Showing 27001 words to 30000 words out of 86876 words
England bai Sanya sauban a idonsa ba, Wanda Sauban ya d'auki Alkawarin yabar gidansu Saudat kenan har Abada bazai Kuma Zama a cikinsaba,
Hotel ya kama sannu a hankali duk ya kwashe kayansa a gidan ya mayar hotel a kusa da d'akin safwan yaci gaba da karatunsa"
Da zarar daddy yakira wayarsa a kullum cemasa yakeyi Yana makaranta jarabawa sukeyi shiyasa har yanzun basu samu ganin junaba."
Hakan sarki Abdulrahaman da sarki Abdullah suka yanke ranar auren Sauban da Saudat wata shidda masu zuwa,
Murna da farin ciki kamar ya kashe Saudat inda bilkisu takejin wani bakin ciki a cikin ranta Akan auren."
Duk abin Nan da akeyi Sauban bai San abinda yake faruwa ba,
Hankalin sa a kwance, domin barin gidan yayi yafi samun Kwanciyar hankali Akan Yana cikinsa,
A d'akin Safwan Yake akwance safwan Yana shirya kayansa a kwati domin gobe zai koma gida Nigeria gaba Daya sakamakon ya kammala karatunsa,
Inda Sauban yake kwance rufe da Ido domin yasan sai yayi kewar abokin nasa,
Yana hakan wayarsa ta d'auki ringing dibawar da zaiyi yaga Abbansa NE."
Dagawa yayi cike da biyayya,.ya gaida Abba ya amsa Masa,
Anan yake bashi umurni akan ya had'o kayansa Yabiyo safwan yadawo gida tinda sun Sami hutu idan hutu ya K'are sai ya koma makaranta akwai maganar da yakeso yayi dashi wacce batayi a waya sai gashi gashi, snn ko banza k'asarsa Nigeria tana kewarsa tare da a halinsa."
Sosai sauban yaji dadin umurnin da Abba ya bashi Wanda dama irin wnn lokacin yake jira Wanda za'a bashi umurnin yadawo k'asarsa ta haihu."
Tare da Safwan suka shiga had'a kayansa, washe gari sukabi jirgin karfe goma suka nufi Nigeria."
Dan Zaman da daddy yayi na sati daya a England abinda bai tab'a yiba iyakacinsa yayi kwana Daya zuwa biyu ya kwana,
A Nan yaga yanda Saudat take gudanarwa da rayuwarta wurin yanayin shigarta da yanda gaba Daya rayuwarta ta turai ce take gudanar wa,
Anan take hankalinsa ya tashi yayi tir da irin wnn rayuwar,.
Kamarsa sarki, Mai mulkin kasar hausa k'asar Addinin musulci k'asar da musulmai sunfi kafirai yawa ace yarsa ta cikinsa wacce yafiso Akan komai take wnn shigar wacce da ita da tsirara batada wani maraba,
Wacce ya kamata a ce tana sanye da sitirarta da Alk'yabbarta ta lullub'e jikinta tana zuba mulki Amma ace itace take bayyanar da suffarta a gaban kafurai makiya ma'aiki ransa ya baci matuk'a,
Anan take yabada umurni su shirya gobe gobe zasu sabar k'asar Nan gaba dayansu Kuma su sani daga har Abada bazasu Kara zuwa turai su zauna ba sai dai su shigota su fita."
Murna Saudat tayita domin itama tana son taje NIGERIA Wanda Sarauniya Bilkisu ta k'ara cika tare da Jin haushi"
Washe gari suka had a kayansu gaba daya tare da fadawa sukabar k'asar zuwa Nigeria."
***************
Biki aka shirya na musamman Dan tarbar Sauban, Wanda ya shekararsa goma Sha biyar kenan rabonsa da k'asarsa,
Sosai Hajjah take murna da jin dadi, hakan fulani Jamila itama ba laifi tanuna farin cikinta tare da matan sarki."
Shigowar Sauban a cikin gidan komai dawo Masa sabo tin daga lokacin da yafito sashen Jamila a lokacin da tabashi abin Wanda sanadin cin abinci bai Kuma sanin inda kansa yakeba sai dai ya farka ya gansa a turai har zuwa gwagwarmayar rayuwar da yasha a cikin gidan, Yar kwallah ta ziraro Masa Ido yayi saurin Sanya hannu ya dauketa a lokaci da yayi Ido da Hajjah tana sakar Masa murmushi farin cikin ganinsa, da sauri yaje ya rungumeta Yana Mai cike da farin ciki hakan ya itama Anna tana farin cikin ganinsa."
Anan aka gabatar da komai,
Masu farin cikin nayi masu bakin ciki Suma sunayi na ganin ci gaban da Sauban ya samu ya girma huta ya zauna a jikinsa kamaninsa da mahaifinsa da mahaifiyarsa sun bayyana a tare dashi, Ina Sadeeq yakejin want sabon bakin cikinsa Sageer Kuma sai murna yakeyi da dawowar Dan uwansa,
Hakan hajaru da Bintu kannensa wad'anda bai tab'a ganiba sai a waya suma suna farin cikin ganinsa."
BaYan komai ya lafa, sarki yakirashi ya zaunar dashi Yafad'a Masa dalilin Kiran nasa da yayi So yakeyi yayi aure snn ya zab'ar Masa matar auren wacce yasan zai farin ciki da sanin ko wacece wato saudat."
Gaban Sauban ya fad'i cike da firgici ya kalli mahaifin nasa,
Amma Dan gudun kada ya fahimci wani abin yayi saurin dakewa tare da sunkuyar da Kai baiyi maganaba, domin baya fatan Allah ya kawo lokacin da zaiyi musu da mahaifin nasa."
Sosai ya amshi auren Saudat hannu biyu batare da yanuna alamar baya sontaba yasan hakan rayuwarsa zataci gaba da tafiya ba wani farin ciki a cikinta."
Anan take maganar auren Sauban ta karad'e gidan sarautar cewar yarima Sauban zaiyi aure zai auri Saudat Yar sarkin Bauchi Amini ga sarki Abdullah."
Ina wuta Jamila ta fad'a wato yarinya da ta kwallafawa Rai Akan Sadeeq ko Sageer dayansu ya aura sabida sarautar masarautarsu gata ita kad'aice a wurin mahaifinta shine aka Bawa Sauban ita,
Ta dafe Kai Wai meyasa duk abinda ta Sanya a gaba sai Sauban yayi Mata katanga dashi, wato ta kashe Bintu Ashe Bintu Bata mutuba kenan tabar baya da k'ura."
Gata Bata isa ta tunkari gimbiya bilkisu akan maganar afasa auren ba domin tsakaninsu Kar ta San Karne domin duk abinda take tak'ama dashi gimbiya bilkisu ta shafeta."
Hajjah tayi farin cikin wnn had'in auren domin tasan sarki Abdulrahaman Aminin Abdullah sannan Yana da karamci a idonta kodan taimakon da yayi masu a lokacin da lular ciwo tasame Sauban,
Zaman Saudat a cikin masarauta Tasha wahala sosai kafin tasaba da saka manyan Kaya tare da Alk'yabba, sai da tasaba snn aka shiga koya Mata yanda zata gudanar da mulkinta a matsayin da Gimbiya Yar sarki,
Anan take Saudat Taji girman Kai ya shigeta tare da jinin mulki dake yawo a jikinta, cikin wata biyu ta Fara taka duk Wanda takeso ta Kuma wulak'anta duk Wanda taga dama dama hakan sarautar masatautarsu take,
A b'angarenta har kujera gareta wacce take Zama ta sarauta wacce take zuba sarautarta Akai tare da mulkinta a yanda take so sai yanzun takejin kanta duk a can baya ba rayuwa takeyiba sai yanzun take rayuwa, b'angaren Mata Kuma ba Wai dainawa tayiba, sai ta kalli cikakkiyae kuyanga wacce taji komai da komai tasaka a gyara Mata su akai Mata d'akinta domin biyan buk'atarta."
Komawar safwan gida ya shima ya tarar da mahaifinsa yasaka Ranar Aurensa wata uku masu zuwa,
Inda ya had'ashi da Yar k'anwar mahaifin nasa Mai suna SAFINA, wacce dama itace zabin safwan,
Wato Sai anyi bikin safwan kenan snn ayi na Sauban."
Bayan bikin safwan inda an Sha shagalin biki na Dan gata komai anyi na k'awatar,
Tare da Sauban aka raki safwan gidan sa wurin Amaryarsa Wanda Sauban baiso zuwa sai da yaga b'acin ran safwan snn ya yarda akatafi kaishi dashi."
Washe gari tin da safe sauban yakira safwan a waya lokacin Yana tare da Amaryarsa rungume a jikinsa Yana shaye Mata Albarkatun kirjinta, Kiran Sauban ya shigo wayar sa da kyar ya Mika hannu ya d'auka, a kasalance yak'ara wayar a kunnensa."
Mere baki sauban yayi daji yanda safwan yake amsa Masa maganarsa,
Karon farko safwan yace "lafiya kuwa Sauban Kira hakan tin da safe ko kamanta ba'a England mukeba snn yanzun fa ni inada iyali ya Ina cikin wata duniya zaka dawo Dani cikin duniyarku fadamun me'akayi."
Dogon tsaki yaja Sauban baiyi maganaba illah ya kashe wayar gaba d'aya Yana tinanin dama akwai duniyar da mutum zai shiga BaYan wacce yake cikinta."
D'an iska kawai ai kasamu abinda kakeso saikafi Mai kura shafawa yacewa safwan sai kace Yana jikinsa😂
Safwan shine baizo wurin sauban ba sai misalin k'arfe hudu na yamma Wanda yasaba da zarar safiya ta waye suna tare bacci ne kawai yake rabasu Amma tinda jiya ya kwana da matarsa sai yanzun yasamu damar fitowa daga gida."
Kallonsa kawai Sauban yakeyi cike da mamankinsa yanda yakejin safwan Yana Masa iskanci Yana fad'in "Haba malam Ni wlh na matso wata uku Nan yazo a Kai maka matarka Saudat a gidanka kaji yanda naji a dare jiya na rantse maka da Allah saura kad'an na shed'e Akan dad'i, Wai kasan duniyar da nashiga kuwa?"
Hmmm Sauban yace yaci gaba da kallon safwan,
zakasha mamaki idan naci gaba da fad'a maka yanda Daren jiya ya kasance mun Ni kam daga yau nagane hanya."
Lumshe Ido Sauban yayi kamar Mai yin bacci Yana saurarensa,
Dariya safwan yasaki yace zaka daina wnn Jin Kan naka idan kashiga hannun macce dan lokacin da zaka durkusa a gabanta bazaka saniba."
Da sauri Sauban ya bud'e idonsa yana Masa kallon bakada hankali, cikin muryarsa tare da maganarsa D'aya Bayan D'aya yace "Ni zan durk'usa a gaban macce?"
Ya mere Baki yace Allah ya kyauta, har yanzun ba'a hallici wnn maccen da zan durk'usa a gabantaba,
har Abada bayan Hajjah babu wata macce a duniya wacce ta Isa na durk'usa a gabanta."
Safwan zaiyi magana Sauban yayi saurin daga Masa hannu yana fad'in "ya Isa safwan maganar ta Isa hakan, Kai da kaji kana iyawa kaje kayi duk abinda zakayi jarabbe kawai meye a jikin macce wacce har kake zaucewa hakan dare Daya duk ka susuci kafita a tunaninka, bazanyi mamakiba domin ka dad'e kana da buk'atar hakan Dole kafi Mai kura shafawa jarabbe kawai."
Dariya safwan yayi yace "naji Ni jarabben ne, amma kasani duk jarabata ban mayar da Shan lemun tsami da ruwan Lipton abincina ba asalima ban tab'a shansu ba." Kuma bana yin azumi a Kai akai kamar yanda kakeyi."
Kallonsa Sauban yayi ya hararesa wato dashi Yake kenan shida yake yawan shansu idan yaji mararsa ta Fara yimasa ciwo, mere Baki yayi yace "wnn Kuma ra'ayinane ba Dan wata manufa nakeyi ba d'an iska kawai."
Dariya safwan yasaki domin yau ya kular da Sauban har yakai dayin doguwar magana hakan."
*********************
Shiryen Shiryen bikin Sauban akeyi inda gaba Daya ko wanne gida suka shiga cikin hidimar biki,
Sarki yasaka aka ginawa Sauban gida Mai kyau da motsi a can bangare d'aya dake cikin gidan sarautar
Ginin gidan yayi kyau domin ankashe kudi wurin tsara gidan, musamman. B'agaren sauban fadin tsaruwarsa Bata lokacine."
Anzubawa Saudat Kaya nafitar hankali hakan duka b'angarenta anzagaye shi da kuyangi tare da bayi,
Ranar juma'a aka d'aura aurenta saudat da Sauban aka kawota masarautar Adamawa a matsayin Matar " *DAN SARKI SAUBAN*
Sosai safwan Yake tsokanar Sauban akan yau zai kashe Arna yau zai Zama mutum yau zai Manta kansa da komai nasa idan ya tsunduma a cikin wata duniyar."
Kyalesa kawai sauban yakeyi Dan shi kad'ai yakai ya Masa hakan ya kyalesa sab'anin sauran k'awayensa wad'anda ko fuska basa gani bare su tsokanesa."
Bayan kowa ya watse Sauban yashiga b'angaren da yanzun komai nasa yadawo wurin,
Babu abinda kakeji yanatashi sai kamshi turare Wanda dama yasan Saudat kwanace wurin zuba turare, mere Baki yayi yayi shigewarsa b'angarensa."
Saudat Kuma dama tace da zarar anga shigowarsa a fad'a Mata domin tasan bazai tab'a iskota a d'akinta ba, suna ganin shigarsa bayinta masu gadinta wad'anda aka zuba Mata suka nufi wurinta cike da girmamawa suka fad'a Mata cewar yarima yashigo."
Kuma Sanyawa tayi aka gyarata aka Kuma feshe Mata jiki da turare snn sukayi Mata rakiya zuwa b'angaren Sauban."
Sai da suka kaita bakin k'ofar d'akinsa tayi masu umurni da suyi tafiyar su snn ta burd'a k'ofar d'akin tashiga,
Kwance Yake Akan gadonsa Bayan yafito wanka Yana sanye da kayan bacci,
yanajin Shigowarta ta hanyar k'amshin turarenta wanda yadaki hancinsa,
Had'e fuska yayi tamkar bai San da akwai wata halitta a wurinba a rayuwarsa ya tsani saudat."
Kai tsaye wurinsa ta nufa saiti k'afarsa taje Wanda ya turo k'asa ta Kai gurfane tare da rok'o k'afar tasa ta fashe da kuka Mai cike da so da kaunarsa tana fad'in "Sadauki kayi hakuri da kaddarar aurena kasoni kamar yanda nake sonka zanyi maka biyya tamakar baiwarka kayi hakuri ka amshe Ni a matsayin Matar aurenka ,
ta Kuma rushewa da kuka."
Tausayinta yashigesa ya tuna da nasihar mahaifinsa a kan zamantakewar aure ya tuna da yanda Abba yayi Masa nasiha Kan ya kyautatawa rayuwar Saudat ko Dan darajar mahaifinta kada ya wulakantata, ya Kare Mata hakkinta snn ya sauke Mata duk wani nauyi dake saman kansa kada ya Bari tayi kuka Akan wani Abun da take buk'ata daga garesa,
Anan ya Sanya hannu biyu ya tallabota zuwa jikinsa yashiga share mata hawaye ba tare da ya Mata magana ba, sai da yaga tayi shuru tana murmushin farin ciki."
Snn ya saketa ya mik'e yashiga toilet ya d'auro Alwala yafito yayi Mata nuni da hannu Akan itama tashiga tayi,
Mik'ewa tayi tashi tanufi toilet domin ai watar da abinda yace Dan idan da sabo tasaba da halin sa na Rashin yin magana sai dai kawai ya bada umurni da hannu."
Bayan tayo Arwala tafito yashiga gaba ya tayar da sallah,
Raka'a biyu sukayi snn ya sallame, tare da yin Addu''oe ya mik'e ya haye Kan gado ya kwanta ya barta anan zaune."
Tana ganin hakan itama ta mik'e ta soma cire Alk'yabbar jikinta anan take wasu fitinannun kayan bacci suka bayya a jikinta farare fes komai nata ana gani a cikin kayan baccin."
Kan gadon ta nufa ta kwanta a bayansa, tare da Sanya hannu ta lakk'amosa ta manna Masa kirjinta bayansa suka tokaresa."
Lumshe Ido yayi yanajinta babu abinda Yake Masa yawo a Kai sai nasihar mahaifinsa Akan ta,
Jin ya gyaleta baiyi Mata maganaba yasa ta zura hannunta tashiga shafa gashin k'irjinsa cikin wani salo,
Anan take yaji tsikar jikinsa tafara tashi mararsa ta murd'a masa sannu a hankali ya Kuma gyara kwanciyarsa kamar Mai yin bacci."
Ganin tana tabasa baiyi maganaba yasa tasaki murmushin mugunta taci gaba da aika Masa da sak'onni,
Wata irin mik'a yayi ya janyota ya had'e ta da k'irjinsa yashiga sarrafata cikin zafin nama domin idonsa a rufe suke duk ta gama birgitashi ta tayar Masa da sha'awar shekara da shekaru wacce ya dad'e Yana juriya a kanta."
Sosai Saudat Taji Dadi yanda Sauban yanke sarrafata,
Yau ya Kai Mata inda ba'a tab'a Kai mataba, taji dad'in da tun da tazo duniya Bata tab'a Jin irinsaba sai Nishi take saukewa tare da Yar kuwa irin yanda taji turawa sunayi a BF.
Sauban Kuma ba abinda Yakeji Dan gane da ita aikin kawai yakeyi cikin wani shauk'i da Yake dibarsa da kyar yasamu yayi relexing snn ya sauka daga kanta Yana sauke dogon tsaki tare da ajiyar zuciya sai mere Baki yakeyi"
A lokacin ba Wanda ya fad'o Masa a Rai sai safwan da yaketa zuzuta Daren farko, Dan kuwa shi baiji wani abinda har ake fadin mutum zai iya Manta kowa da komai na a jikin macce☹."
Mararsa yaji ta Kuma murd'a Masa sai da yasha ruwan Lipton snn ya Dan samu sansauci snn ya tashi yashiga toilet ya tsaftace jikinsa yayi wanka yafi ya d'auki fillo yajefa a kan kujera yaje yayi kwanciyarsa Yana tinani iri iri a ransa."
Hakan itama Saudat tashi tayi ta gyara jikinta tafito tayi hayewarta akan gado tayi kwanciyarta domin yau burinta ya cika ta d'and'ani zumar sauban,
Wanda taji wani matsanancin sonshi da kaunarsa ya kuma dirar Mata jitakeyi idan wata macce tace taza rab'eshi tabbas zata iya rabata da numfashinta."
Washe gari Saudat ta shirya tare da bayinta suka rakata domin ta gaida mutanen gidan daga Nan ta zagaya gida wurin Hajjah ta Fara zuwa,
Hajjah tana ganinta tayi murmshi tare da yi Mata sannu da zuwa anan Hajjah tasamu damar k'arewa Saudat kallon sama da k'asa, anan taga tsantsan mulki a tare da ita tare da tsantsar soyayyyar mijinta a cikin idanunta,
Anan Hajjah taji dad'in ganin hakan ko ba komai jamila tasamu wacce zasu Kara da ita a cikin gidan nan,
Hajjah ta gyara Zama tashiga karantowa Saudat duk halinda mijinta Yake ciki Akan makiya domin zagaye Yake da makiya rayuwarsa tana cikin hatsari don ana amfani da abin Sha ko abinci ana cutar dashi Dan hakan in har tana buk'atar rayuwar mijinta sai ta tashi tsaye Akan mijinta.
Anan Hajjah tayi ta karantar da ita yanda zatayi tattalin mijinta Wanda tuni Saudat tasan da hakan domin yanda takejin Sauban ko baiwa ta Kama tana kallonsa sai ta fille Mata Kai Ko tayi mata hukunci mafi tsanani to bare har tabasu abinci sudafa su bashi yaci, to ita meye amfaninta."
Godiya tayiwa Hajjah snn ta tashi ta shiga b'angaren duka matan sarki suka gaisa,
Har b'angare fulani jamila inda tabi Saudat da kallo cike da kyashi da hassada Dan ko kayan jikin Saudat abin kallo ne bare gwala gwalan dake sanye a jikinta,
A ya tsine take kallon Saudat wacce itama Saudat take Mata kallon Mai bisa ruwa."
Kalmar da tafito a bakin fulani Jamila itace "ba girin girin ba tayi Mai Allah yasa ankawo budurci a gidan mijin Domin Banga farin gyalle Yana yawo a cikin gida ba kamar yanda Al'ada take."
Kallon shekeke Saudat tayi Mata tace "ai Koda farin gyalle zaiyi yawo bazai tab'a Shigowa wnn bangarenba domin an kusan walkiya komai zai bayya Dan Ina sa ran shigowata cikin gidan sai na bayyak'o asirin kowa daga ciki harda masu yunkurin kashe farin cikin rayuwata,
Tana kaiwa Nan tayi ficewarta."
Zufa tashiga karyewa Jamila me wnn yarinyar take nufi ne?"
Tana nufin tasan komai a kanta ne?"
Tana cikin tunanin hakan hankalinta a tashe taji wayarta ta d'auki ringing debawar da zatayi taga sunan Sarauniya Bilkisu wato Mahaifiyar Saudat kenan,
Cikin ran Jamila tashiga fadin Kiran me bilkisu takeyimun BaYan ta hanawa d'ana auren marar kunyar yarta, kafin wayar ta tsinke tayi saurin d'auka tare da karawa a kunnenta."
Sautin muryar Sarauniya Bilkisu taji tana fad'in "Sarauniya Jamila matar sarki Abdullah Kuma fulanin sarki Abdullah maccen da take mulkin cikin gidan masarautar Adamawa,
Kira nayi domin na fad'a maki 'yata tashigo cikin masarautarku,
Kada wani abun yasami 'yata,
Tsakanina dake kin sanni na sanki Kar Tasan Kar ne,
Na rantse da Allah inda nashiga a cikin duniyar Nan Koda mafarki bazakiyi tinanin Zaki shiga wurin ba, nasan bakya buk'atar k'arin bayani Dan gane da koni wacce ce,
Dan hakan a kiyaye aso abinda 'yata takeso koda mafarki kada ayi yunkurin cutar mun da ita Dan bazan tab'a yafewa Wanda yayi yunkurin yin hakan ba."
D'if taji ankashe wayar."
Mik'ewa tsaye tayi tana safa da Marwan me Sarauniya Bilkisu take nufi