Showing 66001 words to 69000 words out of 86876 words
sauban ya nemi ciwo a jikinsa ya rasa, sannu a hankali ya tashi zaune da kansa idonsa na kan safna yana kallonta ganin ta goge ta koma 'yar birni yar gayu duk wannan dattin da k'auyanci duk babu shi,
Yasaki murmushi, itama ta kallesa tasaki murmushi tare da rufe fuskarta cike dajin kunya."
Sunanta yakira cike da kulawa yace "safna hakika tausayinki tare da tausayin halinda zaki shiga a lokacin da natafi nemanki a k'auye akacemun kinb'ata shi yasakani shiga cikin wannan halin,
bani labarin rayuwar da kikayi bayan shad'inki har zuwa tafiyarki da yanda kikayi kika had'u da mahaifanki."
Sunkuyar dakai tayi tana wasa da ya tsun hannunta tashiga bashi labarin duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe."
Sosai ya tausaya mata wani b'angare kuma yayi farin cikin ganin mahaifanta da tayi."
*********************
Kuyangin saudat tare da hajjah da maimartaba tsaye a kanta tana kwance akan gadon asibity ruwa suna jone a hannunta,
Babu abinda yake fita a idonta sai hawaye, Wanda anyi bata hakuri takasa hakura,
Babu abinda take gani a idonta sai mijinta masoyinta da macce a kan jikinsa yana sakar mata murmushin da bai tab'a yimata irinsaba."
Kuka takeyi sosai tana doka kanta a jikin k'arfen gado dake saiti da kanta, tana fad'in bazai yiwoba sai a bayan raina."
Sallamar shigowar gimbiya Bilkisu sukaji tare da maimartaba mahaifin saudat Wanda labari ya samesu cewar Saudat ta yanke jiki ta fad'i itama tana asibity a kwance,
Shine suka biyo jirgi hankali a tashe suka iso yanzun nan."
Saudat tana ganin shigowar mahaifanta ta mik'e da sauri ta cire ruwan dake jone a hannunta ta nufi wurin mahaifiyarta ta rungumeta ta kuma sakin kuka mai sauti, tare da furta na shiga ukuna mommy mutuwa zanyi."
[3/30, 9:56 PM] Hayat: *DAN SARKI SAUBAN*
*Writing by*
*Ummu Safwan*
( _Fareeda Basheer_ )
*41*
"Bazaki mutuba inji gimbiya bilkisu ta janyo hannun saudat suka zauna a gefen gado ta shiga share mata hawaye,
Meyake damunki meke faruwa?
Nasan Ko baki fad'aba matsalarki d'aya ce Sauban,
Meya maki meyake faruwa?"
Kuka saudat ta kuma fashewa dashi Wanda ya janyo hankalin mahaifinta da sarki Wanda suke tsaye a gefe d'aya suna gaisawa
Lokaci d'aya Suka juyo tare suna kallonta,
Mahaifinta ya matso kusa gareta yana fad'in Saudat sannu ki daina kuka ba'ayiwa ciwo kuka Allah zai baki lafiya,
Ya juya ya kalli sarki dake tsaye a gefe d'aya yana kallonsu,
Yace " Ashe jikin nata da sauki sosai, dana san hakan Zan sameta da banzo da kainaba,
sai dai na turo mahaifiyarta ta dibata, saboda inada aiki mai tarin yawa na ajiye nazo,
lokacin da labari ya samemu cewar ta yanke jiki ta fad'i, hankalinmu a tashe ido rufe muka iso, Ashe da sauki sosai,
Ya juya ya kalli sarki yace wai meyake faruwa ne?me yake damunta?"
Itadai hajjah tuni tabar d'akin tun da suka gaisa da mahaifanta,
domin itama a halin yanzun jarabar kishin Saudat ya soma bata haushi,
Ba'a aure aka aureta?
Ko so takeyi yanda ubanta ya zauna da mata d'aya shima sauban ya xauna da ita kad'ai,
To uwarta tafi k'arfin ubanta shiyasa ya kasa k'ara aure,
Tunda tarigada ta magance shi shiyasa yake tsoron yai Mata kishiya,
To sauban yafi k'arfin sihirinsu domin tinda aka haifeshi na d'auki mataki a kansa sai dai a buga a barsa ba wata shegiya da zataci galaba akansa indai ba Alheri a tare da ita."
Sarki ya kalli mahaifin Saudat yasaki murmushi yace mutafi waje zamuyi magana,
Hakan suka jera suka fita suna hira cikin farin ciki, kasancewar akwai kyakkyawar fahimta a tsakaninsu."
"Gefe d'aya sukaja suka tsaya,
Wata sabuwar gaisuwar suka soma,
Mahaifin saudat yake tambyar yaya jikin sauban da fatan andace ansami abinda yakeso."
Murmushi Sarki yayi, yace "Alhmdulillah sauki yasamu,
sakamakon nemo masa yarinyar da akayi,
Ashe ita yarinyar 'zaman 'ya take a garemu, 'yar gidan Alhaji Habib Naira ce,
Wanda ta b'ata tun tana k'arama,
Allah ya kaddara ya gane yarsa,
itace safna wacce sauban yake so."
Alhmdulillah mahaifin Saudat yace "tare da cewa komai yazo gidan sauki kenan,
Yanzun abinda za'ayi a gaggauta a d'aura masu aure shikenan hankalin kowa sai ya kwanta."
Shuru Sarki yayi baiyi maganaba,
Mahaifin Saudat ya d'aga kai ya kallesa yace yanaji kayi shuru ko akwai matsala ne?"
Sarki ya sauke ajiyar zuciya yace "akwai matsala."
"Matsala kuma daga ina?"
Wacce irin matsala kuma?"
Sarki ya kallesa yace "dalilin ganin safna da Saudat tayi a tare da sauban shine yasaka ta yanke jiki ta fad'i batare da ta saniba."
Abokina kafi kowa sanin mata suna da tsananin kishi zasu iya aikata komai a kan kishiya,
Banason Saudat ta shiga cikin wani hali akan auren safna da sauban zaiyi, Dan hakan nake tunanin akwai matsala anan gaba kodai a fasa."
"Ita d'in banza inji mahaifinta,
Akan kishinta na banza za'a hana yaro auren wacce yakeso?"
To bata isaba idan kaga sauban bai auri Safna ba to sai dai idan Allah ya rubuta ba matarsa bace, amma akan bak'in kishi na Saudat Wanda ta gada a wurin uwarta bata isa ta hanaba,
to bari kaji koni nan mahaifinta neman Aure nakeyi ban fad'awa kowa ba sai kai,
a halin yanzun Zan cen danake maka jiyan nan aka kaimun laife, so nakeyi sai an d'aura auren sannan kowa zaiji bayan ankawomun Amaryata cikin gidana, illaso duk Wanda zai fad'i ya mutu sai dai ya mutu a kan masifar kishi,
haba zama zanyi na mutu da mace d'aya to asirin da ake cewa anyimun yanzun ya karye hud'u zan aura domin inda buk'atarsu a matsayina na sarki?
Dariya Sarki yasaki ya bashi hannu suka tab'a yana fad'in "Ashe wannan karon abokina ya turza, ai duk a tunanina bakada lafiya shiyasaka ka zauna da macce d'aya."
"Mahaifin Saudat yana dariya yace " lafiya ta k'alau, zaku tabbatar da hakan idan na ajiye hud'u shekara ta zakagayo duk kuka gansu d'auke da ciki."
Suka kuma sakin wata dariya,
Mahaifin Saudat yaci gaba da cewa "Allah danasan ciwon kishine da ba abinda zai sanyani nazo,
Sai dai na turo mahaifiyarta tunda a wurinta taji wannan shegen kishin na tsiya."
Auren sauban kuma ba abinda za'a fasa ba barama kaji baxan bar garin nan ba sai natafi da kaina na nemo masa aure a wurin Alhaji Habib duk dai komai ya zama
Na gida, idan aka tsayar masa da rana sannan hankalina zai kwanta sai na koma gida"
Sosai sarki yaji dad'in kalaman abokin nasa koba komai yasan Alhaji Habib idan yaga idon sarki Abdulrahaman zaiji nauyi da kunyar aikata abinda yayi niya saboda akwai yarda da Amana a tsaninsu,
Dan ya tabbata idan ba atare suka tafiba akwai d'aukar fansa a cikin idon Alhaji Habib akansa."
*******************
A can d'akinsu Saudat kwance take akan jikin mahaifiyarta sai kuka takeyi mahaifiyarta tana lallashinta tare da share mata hawaye,
so takeyi hankalin 'yarta ya kwanta ta fad'a mata damuwarta."
Bayan Saudat tayi shuru tare da Jan doguwar ajiyar zuciya,
Tamik'e zaune tana kallon mahaifiyarta wacce take tambyar wai meke damunta KO sauban ne ya mutu?" Ta girgiza kai alamar A'a ciwonsa ne yayi tsanani ta girgiza kai alamar A'a to meyake faruwa ne?" Hawaye suka kuma zuba a idonta
Tabud'e baki cikin sigar kuka tace "mommy yarinyar nan bata mutuba,
Yanzun hakan suna tare a wuri d'aya akan gado d'aya a cikin asibityn nan tare da sauban."
ta fashe da kuka mai sauti tana fad'in a gaban idona suka Rik'e hannun juna cike DA k'auna da shauk'i,
Mommy a gaban idona wata macce take bawa mijina ruwan Te a baki, idonsu sarke dana juna suna kallon k'auna."
Ta dafe zuciya tace "Mommy Mutuwa zanyi idan sauban bai rabu da yarinyar nan ba."
Zaro ido mommy tayi cike firgici domin jitakeyi zuciyarta tana harbawa tamkar itace akayiwa wnn cin fuskar,
Jitakeyi kamar mijinta ne ta hango tare da wata kamar yanda saudat ta fad'a Mata."
"Karya ne wlh idan inada rai ina numfashi a doron k'asa sauban bai isa yayi wani aurenba,
cin fuska 'yata a gaban idonta, Ina raye a doron k'asa, baxai yuwoba wallahi, yanda yabar shan nonon uwarsa hakan zai bar shegiyar yarinyar nan har abadan duniya koda zai mutu"
Zabura Saudat tayi tace "A'a mommy banda mutuwa banason ya mutu."
A harzuk'e mommy ta dubeta cikin masifa da b'acin rai tace "yimun shuru shasha sha, to bari kiji da mijinki yai maki kushiya gara ya mutu, kiyi sunan ke kad'aice a wurin mijinki har ya mutu ya barki,
sakarai wacce batasan inda yake Mata ciwoba, idan Kika sanya tausayi a ranki, Kika bari ya auro maki shigiya marar asali kinshiga uku kashinki ya bushe, domin kuwa saikin zama banza a wurinsa, don ita shegiya gadon bariki tayi tun a wurin mahaifanta tunda a kan hanyar bariki aka haifeta, Dan hakan koda zata shigo gidanki, tariga da tasan komai tun a kan hanyar bariki tayi wayo,
kinaji kina gani sai dai ki Koma gefe kizama 'yar kallo, domin kina gani da rayuwarki a gaban idonki wata shegiya tsintattaciyar mage ta karb'e maki mji, dama ba sonki yakeyi kece kike sonsa."
Saudat ta d'aga ido ta kalli mahaifiyarta tace "mommy inaji ana fad'a cewa wai angane iyayenta."
Mere baki mommy tayi tace 'yar wacece a cikin garin nan suwaye mahaifanta a cikin garin Adamawa."
Saudat tace "Naji ana fad'ar wai ko 'yar wani Alhaji Habib Naira ce wacce ta b'ata tin tana jaririya."
Gaban mommy yabada dam,
Ta zaro ido waje tana tunanin kaddai a ce 'yar Hajiya Laila ce wacce ta b'ata tun tana jaririya, itace Safna."
Hajiya Laila babbar Aminiyarta ce,
Itace take sayar mata da kayan sakawa tare da turarunka masu k'amshi da kayan mata,
Hajiya Laila itace ke koyamata yanda zata gyara jikinta a koda yaushe yazamana tana cikin k'amshi, da tsafta
Ita ke d'orata a kan hanyar da zata mallaki mijinta ita kad'ai batare da ya hango wata a waje ba, ko da ya hango wata d'in bazatayi tasiri a wurinsa ba."
Tirk'ashi da 'yar gidan Hajiya Laila Saudat zatayi kishi?🙆🏻 kaddai ace 'yarsu SUHAILAT wacce b'arayi suka sace itace takoma Safna."
Tirk'ashi, Ta tabbata duk abinda takeji Hajiya Laila tafita jinshi,
Ita batabin malamai da bokaye, makirci da kisisina Mai had'e da tsaftar ciki data waje shi take amfani dashi wurin tafiyar da mijinta, gaba d'aya ya rud'e akanta bayajin kunyar ko a gaban kowaye ya nuna mata tsantsar soyayya da k'auna."
Ta juya ta kalli Saudat wacce itama, ita take kallo cike da mamakin ganin jikin mommy yayi sanyi a lokaci d'aya."
[3/30, 9:56 PM] Hayat: *DAN SARKI SAUBAN*
*Writing by*
*Ummu Safwan*
( _Fareeda Basheer_ )
*43*
Yana gama fad'in hakan ya juya ya koma ciki, zuciyarsa
Cike da murnar ganin abokanansa musamman Sarki Abdulraham Wanda ya dad'e basu had'uba sai dai a waya."
Yana shiga ya Tarar da Hajiya Laila ta shek'a wani irin wanka Mai firgitarwa sai k'amshi take zubawa,tsayawa yayi cak yana kallonta tare da kashe mata
Ido d'aya ya taka sannu a hankali zuwa gareta ya janyota zuwa jikinsa yashiga shisshinarta a duk inda yaci karo dashi bakinsa a kunnenta cikin wani salo yake fad'a mata,
Sarauniyar mata munyi manyan bak'i fa suna falo zaune."
Fari tayi da ido cikin wani salon, tace suwaye sukazo mana kai tsaye batare da sanarwa ba."
Dogon hancinta yaja yana murmushi yace "surunki kine Sarki Abdullah tare da Abokina, Sarki Abdulraham."
Yana murmushi yake cewa "Nasan dalilin zuwan nasu,
surinki ne
yaji tsoro, sosai wnn dalilin yasa ya janyomun sarki Abdulraham ya Kai k'arshen maganar yana dariya."
Had'e hannu biyu tayi wuri d'aya alamar rok'o👏🏻 tace "ina kuma rok'awa surukina afuwa tuba yakeyi ayi hakuri komai ya wuce a saka masa rana."
Zaro ido yayi yace "dawuri hakan?"
Ko Jan aji babu?"
Kinmanta lokacin da natura Neman aurenki sai da aka jamun aji kamar nayi kuka."
dariya tayi tace "wato ramuwa zakayi a wurin abokinka kenan,
haba Alhajina komai ya wuce mana."
Murmushi yasaki yace kada kidamu, zan amsa duk abinda sukazo dashi da hannu biyu biyu"
Ya juya yanufi toilet yayi wanka ya shirya cikin dakakkiyar shadda sai k'amshi yake zubawa yanufi babban falon saukar bak'i."
fad'in tsaruwar falon da kyansa b'ata lokaci ne
Cikin farin ciki da dariya mai cike da murna suka tarbi junansu suka gaisa tare da barkwance a tsananinsu."
Anan take aka cika masu gaba da kayan motsa baki,
wannan hikimar Hajiya Laila ce."
Bayan sun kamallah motsa baki tare da ciye ciye, suka sake sabuwar gaisuwa,
Sarki Abdulrahaman yake tambayar Alhaji Habib yaushe gamo sai dai a waya."
Murmushin farin ciki kawai Alhaji Habib yake suna tsokanar junansu,
Snn Sarki Abdulrahaman ya fara da cewa "Ina tayaka murna, ko nace muna taya junanmu murna ganin 'yarmu da akayi cikin k'oshin lafiya,
Alhmdulillah nayi farin ciki sosai danasami labarin bayyanar 'yarmu Suhailat Allah ya tsare gaba ya kauda kaddara."
"Ameen suka amsa gaba d'aya falon cike da farin ciki,
Snn Sarki Abdulraham yaci gaba da cewa,
Sai kuma naji labarin d'anmu Sauban shine ya taimaketa a lokacinda take cikin kunci da damuwa
Daga k'arshe ya fad'a cikin tsananin sonta Wanda har yakaishi da kwanciya a asibity,
Hak'ik'a nayi farin ciki da jin wannan labarin domin duka abin d'aya ne sauban da Suhailat duka 'ya'yanmu ne tuwona maina,
Wannan labarin danaji yasakani farin ciki sosai Dan hakan nace Sarki ya rakoni wurinka na nemawa sauban auren Suhailat a wurinka."
Shuru Alhaji Habib yayi yana kallonsu yana sakin murmushi, domin yarasa abinda zaice."
Sarki Abdullah ya amshe maganar da cewa,
Abokina ka manta da komai a ranka,
Ka manta da kalaman danayi a baya duk rashin sanine, Wanda nayi nadamar fad'ar hakan, tabbas nayi kuskuren banbata d'an sunnah da d'an kan titi,
a lokacin baya idona ya rufe akan son Kaina danayi,
Amma yanzun na hankalta na fahimci abinda kake fad'amun nagane d'an kan titi da d'an sunnah duk d'ayane a wurin Allah basuda wani banbanci,
Banbancinsu d'aya ne shine Wanda yafi wani jin tsoronsa."
"Alhmdulillah Alhaji Habib yace "yana murmushi domin ko d'aya bai Rik'e Sarki a ransaba dama hakan yakeso yaji a bakinsa,
Yanason yagane ko ba'a kan safna ba, ko anan gaba zai gyara kuskurenshi, ya fahimci d'a na kowa ne ba'a kyamatar d'a a duk inda yake."
Ya dafa kafad'ar Sarki yace komai ya wuce abokina Allah ya tsare gaba yana murmushi ya kallesu gaba d'aya yace Suhailat Ai 'yarkuce zaku iya zartar da hukunci akanta sauban shine nawa Dan hakan ni zan karb'ar masa aure a wurinku."
Alhaji Habib ya kalli Sarki Abdulrahaman yace "Ina nemawa d'ana auren 'yarka domin yaganta yanaso Kuma sun fahimci juna "
Sarki Abdulrahaman yace naba d'anka auren yata Suhailat,
Ka kawo sadaki a duk lokacin da ka shirya Zan d'aura masu aure."
Sarki Abdulrahaman yace "nasaka ranar aure wata uku basu zuwa shin ko hakan yayiwa d'anka?"
Alhaji Habib yace 'dana a shirye yake KO yanzun za'a d'aura bayada matsala,
Suka saki dariya gaba d'ayansu Mai cike da farin ciki,
Sarki Abdullah akan farin ciki jiyayi kamar ya zubar da hawaye,
Hakika babu abinda zai cewa wad'an nan abokanai nasa sai godiya da sanbarka Allah ya kara masu dankon Aminci da k'aunar juna."
Hakan sukayi firarsu daga k'arshe sukayi sallama,
Tare da tabbatar juna cewa an saka ranar,auren Sauban da Safna wata uku masu zuwa."
Ko wanne yana farin ciki yashiga motarsa,sunayiwa juna fatan Alheri,
Duk abinda akeyi Hajiya Laila tanaji kasancewar sautin maganar da sukeyi yana kaiwa a falon da take a zaune,
Tayi farin ciki sosai dajin duk abinda ke faruwa da hukuncin da suka zartar sanya ranar aure nan da wata uku,
Shigowar Alhaji Habib kenan fuskarsa cike da farinciki Hajiya Laila ta tarbeshi ta rungumeshi tare da zuba masa kirari Wanda kesakashi farin ciki,
Anan take kan Alhaji Habib ya juya da tsananin bukatar matarsa ya duk'a ya d'auketa yanufi bidrom da ita."
Domin yasan farin cikin da takeyi baya rasa nasaba da jin tattaunawar da sukayi da abokanansa Dan hkn bari ya kuma Sakata cikin wani farin cikin domin hakan shine burinsa."
*******************
Alhmdulillah jikin sauban yasami sauki sosai ya murmuje ba abinda yake masa ciwo saka makon Albishir da mahaifinsa ya masa na cewar an saka ranar aurensa ,wata uku masu zuwa."
Bai sauban kadai yyi farin cikiba duk wani masoyinsa saida ya tayashi farin ciki musamman Safwan da bakinsa yaki rufuwa."
Anan take likita ya bashi sallama, domin komawa gida."
Hakan itama Saudat jikin nata da sauki sosai duk da bawata matsala bace kedamunta bayan jarababben kishi dake cinta."
A ranar da akayi sallamar tunkafin sutafi gida Alhaji Habib ya iso asibity tare da Hajiya Laila,
Domin tafiya da Safna."
Sosai Sauban yashiga damuwa tafiyar da za'ayi da safna
Hajjah tashiga lallashinsa tare da tuna masa da cewa saura wata uku sukasance a cikin inuwa d'aya su zauna a tare zama na har Abada,
Sannan kafin zuwan lokacin duk lokacin da yakeson ganinta zai iya tafiya gidansu suyi zance yadawo,
Ya mutsa fuska yayi irin shifa ba abinda yake damunsa akan tafiyar da zatayi,
Dariya hajjah tasaki tana fad'in miskili kafi mahaukaci ban haushi."
Hakan suka saka safna a mota tare da yiwa sauban fatan Alheri suka tafi,
Ba sauban ba hatta da hajjah taji ba dad'i tafiyar safna
Domin a d'an za man da sukayi ta fahimci yarinyace Mai hankali da natsuwa tasami tarbiya mai kyau a wurin iyayenta,
Sosai ta kwantawa hajjah a rai Wanda take Addu'ar Allah ya nuna mata wata uku zata dawo cikin halinsu su zauna da ita zama na har Abada."
bayan tafiyar su safna,
Sauban yashiga tattara kayansa domin barin asibityn,
Hakan itama Saudat tare da mahaifiyarta wacce Sarki Abdulrahaman ya barta domin tayi jinyar yarta har zuwa lokacin da zata sami lafiya, suma suka shiga tattara kayansu dan barin asibityn."
A tare suka fito da sauban suka nufi wurin motocinsu suka shinshiga suka d'auki hanyar masarauta."
*********************
Kwanan mahaifiyar Saudat d'aya a cikin gidan sarautar ta had'a kayanta ta koma gida, cike da jimami da bak'in cikin ranar Auren da aka Sanyawa sauban da safna,
Hankalinta yakan k'ara tashi idan ta tuna da ko wacece safna 'yar Hajiya Laila ce."
Amma tasan hanyar da zatabi insha Allah idan har tana raye baza'ayi auren nan ba."
********************
Sosai hankalin gimbiya Jamila ya tashi a lokacin da labari ya sameta cewa sauban yadawo gida cikin k'oshin lafiya ya sami sauki sosai tamkar bai kwanta jinyaba,
Sosai tayi bakin ciki dajin wnn mummunan labarin domin duk a tunaninta asirin da