Showing 69001 words to 72000 words out of 86876 words
takeyi mashine ya kwantar dashi ciwo,
Ciwon da d'ora mashi mutuwa domin daga can sai kabari injita."
bata kuma firgita da lamarin sauban ba sai da sarkin gida ya nufota a firgice ido rufe yana sheda mata cewa ansaya ranar auren sauban da yarinyar da yakeso wata uku masu zuwa."
Wani irin zabura tayi ta mik'e tsaye idonta a rufe, lokacin yayi daidai da shigowar sadeeq, ta d'aga hannu cikin tsananin b'acin rai ta d'aukeshi da mari,
Tana hucin Mai cike da takaici da bakin ciki, tana fad'in "na haifeku ne domin na d'ebe takaicin haihuwa, na haifeku ne domin kuzama jigo abin alfahari a cikin masarautar nan,
Nakan hana idona bacci na hana gaggar jikina hutawa,
Na kashe kud'i wad'anda bansan iya adadinsu ba duk dan kusami sarauta ku mallaki masarauta da duk wani Abunda ke cikin masarautar,
kaida d'an uwanka sageer, duk abinda nakeyi a banza yake tafiya saboda bakusan ciwon kankuba,
Yanzun labari yazomun cewa Sauban aure zaiyi zai auri Mata ta biyu,
Tunda ta farko bata haihu ba ya zama dole ta biyu ta haihu,
Idan matarsa ta haifi d'a namiji shikenan yayi zarrah a cikin gidan nan,
kuna nan zaune, ko da wasa bantab'ajin d'ayanku ya furta cewa zaiyi aureba bare ya haihu."
Ta nuna masa hanyar fita tace "kafita kabani wuri,
Kafad'awa d'an uwanka cewa sati biyu kacal nabaku kafin d'aurin auren sauban Ku tabbatarmun da cewa kunfitar da matar da zaku aura."
Idan ba hakan ba kowa zaiga b'acin raina a cikin gidan nan."
[3/30, 9:56 PM] Hayat: *DAN SARKI SAUBAN*
*Writing by*
*Ummu Safwan*
( _Fareeda Basheer_ )
*42*
"A d'akinsu Sauban Safna tana gefen gadonsa akan kujera zaune,
Idon sauban yana kanta duk wani motsi nata akan gadonsa takeyinsa,
Jiyakeyi babu abinda yake masa ciwo a jikinsa a sallamesa ya koma gida kawai yake buk'ata."
Hajjah ta turo k'ofa tashigo tare da sallama tafito daga wurin ganin saudat,
Amsa Mata sallamar sukayi suna kallonta,
Itama kallonsu tayi tasaki murmushi mai cike da tsokana tana kallon sauban tana fad'in "oh ni hajjah yanzun shikenan yaron nan yadawo daga duniyar mutuwa,
Ashe haka ciwon soyayyah yake."
Had'e fuska sauban yayi bayason hajjah da Safwan suna masa wannan maganar a gaban Safna salon ta raina shi."
Hajjah ta mere baki tace miskilin mutum Mai ban haushi,
Ba had'e fuska zakayiba, idan katashi kasaka kuka, amma baka isa ka rufemun bakiba, saina fad'i abinda ke raina."
Lokacin da ciwon soyayya ya kamaka har kuka kakeyimun Anna itace shaidata."
Guntse baki safna tayi tanaso tayi dariya ba fuska, sauban ya tsare gida."
katse hajjah yayi daga maganar da zatayi dan bai san abinda zata fad'aba a nan gaba, yace Yaya jikin Saudat taji sauk'i kuwa?"
Kuma mere baki hajjah tayi, tace tasami sauk'i tana can tare da uwarta,tana sak'a Mata,
murmushi sauban yayi yace "me likita yace dangane da abunda yake damunta?"
Hajjah mere baki tace "kafi kowa sanin halin matarka tare da dalilin fad'uwar da tayi,
Idan kana iya tafiya ka tafi ga ganewa idonka halin da take ciki DaGa nan saika tambayeta bayanin da likita yayi
Murmushi yayi yace yanzun kuwa Zan tafi tinda ke bazaki fad'amun ba ."
Ya kalli safna wacce ta daina murmushin da takeyi fuskarta ba yabo ba ballasa yace "Mutafi mugano Antynki."
"to tace "tare da mik'ewa tsaye,
tsaye tayi tana kallon yanda zai sakko daga kan gadon,
Sannu a hankali ya zuro kyakkyawar k'afarsa izuwa saitin silifas d'insa Wanda safna ta saita masa su wuri d'aya,
Zura k'afarsa yayi yasaka ya cije leb'onsa na k'asa sannu a hankali ya mik'e tsaye jiki ba kwari"
Murmushi farin ciki hajjah tayi ganin ya tashi da kansa,
Ido biyu sukayi dashi ta mere baki,
Tace sannu kinji safna kinceci rayuwar wani daga mutuwa."
Murmushi kawai safna tayi tashige gaba sauban yabi bayanta, Fuska had'e yake hararar hajjah."
Sannu a hankali suke tafiya,
Inda fadawa wad'anda ke tsaronsa suka take masu baya suna zuba masu kirari,
Tafiya sukeyi cike da farin ciki,
Sauban jiyakeyi wani iska Mai dad'i yana ratsashi farin ciki yakeji yana wanzuwa a tare dashi."
D'aya daga cikin bafad'en yayi saurin zuwa ya bud'e masu k'ofar d'akin da saudat take ciki,
Hakan yanunawa sauban nan ne aka kwantar da ita."
Hannu ya d'agawa fadawan alamar su jirashi waje,
Sannan yashiga d'akin hannunsa sanye a Aljihun rigarsa safna tana biye dashi a baya."
Saudat tana kwance a kan k'afar mahaifiyarta tana kwantar mata da hankali akan tabar komai a Hannunta,
Sukaji sallamar shigowar sauban."
Zubbur Saudat tayi ta mik'e zaune tana murmushi cike da farin ciki, take kallonsa,
D'an murmusawa yayi ya kalle inda mommy take ya gaida ita,
Hakan itama safna ta duk'a ta gaida ita,
Amsawa mommy tayi fuska ba Annuri ta kafe Safna da ido tana kallonta sama da k'asa tabbas wnn 'yar Hajiya Laila ce ko ba'a, fad'aba kamanni ya nuna,
Wanda kallon yasaka safna sarguwa takame gefe d'aya."
Wurin Saudat ya nufa cikin murya k'asa k'asa yanda ba wanda zai iya jin abinda yake cewa yace "yaya jikin naki?"
Turo baki tayi alamar shagwab'a tace naji sauk'i,
Tsare gida yayi yace "meyake damunki?"
Kuma turo baki tayi tana fadin "ba Kai neba?"
"Nine danai maki me?"
Meya faru?"
Dam gaban safna ya fad'i ganin yanda Saudat take zubawa sauban shagwab'a shikuma yana kallonta yana biye mata Allah kadai yasan abinda suke cewa.
Wani abinda taji yana taso mata a zuciya tayi saurin Dannewa tare da karanto duk Addu'ar da tazo ranta."
" tsareta yayi da ido yana fad'in inajinki mena maki?"
Tayi shuru ba amsa."
Ya mere baki yace "To shikenan tunda baxaki fad'aba Allah yabaki lafiya,
Ya juya ya kalli inda safna take,
Yakira sunanta yace "Safna zo ki gaisa da Antynki kiyimata ya jiki."
Cikin natsuwa safna ta tako zuwa gadon saudat, Saudat na ganinta, sukayi ido biyu da ita gabanta ya fad'i, gani tayi duk duniya ba wanda yafita kyau wani tsantsar kyan safna ta hango a tare da ita,
Cikin sauri ta Kai kwance tare da runtse ido tamkar wacce take bacci, domin ko a lahira bata fatan ta kumayin ido biyu da safna,
Safna tace "Anty Ina wuni ya ya jiki?"
Saudat tayi banza da ita idonta a rufe hawaye suna zuba a gefen idonta a duniya babu abinda ta tsana sama da safna,
Yau itace a gabanta wata macce take tsaye da mijinta,
Kuka tasaka mai sauti tana fad'in "mommy kiyi masu magana suyi tafiyarsu bana son gaisuwar."
A harzuk'e mommy tace "Ai sai kutafi wacce kukazo gani tace bata son ganinku."
Shuru sauban yayi fuskarsa a had'e yana karantar duk abinda ke faruwa,
Sautin muryar mommy yaji tana cewa safna "malama ke ai saiki fita tunda mijinta baya iya tafiya ya barta,
Kifita Daga waje kijirashi batada bukatar ganinki."
murnushi safna tayi ta d'aga kai ta kalli sauban yana nan tsaye a inda yake ko motsawa baiyiba, alamar bayason barin wurin, kenan
jiki ba kwari ta juya zata fita,
Caraf ya rik'e hannunta yana fad'in kijira mufita a tare mana, ai a tare muka shigo,
Yaje saiti wurin fuskar Saudat ya shafi fuskarta da hannunsa wacce take jike da hawaye yace "Allah yabaki lafiya ya kawo maki sassauci akan abinda yake damunki,
Ya Juya ya fita yana janye da hannun Safna."
*****************
A gidan Alhaji Habib Naira,
Yau kwana biyu kenan ba Safna a tare dasu,
sosai Alhaji Habib yashiga damuwa, iya d'an zaman da sukayi da yarsu sunyi matuk'ar sabo a tsananinsu."
Hajiya Laila take kwantar masa da hankali cikin natsuwa tare da jansa a jiki cikin hikima irin ta 'ya mace take lurar dashi cewa "ya daina sanya damuwar rashin suhailat a kusa dasu,
Yasani cewa suhailat 'ya mace ce, aure zatayi ta tafi gidan wani, shikenan tabarsu gaba d'aya ta koma wani gidan da zama,
Meye abin damuwa na rashinta da yayi kwana biyu."
Anan taci gaba da lurar dashi akan k'arfin Amintarsu da sarki kada yabari shaid'an yashiga tsakaninsu ya raba tsakaninsu akan 'ya'ya."
Ko ba'a fad'aba yasan sarki yaji kunya tare da nadama Mai cike da danasani akan kuskuren da yayi a baya."
Sosai Alhaji Habib yaji dad'in magagganun matar tasa, ya janyota zuwa jikinsa yana shafata tare da sanya mata Albarka, dayiwa Allah godiya daya bashi Mata ta kwarai,Mai tunani da hangen nesa."
Kwakwasa k'ofar falo da akeyi yasa Hajiya Falmata ta janye daga jikin mijin nata Wanda har ya fara fita daga hayyacinsa,
Janyota ya kumayi ido rufe yashiga aika Mata da sakon ninsa,
K'arar dukan k'ofar yasa Alhaji Habib yasaki umma yafita a fusace domin ganin ko waye."
Maigadi yagani tsaye a bakin k'ofa,
Ganin fuskar Alhaji ba fara'a tunkafin Alhaji yayi magana, maigadi ya zube k'asa yana fad'in tuba nakeyi ranka ya dad'e ayi hakuri, kasan ba halina bane dukan k'ofa, bak'ine kayi,
Manyan bak'i sarakuna ne da kansu suke
nemanka.'
Ido sarki ya d'aga ya hango ta gawar motoci fadawa Acan cikin harabar gida sai jiniya akeyi,
Mamaki yashigayi yanzun duk jiniyan nan da akeyi baijiba."
_yo Abba yaza'ayi kaji ka tsunduma cikin wata duniyar_🙊
Hannu ya d'agawa maigadi akan yayi tafiyarsa,
Yakira escort nashi wad'anda suke zagaye a gidan, yace a bud'e masu babban wurin parking space dake can gefen gidan su ajiye motocinsu sannan ayo masu iso zuwa babban falon ajiye bak'i."
[3/30, 9:56 PM] Hayat: *DAN SARKI SAUBAN*
BY
UMMU SAFWAN
(FAREEDA Basheer)
*44*
Tana Huci ta nunawa sarki gida k'ofa fita tace 'kaima tashi kafita saina nemeka munafuki kawai"
Jikin sarkin gida yana rawa yafita yana zarar ido,
********************
sauban sai kuma murmurewa yakeyi a kullum da tunanin safna yake kwana yake tashi a ransa,
A D'ai rana yakan yimata kiran a wayar Hajiya laila yafi ak'irga
hakan zasu sudinga fira mai cike da shaukin so da kauna,
Wani lokacin yakanyi mamakin kansa idan ya zauna yana tunaninta, ta yanda baya iya awaya daya baikirata yaji muryarta ba,
Wanda yake tunanin kodai sonta yakeyi da gaske kamar yanda Safwan yake fad'a masa cewar ya fad'a tarkon so,
Girgiza kai yayi yana fadi a ransa "ina baitab'ayin soyayyaba a rayuwarshi baisan yanda so yakeba, abinda yasani yana tsananin tausayinta ne kawai shine dalilin damuwar da yayi da ita."
*****************
Yau safwan cike yake da murna da farin ciki masoyiyarsa matarsa Safinat ta haihu anhaifa masa d'a namiji,
Inda ya d'aga waya yakira sauban Wanda yake zaune a d'akinsa ya sanya Saudat a gaba yana tambayarta saita fad'a masa abinda yake sanyata tana rama, duk tabi ta rame ta fita hayyacinta saboda tsananin kishi,
Kuka take masa tana fad'in babu abinda yake damunta ita,
Suna cikin hakan wayar Safwan tashigo wayarsa ya dauka anan yake masa Albishir cewa yazama daddy safinat ta haihu yanzun suna asibity ta haifi d'a namiji ya rad'a masa Suna SAUBAN,
Masha Allah sauban yace cike da farin ciki samun takwara da yayi yace " ganinan zuwa asibityn yanzun nan."
Ya mik'e cikin hanzari ya d'auki key din motarsa ya d'an tsaya yana kallon Saudat sannan yace "Zan tafi nadawo ki tabbatar da kin tanadi amsar da zakibani,
Inason nasan sanadin ramar da kikeyi,
Yana gama fad'in hakan ya juya ya fita."
Kai tsaye asibityn yanufa cike da farin ciki domin jiyakeyi tamkar shine akayiwa haihuwa, sauban yana tsananin son 'ya'ya Allah ne kawai baibashi bane hakan yake dannewa a ransa bazaka iya gane abinda yakesoba da Wanda bayaso."
kai tsaye d'akin da ake kwantar da wadanda suka haihu ya nufa kasancewar asibity sananniya ce sai wane da wane suke zuwa cikinta,
Yana murmushi ya tura d'akin yashiga da sallamarsa ya tarar da Safwan zaune a bakin gado yana rungume da jariri bakinsa cikin bakin safinat yana tsotsa tare da shafa mata kai da hannunsa d'aya yana jera mata sannu,
yana sane da shigowar sauban amma sai yayi kamar baisan ya shigoba,
mere baki sauban yayi yayi gyaran murya yana fad'in maye kawai hatta a cikin asibityn baza"a bar mayyatarba, d'an iska kawai."
Dariya Safwan yasaki ya Saki safinat ya taso daga kan gadon yana fad'in barka da zuwa abokina ai bansan kashigoba, Ina tayaka farin cikine samun takwara da kayi." ya mik'a masa jaririn."
Amsar yaron sauban yayi yana murmushi yana kallonsa, cike da burgewa da ban sha'awa karon farko dayaji sha'awar inama wnn yaron d'ansane ina Saudat ta haifa masashi dasai yafi kowa murna da farin ciki,
Ya ciro wayarsa a gaban Aljihu yashiga d'aukar yaron hoto,
Wanda hakan yayi matukar farantawa Safwan rai,
Domin wnn shine karon farko da abokinsa ya sanya wayarsa ya dauki hoton wani abu da kansa,
tabbas Ya tabbata bakaramun farin ciki yayi da wnn haihuwarba."
Safwan yana murmushi mai cike da tsokana yakalli sauban yace "ni nakawo rumfata saura kaima kakawo taka, koda yake ba mamaki basir ne yake d'awainiya dakai abokina Zan nema maka maganin basir."
Had'e fuska sauban yayi ya wurgawa Safwan harara,
Bai tanka masaba illah yaci gaba da d'aukar Sauban junior a waya, aka kumayi sa'a jaririn ya bud'e idonsa kwanin ban sha'awa yana kallon sauban,
_Kusan jariran yanzun da Zarar katafi barka idon biyu kake ganin jariri yana kallonka kana kallonsa_😂
Saida aka sallami safinat snn sauban ya koma gida bayan ya rakasu har gida, har yakeji a ransa inama abar masa jaririn ya tafi dashi."
a gajiye ya koma gida kai tsaye d'akinsa ya nufa, ya cire kayansa ya fad'a toilet domin ya watsa ruwa ko zai sami sassaucin gajiyar da yakeji,
Bayan yafito daga wanka yana d'aure da towel a k'ugunsa,
Hannunsa d'auke da d'an k'aramun towel din yana goge ruwan jikinsa zuwa kansa."
Saudat ta turo k'ofa tashigo hannunta d'auke da wani kyakyakkyawan tire Wanda yake jere da kulolin abinci na alfarma, tayi kwalliya sai k'amshi take zubawa,
akan dining table tanufa ta ajiye abincin snn tadawo zuwa wurinsa ta karb'i towel din hannunsa tashiga goge masa jikinsa,
Shuru yayi yana saurarenta baiyi yunkurin dakatar da itaba kamar yanda yasaba saboda a halin yanzun tausayi take bashi,
Saida ta kammala goge masa jikinsa sannan ta d'auko jallabiyarsa tare da gajeren wandonsa ta ajiye masa a gefen gado zata juya tafita domin ta bashi wuri ya sanya kayansa kamar yanda yake bata umurnin fita idan zai sanka kayanshi,
Saiji tayi ya ruk'o hannunta ya dawo da ita yana kallonta cike da tausayi,
Ya nufi kan gado da ita ya zauna ya d'orata akan k'afarsa ya juyo da fuskarta saiti fuskarsa suna kallon juna cikin murya k'asa k'asa yace "fad'amun damuwarki saudat meyake damunki?"
Ko wani abu nake maki Wanda bakijin dadinsa a gidan nan?"
ko wani yake takuraki a cikin gidan nan fad'amun naji."
kanta ta sunkuyar k'asa hawaye suna zuba a idonta har suna sauka akan k'irjinsa,
Yayi saurin runtse idonsa cike da damuwa domin a duniya idan akwai abinda ya tsana bai wuce kukan mace ba."
Cikin muryar tausayi yace fad'i naji ina saurarenki."
Zamewa tayi daga kan k'afarsa ta sakko k'asa ta tsuguna a gabansa tare da sunkuyar da Kai hawaye sukaci gaba da zuba a idonta,
Cikin muryar kuka tafara da cewa,
"Ina tsananin sonka da k'aunarka mijina,
Tunda Allah ya halliceni bansan soba sai a kanka, bansan shakuwa ba sai a kanka, duk da dai kai baka sona ni Ina tsananin Sonka Zan iya rabuwa da komai da kowa akan sonka,
Soyayyar da nake makace ta janyo nake tsananin kishinka ka taimakamun Yaya Sauban zuciyata tanada rauni akan soyayyarka Zan iya rasa rayuwata idan ka k'ara aure
Bana iya jure ganin wata macce a tare dakai a shinfida d'aya da sunan matarka ta aure
Sadaukina ka taimakeni ka taimaki rayuwata kace kafasa Auren,
Kaxauna dani ni kad'ai nayi Alk'awarin duk halina Wanda bakaso Zan daina wlh zan daina takai k'arshen maganar tare da sakin kuka mai sauti gwanin ban tausayi."
Kallonta yakeyi cike da tausayi,
Dama yasan matsalar Saudat bata wuce kishi, tsananin kishintane yake sanya take ramewa,
Hannunsa yasaka ya tallabota ya mikar da ita tsaye ya janyota zuwa jikinsa,
ya kai kwance akan gadon ya d'orata a kan faffad'an kirkinsa mai cike da yalwan gashi wanda yayi kwance gwanin ban sha'awa a kirjinsa,
ringumeta yayi yana bubbugar bayanta alamar tayi shuru ta daina kuka,
Sannu a hankali ta fara samun natsuwa ta nemi hawayen dake zuba a idonta ta rasa,
Cikin wani salo ya kara bakinsa a kunneta yashiga rad'a Mata, "kiyi hakuri Saudat ba abinda kikayimun iya zamana dake bare nafad'a maki ki gyara,
A tsarin rayuwata bana da ra'ayin ajiye Mata sama da d'aya domin tara yawan mata baya d'aya daga cikin tsarina,
Nima Ina mamakin wnn auren da zanyi Wanda ni Karan kaina na. Amince dashi nake kuma jin yarinyar da Zan aura har cikin raina,
Kiyi hakuri ki 'dauki kaddara auran nan,
Kicire damuwa a ranki, insha Allahu Zan kwatantamaku adalci, ki daina cewa bana sonki, Saudat Ina sonki da bana sonki da baxan zauna dake a matsayin matar aurena ba."
Na rok'eki da ki sassautawa rayuwarki wannan zazzafan kishin dake damunki,
Yana kawai nan ya tura bakinsa a cikin bakinta yashiga aika mata da sak'onninsa Dan kawai ya sanyaya Mata rai."
Ai kuwa yayi nasara sosai wurin farantamata domin taji ranta yayi Mata sanyi sosai yau sauban ne da bakinsa yake furta Mata kalmar yana sonta,Har yake aika Mata da salonsa mai rikitarwa."
Kamar koda yaushe a yanda yasaba jinta hakan yauma yajita salam duk tasaki babu abinda yake fita a gabanta sai wani farin ruwa Mai kauri da yauk'i,
Hakan yagaji Dan kansa ya sauka akanta badan yasami kamsuwaba koyaji wani dadi a tare da ita, idan dasabo ai yasaba dajin Saudat a hakan."
Toilet yashiga yayi wanka yafito ya dauki jallabiyarsa yasaka sannan yanufi wurin dining domin ya zuba abinci yaci."
[3/30, 9:56 PM] Hayat: *DAN SARKI SAUBAN*
BY
UMMU SAFWAN
(FAREEDA BASHEER)
45
Hakan Saudat tayita lallashin zuciyarta tare da danne kishinta, babu abinda yafi d'aga Mata hankali duk takira wayar mahaifiyarta wacce take kwantar Mata da hankali ta kuma yimata Alkawarin idan har tana raye sauban baxaiyi aureba,
akashe ake cewa wayar take,
Wayar mahaifinta kawai take samu,
Idan ya dauka suka gaisa idan ta tambayeshi mahaifiyarta zaice lafiya kalau take takira wayarta mana."
Idan tace takira a kashe takejinta zaice network ne taci gaba da nema zata samu hakan zasuyi sallama ya kashe wayarsa."
Mahaifiyar saudat kuma gimbiya Bilkisu tana can itama cikin tashin hankalin fitinar kishi gobe za'a kawo mata kushiya,
Ba Saudat ce a gabantaba ita keyiwa kanta yaki wnn karon,
Tayi kuka tayi birgima tayi tashin hankali Wanda har yayi sanadiyar kwanciyar bayinta biyu a asibity akan wani mugun duka da tayi masu akan tana cikin zafin kishi, suka bata hakuri"
Macce d'aya ce zata iya kwantar Mata da hankali tare da bata shawarwari itace Hajiya laila, gashi kuma yarta zata aurawa mijin Saudat dan hakan ta dauki tsanar duniya ta Dora mata,
Tarasa dubara bare