Showing 6001 words to 9000 words out of 86876 words

Chapter 3 - DAN SARKIn SAUBAN COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

7409

hanzari,
Ta xube gabanta tace "ranki ya dad'e naji wani labari marar dad'in ji da sauraro Yana yawo a cikin gidan Nan cewa wai sarauniya Hajjah ta karb'e key d'in store a hannnki."

Kallon jakadiya jamila tayi ta furzar da iska Mai zafi snn tace "hakan ne Sarauniya ta karb'e key a hannuna,
ta nunamun ban isa akan komai na gidan Nan ba, ta nunawa jama'ar gidan ni ba abakin komai nake ba
Wlh tallahi jakadiya na tsani matar nan, na rantse da Allah Da ba itace Mahaifiyar mijina Abdullah ba da tuni an Manta da tarihinta a cikin masarautar Nan."

Jakadiya tace "wnn hakan Yake Amma duk da hakan ba a hakan za'a bartaba domin idan kika zuba Ido ko Mai sai dai kiga ana gudanar dashi a gidan nan, ke Kuma kina gefe kina kallo a matsayinki na gimbiya matar d'an sarki Mai jiran gado."

Kallon jadiya tayi tace "meye mafita?"
Dariya jadiya tasaki tace "mafita d'ayace akwai wata bokanya a can wani k'auye Wanda ake kira da k'auyen bokanya k'araba, ita wnn bokanyar babu abinda Bata iya aikatawa idan kaje Mata da buk'atarka anan take zata share maka hawayenka,
Shawarar da zan Baki ya uwargijiyata itace kikawo kud'i masu yawa natafi wurin bokanyar nan nasaka tayi maki aikin da Zaki mallake komai na gidan Nan , ya zamana komai ya dawo a hannunki sai yanda kikayi dashi"
Snn na Nemo mki maganin haihuwa da zarar kin haihu kin haifi d'a namiji,
Kinga daga Nan sai musan yanda zamuyi mu kawar da sarki Akan kujerarsa sai mijinki Abdullah ya hau karagar mulki, Kinga sarautar duka ta dawo hannunki sai yanda kikayi da kowa dake cikin gidan nan domin kin Zama matar sarki kuma sarauniya ga Kuma d'anki yarima Mai jiran gado a hannunki."

Wata irin dariyar farin ciki jamila tasaki Domin har tafara hango mijinta a kan kujerar mulki ita Kuma tazama Sarauniya,
Tace "wnn shawara taki tayi jakadiya.
Dan hakan nake sonki duk a cikin ma'aikatan gidan Nan,

Tashiga bedroom dinta taciro kud'i masu yawa tafito ta mik'awa jakadiya tace tashi kitafi yanzun Nan kisani na mallaka komai a hannunki, idan kika zalinceni Zaki had'u da fushina domin kinsan ba kyau ne daniba, ban sassauci."

Jiki na rawa jakadiya ta k'arb'i kud'in tana fad'in "Har Abada bazan tab'a zalintarkiba ya uwargijiyata ki daina ko kwanta a kaina, ta mik'e tsaye tace natafi sai nadawo."

Hakan jadiya ta tafi k'auyen bokanya k'araba ta k'arb'o magani Wanda za'a sanyawa Hajjah a cikin abinci ko lemun Sha da zarar Tasha to duk abinda Jamila tace shi za'a aikata a gidan."

Abinci suka shiryawa Hajja na musamman wanda yasha magani har ya gaji,
Hakan Jamila ta sanya bayi suka d'auko abincin tana gaba suna bayanta a biye suka nufi b'angaren Hajjah dashi,
Wanda suka sameta kishin gid'e tana cin Ayaba fuskarta cike da murmushi da Annuri kamar ko da yaushe,
Tana ganinsu murmushin fuskarta ya kuma k'aruwa ta tashi zaune tana murmushi takai dibanta a wurin kuyanginta tace "kutafi ku huta saina nemeku."

Cike da ladabin munafurci Jamila ta Kai zaune a gefen Hajjah tana Kai gaisuwa gareta snn ta gabatar Mata da abincin da tadaho Mata."

Murmushi Mai cike da murna da Jin dad'i Hajja tayi,
Tana kallon Jamila tana fad'in godiya nakeyi gimbiya Allah ya biyaki yabaku zuri'a Mai Albarka."

"Ameen Jamila tace tare da janyo abincin ta Fara xubawa Hajjah a cikin plate tuwo ne miyar taushe Wanda tasan Hajja tana tsananin so."

Murmushi kawai Hajjah take saukewa a fuskarta snn ta sanya hannu ta k'arb'i abincin tafaraci,

Sai da tacinye tuwon dake cikin plate d'in tas snn Jamila ta zuba Mata ruwa ta wanke hannunta Tana murmushin farin ciki,
Hajjah Kuwa sai Sanya Mata Albarka takeyi tare da yimasu Addu'ar samun zuri'a
Domin a kullum Addu'arta d'aya ce Allah yabawa Abdullah haihuwa Mai Albarka ita dai taga 'yan jikokinta tun tana raye."

Tin lokacin da Hajja taci abincin Nan Wasa Wasa yau ciwo gobe lafiya ya zamana komai na gidan sarautar ya Fara ja baya, anan take ta aika
aka Kira Mata Jamila ta dank'a Mata key d'in store tare da duk wata ragamar gidan Domin taci gaba da kula da komai saboda a yanzun ba wata isanshiyar lafiya ne da itaba."
Murna a wurin Jamila a lokacin abin ba'a magana, ai Kuwa a ranar sai da tayiwa jadiya kyauta ta ban mamaki, tin daga lokacin ragamar komai ta cikin gidan sarautar ya koma A hannun Jamila, tamkar itace matar sarkin."


Shekarar Abdullah biyar da Jamila ko b'atan wata Bata tab'a yiba,
Inda sarki yashiga damuwa sosai, shi Kuma Abdullah ko a jikinsa domin yasan Allah shike bada haihuwa ga Wanda yaso,
Kuma shike hanawa ga Wanda ya ga dama,
snn Allah baya tambayarka ya akayi baka haihuba, Amma idan ya baka haihuwa zai tambayeka yanda ka rik'e Amanar da ya baka,
Sai dai ita haihuwa tana d'aya daga cikin kaso biyar cikin goma najin dad'in duniya, musamman a gidan sarauta."

Wasa Wasa sai da Jamila ta shekara bakwai ba haihuwa ba alamarta, hankalin sarki Abdulsalam mahaifin Abdullah ya Kuma tashi
yashiga nema Masa auren 'yar sarkin zamfara wato bintu,
Abdullah bai san abinda akeyiba."

Sai da suka kammala shirya komai na dangane da auren Abdullah da Bintu tare dashi da mahaifin bintu,
har ranar d'aurin aure sai da suka tsayar snn sarki Abdulsalam ya Kira Abdullah yake shaida Masa tare da bashi umurnin ya tafi garin zamfara domin ganin matar da zai aura su fahimci juna domin aure ne ba fashi sai an d'aura, Nan da wata biyu masu zuwa."

Baiyiwa mahaifin nasa musuba ko jayayya domin Abdullah yaro ne Mai biyayya da kawaici musamman a wurin mahaifansa,
Yana komawa yashiga shiri washe gari yashiga jirgi yanufi zamfara,
A ransa Yake sak'awa tare da Bawa zuciyarsa hakurin duk yanda yaga yarinyar a hakan zai aureta tinda mahaifinsa hakan ya ke so, baya fatan ya watsa Masa k'asa a Ido."

Saukarsa a masarautar zamfara yaga tarbo da kulawa na samman anan take akayi Masa masauki a cikin wani k'ayatattacen d'aki Mai adon gaske, aka cika Masa gabansa da kayan marmari,
Minti goma da zamansa a d'akin, Bintu tashigo cikin shigarta ta Alfarma sanye take da Alk'yabbarta ruwan Madara wacce tak'ara yiwa fuskarta kyau da kwarjini, bayinta suna biye da ita a bayanta tare da yimata kirari 'yar sarki jikanyar sarki matar d'an sarki Wanda zai gaji sarauta , d'anki ma sarki hak'ik'a kinyi gadon sarauta gaba da baya Allah ya taimakeki ya k'ara mki lfy Fara Mai farar aniya."

Hannu ta d'aga masu, tare da juyawa ta kallesu, cikin d'aure fuska tace "Ashe banyi maku gargad'i akan kudaina yimun kirariba?" Ashe bance ku daina k'ask'antar da kanku gareniba, Nasha fad'a maku cewa ni mutumci kamar ku, Dani daku duk d'ayane ba wani banbanci a tsakaninmu a wurin mahaliccinmu to kusani wnn shine gargad'i na k'arshe da zan mku a kan hakan, kutafi sai na shigo."
Snn ta nemi wuri ta zauna tare da sunkuyar da Kai a gaban Abdullah tashiga gaidashi cike da girmamawa."

Kallonta yakeyi Yana murmushi Yana Hamdala wurin ubangijinsa domin Bintu ta dace da rayuwarsa kyawawan halayanta sunyi matuk'ar burgeshi, uwa uba bintu kyakkyawa ce ajin farko domin tafi Jamila komai ta kereta ta ko Ina, yashiga godewa Mahaifinsa domin ya zab'a Masa abinda ya dad'e Yana nema a rayuwarsa."
Ai kuwa cikin a waya uku da sukayi a tare suka fahimci junansu soyayya Mai k'arfe tashiga zukatansu kowa ya fahimci d'an uwansa tare da yiwa junansu fatan Alheri snn Abdullah yayi Mata kyauta Mai girman yayi Mata sallama ya dawo gida cike da farin ciki."

Yana sauka Kai tsaye fada yanufa wurin maimartaba cike da farinciki gabansa ya Kai durk'ushe Yana zuba Masa godiya tare da fatan Alheri,
Murmushi sarki yayi irin nasu na manya snn ya dubeshi yace "Magaji da alama zab'ina yayi maka naji dad'i da ganin hakan sai kafara Shirin auren ku Nan da wata biyu, godiya Abdullah ya shiga yiwa sarki snn ya Masa sallah yatashi yafita cike da farin ciki."

Rasa yanda zai fad'awa Jamila yayi, Wanda yaga yanzun kwata kwata Bata da lokacinsa Bata bashi kulawa kamar da, mulki kawai ta sanyawa gaba,
Dan hakan shima ya kyaleta ya zura mata Ido,
Wasa Wasa duk safiyar Allah ta waye Abdullah da Bintu sai sunyi waya tafi a k'irga a tsakaninsu wata irin shakuwa da soyayya ta Kuma shiga Wanda sukeji idan d'aya bai auri d'aya ba bazai iya rayuwa ba."

Biki sai k'aratowa yakeyi Wanda ya rage saura sati d'aya d'aurin aure, duk masarauta ta d'auka yarima Abdullah aure zaiyi kowa sai murna yakeyi sunajin dad'i wata k'ila canji zai shigo a cikin gidan sarautar, duk abin Nan da akeyi gimbiya Jamila Bata da labarin komai harkokinta kawai takeyi,
Snn kowa tsoron tunkararta yakeyi ya fad'a Mata.
A nan take aka shiga gyaran d'aya b'angaren dake kallon sashin Jamila,
Inda Jamila tacika da mamakin ganin ana gyaran wurin to kyaran me akeyi a d'aya b'angare irin nata Wanda babu abinda ya banbantashi da b'angarenta
Bata kammala tunaniba jakadiya tashigo Mata a firgice ta zube gabanta tana fad'in ranki ya dad'e najiyo wani labari a majiyar da Bata k'arya cewa yarima Abdullah mijinki aure zaiyi Nan da sati d'aya za'a d'aura auren."

Wata irin zabura tayi ta mik'e tsaye daga kujerarta ta mulki tana fad'in k'aryane wlh babu wata Wanda da Isa ta jadani a gidan Nan ta zauna lafiya."

Kirawomun bokanya k'araba yanzun Nan a waya tayi mun bugun k'asa taganemun tabbas da gaske Yarima Abdullah auren zaiyi ko maganar mahassadane da 'yan bak'in ciki."

Cikin minti biyu jakadiya tashiga Kiran bokanya, ai Kuwa Kira biyu bokanya ta d'auki waya tana dariya Mai cike da Ban tsoro tace
"anayimun waya daga masarautar Abdulsalam Akan maganar d'an sarki yarima Abdullah tabbas yarima Abdullah aure zaiyi Nan da sati d'aya Kuma aurensa dole ne za'ayi shi ba fashi babu ja da baya domin tauraruwar yarinyar da zai aura tana da haske sosai, snn akwai wani haske a tare da yarinya bugu da k'ari zatakawo farin ciki a cikin gidan sarautar,
Saboda 'yar sarki ce, ubanta tsaye Yake akanta,
idan kika matsa dole sai anfasa auren Zaki iya rasa rayuwarki koki haukace."
Bokanya tana gama fad'in hakan ta yanke wayar."

Wani irin gumine yashiga tsattsafowa Jamila a jiki tashin hankali Wanda ba'a Sanya Masa Rana,
Ba babban tashin hankalinta jin cewa zatazo da farin ciki a cikin masarauta meye wnn farin cikin?"

Jakadiya tayi karaf tace haihuwa ya uwar gijiyata,

Hannu ta d'aga ta wanke fuskar jakadiya da Mari tana "fad'in k'aryane wlh babu wata wacce ta Isa ta haihu da Yarima a gidan Nan bayan ni."




*Hmmmmm fitinar mulki kenan*🤔🤔



*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍



🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*DIDECTED TO Fateemah M Uthman*





*Page 6*






Sunkuyar da Kai jakadiya tayi hannunta dafe da kuncinta tana fad'in "Allah ya huci zuciyarki ya uwargijiyata, abinda kike nufi bashine manufata ba,
Tare da mik'ewa tsaye ta d'an runsuna tace "ki huta lafiya gimbiya snn tafita."

Bak'in ciki duk ya gama lullub'e gimbiya Jamila sai zufa take fitarwa gaba d'aya a jikinta kamar wacce tafito daga wanka,
tarasa mafita, anan take tashiga tunanin,
ita Abdullah zai yaudara,ita Abdullah zai zalinta ace saura sati d'aya d'aurin aurensa Amma bai fad'a mataba meta mashi a rayuwa?"

Takai zaune dafe da Kanta hawayen bakin ciki suka Fara wanke Mata fuska."
Shuru tayi tashiga tunanin yaushe rabonta da Abdullah,
Yaushe rabon da su tsaya suyi magana Kota minti talatin ne,
Baza Manta Yana yawan aiko kuyangi kiranta mantawa takeyi Bata zuwa har ya gama jiranta yayi tafiyarsa,

hakan ko a wurin kwanciya,
Tana d'akinta Yana d'akinsa Bata zuwa wurinsa Domin jitakeyi tayi aiki ta gaji hutu take buk'ata,
Shi Kuma Abdullah namijine Wanda baya bin macce d'akinta duk yanda yakejin buk'ata idan Bata kawo kantaba sai dai ya hakura."

Wani kuka yazo Mata Mai k'arfi tayi saurin rufe bakinta dan kada kuyanginta sujita Su fahimci halin da take ciki,
ta shiga fad'in nashiga uku "
Ko saboda hakan zai k'ara Aure?"
Wlh na daina Abdullah kazo kace mun kafasa Auren Nan zan gyara duka kuskurena."

Mik'ewa tayi ta shiga toilet ta wanke idonta tafito ta Fara shirya tarbon mijinta, Domin yau ta shirya bashi hakuri idan wani laifi tayi Masa ko wani kuskure Wanda zai Sanya ya k'ara Aure yayi hakuri ta daina zata tarairayeshi fiye ma da da,
Abinda Bata saniba Abdullah ya tsufa a zamfara bazai dawoba sai da matarsa."

Shuru ba Abdullah ba labarinsa har zuwa k'arfe goma na dare Wanda a iya saninta dashi baya kai k'arfe goma batare da yadawo gida ba."

Wasa Wasa har safiya ta waye ba Abdullah, hakan yasa ta yanke hukuncin zuwa sashen Sarauniya Hajjah Domin ta tambayeta ina Abdullah ya tafi duk da dai har da sa hannunta Abdullah zaiyi Mata kishiya."

Zuwanta wurin Hajjah anan Hajjah take fad'a Mata ai Abdullah Yana zamfara bazai dawoba sai angama d'aurin aure sa."

Wani bak'in cikin da takaici Mai had'e da zazzafan kishi ya rufe idon jamila Anan take tashiga fad'awa Hajjah maganar da duk tafito a bakinta taciwa hajjah mutumci
Daga k'arshe tace ita meyasa sarki baiyi mata kishiyar bane."

Ido kawai Hajjah tabi Jamila dashi cike da mamaki da Al'ajabi Domin a duniya babu Wanda ya tab'a ci Mata mutumci ido cikin Ido kamar Jamila surukarta matar d'anta."

Sai da Jamila ta gama cin mutumcinta snn tafito daga b'angaren Hajjah a fusace tanufi sashenta zuciyarta na k'una da rad'ad'i."

Bayan d'aurin auren Bintu da Abdullah, aka d'auko Amarya daga masarautar zamfara zuwa masarautar Adamawa, wani sabon bikin ne aka had'a a gidan Ango tare da wasanni irin na gidan sarauta, Wanda hakan ya K'ara kunawa Jamila rai ganin ita a lokacin da aka auro ta ba ayi hakan ba, ta Kuma d'aukar wani Alwashi a ranta, tare da Jin tsanar Bintu Mai tsanani ta d'arsu a zuciyarta."

Shigowar Bintu a cikin gidan sarautar canji ya Fara samuwa a cikin gidan, Domin duk wani k'unci da ake Sanyawa fadawa da bayi tare da kuyangu duk ya kau, Domin Bintu macce ce wacce ta tashi a gidan sarauta tasan yanda ake gudanar da mulki cikin Adalci snn gata da tausayi Bata kaskantar da talaka da bayinta ta d'auka da ita dasu duk d'aya na wurin ubangiji bawani babbanci snn Bata d'aukar kanta ita wata ce, kamar Jamila."

Hakan yayiwa Hajjah dad'i ganin. Halayya Bintu Mai kyauce sai yanzun take farin ciki da dariya ganin tilon d'ansu ya dace da macce ta gari wacce take dai dai da rayuwarsa."
Hajjah taja Bintu a jikinta tashiga fad'a Mata duk wani sirrin masarautar Wanda Bata tab'a yarda Jamila ta sandasuba domin tin farko ta fahimci rayuwarta maccece Mai son kanta ga kuma mugunta."

Kowa a gidan idan kaji ya bud'e Baki ba Wanda zai ambata sai Bintu Alherinta ake fad'i tare da Adalcinta, snn Bintu kaifi d'ayace ba tsoro ko shakka a tare da ita Dan hakan suke fito na fito da Jamila, Dan Bata tsoronta ko kad'an musamman da ta fahimci halayanta ba masu kyau bane, hakan yasa Sam basa Zama a inuwa d'aya Jamila tanaso ta Fara tin karar Bintu Amma kwarjininta yake hanata aikata Mata komai,

Snn a duk lokacin da take yunkurin ai watar da wani zalinci a gidan,
Bintu takan dakatar da ita ba tsoro ko shakka, zata shiga karanto Mata k'undun tarihin mulki.ba hakan yace ayiba."

Dole Jamila takeja baya Domin tasan kowa Yana bayan Bintu a gidan daga ciki kuwa har da maimartaba sarki,
Tabbas maganar bokanya tafito cewa Bintu zatazo da wani haske a gidan, to gashi ta Fara gani tanaji tana gani komai ya tsaya Mata cak."

Abdullah Yana tsananin son Bintu Wanda son da Yake Mata yasa yakasa b'uyeshi a duk inda yake a duk yanayin da ya tsinci kansa,
Hakan Jamila ta Kuma Jin haushi da takaici tashiga tunanin Ina wuta tajefa Bintu,

Ana hakan Bintu ta Fara laulayin ciki, irin laulayin Nan Mai sakarwa mutum kasala da yawan amai anan take komai yayi sanyi a tare da ita."

Kwajin farko aka tabbatar da cewa tana d'auke da ciki d'an wata d'aya.
Murna a cikin masarautar abin ba'a magana har da d'an kwarya kwaryar biki aka shirya,
Anan take sarki yayi Mata kyauta taban mamaki, hakan Hajjah wacce lafiya ta Kiya mata yau ciwo gobe lafiya, itama tayi murna sosai dama babban burinta kenan taga jikokinta."

Jin labarin bintu tana da ciki ya k'ara d'aga hankalin Jamila ganin daga zuwanta daga baya har tasamu ciki dama tasan za'ayi hakan Kuma tasan ba Dan komai akayi Auren ba sai Dan ta shigo gidan ta haihu domin ta gaji sarautar masarautar tinda sun saba da mulki sunsan da d'insa,
Ynzun ana nufin idan ta haihu d'anta kenan zai hau kujerar mulki, Ina bazai yuwoba,
Anan take tabawa jakadiya kud'i masu yawa tace "taje wurin bokanya duk yanda za'ayi ayi a zubar da cikin dake tare da Bintu kada asake a barta ta haifeshi Kai idan da Halima har itama Bintu tabi cikin nata zuwa lahira."

"Angama ya uwargiyata wnn shi dai dai kinyi tunani Mai kyau Allah ya k'ara maki kaifin basira snn jakadiya ta tashi tafita tanufi k'auyen bokanya k'araba."

Karon farko bokanya da tayi diba tace "Ina ciki bazai zubeba sabida yarinyar da abinda ke cikinta haske ne dasu, tin farko nariga da ta fad'a Maku cewa tauraruwar yarinyar haske gareta,

Jakadiya tace "Allah ya k'ara maki lafiya ya bokanya k'araba ba wani abu da za'ayi akan sai cikin da ita kanta idan da Hali akasheta tamutu ta tafi da cikin can lahira."

Bokanya k'araba ta d'aga murya cikin wani sauti Mai firgitarwa tace bai yuwoba,zai yiwo a kashetaba domin idan akayi yunkurin kasheta komai zai iya faruwa dagani har ku,

Sai dai ayi asirin da zata haifin abinda ke cikinta yafito duniya ba rai."

Jakadiya tace "wnn ma yayi."
Aka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login