Showing 42001 words to 45000 words out of 86876 words
nan Zan zauna tana nuna k'asa."
Kallon d'an k'aramun bakinta yayi tare da kyakkyawar fuskarta yaji ta burgeshi,
Yace "safna musu zakiyi dani tin yanzun?"
Da sauri ta girgiza kai alamar "A'a."
Yace "zo nan ki zauna, ya kuma nuna mata gefensa."
A hankali ta tako tanufi inda yace ta zauna, tare da sunkuyar da Kai ta zauna"
Idonsa akanta yana murmushi,
Yace "safna wnn kunyar tayi yawa a d'an ragemun ita."
Rufe fuskarta tayi da tafin hannunta tana murmushin jin kunya."
Murmushin shima yakeyi yace "ko sannu ya jiki baki cemun ba, bayan akanki aka dokeni."
Janye hannunta tayi a fuskarta ta kallesa cike da tausayi ta zame daga kan gadon zuwa k'asa tana kallonsa tace "kayi hakuri ya jiki?" Insha Allah zakasamu sauk'i."
Kallonta yakeyi cike da burgewa ji yakeyi kamar ya janyota ya d'orata akan k'irjinsa,
Cikin kasalalliyar murya yace "tashi kidawo inda kike ki zauna,
Cikin shagwab'a wacce d'abi'ar tace,
Take fad'in ni sai ka amsamun gaisuwata ko Zan tashi."
"Wow Sauban yace domin tayi matukar burgeshi shagwab'ar tayi mata kyau,
Ajiyar zuciya ya sauke snn yace "Alhmdulillah naji sauki Safna rigima sai a tashi azo a zauna."
Tana murmushi tazo ta zauna a gefensa,
Yana kallonta yace "Safna burina a koda yaushe naga wnn murmushin ya danwama a kan fuskarki banason ganin kukanki,
dan hakan na yanke shawarar Zan amshi Aurenki domin d'orewar farin cikinki kinsan dama nayi maki Alk'awarin Zan taimakeki Zan samar maki farin ciki Mai d'orewa,
Safna ki yarda dani?
Zaki Aure ni?"
Hawayen farin ciki suka shiga d'iga a idonta, domin tarasa bakinda zatayi masa magana,
A gabansa takai durk'ushe hawaye suna zuba a idonta,
Tace ni wacce ce da Zan furta bana sonka,
Kai ka taimakeni kayimun dukan komai a rayuwata, yarima nasan kafi k'arfina ni ba ajin aurenka bace, amma saboda ganin nasamu farin ciki wanda iyayena basa tunanin nasameshi tinda suka iya jefar dani akan titi, batare da sunyi tinanin halin da zan shigaba, Kaine mutum na farko da ka sanyani farin ciki, kaina wanda kake tausayina kake sharemun hawayena
Ni wacce da zan furta bana son ka?"
Kaine wanda ya taimakeni daga fad'awa daga cikin wata rayuwa wacce har gara wacce nake cikinta a yanzun da wacce Zan fad'a a hannun jarmai,
Babban burin yarima shine ya taimakeni ya bani gata ya 'yanta daga cikin k'angin bauta,
bakinta yana rawa akan kukan da yakeson yaci k'arfin ta kuma matsowa daf dashi saiti k'afafunsa ta sunkuyar da kai tace Yarima inasonka zan Aureka Zanyi biyayya a gareka tamkar baiwa,
Zan bi dukkan umurninka fatana kada kajuyamun baya idan katina da ni shegiya ce banada iyaye, ta fashe da kuka mai sauti tamik'e tafita da gudu tabar d'akin tanufi hanyar gida tana kuka."
Runtse idonsa yayi zuciyarsa cike da tausayinta yakai kwance anan take zazzab'i Mai zafi ya rufeshi."
Safwan ne yashigo ya tarar dashi cikin yanayin zazzab'i,
Anan take yakira direba suka shiga shirin tafiya domin yaga likita."
Sauban yana jin jiki, amma
Hankalinsa yana kan zuwa wurin maigari domin ya gana dashi yayi maganar safna akan gobe zai turo iyayensa."
Zazzab'in da yake damunsa yaci k'arfinsa sosai ko magana baya iyayi idonsa a rufe,
cikin gaggawa Safwan ya Rik'ashi yasakashi a mota suka bar k'auyen suka nufi gida."
********************
Mota goma sarauniya Bilkisu tacika da dakaru masu shirin yak'i domin sutafi k'auyen su safna sutayar da garin"
Kafin sutafin sai da takira Saudat tak'ara yi masu kwatancen k'auyen,
kamar yanda fadawa suka fad'a mata."
gudun kada asami matsala wurin aiwatar da aikin tacewa fadawan da tatura,
Tabasu umurnin akan su dakata kada sudawo sujira zata turo dakaru domin su nuna masu gidansu safna,
Tana buk'atar a tashi k'auyen gaba d'aya."
Anan suke fad'a mata yarima Sauban yabaro k'auyen yana kan hanyar komawa gida."
[9/9, 6:09 AM] Hayat: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍
🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴
Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)
*Page 27*
***** " murna Saudat takeyi jin sauban yabaro k'auyen,
yanda dakaru zasu sami damar cika aikinsu batare da wata matsala ba."
Kiran sarauniya Bilkisu Saudat tayi, tace "mommy bani d'aya daga cikin shugaban dakarun zanyi magana dashi."
Mommy tabata shugaban rundunar gaba d'aya Wanda yafi sauran rashin imani da kafirci."
Saudat takira sunansa "tace "Barde kanajina, umurni nabaka kafin Ku cinnawa gidansu yarinyar wuta, Ka tabbatar da kayi mata kaca kaca kayi mata fyad'e Wanda har abada bazata k'ara moruwa ba, snn ku cin nawa gidan wuta duk su k'une da duk zuri'ar su."
Dariya Bard'e yasaki yana fad'in "angama ranki ya dad'e duk abinda kikace hakan zamu aiwatar Allah ya k'ara girma da d'aukaka,
Snn ta kashe wayar a jiye gefe d'aya tana sakin dariyar farin ciki da jin dad'i, burinta ya cika domin da zarar anruga kauyen anyi Mata fyale koda ta rayu a duniya bazata tab'a moruwaba, yarima zaiji ya tsaneta tinda ta riga da ta nakkasa."
A guje dakaru suke shek'a gudu bana wasaba, duk wasu kayan aiki sun tanadesu cikin motocinsu Kai tsaye suka nufi k'auyen Lassa."
****************
A gaggauce Safwan suka iso,
kai tsaye asibity aka nufa da sauban domin jikin nasa yayi nauyi sosai numfashi kawai yake saukewa baya iya bud'e idonsa,
Taimakon gaggawa likitoci suka shiga bashi,
Snn safwan yakira maimartaba yake shaida masa a inda suke a yyanzun,
suna asibity da sauban ankwantar dashi baya da lafiya."
Hankali maimartaba ya tashe idonsa rufe yakira Hajjah ya fad'a mata halin da sauban yake ciki
Anan take, Hajjah da Anna suka shiga shiri tare da fadawa suka nufi Asibityn."
ai kuwa cikin minti goma gidan sarautar ya d'auki Labarin yarima Sauban baya da lafiya yana kwance a asibity."
Inda Sarauniya jamila tayi murna tayi farin ciki tare da Addu'ar Allah yasa daga can sai k'abari
A bakin wata baiwa Saudat taji labarin cewar mijinta baya da lafiya,
Ai kuwa hankalinta ya tashi cikin zafin nama da k'unar zuci, tashirya ta nufi asibityn kasan cewar family hospital ce kowa yasanta."
bak'aramun tashin hankali hajjah tashi cikin saba a lokacin da taga yanda sauban ya rame lokaci d'aya,
Uwa uba taga duk jikinsa kwancin bulala ne, tayi masa jajir akan farar fatar jikinsa,
Wurinsa tanufa cike da tashin hankali,
yana kwance a kan gado ana masa k'arin ruwa idonsa a rufe yana bacci tare da sauke numfashi sannu a hankali, kansa tashiga shafawa tana fad'in Sauban meya sameka?" Meya faru da kai?, nashiga uku wnn yaro marayan Allah kana ganin rayuwa iri iri."
Saudat ta bud'e k'ofa ta shigo ido rufe tanufi wurin sauban ta fad'a kan jikinsa ta saki kuka mai sauti."
Kallonta hajjah takeyi cike da tausayi ta janyota zuwa jikinta ta rungumeta tana lallashinta,
Ganin yanda jikin Sauban ya kwanta da bulala ya kuma sanya Saudat ta fashe da kukan bak'in ciki da tsananin kishi, domin tasan dukan da akayi masa ne akan tsinanniya yarinyar da yakeso 'yar k'auye, yanzun gashi nan yana neman ya hallaka kansa da rayuwarsa."
Likita ya turo k'ofa yashigo tare da Safwan yana biye dashi a baya, kai tsaye wurin sauban likita yanufa, ya k'ara dubashi tare da yi masa Allura,
Safwan yana bayan likita a tsaye yana kallon sauban cike da tausayi"
Kallon Safwan Hajjah tayi tace "Safwan meyasami abokinka ne a lokacin da kuka tafi gidan gonar?"
Turo k'ofar da akayi ita ta hana Safwan ya bawa hajjah amsar tambayar DA tamasa."
Maimartaba sarki ne da kansa ba aike ba,
Yashigo fadawa suna biye dashi a baya,
Ganin yanda Sauban ya koma lokaci d'aya ba k'aramun firgita sarki yayi ba, musamman yanda yaga jikin nasa duk ya kwanta da shatin bulala."
Safwan sarki ya kalla cike da ayar tambaya yace "Safwan meyasami magajin Sarki hakan?"
Ya akayi naga jikinsa da kwancin bulala?" Meya faru a cikin gidan gonar?"
Sunkuyar da kai Safwan yayi cike da ladabi yashiga bawa sarki labarin shad'in da akayi da yanda sauban ya kamu da son yarinyar bai san yanayi ba."
Sautin kukan Saudat sukaji wacce tafita a d'akin da gudu saboda bakin cikin abinda Safwan yake fad'a."
Sosai maimartaba ya tausayawa sauban domin yasan zafin dafin so tin a kan mahaifiyarsa Bintu,
Yasan yanda so yake illahta zuciya da gaggar jiki gaba d'aya,
so yakansa mutum ya makance ya daina ganin kowa sai abinda yakeso
So ya kansa mutum ya haukace ya zama tamkar marar, hankali ya dinga sabbatu a duk inda ya tsinci kansa,
masoyi zai iya sadaukar da rayuwarsa da,farin cikinsa da lafiyarsa a kan masoyinsa,
Wanda shine sauban yayi ya sadaukar da gaggar jikinsa,da lafiyarsa domin ganin ya ceto masoyiyarsa daga halaka."
girgiza kai maimartaba yayi yana murmushi domin shi sam baiga laifin sauban ba, idan akace bintu zata dawo duniya zaiyi abinda yafi hakan akanta."
Ran Hajjah ya b'aci matuk'a musamman da ganin Saudat tafita tana kuka,
Tace "wnn ai sakarci ne, ta yaya zai kara jikinsa a dinga zuga masa bulala har hakan a kan macce wace irin macce ce wnn wace tafi sauran matan duniya,
Na rantse da Allah da Nasan wnn sakarcin zaitafi yayi da bazan barshi ya tafi gidan gonar ba."
Murmushi maimartaba yayi yace kiyi hakuri Hajjah jarumin namiji shike nuna bajintarsa akan abinda yakeso,
sauban yayi matukar k'ok'ari wurin karawa da fulanin daji a wurin shad'i, wnn ya nunamun cewa Sauban jarumine ko a fagen yak'i zai iya fafatawa da mak'iya ."
Hajjah ta wurgawa sarki harara cike da jin haushi tace "ai dama duk abinda sauban yakeyi kai kake d'aure masa,
Har yaje ya kashe kansa da kansa a kan macce."
Cikin fushi hajjah tabar d'akin saboda takaici tanufi wurin Saudat domin ta lallasheta,
Wayam tagani ba Saudat ba fadawanta ba alamarta,
Alamar tayi zuciya kenan tabar asibityn."
********************
Sai wurin k'arfe goma na dare dakaru suka Dura k'auyen su safna,
Rarraba k'afa sukayi gaba d'aya suka zagaye k'auyen,
Fetur suka fito dashi da ashana karon farko suka shiga kunnawa runbun hatsin da duk sukaci karo dashi,
Anan take garin ya d'auki hasken wuta, tanaci bal bal,
Tin shigowarsu hankalin mutanen k'auyen ya tashi domin yanda sukaji shigowar motocin suka tabbatarwa da kansu ba lafiya,
duk Wanda yake bacci aka tayar dashi yara k'anana iyayensu suka goyasu a bayansu sukayi tsaitsaye suna jiran mutuwa ko rayuwa."
Hakan gidansu safna Wanda yake zagaye da dakaru,
Idon safna biyu domin batayi bacci ba gabanta kawai takeji yana fad'uwa yarima take gani yana mata gizo a idonta, anan take ta tabbatarwa da kanta yana cikin mawuyacin hali."
Sautin maganar mutane taji a bayan d'akinta suna fad'in mu cinawa gidan wuta kawai kowa ya k'one,
Wani Mai kakkausar murya yace "gimbiya Saudat tace "na haye yarinyar na moreta son raina, snn daga k'arshe mukasheta."
Idonta ya cika da hawayen tausayin kanta domin, ta tab'ajin sunan matar yarima Saudat a bakin Safwan,
Wani lokacin suna tare da yarima safwan yakira wayar sa,
Yake shaida masa da cewa ya ina ne,
GIMBIYA SAUDAT takira wayarsa tace tajita a kashe,
tace ya kirata tanason zatayi magana dashi,
A lokacin dogon tsaki taga sauban yaja bai bawa Safwan amsaba illah ya kashe wayar gaba d'aya ya ajiye,
anan ta fahimci matarsa ake nufi
Cikin ranta tashiga fad'in Ashe sunanta Saudat, tin daga lokacin sunan Saudat ya tsaya mata a rai,
Duk lokacin da taji an anbaci sunanta takanji gabanta ya fad'i ta rasa dalili hakan da takeji,
hannu tasaka tashare wayen fuskarta ta mik'e tsaye, tanufi k'ofar fita,
Tana fad'in wato itace ta turo a kasheni kenan burinta ayi mun illah a rayuwa mai natare mata?" Hasalima bata sanniba ban santaba."
Tanajin muryar su a waje suna shawar yanda zasu shigo cikin gidan,
Cikin sand'a tabud'e k'ofar d'akin tafita tanufi d'akin baba Wanda suke tare da inna idonsu biyu sunajin duk abinda ake fad'a a waje ko wanne sai zarar ido yakeyi cike da tsoro,
Ganinta da sukayi Baba ya taso ya rungumeta yasaki kuka itama safna kuka takeyi domin sun rigada sun sadakar lokacin mutuwarsu ne yazo,
Inna sai fad'I takeyi muna zaman zamanmu lafiya muka d'aukarwa kanmu bala'i da masifa Safna ke annoba ce a rayuwarmu."
Jin anfara durowa cikin gidan, yasaka inna yin shuru, bakinta kawai ke rawa."
Hannu Baba safna ta Rik'e cike da zafin rai tace "baba mugudu bana son rabuwa da Kai."
Girgiza kai Baba yayi yace "Safna ta ina zamu gudu bayan gasu nan suna shigowa cikin gidan da Zarar munfita kashemu zasuyi."
Safna tace "baba idan bamu fita a gidan nan ba cinnawa gidan wuta zasuyi duk muk'une a cikinsa,
Baba zaiyi magana wani k'arfi yazowa Safna ta fisgo hannun Baba suka bud'e k'ofa suka fito inna tana biye dasu a baya,
K'atti majiya k'arfi hud'u suka gani a cikin gidan sun juya baya sunajiran shigowar Sauran,
Cikin sand'a safna take Rik'e da hannun Baba sukabi ta bayansu suka nufi k'ofar baya sukafita, Wani irin ihu inna tasaki a lokacin da ta taka k'usa a k'afa, Wanda ya hankaltar da dakarun inda suke."
Suka nufo wurin inna tana kwance rik'e da k'afa,
Safna tana rik'e da hannun Baba sai gudu suke shek'awa."
Ai kuwa dakarun sukace gata can ta gudu,
Suka dafawa safna,
Gudu kawai sukeyi dakaru suna biye dasu a baya da makamai a hannu,
Baba ya fisge hannunsa daga na Safna sakamakon gajiyar da yayi da gudu ji yakeyi kamar numfashinsa zai d'auke,
Ya kalli safna hawaye suna zuba a idonsa yace "safna kiyi tafiyarki Allah zai taimakeki zai tsiratar dake a duk inda kika tsinci rayuwarki, kibarni su kasheni domin baxan iya kub'utar DA kaina daga garesuba, bazan iya aikata komai ba, Allah yayi maki Albarka,
Ki mik'e kada ki karya kwana a kan hanya kike, zatayi magana kenan ta hango dakaru sun kusan zuwa wurinsu, a lokacin Baba ya zube ya d'auke numfashi,
tanaji tana gani tabar Baba a wurin ta keci daji da gudu,
Gudu takeyi suna biye da ita a baya jefa k'afa kawai takeyi a cikin daji batasan inda takeba ga duhun daji."
*Wayyo safna*😭😤
*Mrs Ana's Bawa*✍
[9/9, 7:43 AM] Hayat: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍
🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴
Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)
*Page 28*
****** " Gudu take shek'awa Idon rufe jefa k'afa kawai takeyi a duk inda tasamu hanya, Wanda takejin zugin zafi k'afarta kasancewar ba talkami a tare da ita,
Wani irin k'aton macije tagani ya tashi tsaye a gabanta Wanda girmansa baya misaltuwa,
Wani irin ihu tasaki ta zube wurin a some."
Sautin ihunta yayi dai dai da farkawar Sauban a kan gadon Asibity, babu abinda yakeji a kunnensa sai sautin kukan safna tare da ihunta da ya farkar dashi."
Waige waige yakeyi akan gadon asibityn domin yakasa barin jin sautin a kunnensa,
Hajjah ta taso tanufoshi tana fad'in "Sauban ka farka me kakeso?"
Girgiza Kai yayi alamar baya son komai, ya lumshe idonsa hawaye suna zuba a gefen idonsa."
Kallonsa takeyi cike da mamakin ganin hawaye suna zuba a idonsa, yaushe rabon da taga hawayen sauban tin yana k'arami, KO a lokacin ba komai yake sakashi zubar da hawayeba,
Sai gashi yanzun da girmansa yana zubar da hawaye."
Matsawa ta kumayi a gefen gadonsa tana share masa hawaye tana fad'in "magaji meyake damunka?"
Me kakeso?"
Kukan me kakeyi?"
Girgiza mata kai yayi alamar ba komai hawaye sukaci gaba da zuba a idonsa."
Babu Neman da dakaru basuwa safna ba a cikin dajin amma basu ganta ba wata alamarta."
ai kuwa Sai k'ara kutsa Kai sukeyi cikin dajin, da manyan fito masu hasken gaske a hannunsu,
D'aya daga cikinsu yaji wani abin ya sareshi a k'afa, wani irin Ashar yasaki ya juya domin ganin Ko meye wani irin k'aton maciji yagani ya nad'e wuri d'aya,
ya kuma kai masa Sara a cinya,
Ihu yasaki ya d'aga murya yana fad'in ku gudu kada ku karaso maciji,
ai kuwa anan take kumfa yashiga zuba a bakinsa ya fad'i wurin a macce,
Sauran dakarun sunajin hakan suka juya a guje, macijin yabi bayansu shima suna gudu yana gudu yana biye dasu a baya yana masu rakiya sai da yayi nasarar kashe mutum biyu a cikinsu snn saura suka tsira."
Koda suka shiga cikin k'auyen suka shiga cinawa gidaje wuta k'urumus suka k'one gidansu safna tare da makotansu snn suka shiga mota sukabar k'auyen cike da bakin cikin mutuwar yan uwansu."
Mutan gari sunajin tafiyar tasu suka firfito suna kuka domin ba k'aramar b'arna akayi masu ba,
Ank'ona masu rumbun abinci ankashe masu shanu wasu sun rasa rayukansu me sukayi masu?
Suwaye suka aikata masu hakan?"
Daren ranar gaba d'aya garin basuyi bacci ba, babban tashin hankalinsu gidajen da aka k'ona daga ciki har da gidansu Safna Wanda a yanzun ya zama fili,
Kuka suka fashe dashi domin sunada ya k'inin har mutanen dake cikin gidan an k'onasu sun mutu."
Yanda sukaga dare hakan sukaga safiya,
Koda safiya ta waye duka garin ya cika da jama'a ana masu jaje tare da amsar gaisuwa,
Acan bayan gari aka hango inna tafe tana jan k'afa fuskarta duk tab'aci da jini ba hijabi bare d'an gwali akanta,
Ai kuwa da sauri aka nufota aka rik'ata aka zaunar da ita,
Ruwa aka bata tasha jama'ar gari suna fad'in Alhmdulillahi Allah ya kub'utar DA lnno ta tsira, cikin muryar kuka tace "dukanmu mun tsira harda malam da Safna domin kuwa su guduwa sukayi,
Ta kuma fashewa da Kuka tana fad'in Safna Annobace a garin nan ranka ya dad'e duk ita ta Janyo mana wnn bala'in."
Maigari yace "subahanallahi Allah ya kyauta, ba Wanda ya janyo mana duk abinda yasamemu daga Allah ne bama d'orawa kowa laifi,
Alhmdulillah tinda sun tsiratar da rayuwarsu Allah ya tsaresu a duk inda suke Mun san zasu dawo garemu komai daren dad'ewa."
Anan sukaci gaba da amsar gaisuwar wad'anda suka mutu tare da jajen shanun da aka kashe."
***************
Cikin wata bunka ta farka ta tsinci kanta a cikinta, gefenta akushine Wanda yake d'auke da waina da miya da manshanu,
Wata mata tagani 'yar fillo irinta sanye da kayan fulani irin nata zaune a gefenta Tana kallonta tana murmushi,
a k'allah matar zatayi shekara 40."
Murmushi safna tasakarwa matar tare da k'ara waigawa domin ganin inda take,
Matar tace "sannu Safna har kin farka."
Zaro ido safna tayi tana mamakin a Ina take? Wacece wnn?" Ya akayi tasan sunanta?"
Anan take komai yadawo mata sabo cikin razana ta motsa tana neman ta firgita, tare da kallon hannunta tana fad'in macijin ya sareni ko?"
Murmushi matar tasaki tace "bai sarekiba ki kwantar da hankali,
Ta mik'a mata Akushin dake d'auke da waina tace 'ga abinci kici."
K'amshin abincin ya daki hancin safna a nan take cikinta ya k'ulle akan yunwa ta tina da rabon ta da abinci har ta manta, ta karbi abincin ta Faraci, citakeyi tana lumshe ido domin ba kad'an