwa,
Yana son kud'i sosai Yana son ya mallaki miliyan 20 din Nan, to Amma idan asirinsa ya tonu Yaya zaiyi da sarki maimartaba Yaya zaiyi da aikinsa Wanda ya dad'e Yana nema da kyar yasameshi."
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍
🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴
Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)
*Page 12*
Taimakon Gaggawa aka shiga Bawa Sauban inda aka sakashi a cikin wata na'ura domin ceto rayuwarsa."
tayi yunkurin shiga inda yake likitoci suka dakatar da ita tare da Bata hakuri da lallashin akan bazata Sami ganinsa ba,
Sai Nan da wata d'aya domin Yana cikin wani yanayi Wanda Addu'arsu kawai ake buk'ata"
Shuru Hajjah tayi taja da baya, hankalinta a tashe Dan ganin takeyi Sauban bazai tashiba mutuwa kawai zaiyi, dibo da yanda taga wani irin kunfa Yana zuba a bakinsa,
Wuri ta nema ta zauna fadawa suka zagayeta babu abinda takeyi sai Addu'ar Allah yabawa Sauban lafiya tare da rayuwa Mai d'orewa."
Gimbiya bilkisu ta matso kusa da Hajjah tace "umma kiyi hakuri da izinin Allah Sauban zai tashi, zai Sami lafiya, har Abada makiya baxasu tab'a samun galaba akansa ba,
Kizo mutafi masaukina ki ki huta har zuwa gobe idan Abdullah yaxo sai a San mafita."
Hakan Hajjah ta amince tabi Gimbiya bilkisu tare da fadawan,
Ko can d'in hakan bilkisu da Anna sukayi ta kwantarwa Hajjah da hankali snn ta Fara sakin jikinta a gidan, sai dai duk wani motsi nata da t Sauban a bakinta tana jera Masa Addu'o,e."
************
Duk iya bincike anyi ba wata alama da tanuni akwai sa hannun wani daga cikin gidan sarautar wurin yunkurin kisan Sauban, domin duk abinda za'ayi Jamila tana tare da Abdullah ana binciken da ita ba abinda takeyi sai aikin kuka a cewarta tana tsananin tausayin Sauban Halin da makiya suka sakashi me ya tare masu a duniya."
Ba abinda Abdullah yakeyi sai Bata hakuri,
hakan yasa ba Wanda yataba kawo bincike a kanta
, hakan shima sarkin gida, Wanda duk abinda za'ayi a gidan shine a gaba Yana bada tashi gudun mawar, sabida Yar jajen sarki ne da Anna sunyi imani bazai tab'a cutar dasu ba, Dan hakan Koda Wasa ba'a tab'a kawo komai a kansuba."
Hakan aka kammala bincike ba wani haske da aka samu, hankalin kowa ya koma England wurin Sauban washe gari Abdullah ya shiga jirgi ya sauka k'asar England domin dibo jikin sauban."
BaYan tafiyarsa da sati biyu komai yayita faruwa daga ciki har da samun nasarar samun lafiyar sauban, domin numfashinsa ya dawo har ya Fara motsi, anyi nasarar gubar Bata iyar da gauraye jikinsaba batayi tasiri a jikinsaba "
Satin Abdullah biyu a can ya dawo gida Nigeria tare da sauran bayi hud'u aka barwa Hajjah d'aya da kuyanga d'aya tare da Anna, domin ganin lafiya ta fara samuwa ga sauban duk da dai har yanzun ba Bari akeyi ana ganinsaba Yana cikin na'ura."
Gimbiya bilkisu itake hidima dasu Hajjah wacce ba yanda Abdullah baiyiba Akan zai kamawa su Hajjah wurin zama Amma saita nuna b'acin ranta, tana fad'in wato zai nuna cewa Hajjah shi kad'ai ta haifa, Banda su kenan,
Har sarki Abdulrahaman ta bugawa waya ta fad'a Masa Wanda shima yanuna b'acin ransa sosai dajin abinda Abdullah yace, hakan dai Abdullah ya basu hakuri yabar Hajjah a Nan snn yadawo gida Nigeria a cewarsa idan Sauban ya cika wata daya kamar yanda likitoci sukace zai Kuma dawowa tare da maimartaba domin su dubashi."
A d'an Zaman da Hajjah tayi tare da gimbiya bilkisu ta Gane bilkisu macce ce Mai tsananin nuna mulki da Isa tare da izzah, sannan tana tsananin nuna soyayyarta ga tilon 'yarta wato Saudat,
Tana son Saudat sosai Wanda sabida son da take Mata Bata bawa kowa rainonta kamar yanda aka San matar sarki Bata rainon d'a da kanta, tsakanin ta da yaro sai dai idan ankawo shi yasha nono, Amma bnda gimbiya bilkisu wacce
a kullum tana tare da 'yarta hakan shima sarki Abdulrahaman da zarar ya bugo waya baya da wata magana sai ta Saudat,
Hajjah ta jinjinawa wnn soyayya da sukayiwa Yar su kwaya d'aya tilo"
BaYan wata d'aya Alhamdulillah jikin Sauban yayi kyau yasamu lafiya Wanda har magana yakeyi Kuma Yana cin abinci sosai."
A ranar sarki da Abdullah tare da sarki Abdulrahaman sukazo k'asar, tabbas sunji Dadi sosai ganin Sauban yasami lafiya Wanda yake zaune Akan kujera ana fira dashi."
Anan sarki Abdulrahaman Ya kalli maimartaba tare da Abdullah da Hajjah ya Fara da cewa "ku ga farce ranka ya dad'e Ina neman wata Alfarma a wurinka Allah yasa zaka Amince da hakan, ranka ya dad'e Ina neman Alfarmar a bar Sauban k'asar Nan wurin gimbiya bilkisu domin taci gaba da kula dashi har lokacin da zai kuma samin lafiya,
Snn idan ya warke Ina neman Alfarma akan a barshi a hannunta yayi karatunsa anan har zuwa lokacin da ya mallaki hankalin kansa yasan abinda Yake Masa ciwo lokacin da zai fahimci makiyi da masoyi snn sai yakoma gida Nigeria,
diba da yanda ake farautar rayuwarsa makiyansa k'ok'ari sukeyi ta ko wacce hanya so sukeyi sai sunga bayansa."
Shuru kowa yayi yarasa amsar da zaibawa sarki Abdulrahaman domin shawarar da yanke tayiwa kowa dad'i a wurin sai murmushi ko wannesu yake saukewa."
Snn Sarkin yayi gyaran murya Fara magana kamar hakan "hak'ik'a Abdulrahaman kayi matuk'ar tunani tare da hangen nesa muna godiya da wnn karamci naka Allah yabar tare ya raya maka zuri'a."
Hakan Hajjah itama tayi Masa Addu'oe godiya tare da sanya Albarka,
Murmushin kawai Abdullah yakeyi cike da farin ciki domin yarasa abinda zaiwa Aminin nasa, iya k'auna sarkin Abdulrahaman ya nuna Masa ita da karamci, mik'ewa yayi tsaye fuskarsa tana saukar da murmushi yanufi inda Abdulrahaman yake zaune Abdullah ya rungume shi Yana Masa godiya, Yana fad'in " nagode Aminina yanda kayi mun Allah yabani abinda zanyi maka fiye da hakan hak'ik'a Kai abokine Kuma Aminine na kwarai."
Yinin ranar kowa cike yake da farin ciki,
Sai da sukayi sati d'aya a lokacin sauban ya Kuma Samun lafiya sosai har an sallamoshi daga asibity sundawo gida,
snn suka tattara kayansu har da hajjah suka dawo gida Nigeria