Showing 15001 words to 18000 words out of 86876 words
d'auki wayar Mana."
Cikin sauri ya Sanya hannu a Aljihu ya d'auko wayar,
Ganin sunan Abokinsa ne Wanda suka tashi a tare wato sarkin Bauchi Wanda mahaifinsa ya rasu aka d'orashi a kan kujerar mulkin,
Yana murmushin ya d'aga wayar tare da karawa a kunnensa da sallama a bakinsa, cike da tsokana Yake fad'in ranka ya dad'e sarki Allah ya k'ara maka lafiya ya kake?"
Murmushi Abdulrahaman yayi yace "yau Kuma 'yar zolayace "to kiranka nayi domin nayi maka Albishir Sarauniya ta haihu ansami 'ya macce."
Masha Allah Abdullah yashiga fad'i tare da cewa Ina kusa da Abba gashi ku gaisa sai ka fad'a Masa."
Jin hakan sarki yasan Abdulrahaman ne sarkin Bauchi yakira Abdullah domin shi kad'ai ne Yake kiransa Abdullah idan suna tare wani lokacin ya kan k'arb'i wayar su gaisa tare da lurar dashi akan abinda ya shege Masa duhu akan lamarin sarauta, kasan cewar mahaifin Abdulrahaman Amine ne a wurin sarki mahaifin Abdullah."
Sarki ya amshi wayar ya kara a kunnensa Yana murmushi bayan sun gaisa,
Abdulrahaman Yake fad'awa sarki anyi Masa haihuwa ansami 'ya macce,
Kasancewar matansa hud'u ba Wacce ta tab'a haihuwa sai yanzun."
Masha Allah sarki yace tare da fad'ad'a fara'arsa yashiga fad'in "Allah ya raya SAUDAT yasanya Mata Albarka."
Murmushi sarki Abdulrahaman yasaki domin yaji dad'in sunan da sarki yasaka ma 'yarsa, yashiga fad'in Masha Allah sunan yayi dad'i Abba Allah yak'ara girma da d'aukaka, tabbas ada nayi rashin mahaifi Amma a yanzun samunka duk ya kawar mun da Kashi hamsin a cikin d'ari na Rashin mahaifi da nayi, nagode Abba,
yashiga godiya sarki Yana amsawa Yana murmushi snn ya mik'awa Abdullah wayar."
Abdullah ya k'arb'a Yana fad'in sunan 'yarmu Saudat lallai Abba ya it's zab'en suna Mai dad'i, Allah ya raya Mana ita sai munshigo bikin suna gaba d'ayanmu."
Hakan sukayi sallama ya kashe wayar,
Snn yayiwa maimartaba sallama ya tashi ya fita cike da farin cikin gobe ne d'aurin Aurensa snn Babban Amininsa ya samu k'aruwar 'ya macce wacce sarki ya SAKAWA suna "SAUDAT."
Washe gari ya Kama ranar juma'a kenan a babban masallacin k'ofar gidan sarki bayan an kammala sallar juma'a aka d'aurawa Abdullah Aure da bayinsa Khadija da Aishat, d'aurin auren da kowa ya shaida."
Wanda Jamila sai dai ta tsinci maganar daga sama bayan anyi komai angama,
Anan take sarki yasaka aka gyarawa kowa part d'inta kasancewar part 4 a b'angaren Abdullah,
Wnn aure ya ba k'anwata Jamila rai musamman da taji duk bayine aka 'yanta Kuma aka aurawa mijinta."
Jikinta baiyi sanyiba sai da safiya ta waye suka shigo gaida ita, anan taga zallar kyau da kwarji, batasan lokacin da idonta ya rufeba tashiga surfa masu ashar tare da korarsu daga b'angarenta."
Kasan cewar sun san halinta Sarai yasa ko wacce daga cikinsu hankalinta bai tashiba illah ma suka sakar mata murmushi suna fad'in Allah ya hushi zuciyarki, dama Yarima ne yace muzo mugasheki ba Wai yin kanmu bane,
suna fad'in hakan suka tashi suka bar Mata sashen nata."
Tabd'i jam Ashe tsugunne Bata k'are kenan tinda Abdullah ya auro wad'an Nan tsala tsalan Yan Mata tabbas tasan ko kallon banza a yanzun Bata ishesaba yo Mai zaiyi da ita Yana ganin wad'an Nan Yan Mata wad'anda bata inda Allah ya ragesu,
Ga wani sabon rainin wayo da suka zo Mata dashi cewar Wai Abdullah ne yace suzo su gaida ita, wato da baice suzoba bazasu zoba kenan, tabd'ijam lallai akwai aiki a gabana,
To ko Bintu da take jinin sarauta gaba da baya ta buga tabarni bareku bayin banza da aka 'yanta,
Ko Bintu da takeji da mulki tayi mun biyayya tabini da dason a zauna lafiya hakan bai sa naraga mataba bareku fitsararri bayin banza."
Ta d'aga murya tana kiran jakadiya! jakadiya!! jakadiya!!!"
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍
🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴
Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)
*DIDECTED TO Fateemah M Uthman*
*Page 10*
Cikin sauri jakadiya taxo ta tsuguna a gabanta tana fad'in "gani uwar d'akina Allah y taimakeki ya k'ara maki lafiya."
Jamila ta dubi jakadiya cikin b'acin Rai tace "kinada labarin abinda yake faruwa a cikin gidan Nan kuwa?"
Jakadiya ta Kuma rinsinawa tare da sunkuyar dakai tace "ranki ya dad'e uward'akina ban San komai ba, me Yake faruwa a cikin gidan nan?"
Jamila ta kalli jakadiya cikin jin haushi tace "
Ni wad'an Nan bayin banzan wad'anda aka 'yanta zasu ciwa mutumci a gaban idona." Ni zasu kalli tsabar idona su cemun Yarima Abdullah ne yaturosu wurina domin su gaida Ni,
wato suna nufin bayin kansu bane kenan tirsasu yayi, a matsayina na gimbiya,
Ta d'aga murya cike da b'acin Rai "k'arya ne wlh duk abinda suke tak'ama dashi nafisu jinsa" dubunsu sun buga sun barni baresu bayin banza da wufi."
Jakadiya tashi kitafi wurin bokanya ki fad'a Mata duk abinda ya ke faruwa, kada a kuskura a barsu su haihu a gidan Nan snn kifad'a Mata tasakasu a b'angaren masu Zaman banza a wurin mijina,
Sauran bayani idan Kika tafi kibani ita a waya zan iyar Mata dashi."
Jiki na rawa jakadiya tamik'e tare da k'arb'ar kud'i tafita tanufi k'auyen bokanya k'araba."
******************
Kwana biyu Kwanciyar hankali tare da natsuwa suka shiga Abdullah inda Yake samun kulawa daga wurin matansa Khadija da Aishat,
Wad'anda kwatakwata basa bin takan Jamila kula da mijinsu kawai sukeyi tare da hidimarsa, hakan itama Hajjah tayi farin cikin ganin yanda hankalin Abdullah ya kwanta sosai."
Ana hakan suka shiga shirye Shiryen tafiya Bauchi wurin bikin sunan 'yar da aka haifawa sarkin Bauchi."
inda Jamila ta shirya tsaf tare da yaranta da Abdullah suka nufi Bauchi biki akabar Khadija da Aishat a gida,
Wad'anda duk a tunaninsu tare dasu za'ayi tafiyar, kamar yanda Abdullah ya fad'a masu akan su shirya dasu za'a tafi, abin mamaki sai dai yakirasu a waya yace suyi hkr ya tafi da Jamila."
Kasancewar Jamila Abokiyar maijego ce sosai"
Basu nuna damuwarsu akan hakan ba illah sukayi Masa fatan Alheri tare da Addu'a'ar a dawo lafiya."
A b'angaren Hajjah bataso akayi tafiyar Nan tare da Jamila ba, saboda sanin halinta da tayi komai zai iya faruwa kafin su dawo."
A garin Bauchi anyi bikin sunan Saudat bikin suna nane na kece raini domin duk Wanda kagani Yana yawo a gidan bikin to jinin sarauta ne ko wanne Yanaji da mulki da Isa,,
Kasan cewar sarautar Bauchi sarauta ce wacce ake nuna tsantsar mulki da Isa tare a cikinta."
sosai Jamila ta yaba da kyawon Saudat inda anan take ta furtawa Mahaifiyar Saudat cewa,
A gaskiya Saudat yarinyar ta shiga raina sosai domin kyakkyawa ce,
Inama Zaki Bawa d'anki Sadeeq ita, domin nayi Masa sha'awar aurenta idan suka girma,
Murmushi Mahaifiyar Saudat ta sauke ta kalli Jamila tayi Mata kallon bakida hankali,
Tace " ai mijin Saudat ba'a K'ASAR Nan Yake ba, domin duk Wanda Saudat zata aura sai ya zamana yayi fice a duniya kowa ya sanshi a b'angaren kud'i da mulki to wnn shine mijin Saudat."
Dariya Jamila kawai tasaki domin idan wani mulki takeji Mahaifiyar Saudat ta shafeta domin ita matar sarki ce ita Kuma matar d'an sarki ce,
Snn idan kyau take ji dashi Mahaifiyar Saudat ta shafeta,
Hakan idan boka take tak'ama dashi Mahaifiyar Saudat tsafi takeyi, tsakaninsu Kar Tasan Karne,
Dan hakan komai rashin mutumcin Jamila tana shafawa Mahaifiyar Saudat lafiya."
Hakan dai suka kammala hidimar bikin suka dawo gida, inda tun a can ta dinga zubawa Abdullah surkullenta a cikin abinci da ruwan Sha Yana shanyewa batare da yasani ba."
Tin kafin su dawo jakadiya ta karb'o sauran ragowar maganin a wurin bokanya tashiga ai watar dashi a cikin gidan sak'o da lungu har part din su Khadija da Aishat."
Sun sauka lafiya Shigowar su cikin gidan sarautar a Nan take Abdullah komai nasa ya canza,
Baya son ganin kowa a duniya sai Jamila, a maimakon ya nufi d'akinsa domin ya huta Kai tsaye d'akin Jamila yanufa suka shiga a tare tana ganin hakan tasan aikinta ya faraci tashiga murmushi murna da farin ciki domin aikinta ya Fara tafiya a yanda takeso saura wad'an can bayin banzan tare da Sauban."
Tin shigar Abdullah d'akin Jamila kwana biyu kenan bai fitoba, hakan yasa sarki yashiga nemansa idan ya aiko kiransa sai Jamila tace "bacci yakeyi idan ya tashi za'a fad'a Masa, hakan Hajjah itama kwana biyu ta daina ganin Abdullah tashiga tambayar ko lafiya?",
Tana zaune labari ya risketa cewa ai Abdullah Yana Nan lafiyarsa k'alau Yana b'angaren Jamila kwanansa biyu bai fitoba ko lek'e, anan Yake Zaune Yana aiwatar da komai nasa"
Murmushi Hajjah tayi tace Akira Mata matan Abdullah Khadija da Aishat,
Bayan minti talatin suka shigo suka durk'usa a gabanta tare da gaida ita cike da biyayya da girmamawa."
BaYan ta amsa gaisuwarsu ne take tambayarsu Ina mijinsu yashiga kwana biyu?"
Shuru sukayi domin basa da amsar da zasu Bata,
Hakan ya tabbatar wa da Hajjah labarin da aka fad'a Mata gaskiya ne kenan,
Murmushi tayi tace kutashi kutafi kuci gaba da hakuri tare da Addu'a komai zaizo cikin sauki."
Cikin ladabi suka mik'e suka fita,
Hajjah na ganin fitarsu itama tamik'e tsaye tare da gyara Alk'yabbarta kuyanginta suka Mara Mata baya tanufi b'angaren Jamila, karo na biyu kenan da hajjah ta tab'a sanya k'afarta ta shiga b'angaren Jamila saboda Hajjah macce ce Mai k'awaici da Alkunya ga duk abinda ya shafi Abdullah."
Kai tsaye part d'in Jamila tanufa tare da sallama d'auke a bakinta,
Jamila tana kishin gid'e a kan kilishinta kuyanginta duk suna zagaye da ita ko wacce tana Mata hidima."
Mamaki Hajjah tacika dashi ganin yanda Jamila take shinfid'a mulki tamkar itace Sarauniya matar sarki,
Ko ita Bata abinda takeyi."
Ganin Hajjah yasaka Jamila mik'ewa zaune tana fad'in "sannu da zuwa umma."
Yawwa Hajjah tace cikin had'e fuska tare da nuna mulki da Isa,
Ta kalli Jamila tace "kirawomun Abdullah "
Jikin Jamila duk ya mutu saitaga Hajjah tayi mata wani irin kwarjini Wanda yasa takasa yimata musu ko jayayya illah ta mik'e tanufi d'akin da Abdullah yake cikinsa ,
A kwance ta tarar dashi Wanda aikin nasa kenan kwanciya yanaso yafita yarasa dalilin nasa na Rashin fitar
, Yana kewar mahaifansa da matansa Amma ya rasa dalilin da yasa baya da k'arfin gwarwar yunkurin fita,
Kallonsa tayi takashe Masa Ido d'aya cike da kissa tace "umma tana falo tanason ganinka tashi mutafi."
Jikinsa na rawa ya mik'e tare da sanya talkaminsa yafito falon,
Kallon juna sukayi da Hajjah yayi saurin zubewa k'asa kamar yanda yasaba ya gaida ita Yana murmushi."
Kallonsa takeyi cike da tausayi taga har ya d'an rame, tabbas Abdullah ya gad'u da shu'umar macce Azzaluma,
snn tasaki murmushi tana amsa gaisuwarsa ta dubeshi tace tashi mutafi inason magana da Kai, Bata Kuma bin takan jamila ba ta juya ta fita."
Jiki a sanyaye yabi bayanta suka nufi b'angarenta."
A gaban Hajjah yake zaune tana Masa fad'a bai tankaba illah ya sunkuyar da Kai k'asa,
" Abdullah meyake damunka ne?"
Ina kashiga kwana biyu mahaifinka yayi ta neman ka?"
Ka kuwa San halin da kajefa mahaifinka kwana biyun na Rashin ganinka bayan kasan baya iya yini d'aya batare da ya sanyaka ido ba,
kasancewar Kai kad'ai yake dashi,
Ina hankalinka da tunaninka suka tafi ne?"
Kana aikin me k'aidin macce da makircinta sukayi tasiri a kanka?"
Shin ko ka Manta cewa wata Rana Kai sarki ne Kai ne zaka gaji sarautar mahaifinka idan kace hakan zakayi wani kallo kake tinanin Al'umma zasu dinga yima ka?"
Meyasa kayi sakaci da Addu'o'e da mahaifinka Yake baka a ko wacce safiya domin kariya daga jikinka da lafiyarka?" nasan kwana biyun Nan ka daina gaba d'aya domin da kanayi da abinda ya Isa yayi tasiri akanka"
Dafe kansa yayi komai yashiga dawo Masa baya, yashiga karanto Addu'oe a cikin ransa tare da runtse idonsa."
Shuru Hajjah tayi tana kallonsa cike da tausayin sa
Sai da taga ya Fara samun natsuwa snn ta dubeshi tanuna Masa d'akinsa dake cikin babban falonta Wanda tin kafin yayi aure wani lokacin anan Yake kwana , tace tashi kashiga ciki kayi wanka ka canza Kaya, sann kayi Arwala kayi nafila raka'a biyu tare da karatun Alk'ur'ani,.idan ka gama ka karanta Addu'ar da mahaifinka Ya baka snn kafito katafi fada Yana nemanka."
Jiki ba kwari ya mik'e yanufi d'akin nasa domin ya ai watar da umurnin Mahaifiyar sa"
Ai Kuwa Yana kammala yin sallar had'eda karatun Qur'ani yaji duk wata natsuwa tashigesa anan take komai nasa ya dawo Wanda ya gushe Masa,
Karon farko matansa yashiga tunani ko lafiya sukeyi,
Meyasa meshi hakan Wanda kamar an mantar dashi komai, a kansa,
Bai gama samun natsuwa ba sai da yashiga karanta Addu'oen da mahaifinsa ya bashi na neman tsari daga sihiri,
Tare da warware sihiri a jikin mutum Koda anyi masa,
Sosai yasamu natsuwa BaYan ya kammala yinsu a Nan take ya dawo cikin hayyacinsa,
snn yafito Yana murmushi ya durk'usa gaban Hajjah yace "umma nagode hak''ika kin kubutar Dani daga duhu, insha Allah hakan bazata Kuma faruwa ba."
Murmushi tasaki tace "sakacinka ne Abdullah, ka daina sakaci da Addu'a domin kasan kana zagaye da makiya da ma hassada tashi katafi fada Idan kafito katafi wurin matanka domin kaji buk'atarsu ka lallashesu ka Kuma kwantar masu da hankali domin Suma sunshiga damuwa Allah yayi maka Albarka ya tsareka da sharrin masu sharri."
Ameen yace "had'ida sunkuyar da Kai ya tashi ya fita yanufi fada,
A fada ma hakan ta kasance nasiha sosai sarki yayita Masa, tare da bashi wani rubutu dake cikin gora ya shanye snn yak'ara Masa wasu Addu'oe
a Nan ya Kuma jinsa ya k'ara samun natsuwa snn yayi Masa sallama yafito,
Da kwarin gwaiwarsa had'ida natsuwa ya nufi sashen matansa wad'an kansu Yake a had'e suna zaune a wuri d'aya a cikin falonsa kasancewar anan suke Zama suna tattauna matsalarsu da yanda zasu b'ullowa Jamila."
Jin sallamarsa yasa suka saki murmushi suka mik'e gaba d'ayansu suka tarbeshi tare da yimasa sannu da zuwa"
Rungumesu yayi ya sunbaci ko waccen su a goshi snn ya Rik'a hannunsu suka zauna a tare a wurin d'aya suka sakashi a tsakiya,
Karon farko hakuri ya Fara basu,
Tin kafin ya iyar suka tareshi cikin kissa suna lallashinsa tare da kwantar Masa da hankali."
Snn daga k'arshe suka gabatar Masa da abincin tare da kayan ciye ciye."
Murmushi yakeyi Yana godewa Allah Akan ni'imar da yamasa na iyaye na gari da Mata na gari,
BaYan yaci abincin ne ya janyo su zuwa jikinsa yashiga kwantar masu da hankali cikin hikima Yashiga basu hakuri."
Kwana biyu komai Yana tafiya dai dai inda Abdullah baya Wasa da ibadarsa tare da Addu'o'e hakan yasa komai ya kwancewa Jamila sai kisan kud'i takeyi ba biyan buk'ata,
Anan ta yanke shawarar janyo kowa a jikinta cikin siyasance har ta cin ma biyan buk'atarta,
Babu abinda yafi d'aga Mata hankali irin yanda taga Abdullah yadawo kamar Abdullah sa na da Wanda tasani, baya shakkarta snn duk abinda zaiyi Mata Kai tsaye Yake Mata , batare da wani dibanya ba ko shakka
Snn ta lura da yanda Yake matuk'ar ji da matansa fiye da ita, domin idan Yana tare dasu baya buk'atar kowa ya rabesa, ba kamar ita da yake Allah Allah safiya ta waye yabar d'akinta snn ko a wurin kwanciya sai dai idan itace ta nemesa."
Snn ga SAUBAN yaron shima komai nasa sai dad'a ci gaba yakeyi, a yanzun Yana aji d'aya a secondry school komai nasa sai dad'a ci gaba yakeyi,
Ita Kuma nata yaran suna Nan a yanda suke komai nasu sai dad'a yin baya yakeyi Wanda har taji haushin hakan ta ciresu a makarantar gaba d'aya tafi buk'atar a Kira malamai a gida a karantar Mata dasu tana kallo."
Dan hakan kowa ya zira Mata Ido akan yaranta daga ciki kowa har da Abdullah Wanda take nuna Masa tamkar bashi ne mahaifinsu ba."
To bare Hajjah wacce da yaran da rashinsu duk d'aya ne a wurinta,
Shi Kuma sarki Yana fada ba komai yake sani Yana faruwa a cikin gidaba saboda a kwai Sarauniya ita ke gudanar da harkokin gida."
Sauban yarone Wanda Yake matuk'ar son zumunci da Yan uwansa, hakan yasa da zarar ya dawo daga makaranta Yake fita Hajjah Bata saniba Yake zuwa part din Jamila wurin Yan uwansa,
Hakan zaije ya zauna Sadeeq yazo wurinsa ya zauna sauban yayi ta koya Masa karatu,
Tin Jamila tana kyamatarsa har ya Kai ta farajansa a jiki domin cikar burinta."
Wata Rana yazo wurin Yan uwansa bayan sun kammala karatu, Jamila ta zubamasa abinci tace gashi yarona zauna kaci yau kahuta da cin abincin hajjah,
Girgiza kai yayi yace "nagode mommy."
Sai a lokacin Sadeeq ya Masa magana duk da ba wata magana yake masaba ko zuwa yayi Sageer kawai Yake kulashi,
Yace haba Yaya Sauba kaci abincin mana, na lura bakacin abincin mommy idan ta baka."
Sauban yayi murmushi yace "ba hakan bane Sageer na koshi ne shiyasa Amma zanci ko kad'an ne."
Ya k'arb'i abincin ya faraci cokali biyu yayi ya ajiye yace "Alhamdulillah had'ida mik'ewa tsaye yace "natafi Y'an'uwa na sai da safenku."
Tafiya yakeyi ya farajin cikinsa Yana hautsinawa Yana daf dashiga b'angaren Hajjah ya yanke jiki ya fad'i, sai kunfa yake fita a bakinsa."
Da gudu bayi suka nufi wurin Hajjah suka fad'a Mata cikin Azama tafito ta tarar da Sauban gaba d'aya ba rai a jikinsa, cikin sauri takira sarkin mota aka nufi asibity dashi "
Da Gaggawa likitoci suka amshesa suka shiga bashi taimako cikin gaggawa,
Sai da aka d'auki lokaci Mai tsayi snn aka samu nasarar ceto rayuwarsa,
Inda duk aune aunen da likitoci sukayi sun rasa gane abinda yaci, Kuma ga duk kan alamu bincike ya nuna akwai abinda yaci Wanda ya haifar Masa da wnn matsalar wacce da ba'ayi saurin kawo shi asibity ba da sai dai ya rasa rayuwarsa ."
Hankalin kowa ya tashi da Jin hakan inda Hajjah ta tabbatar da Sauban bayacin abincin kowa a gidan sai nata
Ko natan sai Wanda ta dafa da hannunta,
To a Ina yasami abinci yacin da yaci?"
Hakan sarki shima hankalinsa ya tashi matuk'a tare da Abdullah, Wanda sai bincike sukeyi a inda Sauban yaci abinci snn menene aka zuba Masa a cikin abincin."
Jamila taji dad'i sosai dajin