Showing 51001 words to 54000 words out of 86876 words

Chapter 18 - DAN SARKIn SAUBAN COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

7419

kamar hajiya laila,
Janyota yayi zuwa jikinsa ya rungumeta yashiga share mata hawayen dake zuba a idonta, cikin sigar lallashi yake kwantar mata da hankali akan ta d'auki kaddara akan duk abinda ya faru ta daina sanyawa ranta damuwar b'atan suhailat."

Doguwar ajiyar zuciya Hajiya laila taja snn tasakarwa mijinta murmushi tare da rik'o hannunsa duka biyu ta saka a cikin nata hannun ta d'an matse kad'an cike da shauk'i
tashiga fad'in na daina mijina ina Addu'a a koda yaushe Allah ya k'aramun dauriya da dangana a kan rashin tilon yata danayi."

Dariya Alhaji yasaki yace "Ameen tare da kashe mata ido d'aya yana fad'in insha Allahu wnn dawowar danayi sainayi k'ok'ari nabaki wata Suhailat d'in kinga shikenan na kashe bakin magana."

Dariya tasaki tana fad'in "kai Alhaji bakada dama mezan iya tsofai tsofai dani."

Hararar wasa ya sakar mata yana fad'in "a Ina tsofan yake, a yanda nakejinki kinfi sabuwar budurwa dal a leda komai,
Dan kuwa duk Wanda ya kalleki yasan nayi dace nayi sa'a a cikin maza samun kyakkyawar macce mai tsafta da iya ado uwa uba ga k'amshi, ni kuwa me zanyi da wata macce a duniya idan kina tare dani."

Murmushin farin ciki take saki domin tana yawan jin wnn yabon a bakin gwarzon mijin nata,
."nagode mijina Allah yaci gaba da faranta maka kamar yanda kake farantamun."

Ameen yace tare da cire hannunsa cikin nata yana fad'in "mutafi naga marar lafiyar Allah yasa ta farfad'o."

Hakan suka bud'e k'ofa suka fita fuskokinsu cike da farin ciki escort suka take masu baya suka nufi d'akinda Safna take ciki a kwance cikin mawuyacin hali."

Wurin gadonta suka nufa inda Alhaji Habib naira yana yin ido biyu da fuskarta sai da gabansa ya fad'i, yayi saurin k'arasawa wurin gadonta yana kallonta,
Hajiya laila kuma ta juya tana bawa escort umurni akan su dakata a waje kafin sufito,
Snn ta juya ta cewa Alhaji mutafi, ganin baya kusa da ita, yasa
Cikin sauri d'aga kai ta hangosa a bakin gadon safna yana k'are mata kallo cike tausayi,
Wurin ta nufa taja ta tsaya a kusa dashi tana fad'in Alhaji kaga yarinyar ko gwanin ban tausayi,
Dam gabanta ya fad'i da tayi ido biyu da safna wacce a lokacin ta farfad'o daga allurar baccin da akayi mata."

Cikin sauri hajiya Laila tanufi wurin safna tana kallonta ido ciki ido Wanda itama safna kallonta takeyi hawaye suna mata zuba a gefen idonta,

Sannu yaya jikin naki Hajiya laila tace."
D'aga Kai safna tayi alamar da sauk'i,
Hawaye kawai kezuba a idonta ga wani irin fad'uwar gaba da takeji tarasa sanin kona meye."

Suna tsaitsaye akan gadon safna ba Wanda ya kuma yin magana dukansu su uku gabansu sai fad'uwa yakeyi bakinsu ya rufe ba Wanda ya kuma furta kalma d'aya,
Likita ya turo k'ofa yashigo tare da sallama."

Gaida Alhaji yyi snn yanufi wurin safna,
yacire mata ruwan da ya k'are ya kuma juna Mata masu,
Ido kawai safna take bin koya dashi tana kallo hawaye suna Mata zuba,
Gyaran murya likita yayi ya kalli hajiya yace "Alhmdulillah ba wata matsala a tare da ita,
Duk iya gwaje gwajen da mukayi mungano buguwa ce kawai tayi a kanta Wanda insha Allah nan da kwana biyu zata sami lafiya."

Alhaji yace Allah ya k'ara bata lafiya."

Suka amsa da "Ameen."

Muryar safna ta tsinke masu magana da take kallon Hajiya laila tace "umma zan sha ruwa, yunwa nakeji."

Dam gaban Hajiya laila ya fad'i, dajin yarinyar takirata da suna umma sai taji sunan ya dace da ita, karon farko Taji wani girma ya darar mata taji k'aunar yarinyar ta shigeta a lokaci d'aya, idonta ya cika da hawaye tayi saurin sanya hannu ta share ta matsa a kusa da Safna ta d'ora Hannu a saman goshinta tana gyara Mata gashin kanta daya kusan lullub'e mata fuska tace "yata yunwa kikeji?"

Safna ta d'aga Kai, alamar eh."

Hajiya laila tasaki murmushi tace "kada kidamu yanzun za'a kawo mki abinci kinji."

Safna ta d'aga kai alamar "to."

Hajiya Laila ta janyo kujera ta zauna tana murmushi tana kallon fuskar safna, domin lokaci d'aya ta tsinci kanta cikin farin ciki da k'aunar wnn yarinyar sai takeji kamar 'yarta ce Suhailat ta dawo gareta."

Alhaji Habib naira yana tsaye a kansu yana kallonsu cike da farin ciki Dan kuwa shima a lokaci d'aya soyayyar yarinyar tashiga ransa."

Hajiya laila ta kamo hannun safna ta rik'e tace "meye sunanki 'yata."

"d'an murmushi safna tasaki domin kalmar da hajiya laila takirata da ita ta 'yata tayi matukar yimata dad'i
domin tinda tayi wayo ta girma idan aka cire Baba ba Wanda ya tab'a kiranta da wnn kalmar ta 'yata, azahiri wasu har kyamatarta sukeyi basa son tarab'esu, saboda tana shegiya bata da asali,

Hawaye suka wanke mata fuska da ta tuno da Baba,
Ta kalli hajiya cikin muryar kuka tace "sunana Safna."

Hannu Hajiya laila tasaka tana share mata hawaye dake zuba a idonta tana fad'in daina kuka 'yata daga yau kukanki ya k'are,
Wanne gari kike suwaye mahaifanki domin Zan tura a sanar dasu halin da kike ciki don gudun kada ayi ta nemanki."

Bana da kowa ni kad'ai nake rayuwata, kowa kyamata yakeyi, mahaifina kuma ya rasu
Ta fashe da kuka mai sauti gwanin ban tausayi."







*MRS ANAS BAWA*✍

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍



🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*Page 31*






Runtse ido hajiya Laila tayi domin tanajin Sautin kukan Safna yana ratse KO wanne lungu da sak'o na jikinta,
Hannunta tasaka tarik'o hannun safna cike da tausayi, ta tashi daga kan kujerar da take a zaune ta hau kan gadon da Safna take a kwance ta janyota zuwa jikinta ta tsura Mata ido sosai tana kallonta snn tayi k'arfin halin yin magana tace "daina kuka Safna,
Allah ya jikan mahaifinki da rahama,
Ki kwantar da hankalinki daga yau kukanki ya k'are bak'in cikinki ya k'are idan duk duniya kowa yana kyamarki mu bama kyamarki domin zamu taimakeki zamu taimaki rayuwarki."

Girgiza kai likita yayi cike da tausayi, Wanda yake tsaye a wuri d'aya yana jin duk abinda yake faruwa,
Hanyar fita yanufa yana mai tausayin rayuwar safna,
yarinya k'arama mai k'ananun shekaru kyakkyawa amma bata da gata, tabbas rayuwarta abar tausayice ."

Bayan fitar likita daga d'akin, direban Alhaji Habib ya turo k'ofa yashigo yana rik'e da ledodin abinci Wanda Alhaji yabashi umurnin ya sawo,
A gaban Hajiya laila ya durkusa ya ajiye snn ya juya ya fita."

Hajiya Laila ta tayar da Safna zaune cikin dabara da kwantar da hankali tashiga bata abinci da kanta tana kumajin k'aunarta da tausayinta suna ratsata, hakan shima Alhaji Habib shi yake tsiyaya mata ruwa a kofi yana bata tare da yimata nasiha akan ta d'auki kaddara a duk yanda tazo mata a matsayinta na musulma."

******************

A k'auyen lassa maigari da fadawansa tare da mutanen gari dake zaune suna zaman makoki akan yan uwansu da sukayi rashi, mutanen k'auyuka na kusa da garin sai ketarowa sukeyi suna masu jaje tare da gaisuwa, KO wanne yana zaune a fadar maigari maza da mata sai jimami akeyi,
Suna hakan zazzaune jigum jigum sukajiyo jiniyi tare da manyan motoci suna shigowa cikin garin."
hankalin kowa ya tafi zuwa wurin domin KO ba'a fad'a masuba tabbas sun tabbata wnn jiniyar da yawan motocin wnnan tafiyar Sarki ne da kansa ba yarima."

A gaban fadar maigari sukayi parking din motocinsu a jere, inda maigari ya mik'e tsaye tare da mak'arabbansa suka nufi wurin motor Sarki domin tarbonsa,

Manyan Fadawan sarki suna Rik'e da manyan buloli, suka zagaye motar Sarki KO wanne ya bud'e babban rigarsa suka kare bakin motar Sarki zaifito daga mota.
Saida yafito aka kuma gyara masa rigarsa snn suka janye domin bawa Sarki hanya ya wuce."

Taku yakeyi cike da k'asaita fadawa suna zuba masa kirari yanufi wurin maigari dake tsaye wuri d'aya tare da hakin mansa cike da farin ciki,
Babbar kujera aka d'orawa sarki ya zauna, snn mutanen gari suka shiga kawo gaisuwa d'aya bayan d'aya,

Sarki yana murmushi yana amsawa fadawa suma suna amsawa, yana k'arewa garin kallo da mutanen dake cikinsa ganin duk mutanen dake cikinsa a hargitse suke,
Bayan an kammala gaisuwa,
kowa ya nemi wuri ya zauna, ana zaman sauraren abinda sarki yazo dashi domin duk a tunaninsu jaje yataho yamasu."

Gyaran murya sarki yayi yafara da cewa, "Alhmdulillah Ina matuk'ar godiya da wnn tarba da nasamu a gareku hakika na dade da sanin mutanen garin nan masu karamci ne da karrama bak'o,
sai dai wannan zuwan da nayi na fahimci gaba d'aya a halin garin dama garin baki d'aya suna cikin damuwa da firgici meyake faruwa?"

Kallon juna suka shigayi ganin a she Sarki baisan abinda yake faruwa ba,

Cikin girmamawa maigari ya sunkuyar da Kai yashiga bawa Sarki labarin duk abinda ya faru ya rufe daga k'arshe ya rufe maganar da b'atan Safna wacce yarima yayi shad'i akanta, tare da mahaifinta har yanxun ba'a gansuba, ba'a sami labarinsu ba."
wasu suna fad'in sun mutu, mafi inganci Labari Wanda mukaji a bakin matar mahaifinta gata can a zaune cewar guduwa sukayi basu mutuba."

"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un sarki yake fad'i cike da jimami da tausayawa,

Maigari ya kalli inno yace matso kiyi masa bayani yanda abin yafaru,
tana rawar jiki ta matso ta Kai durk'ushe a gaban Sarki tare da sunkuyar da kai tana fad'in ranka ya dad'e ba mutuwa sukayiba guduwa sukayi, nima naso nabisu mugudu a tare, fad'uwa nayi sakamakon k'usa da nataka a k'afata,
Ranka ya dad'e Allah kawai ya k'addari zan rayu da a kwai kwana na gaba,
saboda a lokacin da nafad'i sai da wani k'aton garde yabi takaina ya wuce yana fad'in zamu dawo mu iyar da kaiki lahira, Inajin hakan na d'aga kaina naga sun dafawa su Malam da safna wad'anda suke rik'e da hannun juna suna gudu,
Ina ganin g
Hakan Nashiga jan ciki har nasamu nakawo kaina bayan gida a k'ark'ashin wani iccen mangwaro a nan na b'uya har suka dawo sunata nemana basu ganniba."

Ta fashe da kuka tana fad'in ranka ya dad'e "Safna Annobace rayuwarmu tunda malam ya tsintota a kan hanya ya kawota cikin gidanmu muke had'uwa da bala'i iri iri, Allah kad'ai yasan irin zuri'ar su."

Fadawa suka daka mata tsawa, ganin nan take fuskar Sarki ta canza alamar b'acin rai, suka shiga fad'in "gyara kalamanki sarki ya gaji da saurarenki kina iya tashi kitafi."

Tana gogar hawaye hannunta d'aya rik'e da zanenta, tanufi wurin zamanta,

Snn Sarki yayi gyaran murya ya kalli maigari yace "gaskiya ne abinda wnn matar tafad'a akan yarinyar da yarima yayi shad'i akanta?"

"Gaskiya ne ranka ya dad'e bamusan asalinta ba a gefen gari malam Audu ya tsinto ta ya kawomun ita, daga k'arshe yanuna yanason ya taimaketa zai rik'eta domin bai tab'a haihuwa ba."

Girgiza Kai Sarki yayi domin duk inda ransa yake ya b'aci,
Wato Sauban yana nufin shegiya 'yar tsintowa zai aura ya shigo da ita cikin gidan sarauta mai cike da asali kyakkyawan tarihi,
Murmushi Sarki yasaki ya danne b'acin ransa yace "hak'ik'a nayi bak'in ciki da tausayin abinda yasami ahalin garin nan Wanda har yayi sanadin mutuwar wasu rayunka daga cikinku,
Kuyi hakuri Ku d'auki kaddara Zan taimakeku Zan tsaya tsayin daka domin ganin ko suwaye suka aikata maku hakan."

Had'a baki sukayi suna godiya,
Snn Sarki yabada 'umurni a bud'e but a d'auko kud'i abawa duk Wanda yake wurin dubu ashirin kafin yayo masu aike."

Hakan aka shiga rabamasu kud'in suna godiya cike da farin ciki tare da yiwa Sarki fatan Alheri,
Snn Sarki yamik'e yashiga mota fadawa suka maramasa baya yafita daga k'auyen KO gidan gona baiyi tunanin zaigashiba domin duk inda ransa yake a b'ace yake."

*********************

Sauban kwance a cikin lambun dake part d'insa inda yake yawan zama yana shan iska, Safwan zaune a gefensa yana bashi labarin yanda ginin kamfaninsa ya wakana bayan kwanciyarsa a asibity, irin cigaban da aka samu, a kamfanin wurin ganin ginin ya fito yayi kyau,
Kasan cewar Safwan yaci gaba da gudanar da komai har komai ya kammala a yanda yasan sauban yakeso."

Fad'a masa yakeyi irin kud'in da aka zubawa wurin gaskiya maimartaba ya taka rawar gani domin ganin komai ya maka a yanda kakeso,
Banza dashi sauban yayi sai dannar wayarsa yakeyi yana kuma kallon kan screen din wayar,
Ba komai yake kalloba sai hotunan Safna wad'anda suka zamar masa madubin dubawarsa akoda yaushe."

A zahirance Kuma duk abinda Safwan yake fad'i yana jinsa yana kuma saurarensa sosai yakejin dadin maganar da yake masa akan kamfaninsa Wanda shine cikar burinsa."

Safwan baidamu da rashin kulawar da sauban baiyi masaba domin idan da sabo ya isa ace yasaba da wnn murd'and'en halin nasa, Wanda duk yanda kake dashi baka isa ka gane farin cikinsa ko Akasin hakan ba,
Yaci gaba da cewa "a gaskiya Abba yana sonka duk a cikin 'yayansa ba wanda yake son yadinga ganin farin cikinsa kamarka,
Shawarata anan abokina itace kaci gaba da yiwa Abba biyayya ka faran tamasa kamar yanda akoda yaushe yake k'ok'arin yaga ya faranta maka,
Allah ya k'ara masa lafiya da nisan kwana."

Sai a lokacin sauban ya d'aga Kai ya kalli Safwan yasakar masa murmushi yace "Ameen."
Tare da d'aukar lemu dake cikin cup yakai bakinsa ya d'an kurb'a snn ya ajiye,
Ya kalli Safwan yace "wani lokacin kana magana cikin natsuwa da hankali tare da fahimta, wani lokacin idan kayi wata maganar nakanji kamar na rufeka da duka."

Dariya Safwan yasaki yana fad'in Allah yabaka hakuri Dan nasan ka kusan sanya fadawa su dakeni,
Murmushi Kawai sauban yasaki,

Safwan ya kallesa yace Abokina nafa manta ban fad'a makaba,
Na kusan zama Daddy Dan kuwa Allah yayi najefa kwallo a cikin raga,
Saura Kai, a gaskiya ya kamata kayi k'ok'ari daren yau kada kayi bacci har sai kasamu kajefa kwallonka a cikin raga."

Had'e fuska sauban yayi ba alamar dariya a tare dashi yaci gaba da dannar wayar hannunsa,
Jiniyar motocin sarki sukaji hakan ya tabbatarwa sauban Abba yadawo kenan."

Shima Safwan yanajin hakan ya mik'e yace "Abokina nizan tafi domin kuwa kasan banason Ina Jan dogon shak'o bana kusa ga love d'ita bare Kasan yanzun laulayi mukeyi,
Ya d'an sunkuya gefen kunnen sauban kamar zai fad'a masa wata magana Wacce bayason kowa yaji,
cike da tsoKana yace "wai kasan wani abu kuwa gani nakeyi kamar 'yan uku ne na zuba Mata a mahaifa."
Yana kaiwa nan yasaki dariya yayi tafiyarsa."

Da kallo sauban ya bishi dashi har sai da ya daina ganinsa snn ya girgiza Kai ya mere baki,
ya tashi yanufi part dinsa domin ya d'auro Arwalar sallar magariba yatafi masallaci,
Domin yana son ganin maimartaba, yanason yaji halin da Safna take ciki,
Murmushi yasaki wata zuciyar tace wata k'ila an d'auro Auren,
Dam gabansa ya fad'i a lokacin da wnn tunanin ya fad'o masa rai."






*pls kuk'ara hakuri dani wlh jikin ne nawa har yanzun sai a hankali pls kucigaba da tayani da Addu'a*



*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍



🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*Page 32*





*Hmmmm ni kuwa readers kuna bani mamaki, a ganina lokacin da nafara nazari da tunanin wurin tsara maku labarin d'an Sarki sauban ba Wanda na nemi shawara dashi, snn ba Wanda yasakani, ko yake sayamun data idan zanyi posting, Wanda sai kunga dama kuke godiya da comment, hakan nake kashe aikin gidana na b'ata lokaci da tunanina na zauna nayi maku typing batare da kun biyani ko sisin kwabo ba, saboda ba Wanda yasakani nice nasaka kaina, hmmmmm amma kwana biyu da kukajini shuru bayan nafad'a maku cewar bana da lafiya, a maimakon kuji tausayina kuzama masuyinmun Addu'a kamar yanda wasu daga cikinku sukayita kirana sunayimun yajiki tare da addu'ar samun lafiya, A'a sai dai dayawa wasu daga cikin ku suka dinga kirana suna zagina tare da bakaken magganu akan cewa ina jamasu rai dan naga ana son buk dina, to na rike kayana, idan nasan bana iya cigaba da rubutu meyasa na fara, ko dai aidiya dinace ta k'are na tsiri cewa bana da lafiya, hmmmmm ni kowa a ganina ai baxakacewa marubuci aidiyarsa ta Kareba tinda ba kaine kasashi yin rubutun ba,*
*TO TUNDA ABIN BANA ARZIKI BANE DUK WANDA YAKESON CIGABAN DAN SARKI SAUBAN SAI YABIYA KUDIN KARATU NAIRA D'ARI biyu SNN ZAICI GABA DA KARATUNSA, ILLAHSO IDAN AKA TASHI ZAGIN NAWA DA FADAMUN MAGGANU SAIKU SHIGO MOTA KUSAMENI HAR GIDA A ZAMFARA KU ZAGENI TES, MASOYANA WASU DAGA CIKINKU SUKA JAMAKU HAKAN KUYI HKR*
*D'ARI biyu NE BA TSADA IDAN KINSHIRYA KI NEMI A NUMBER WAYATA 07066214433 KO KUMA YIMUN TRANSFER A ACCAUNT NO 2261274790 zenith bank Farida mansur zaku sami cigaban Dan Sarki sauban Alhdulillah nasami Lafiya sosai yanzun zaku rik'a Samun typing kullum kamar koda yaushe lokacin baya ngd sainajiku masu zagina kuci gaba amma kusani Allah yana nan baya bacci*







Jiki ba kwari Sauban ya soma tafiya yanufi masallaci domin a halin yanzun ba Wanda yakeson gani sai maimartaba ."

Maimartaba sarki tsaye a cikin d'akinsa a can cikin bedroom nasa sai safa da marwan yakeyi hannunsa goye a bayansa,
Babu abinda yake tunani sai Irin rashin hankali da tinani Wanda yasami sauban yanzun a baya bayan nan,

Inbanda rashin hankali da rashin tunani, akan shegiya marar asali ya bada gaggar jikinsa da rayuwarsa a k'auye ayita dukansa, har sai da kwanta asibity, wai a cewarsa taimakonta zaiyi,
marar asalin shegiya tsintattaciya zai taimaka ya d'auk'ota yakawo cikin masarauta Mai cike da asali dana garta,
ina hankali da tunanin sauban yatafi ne?
Meyasa yabari yafad'a tarkon son yarinyar da ko baya da rai baiyafe ya aureta ba."

Lallai hajjah tayi gaskiya da tace a tsaya ayi bincike kamar tasan abinda zai faru."

Girgiza kai yayi ya juya yashiga toilet ya d'auro arwala yafito yanufi masallaci."

A sahu d'aya sukayi sallah da sauban kamar yanda suka saba,
Sai dai wnn karon ba wani alamun wasa. Ko sauk'i a fuskar maimarta."

Hakan da Sauban yagani ba k'aramun firgitashi yyi ba, hankalinsa ya tashi, jira kawai yakeyi ayi sallar isha'i sufito yaji meyake faruwa a tafiyar da sukayi."

Bayan sun kammala sallar isha'i sukayi Addu'oe kamar yanda suka saba, sannan maimartaba ya fara fitowa sauban yana biye dashi a baya kamar yanda sukeyi a duk lokacin da suka fito daga masallaci,
Tafiya sukeyi ba Wanda ya tankawa d'an uwansa fuskar Sarki a had'e ba alamun wasa a tare dashi,
Sauban yace "Abba Ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login