Showing 54001 words to 57000 words out of 86876 words

Chapter 19 - DAN SARKIn SAUBAN COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

7432

wuni ya hanya,?"

Lafiya k'alau Alhmdulillah Sarki yace yaci gaba da tafiyarsa sauban yana biye dashi a baya jiki a macce,
Sai da ya kaishi har cikin falonsa kamar yanda yasaba,
Sarki yanemi wuri ya zauna a kan d'aya daga cikin kujerun dake zagaye a falon,

Sauban ya zauna k'asa dai dai gefen k'afar sarki tare da sunkuyar dakai yanajiran yaji abinda Sarki zaifad'a dangane da tafiyar da sukayi k'auyen su safna."

Shuru yaji Sarki baiyi maganaba,
A hankali ya d'aga Kai ya kalli mahaifin nasa,
Ganinsa yayi zaune a inda yake yana duba jarida."

Gaban sauban ya fad'i, a nan take ya tabbatarwa kansa akwai matsala,

Jiki ba kwari ya mik'e tsaye yana kallon Sarki Wanda hankalinsa yake kan jaridar hannunsa,
Ya d'an runsuna yace "Abba zantafi na kwanta sai da safe."

Hannu Sarki ya d'aga masa alamar sai da safe,
cikin mutuwar jiki yanufi hanyar fita,
Yanajiran yaji Sarki yakirashi yaji shuru,
Har zai fita ya juyo yace "Abba magana kakeyi ne?"

Kai Abba ya d'aga ya kallesa ya kuma had'e fuska yace, "cewa nayi idan kafita karufomun k'ofa."

"To sauban yace, yafita jiki a sanyaye tare da rufuwa Sarki k'ofa kamar yanda yace,
Kai tsaye b'angaren hajjah yanufa domin yasan ita bazata b'oye masa Komai ba, dangane da tafiyar dasu Abba sukayi."

Zaune ya tarar da hajjah akan sallaya tana lazimi, sallama yayi yanemi wuri ya zauna yana jiranta,
Ganin shigowarsa yasaka hajjah tak'aitawa ta shafa tare da juyowa ta kallesa cike da k'aunar jikan nata,
Murmushi yasaki ya d'an sunkuya ya gaida ita cike da girmamawa."

Murmushi tasaki tana amsawa tare da tambayar yaya jikin nasa?"

Alhmdullillah yace, ya Kuma natsuwa ya kalli hajjah yace "Hajjah me Abba yace maki dangane da tafiyar da yayi k'auyen gidan gona."

Kallonsa hajjah tayi tace "nima abinda nakeso naji kenan domin tunda yadawo bansaka shi a idoba,
nima inason nasan abinda yafaru a can."

Kajira zuwa gobe zai nemeka ya fadamaka komai, akai."

Mik'ewa yayi tare da yimata saida safe yanufi b'angarensa,

jiki ba kwari, zuciyarsa a dagule domin yanda yaga fuskar sarki yasan akwai matsala,
Kuma yasan matsalar d'aya ce sarki ya binciko asalin safna yasan ko wacece safna,
Tabbas akwai babban tashin hankali a gabansa, idonsa a rufe yake
ya tura k'ofar d'akinsa yashiga domin baya ganin gabansa,
Kai tsaye kan gadonsa yanufa ya fad'a,
Jinsa yayi ya fad'a a jikin mutum,
K'amshin turarenta ya tabbatar masa da Saudat Ce,
Cikin mutuwar miji da kasala, ya bud'e ido ya kalleta sanye take cikin fitinannun kayan bacci farare fes, Wadanda sukayi Mata kyau, Murmushi yasakar Mata ya mayar da idonsa ya rufe , zuciyarsa tana masa zafi Allah Allah yakeyi safiya ta waye yaji abinda Abba zai fad'a akan safna"

Saudat yaji ta kuma rungumeshi tasakashi a jikinta tana Shafa bayansa zuwa kansa cike da kulawa,
Sannu a hankali ya fara sauke ajiyar zuciya cikin minti 30 bacci yayi awon agaba dashi."


Washe gari bayan sundawo daga sallar asuba hakan taka sance tsakaninsa da Sarki sai dai gaisuwa,
Bayan sauban ya dawo part dinsa yayi wanka ya shirya misalin k'arfe goma na safe yanufi fada domin yau zaiyiwa Sarki magana da kansa tunda bai ce masa komai ba har yanzun, saima wani had'e fuska da yaga Sarki yanayi da zarar ya sunyi ido biyu
Kai tsaye yashiga cikin fadar,
Fadawa suna ganinsa sukayita zuba masa kirari,
Yana amsawa snn suka basu wuri domin ya gana da mahaifinsa,

Durkushe ya Kai a gaban Sarki ya kuma gaidashi,
Sarki ya amsa yana kallonsa domin ya fahimci akwai magana a bakinsa,

Sunkuyar da Kai sauban yayi yace "Allah ya taimakeka dangane da maganar safna tafiyar da kayi a k'auyen gidan gona Abba banji abinda kafad'a ba akan taimakon da zanyi"

Had'e fuska Sarki yayi ya kalli sauban yace "abinda yafaru kakeso kaji?"

Sauban ya d'aga Kai yana murmushi alamar eh."

Sarki ya girgiza kai cike da b'acin rai, yace "yarinyar DA kake so ka taimaka shegiyace bata da asali, a gefen gari aka tsinceta,
snn a halin yanzun bata raye ta mutu da ita da Wanda yake Rik'on Nata sakamakon harin da aka kai a garin aka cinnawa gidansu wuta,
Dan hakan saika cireta a ranka idan taimakon marasa asali kakeso kayi katafi gidan marayu ka kai taka gudun mawa zaka sami lada, amma banda d'aukomun shegiya kace zaka aureta ka cud'amun ita a cikin kyakkyawar zuri'a ta."

Gaban sauban ya fad'i, jikinsa ya fara rawa, yashiga tambayar kansa safna ta mutu?"
Ya girgiza kai yafada a zuciyarsa yace "Ina bazai Safna tana raye bata mutuba naji ajikina tana raye,

Da kyar ya nemo natsuwa ya sakawa kansa ya maida Kallonsa a wurin Sarki wanda yake binsa da kallo ganin nan take sauban ya fara firgicewa idonsa yayi ja, amma a yanda yakeji koda sauban zai mutu bazai auri shegiya marar asaliba"

Mik'ewa tsaye sauban yayi tare da yiwa Sarki sallama yafita daga fadar."

Tafiya yakeyi idonsa a rufe baya kallon gabansa Kai tsaye wurin motoci yanufa ya bud'e motarsa yashiga wurin zaman direba ya kunna ya figeta da k'arfi yafita ya d'auki hanyar k'auyen su safna,

Da gudu direba yafito daga d'akinsu yana fadin ranka ya dade Ina zakatafi tuba nakeyi ina tuni sauban yafice,

Kowa sai mmki yakeyi sauban da tuk'i da kansa, kuma ga duk kan alamu baya cikin hayyacinsa, to ko ina yanufa?"

Suka shiga yimasa Addu'ar sauka lafiya a duk inda ya nufa



*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*



🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*Page 33*


*IDAN KINSHIRYA SAYEN LITTAFIN DAN SARKI SAUBAN KIYIMUN MAGANA A WNN NUMBER D'ARI BIYU NE 07066214433*





Gudu yakeyi idonsa a rufe, wanda har baya iya ganin gabansa burinsa kawai ya bud'e ido ya gansa a k'auyen Lassa, a gaban safna."

Gabansa sai fad'uwa yakeyi idan ya tina da kalaman Sarki da yake cewa safna ta mutu tare da mahaifinta,
Dukan sitiyarin mota yayi yana fad'in Safna kina raye baki mutuba, baxaki mutu yanzunba sai na taimakeki na inganta rayuwarki na baki gata tamkar iyayenki suna raye."

Allah kad'ai ya tsareshi ya kaishi k'auyen lafiya, kai tsaye gidansu safna yanufa,
Dam yaji gabansa ya fad'i idonsa ya rufe ya Kai jingine a bakin mota ganin gidansu safna ya koma fili tamkar ba Wanda ya tab'a rayuwa a cikinsa."

Idonsa ya shafa yaji wasu ruwa suna zuba a cikin idon nasa,
Tabbas Ko ba'a fad'a masaba yasan hawaye ne ke zuba a idonsa,
Hannu yasaka ya share hawayen yana girgixa kai tamkar marar hankali yana fad'in ina safna baki mutuba, inaji a jikina kina raye."

Motarsa yaja yanufi fadar maigari,
Bayan duk wad'anda ke gurin sunkawo gaisuwa a wurinsa, Yana amsawa,
ya kalli maigari yace "ranka ya dad'e bani labarin abinda ya faru a k'auyen nan?"

Kamar yanda aka fad'awa Sarki hakan aka fad'awa sauban,
Cewar har yanzun ba'asan inda safna da mahaifinta sukeba, maigari yanuna hanyar da safna da mahaifinta suka yanka a cikin daren,
yace mahaifiyar safna tace anan suka bi a guje hannunta rik'e da na mahaifinta suna yankan gudu."

Cikin sauri sauban ya mik'e tsaye ya koma cikin motarsa ya shiga ya bata wuta tare da yin kwana yanufi hanyar da aka nuna masa su safna sunbi,
Jama'ar gari suka nufeshi suna fad'in ranka ya dade hanyar bata da kyau mota bata bi ta wurin,
KO kallon inda suke baiyiba bare ya sauraresu yabawa motarsa wuta yanufi wurin."

Gudu yake shekawa a cikin dajin yana kiran safna cikin k'arfin murya amma shuru yakeji ba wata safna bare alamunta,

Hakan yake gudu da mota a cikin dajin da bakajin motsin komai sai na tsuntsaye, Dajin k'are kukan kenan domin komai zai iya faruwa da kai batare da wani yasaniba,
Hakan yake tafiya da mota sai kiran safna yakeyi, idonsa a rufe, wani abin yaji ya taka da motarsa Wanda yasaka motar tsayawa,
Cikin zafin nama yafito domin ya duba yagani abinda ya taka, wani irin k'aton k'arfe ne Wanda yasaka tayarsa yin faci
Runtse idonsa yayi bakinsa duk ya bushe idonsa yayi ja ya fad'a, saboda damuwa, d'aga murya yayi da k'arfi yana fad'in Safna kifito ga yarima yaxo zai taimakeki, safna kada kitafi kibar yarimanki, Anan ya bar motar yashiga takawa da k'afa yana shiga cikin dajin ga yamma tayi gaba d'aya babu tsoro a ransa burinsa yaga safna."

Wani abin haji ya sareshi a k'afa,
Dubawar da zaiyi yaga kunama ce tayi masa sara biyu,
Anan take kansa ya sara ya fara ganin jiri, amma tafiya yakeyi yana kiran safna,
Duhu yashiga gani a idonsa anan take ya yanke jiki ya fad'i a wurin a some bakinsa ya rufe da kiran sunan safna."

Dattijiwar nan bafulatana ta bayyana a gabansa, tana murmushi cike da burgewa da tausayin sauban,
Cak ta sanya hannu ta d'aukeshi a wurin tanufi motarsa dashi, shafar tayar motar tayi ta gyaru tashiga motar tafita dajin gaba d'aya,
A cikinn runfar da safna ta zauna a lokacin da ta taimaketa a cikin dajin a anan tasaka sauban Wanda yake kwance a some kamar Wanda babu rai a tare dashi, taimaka masa tayi tacire masa dafin kunamar a k'afarsa snn ta shafi wurin da hannunta anan take ya daina yimasa ciwo snn ta hura masa iska a baki anan take sauban ya bud'e idonsa tare da karanto Addu'a a bakinsa amma abin mamaki Kafin yakai k'arshen Addu'ar zaiji matar ta iyar masa,
Ido yabita dashi yana fad'in a Ina nake?"
Wacce ce ke?"


Murmushi tayi tace "ka kwantar da hankalinka don kuwa suma kayi a cikin daji mai had'arin gaske, kada ka kuma gigin cewa zaka koma cikin dajin domin komai zai iya faruwa da Kai."

Kallonta yakeyi baiyi maganaba,
Hawaye kawai yaji sunabin fuskarsa, cikin yanayin tausayi yace "yanzun shikenan safna ta mutu?"
Safna marainiyace bata da iyaye hakan rayuwarta ta k'are cikin wahala daga k'arshe tayi mutuwar wulak'anci a cikin Daji,
Ya juya ya rik'o hannun dattijiyar yace " Inna "bansan so ba, bansan KO meye so ba, amma abokina Safwan yana yawan fad'amun cewar son safna nakeyi nakanji duk wani bugun zuciyata safna ce duk wani numfashi na safna ce inna hakan shine so?
A yanda nakeji a cikin zuciyata tunda safna ta mutu nima mutuwa zanyi."

Girgiza kai dattijiwar tayi tace "baxaka mutuba d'ana, Safna tana raye bata mutuba,

Cikin sauri sauban ya kalleta cike da mamaki tace "nice na taimaki safna a cikin wnn dajin kamar yanda na taimakeka a yanzun, safna tana raye tana zaune a cikin garin adamawa sai dai tana tare da farin cikinta, kashiga gari ka nemeta dan kuwa ba'a samun macce kamar safna mai tsananin baiwa a kyauta, batare da ansha wahala ba."
Akwai farin ciki a tsakaninku akwai wani haske a tsakaninku itace komai naka itace majinginin rayuwarka kamar yanda mahaifiyarka ta fad'a Dan haka ya zama dole kashiga gari ka nemo safna a duk inda take."

Cike da mamaki yake kallo dattijiwar yace "Inna dama kinsan mahaifiyata ne?"

Murmushi ta saki tace "yanzun ba lokacin wnn tambayar bane katafi kaje kayi abinda nace,

Cikin sauri ya mik'e tsaye batare da yamata musuba, ta mik'a masa key din motarsa ya bud'e yashiga ya tayar ya dauki hanyar gida."

Hankalin Sarki idan yayi dubu to ya tashi, a lokacin da labari yazo masa cewar sauban yafita da mota shikad'ai snn koda yafita baya cikin natsuwar shi, hankalinsa bakaramun tashi yayi ba sai zufa yake gogewa a kai akai, yana kiran wayar sauban din kashe take."

hankalin kowa a tashe har magariba sauban baidawoba,
Saudat sai kuka takeyi tana fadin tabani ta lalace, sadaukinta ya b'ata

Sarauniya Jamila sai murna takeyi domin duk a tunaninta asirin da tamasa ne ya fara aiki a kansa sai fad'i takeyi daga can sai bangon duniya."

Ana kiran sallar insha'i sauban yana shigowa gidan,
anan take labari yasami Sarki cikin gaggawa yatura a Kira masa shi,

tun kafin yashiga b'angarensa umurnin kiran mahaifinsa ya sameshi,
Ya juya ya fasa shiga part din nasa yanufi wurin mahaifinsa."

Fad'a sosai Sarki yake masa akan fitar da yayi batare da izininsa ba, snn Ina yatafi?"
Sunkuyar da kai k'asa sauban yayi yace "Abba kayi hakuri kauyen gidan gona natafi domin na duba safna, saboda tun lokacin da kacemun ta mutu hankalina ya tashi nakasa samun natsuwa har sai da natafi k'auyen da kaina."

Mari Sarki ya tsinkawa yarima abinda baitab'a yimasa ba tinda aka haifesa, cikin fushi yace "wato ni k'arya nafad'a maka kenan KO?
Wanda har yasaka sai da katafi da kanka kayi bincike, akan shegiya marar asali."

Sauban yana Rik'e da kunci kansa sunkuye a k'asa,
Yace "Abba kayi hakuri na tuba baxan sakeba, amma tafiyar da nayi nasamo labarin Safna tana raye bata mutuba tana cikin garin nan na adamawa."

Sarki ya kuma har zuk'a yace "wallah tallahi na rantse da Allah bazaka auri shegiya marar asaliba kana matsayin d'an gidan sarauta, kai ko bayan raina ban yafe ka aureta ba, Kai koda mutuwa zakayi a kan sonta gara ka mutu na d'auki gawarka na binne a cikin cikin k'asa, da hannuna *TIRK'ASHI* zaro ido sauban yayi idonsa yana fitar da hawaye abinda Sarki baitab'a ganiba akan idon d'ansa cikin sakan d'aya sauban ya zube a wurin bakinsa yana zubar da jini da hancinsa,

Cikin dakewar zuciya Sarki yakira fadawa yace ku d'aukeshi kuyi asibity dashi gani nan zuwa yanzun."

*************************

Alhmdulillah jikin safna tasami lafiya sosai inda take samun kulawa a wurin Hajiya falmata, da Alhaji Habib naira inda suke janta a jiki suke jikinta tamkar yarsu wacce suka haifa da cikinsu,

Ganin tasami lafiya likita yabasu sallama Hajiya falmata ta Rik'a safna suka nufi gidanta da ita dake cikin garin na adamawa,
Sosai Hajiya falmata ta gyara safna da kanta ta zuba mata ruwan wanka tare da turarunka masu k'amshi ta, tanuna mata duk yanda zatayi amfani da duk abinda ke cikin toilet din,
Bayan safna tayi Wanda tayi brush hajiya falmata tashiga wanke mata kanta da mayunkan wankin kai, anan take gashin safna ya fara haske da gyalli, yazubo mata har a gadon bayanta,

Masha Allah Hajiya falmata tace tana kallon safna cike da sha'awa da burgewa, ta rungumota zuwa jikinta suka fito daga toilet din,
Da kanta ta gyara mata gashin ta saka ribon ta daure matashi, snn Tashafa mata Mai ajikinta tayi mata kwalliya ba mai yawaba, ta d'auko wata doguwar rigar abaya bak'a cikin wad'anda akayi mata odarsu daga Dubai kasancewar itace sa'arta, tasakawa safna tare da d'aura mata d'ankwalin, Masha Allah kuzo kuga yanda safna tafito tayi kyau gaba d'aya Annurin fuskarta da kyawonta da kwarjinita duk sun bayyana,
Babu abinda Hajiya falmata kecewa sai Masha Allah,
Kunya ta kama safna tasaki murmushi ta rik'a hannun Hajiya falmata wacce take Kira da umma, tace "umma nagode Allah ya faranta maki kamar yanda kike k'ok'arin farantamun yanda kika taimakeni kema Allah zai taimaki ya k'ara d'aukakaki"

Dam gaban Hajiya falmata ya fad'i, yanda taga safna tana murmushi tamkar Alhaji Habib ne mijinta yake murmushi a gabanta, yanda safna take magana tana rausayar Kai hakan Alhaji Habib yake magana wani lokacin har kwaikwayonsa takeyi, kuma kallon fuskar safna tayi sai gani tayi ta koma Mata sak mijinta Abin k'aunarta Alhaji Habib, wani murmushin safna ta kuma Saki Wanda yasaka har k'oranta suka bayyana, a k'asan leb'onta Hajiya falmata taci Karo da wani tabo Wanda harta mutu baxata manta da wnn tabonba a bakin sulaihat 'yarta, Wanda tabon na gadone gadarsa tayi a wurin mahaifiyarta."

Da sauri Hajiya falmata ta mik'e tsaye cike da firgici





[3/30, 9:56 PM] Hayat: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍



🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*Page 35*






A kan gadon Alhaji Habib Naira ya nufa ya nemi wuri ya zauna a gefen gado, ya Rik'o hannun safna yana kallo,
tabbas komai nata irin nasane yace zonan 'yata ya janyota zuwa jikinsa ya d'ura kanta akan kafad'arsa yana fad'in "hak'ik'a ke 'yatace ke jina nace na tabbata hakan tun ranar da nafara ganinki a asibity jikina yabani ke jinina ce.",

Ya kalli Hajiya falmata yace "Hajiya kinga yanda Allah yake nasa iko, 'yarmu tadawo garemu cikin ruwan sanyi, bayan munshare shekaru muna nemanta, ya d'aga hannu sama yana fad'in Kai Alhamdulillah Allah mungode maka."

Kuka Safna ta fashe dashi, ta tashi daga kan jikin mahaifin nata tace "Abba umma meyasa kuka jefar dani a lokacin da nake neman taimakonku? Menamaku kuka watsar da rayuwata a gefen hanya, bakuyi tunanin halin da Zan shigaba na tsakanin mutuwata da rayuwata."

Janyo ta Hajiya falmata tayi tana lallashinta tace "Suhailat shine ainahin sunanki Wanda mahaifinki ya nad'a maki, a ranar sunanki kasan cewar ke kad'ai muka mahaifa a duniya kuma tin daga kanki bamu kuma samun wata haihuwar ba ."

Mahaifinki yanada Mata biyu nice Amaryarsa uwargidansa Allah ya Mata rasuwa a sanadin ciwon hawan jini Wanda baya rasa nasaba da rashin haihuwar da Allah bai bata ba."

Ranar juma'a aka haifeki a babbar asibityn kud'i dake garin nan na Adamawa,
ranar da aka haifeki a ranar mahaifinki da duk wasu masoyinsa sai da suka tayashi murnar samun haihuwa da akayi masa a gidansa, Wanda sun san ita kad'aice Allah bai bashiba amma duk wani jin dadi na duniya mahaifinki yana dashi."

Anan take haihuwarki ta zagaye garin Adamawa dama wajenta domin mahaifinki babban mutum ne ya tara dukan komai a rayuwa uwa uba ga taimakon talakawansa."

Ranar sunanki, a ranar munga duban jama"a wadan baki bazai iya fad'ar iya adadin mutanen da suka halarci bikin sunanki ba,
Kafafen yad'a labarai kuwa ko ta ina watsa hotunanki akeyi ana sambarka."

washe garin sunanki misalin k'arfe uku na dare kina tare da mahaifinki akan gado d'aya,
kasancewar dake yake kwana akan kirjinsa sai dai idan kikayi kuka na farka nabaki nono kisha ya kuma karb'arki ya d'ora akan k'irjinsa, yana matuk'ar ji dake Wanda yakai baya iya b'oye soyayyarki a duk inda yake."

Kwatsam na kammala baki nono kenan na mik'awa mahaifinki ke ya rungumeki,
sai ganin mutane mukayi a gabanmu Rik'e da bindigogi dukansu fuskarsu a rufe take basa da kyan gani saboda girman halittarsu,
Hannu suka mik'awa mahaifinki suna fad'in kabamu ita,
Ita kad'ai mukeso, bamason komai naku."
Idan ba hakan ba zamu kasheku dukanku mu d'auketa mutafi da ita."

Babu irin magiyar da mahaifinki baiyi masuba akan suyi hakuri zaibasu duka abinda ya mallaka a duniya, amma sukace sam basaso ke sukeso sutafi dake,
Narasa dalilinsu nayin hakan,
Anan mahaifinki yaga da gaske tafiya zasuyi dake ya rungumeki yana fad'in sai dai sukashe shi amma baxai bayar dakeba,

Babban cikinsu ya saita bindiga ya harbi mahaifinki a k'afa Wanda idan kika lura da tafiyarsa baya tafiya dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login