Showing 30001 words to 33000 words out of 86876 words

Chapter 11 - DAN SARKIn SAUBAN COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

7411

ne?"
Tabbas tasan bilkisu hatsa bibiyace, da duk wani abinda take tak'ama bilkisu ta shafeta, idan tana karama da mulkin miji bilkisu har gobe ita kadai ce a wurin mijinta. Bata da kishiya idan tana tak'ama da mulkin cikin gidan kujerar Saudat ta mulki ta cunawa kujerar ta,
Idan tana tak'ama da bokaye bilkisu tsafi takeyi tabawa bunki jini ya Sha."
Tayi saurin kaiwa zaune ta d'ora hannu a hab'a🤔 tana tunanin Allah yasa ba'ajalinta bace Saudat aka kawo a cikin gidan nan"

Tin daga lokacin Jamila Koda Wasa Bata kallon Saudat da sunan jefa Mata habaici ko wata magana, inda Saudat take batabi ta wurin ta wuce snn mulki a cikin gida tanayi Saudat nayi ba Wanda ya Isa ya takura wani,
Dan mulkin Saudat yafi karkata Akan mijinta saboda tana son mijinta tana Kare Masa lafiyar sa, duk abinda tasan Sauban Yana buk'ata da kanta take Masa hatta abincinsa da kanta take girka Masa kofin ruwansa ba wata kuyanga ko baiwar da ta Isa ta Sanya hannu ta tabashi idan Bata hukuntataba,
Hakan da zarar Sauban yafito daga b'angarensa bayi da kuyangi suke sunkuyar da Kai k'asa suna Mai gaisuwa a garesa har sai lokacin da yawuce snn suke daga kansu,
Domin duk wacce tasake ta kallesa bare ta kalle kayan da yasaka hukuncinta na daban ne."

_Saudat kina wuta_🤙

Sosai hankalin hajjah ya kwanta tare da maimartaba domin Sauban Yana samun kulawa a wurin matarsa."

Wanda sauban duk abinda takeyi baya gaban sa domin kallon marar tarbiya Yake Mata wacce take azabtar da bayinta hakan Yana tsananin K'ona Masa Rai
Wanda shi mutum ne Wanda yasan darajar Dan Adam."

Aurensu da wata uku ya shirya ya koma England domin ci gaba da karatunsa,
Yabar Saudat a Nan wacce Bata damu da tafiyar tasa ba saboda akwai Mata a kusa da ita wad'an sai ta darje domin biyan buk'atar ta."

Komawarsa makaranta asirin wasu daga cikin fadawan masatautarsu ya Toni inda sukaje makaratar su Sauban suka kaiwa shugaban makarantar kud'i har miliyan goma Akan duk Sauban yayi jarabawa ya dinga zubar dashi."

Shugaban makarantar baiyi k'asa da gwaiba wurin Kiran jami'an tsaro aka catke Masa su, dama sunyi magana da sarki Abdullah da zarar irin hakan ta faru ya d'aga waya yakirashi zaizo yaga wad'anda sukeyiwa Sauban wnn zalincin, na mayar dashi baya a karantunsa."

Washe gari sarki Abdullah ya duro k'asar inda aka kaishi wurin mutanen abin mamaki fadawansa yagani wad'anda yayi matuk'ar yarda dasu,
Abin ya d'aure Masa Kai tare da Sanya shi cikin rud'ari, hakan ya bada umurni ayi ta dukansu har sai sunfadi Wanda yasakasu,
Duka akayi masu sosai Amma basu fad'aba daga k'arshe da kansu suka Sha guba suka mutu domin dama aikin sai da rai suka fito mutuwa ko rayuwa."

Sarki yayi bakin cikin mutuwar tasu hakan yasaka aka rufeso yabaro k'asar tare da yiwa shugaban makaranta godiya,
Tin daga lokacin sauban yasamu dama da Kwanciyar hankalin yin karatunsa har yasamu nasarar kammalawa shekara D'aya da ta rage Masa yadawo gida Nigeria Cike da murna da farin ciki."
kamar yanda kuka gani a cikin page 1 yanda ake murnar dawowar tasa."






_Mu Koma Kan labarinmu na baya muka had'e a page 15_



_idan ba comment yasin sai kunyi sati daya ba posting_🤒





*Mrs Ana's Bawa*✍
[8/2, 7:31 AM] Hayat: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍



🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*Page 15*




_hmmmm mutum mutum sai Allah🤔 Ina kallonku masu Kan kwakwa aci gaba da zuwa Rafi wata Rana tulu zai fashe 'yan bu........._🙊




_Cigaban labari_
Da kyar ya samu asuba tayi sai sak'awa yakeyi Yana kwancewa Akan Saudat,
Gaba D'aya zuciyarsa a dagule take, Wanda yarasa dalilin hakan,
Hakan jiki ba kwari ya fad'a toilet yayi wanka tare da d'auro Alwala yafito yanufi masallaci domin gudanar da sallar asuba."

Sahu D'aya suka jera da maimartaba mahaifinsa, Bayan sun kammala yin sallar ne suka fito a tare suka jera suna ,
Tafiya suna Hira cike da burgewa suka nufi b'angaren sarki,
sarki Yana tsananin son d'ansa Sauban saboda hankalinsa da tunaninsa ga ibada Wanda duk iya Zaman da yayi a turai bai Sanya ya zubar da Addininsa da Al'adarsa ba,
Yana jijjina tarbiyar Sauban tare da yaba Masa duk da baiyi rayuwa a cikin masarauta ba Amma yafi sauran yaransa Sadeeq da Sageer tarbiya da son Addini, wad'anda kafin ka gansu sunfito sallar asuba a masallaci ma wuyacin Abu ne,
Wani lokacin har sai ya shiga da kansa b'angaren nasu ya tayar dasu Daga bacci suna kunkuni suna komai snn suke fitowa massalaci ayi sallar dasu,
Sab'anin Sauban Wanda in har Yana garin Nan sahu. Daya suke Zama dashi ko wacce sallah wani lokacin har shi yake tayar dashi idan yarigashi fitowa, hakan ba k'aramun Burgesa yakeyi ba tare da sanyashi farin ciki,
yasan ko yanzun ya fad'i ya mutu ya bar magajinsa Wanda zai rik'e Al'umma da gaskiya da Amana ga Kuma Addinin."

Tafiya sukeyi a jere sai da Sauban ya Kai sarki har cikin d'akinsa ya zaunar dashi a kan kujera snn ya D'uk'a a gabansa cikin girmamawa yana fad'in "ABBA barka da asuba Ina kwana."

Murmushi sarki yasaki Yana kallon d'an NASA mafi soyuwa a ransa, yace "barka Kade magajin sarki, katashi lafiya ya kwanan iyali?"

Sunkuyar da Kai Sauban yayi cike da jin kunya yace "lafiya k'alau Abba."

Cikin zolaya Abba Yake kallonsa yace "Alhamdulillah tinda ka kammala karatunka lafiya hankalina ya kwanta muna fatan result Dinka shima zaiyi kyau, kamar ynda muke hasashe
Yanxun Abu D'aya nakeso a wurinka shine kabani jika,
Inaso Naga zuri'arka a doron k'asa tin kafin mutuwa ta daukeni, Wanda nasan burin Hajjah Kenan itama taga d'an jikanta mafi soyuwa a ranta."

Sunkuyar da Kai Sauban yayi cike da jin kunyar maganar Abba,

Abba yasaki dariya ganin Sauban yanajin kunyar maganarsa yace "Ina ganin wata k'ila d'ana Sauban baya da wani kuzari a wurin iyali,
tabbas sai na gana da jakadiya domin naji tabbas kuwa tana baka dauri kana Sha."

'yar dariya sauban yasaki ya sunkuyar da Kai cike da jin kunya,
A zuciyarsa Yana fad'in dama ruwan zafin da Anna take kawo Masa masu kamar wani ganyen magani ta tsareshi a gaban idonta tace Dole sai ya shanyesu a she akwai wata manufa a cikinsu,
Dan hakan yakeji da zarar ya shanye ciwon Mara Yake sanyoshi a gaba har sai ya Kai da Shan ruwan Lipton da lemon tsami snn yakejin saukin jikinsa."

Sarki ya katseshi da fad'in "Allah yayi maka Albarka Sauban tashi katafi wurin iyalinka."

Har zai Mike ya kuma komawa ya zauna ya d'an runsuna yace "Abba yau ne nakeso zan tafi gidan gonata tare da Safwan domin mukai ziyara daga can inaso zan wuce masarautar zamfara domin mukai gaisuwa. "

Murmushi sarki yayi "yace Allah ya taimaka tabbas kayi tinani Mai kyau na zuwan naka zamfara ziyara idan katafi kace Ina gaida sarki Abdulmalik."

Zan fad'a Masa insha Allah inji Sauban snn yayi Abba sallama yafita."

Kallo sarki yabi bayansa dashi cike da k'aunar sa tare da sauke murmushin farin ciki Yana godiya ga Allah da yabashi d'a nagari Wanda yafito a tsatson tarbiya."

*******************

A d'akinsa shiri yakeyi cikin wata dakakkiyar shadda milk colour Wacce tasha aiki a jikinta ya d'auko hula yasaka itama milk colour agogonsa na gwal wanda sai kyalli yakeyi ya d'auko daga Kan madubi ya d'aura Akan tsintsiyar hannunsa, ya tsun hannunsa guda uku suke sanye da zoben azurfa da zinari Mai shegen kyan gaske sai kyalli sukeyi,
talkaminsa ya saka Suma milk colour ya Kuma feshe jikinsa ta turarensa Mai dad'in k'amshi,
kansa ya kalla a madubi Yana gyara Zaman hular kansa,
tabbas Sauban yayi kyau iya kyau domin kuwa dama kyakkyawa ne."

K'arar bud'e k'ofa yaji anshigo tare da sallama ko ba'a fad'a ba yasan Saudat ce,
Amsa sallamar yayi yaci gaba da shirinsa,

d'auke take da tiren break fast nashi,
Itama Tasha ado cikin wani leshi Wanda ya amshi jikinta sai kamshi take zubawa dama Saudat gwanace a wurin kamshi."

A jiye tire tayi a kan d'an matsakaicin dining table dake cikin d'akin, Wanda Yake Zama akai yake cin abinci wani lokacin."

Tana ajewa taJuyo ta tanufeshi tana kallonsa cike da sha'awa tare da matsananciyar k'aunarsa Mai cike da sonshi da yake fisgarta,
A gabansa taje ta tsaya tare da rik'o hannunsa duka biyun ta d'an sunkuyar da kanta saiti fuskarsa tana kallon cikin idanunsa,
k'amshin turarensa ya daki hancinta tayi saurin lumshe ido, ta furta kayi kyau mijina Ina Alfahari da Kai."
had'e fuska yayi ba alamar dariya a tare dashi."

Ganin hakan ta saki hannunsa ta d'an ja baya ta had'e hannuwanta wuri D'aya tana kallonsa👏🏻 tace "Sadaukina Ina kwana?"

Murmushi ya D'an saki Akan lab'b'ansa domin taso tasakashi dariya yace "lafiya k'alau kintashi lafiya?"

Murmushi tayi na farin ciki, tace lafiya k'alau break fast Yana jiranka komai ya kammala."

Baiyi magana ba ya dubi agogon hannunsa yaga k'arfe 10am lokacin break d'insa yayi ga lokaci Yana tafiya har yanzun safwan baizoba bai Kuma kirashiba, Kai tsaye wurin dining table din yanufa,
Cikin tafiyarsa ta k'asaita, hakan tabi bayansa kowa Yanaji da mulki Yana yawo a cikin jinin jikinsa,
tana ganin ya zauna akan kujera itama taje ta zauna a kan kujerar dake kallonsa,
tashiga zuba Masa duk abinda tasan Yana buk'ata ruwan te sune farko."

D'auka yayi ya Sha Yana lumshe ido,
zuba Masa Ido tayi sai kallonsa takeyi kamar ta cinyeshi Akan so,
Dan kuwa kwalliyarsa tayi Mata kyau, don ta amshi jikinsa
a ranta tace "Sadaukina kayi kyau manyan kayana suna maka kyau."

Ashe maganar tafito fili yanajinta Sarai yayi kamar baiji abinda taceba,
don fahimci Saudat irin matan Nan ne Masu yawan naci Akan abuda suke so,
snn ya lura duk mulkinta duk k'asaitarsa duk wulak'anta mutanen da takeyi tana D'an Jin shakkarsa,
snn macce ce jarabarbiya Mai yawan son a Koda yaushe a kusanceta tafison Koda yaushe namiji Yana kanta,
Wanda shi a wurinsa wahalar da gab'ob'en jikinsa kawai yakeyi dan ba wani abunda Yake amfanuwa da yin hakan,
Illah sai ita da yakejin tana sauke numfashi tare da kuwa kamar alamar tanajin Dadin hakan,
mere Baki yayi ☹ Wanda d'ali'arsa ce,ya ya mai da idonsa Yana kallon agogon hannunsa yaga 10:30am ya ajiye cup d'in hannunsa ya mik'e tsaye tare da d'aukar wayarsa ya shiga Kiran number safwan."

Ringing biyu safwan ya d'aga a dai dai lokacin da yafito wanka SAFINA tana rungume a jikinsa dukansu ba Kaya a jikinsu sai zuba Masa shagwaba takeyi zaiyi tafiya ya barta. Baisan lokacin da ya d'auki wayarba ya k'ara a kunnensa, a maimakon yayi magana hankalinsa ya tafi wurinta yaci gaba da lallashinta Yana fad'in
"sorry baby bafa tafiyar kwana zamuyi ba, kekoda kwana ya riskemu bazamu wuce kwana biyu mudawoba sorry kinsan Ina tare da ke akoda yaushe zumata."
saukar dogon tsaki yajiya da k'arfi a kunnensa
Wanda Sauban ya sakar Masa cike da Jin haushin iskancin safwan,

Safwan Kuma Gaba ya Manta da ya d'auki wayar sauban safina duk ta rikitashi."

Murmushi safwan ya saki Yana fad'in yi hakuri abokina gani Nan zuwa yanzun nan,
Na tsaya aikin lallashi Dan kada naje na dawo a juyamun baya nashiga uku na."

Kuma Jan wani tsakin Sauban yayi baiyi magana ba ya kashe wayarsa."
Kan gado yanufa ya zauna, a rayuwarsa ba abinda ya tsana kamar jira Kuma Safwan yafi kowa sanin hakan."

Saudat ta matsa taje kusa dashi ta zauna har kafafunsu suna gogar na juna idonta a kansa, don idan zata shekara tana kallonsa bazata tab'a gajiyaba,
Cikin muryarta ta Mai cike da k'asaita tace "Sadaukina tafiya zakayi ne?"

Kallonta yayi yaga ta D'an bashi tausayi ya d'an janyota zuwa jikinsa, ai Kuwa ta lafe tana shak'ar k'amshin turarensa, cikin muryarsa Mai tsada yace "gidan gona zan tafi tare da Safwan."
Iya abinda yace da ita kenan yaja bakinsa yyi shuru."

Lumshe idonta tayi wata irin wutar kaunarsa takeji tana ruruwa a zuciyarta,
Tashiga tinanin yanzun tafiya zaiyi da wnn kwalliyar Wacce tayi tsananin yimasa kyau jikinsa,
Kafin ya Kai mota Allah kad'ai yasan bayi da kuyangi Mata wad'anda zasuyita kallonsa,
Snn idan yatafi Allah kad'ai yasan adadin maccen da zata kallesa ta yaba kyansa."
Wasu siraran hawayen kishin mijinta suka zubo Mata Akan fuska tayi saurin Sanya hannu ta daukesu,
Tana kallonsa tana fad'in "Allah ya tsaremun Kai a duk inda ka Sanya k'afa, Allah ya makantar da 'yan Mata daga kallon kyakkyawar fuskarka, hak'ik'a Ina kishinka mijina."

_hmmmm Saudat kenan_🤔

Wani murmushin gefen Baki yasaki Dan yasan kishin saudat Sarai tun a turai,
mik'ewa tsaye yayi yafita sakamakon Kiran wayar safwan da yashigo wayarsa alamar ya iso."

Bayansa tafi suka jera suna tafiya a tare , tin daga harabar b'angarensa bayi Mata da kuyangi suke zubewa k'asa tare da sunkuyar da Kai suna Kai gaisuwa ga yarima,
daga masu hannu kawai yakeyi alamar ya amsa."

Sai da ta kaishi bakin get din fita daga part dinsu snn ta d'aga Masa hannu ta juyo cike da k'aunar mijinta tare da kishinsa."

A bakin motar da zasuyi tafiyar ya tarar da safwan Yana jiransa sai waya yakeyi yana dariya da alama da safina yakeyi domin ita kad'aice matsalar safwan inji sauban😄"

Tsaki Sauban ya Kuma ja, yabawa fadawa umurni tare da jami'an tsaro wad'anda zasuyi tafiyar a tare umurnin da sushiga mota sutafi, a bar safwan wurin tinda bai tashi lafiyarba😄

Kasancewar duk inda zaitafi indai tafiya Mai nisace sarki yaba umunin yadinga tafiya tare da fadawa da matakan tsaro saboda tsaro da Kuma kula da lafiyarsa."

Cikin sauri fadawa suka bud'e masa mota ya shiga safwan shima ya shiga aka rufe k'ofar, motoci suka Fara fita daga gidan D'aya Bayan D'aya Wacce mota zata Kai kusan guda goma a Nan take aka Fara sakin jiniya Wacce ta Karad'e gaba D'aya gidan sarautar alamar d'an sarki zai fita kenan."

Safwan wayarsa kawai yakeyi da matarsa yana dariya harda su d'aga k'afa yanayi Yana kallon sauban cike da tsokana,
Yana fad'in "haba Zumata nafad'a maki ki kwanatar da hankalinki, Ni dai tafiyar Nan idan bakyaso Allah yazun zan iya dawowa gida"

Wani kallo Sauban ya wurga Masa Mai cike da harara Mai dauke da ma'anar baka da hankali."

Can yaga safwan ya tintsire da dariya Yana fad'in ok to shikenan ki gyaramun komai naki, ki kula da kanki domin idan Kika Bari wani abin yasameki bazan tab'a yafe makiba, yasakar Mata kiss a waya tare da kashe wayar "

"Mere baki sauban yayi yace" dama d'an iska a duk inda Yake zai iya nuna halinsa."

Kallonsa safwan yayi Yana dariya yace "ranka ya dad'e ko gaisawa bamuyiba sai zagi ya biyo baya."
Da matata fa nake waya zaka Kira da Dan iska, to idan hakan ne Kai wayasan iskancin da kayi kafin kafi cikin gidanka."

Gyaleshi Sauban yayi ya janyo laptop d'insa yashiga dannawa."

*****************

K'arar jiniyar da ta karad'e gaba D'aya gidan sarautar alamar " *D'AN SARKI SAUBAN* zai fita kenan
Hankalin Sadeeq ya tashi matuk'a domin idan shi zai fita mota D'aya ake bashi ta fadawa wad'anda bazasu wuce guda biyar ba, wad'anda zasuyi Masa rakiya Amma Sauban harda wasu jami'an tsaro suke dafe Masa baya ana Masa jiniya"

Kai tsaye wurin mahaifiyarsa yanufa fulani, Yana huci,
Fulani dake kishingid'e ana Mata tausa,
Tana ganin shigowar Sadeeq Ransa a b'ace tabawa baiwar umurnin tafita zata gana da yarima cikin saurin baiwar tafita."

Ta kalli Sadeeq tace "yarima lafiya meya faru?"

Cikin maganarsa ta rashin tarbiya yace "meyasa ake nuna Mana fifiko a cikin gidan Nan,
Sauban yafimu ne ko yafi kowa ne a cikinmu idan zaifita tamkar sarki zaifita yanda akeyiwa sarki jiniya hakan ake Masa sab'anin mu da ake sakinmu a sake, ba matakan tsaro wato Ana nufin mu ba Yaya bane shine d'a."

Na rantse da Allah sai Naga Bayan Sauban sai Naga Sauban baya motsi a doron k'asa, bana sonshi yanda na tsini mutuwata hakan na tsaneshi."

Murmushin farin ciki fulani Jamila tayi, tajanyo hannun Sadeeq tace "zauna d'ana yanzun na tabbatar da kasha nono na,
Kabar komai a hannuna Ni nasan abunda nake shiryawa,
Abunda nakeso da Kai ka rage nuna tsanarsa a gaban mutane kabar abin a ranka
Indai Ina motsi a doron k'asa Sauban bazai tab'a Kai labari ba."




_kuyi hkr nasan kun Matsu labari Sauban ya Kare mukoma Kan labarinmu to Amma idan Kuna biye Dani sai kun fahimci tushen labari snn zaku fahimci duk abinda zaici gaba da faruwa a Nan gaba idan muka Koma Kan labarinmu,_





*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍



🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*Page 16*



Jiniya kakeji tana tashi sannu a hankali manyan motoci kirar jeb bak'ak'e suke ta gangarawa a cikin k'aramun k'auyen Lassa dake k'aramar hukumar mulkin Adamawa."

gaba D'aya jiniyar ta k'arad'e dukan k'aramun k'auyen Wanda maza da Mata tare da dattijai da samari kowa sai Kama 'ya'yansa yakeyi yana shigarsu cikin gida wasu Kuma sai gudu sukeyi suma fad'in sarki ne yazo tare da 'yan sanda.

_kusan fulani da tsoron Yan sanda lol_🤪

Babu abinda yafi daga masu hankali irin jami'an tsaro Yan sanda da sukaga gani tsaitsaye a Bayan mota ko wanne ya hak'a bindigarsa kamar wad'anda ke fagen yak'i
fuskokinsu ba wani alamar sauki ko dariya a tare dasu."

Kai tsaye babban gidan gonar suka nufa, Wanda Yake zagaye da fadawa da masu gadin wurin, cikin zafin nama aka hangame masu k'atun get din gidan gonar suka dinga shigar da motocinsu d'aya Bayan Daya."

Murmushi kawai sauban yake saukewa domin tinda aka shigo k'auyen na Lassa ya tsinci kansa cikin wani farin ciki tare da Annashawa duk ya Manta wata damuwarsa domin Yana tsananin son k'auyen nan tare da gidan gonarsa"

Parking motocin suka shigayi a cikin parking space, sai da suka tsaitsaya,
Snn cikin sauri fadawa suka nufo motar da Sauban Yake a cikinta suka bud'e Masa, tare da zagaye motar har da jami'an tsaro suna jiran fitowarsa."

Sai da ya d'auki minti biyar kafin yafito, Wanda Al'adarsa ce baya saurin fitowa a mota lokaci daya sai ya d'auki minti biyar zuwa goma saboda tsaro😎."

Safwan ne yafara fitowa snn

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login