Showing 9001 words to 12000 words out of 86876 words

Chapter 4 - DAN SARKIn SAUBAN COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

7417

Bata wani turaren Wanda zasu dinga turarawa a lokacin da sukasan Bintu zata shak'i warin turaren a ko wacce Rana har tsawon wata bakwai,
Wanda da zarar tana shak'ar warin turaren ako da yaushe to abinda ke cikinta bazai tab'a fitowa da raiba sai a macce."

Hakan akayi kullum safiyar Allah sai sunyi turaren wnn maganin a k'ofar b'angaren Bintu a inda aka San Bata gani."

Bintu baiwar Allah tana ciki a kwance tana fama da laulayin cikinta kuyangi sai hidima sukeyi da ita,
dazarar sunyi turaren tashak'i warinsa, zata dingaji tamkar an k'ara mata wani wutar azabar ciwo a tare da ita."

Wasa Wasa Bintu duk ta rame ta fita a hayyacinta ga azabar laulayi ga a azabar turaren da Jamila take turara Mata, Abdullah ya Kuma tud'ewa Yana tausayinta sai kula yakeyi da ita fiye da tunanin Mai karatu, wani lokacin yakanji warin turaren Amma baya kawo komai a ransa."

Ana hakan cikin Bintu ya tsufa ya Kai wata Tara ya girma sosai a lokacin lafiya ta Fara samuwa da ita duk wani laulayi ya Kau haihuwa ake jira, da zarar jamila tayi Ido biyu da cikin ji takeyi kamar ta kurma ihu ko tasanya bindiga ta harbeta daga ita har cikin su mutu kowa ya huta."

Wani Lokacin takan Kira jakadiya ta dinga ce Mata Anya kuwa abin dake cikin Bintu ya mutuwa kowa?"
Jakadiya zatace ki daina ko kwanto a Kai yamutu ranki ya dad'e domin bokanya Bata k'arya da zarar tafad"i magana to sai ya faru."
Snn hankalin Jamila ya kwanta ta d'an saki murmushi, tace na tsani Bintu kamar yanda na tsani mutuwa ta."

Wani dare da k'arfe uku Bintu ta tashi da nak'uda a lokacin tana tare da Abdullah ganin yanayin da take ciki yasa yafita yaje yakira jakadiyar Hajjah Domin yasan Hajjah kawaici ne da ita ko ya fad'a Mata bazuwa zatayiba
Jakadiyar Hajjah danjijuwace wacce zata iya Kai shekara 45 Amintacciyace a wurin Hajjah Domin Yardar da Hajjah tamata itace ta raini Abdullah tin Yana k'araminsa tsakaninsa da mahaifiyarsa hajjah sai dai yasha nono ya tafi wurin jakadiyar Mai suna ANNA."

Suna zuwa tare da Anna cikin sauri sai dai sukaji kukan jariri Wanda kukansa ya k'arad'e b'angaren Yarima Abdullah duk wani mutum Wanda yake rayuwa a cikin sashen gaba d'aya yaji kukan jaririn,
zubbur Jamila tayi tafito daga d'akinta Jin kukan jariri da tayi,
Dama wani bacci kirki takeyiba domin tinda taga cikin Bintu ya tsufa ya Isa haihuwa ta daina kwana da Ido biyu sai da da Ido d'aya Domin tana sauraron taji bintu ta haihu,
babban burinta shine taji ance Bintu ta haihu abin da ta haifa ya mutu, idan da Hali tafison tabi d'anta su mutu a tare."

Jin kukan jaririn da tayi yasa tafito da sauri ba ko mayafi a kanta,
tana zarar Ido tanufi b'angaren Bintu tana fad'in a Ina nakejin kukan jariri."

kitibis tayi da santalelen d'a namiji sak mahaifinsa wani b'angare ya d'ebo mahaifiyarsa Yana hannun Anna ta gyarashi cikin kayan sanyinsa ruwan Madara masu tsananin kyau."

Ido biyu sukayi da Anna suka kalli juna,
Jamila tayi saurin sakin murmushi tare da mik'a hannu zata k'arb'e jaririn tana fad'in "ya akayi hakan, taga yaro Yana motsi cikin k'oshin lafiya, gabanta ya fad'i ta mere Baki tace Amma dai
macce ce aka haifa ba namijiba,
Anna tace namiji ne magajin sarki insha Allah had'ida mik'awa yarima Abdullah jaririn,
Wanda hankalinsa Yana kan Bintu wacce take kwance a kan gado tana kallon kowa d'aya bayan d'aya tana murmushi."

Jamila na ganin Anna ta hana Mata jaririn yasa taja da baya ta juya tafita daga d'akin Bata Kuma furta komai ba zuciyarta tana tafarfasa,

tsakanin Anna da Jamila Kar Tasan Karne domin Anna tasha Kama Jamila a bayan gida tana bine wani abin ko tasamesu suna magana tare da jakadiyarta,
Wnn dalilin yasa Jamila take shakka Anna domin rufuwar asirinta domin tasan Anna jardadiyar sarki ce sosai komai tafad'a Masa baya musu zai yarda"

A Ranar kasa Zama Jamila tayi sai hawayen bak'in ciki yake Mata Ambaliya a fuska ganin tanaji tana gani wata tazo daga baya ta haihu kuma d'a namiji ita Kuma ko b'atan wata bata tab'ayiba tabbas dole ne ta Hana wnn yaron Zaman duniya dole ne ta salwantar da rayuwarsa Kai har ma da rayuwar mahaifiyarsa."

Washe gari gaba d'aya gidan sarautar ya karad'e da murna bintu matar Yarima Abdullah ta haifi d'a namiji,
Maimartaba sai da yayi sujjada ga mahaliccinsa domin Jin dad'i Wanda Kuma yazo Masa da Albishir ya Masa kyauta ta ban girma, hakan Hajjah sai da ta zubar da hawaye Dan murna,
A ranar gidan kowa cike yake da murna da farin ciki sai hada hada akeyi fuskokin kowa cike suke da murna Amma Banda Jamila da jakadiyarta."

A ranar suna yaro yaci sunan SAUBAN, Wanda maimartaba sarki yasaka Masa sunan da kansa sabida Yana tsananin son sunan domin ya Sha Alwashi da zarar anyi haihuwa a gidan indai namiji aka haifa to baya da wani suna da za'a saka Masa bayan SAUBAN."

Bikin sunan Sauban bikin sunane Wanda ba'a tab'ayin irinsa ba a gidan sarautar domin bikine na masarauta biyu masarautar zamfara da masarautar Adamawa ko wanne yanaji da kud'i da mulki kuma ko wanne Yana nuna farin cikinsa da tashi bajinta domin Sauban shine jika na farko a masarautar biyu."

Farin ciki a wurin Abdullah Abin ba'a magana domin duk inda yake Yana tare da matarsa da d'ansa Wanda hakan ya Kuma k'onawa Jamila rai k'ara d'auki Alwashin sai ta salwantar da rayuwar Bintu da d'anta Sauban."






*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍



🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*DIDECTED TO Fateemah M Uthman*





*Page 7*






Bayan bikin sunan SAUBAN Anna ta dawo da Zama gaba d'aya a b'angaren Bintu domin kula da ita da jaririnta, bisaga umurnin Hajjah domin tasan Jamila zata iya aikata masu komai idan taga ba kowa a kusa dasu tinda ba mutumci da imani ne da itaba."

Sauban da mahaifiyarsa sun Sami kulawa ta musamman.a wurin Anna domin gasasu takeyi da ruwan zafi yanda ya kamata."

Wanda hakan yayi matuk'ar k'ona ran Jamila,
domin bataso Anna ta dawo b'angaren Bintu da zamaba,
burinta shine ta fakaici idon mutane tashiga d'akin ta Sanya hannu ta shak'e wuyan Sauban ta kasheshi da hannunta kowa ya huta, Amma Ina ba Hali Anna ta saka Mata Ido sosai."

Hakan suka kammala jegonsu cike da kulawa tare da tarairaya a wurin Anna da Abdullah."

Sauban ya girma yayi wayo ya taso cikin farin jinin Al'umma gashi kyakkyawa ya d'ebo kyawon mamansa da babanshi duk Wanda yaga Sauban sai yaji yaron yashiga ransa, Wanda Jamila da zarar tayi Ido biyu dashi takejin tsananin tsanarsa a ranta Bata k'aunar ta gansa Dan hakan duk wata hanya da zaisaka ta tayi Ido biyu da Sauban Bata bi,
A kullum safiyar Allah tunaninta d'aya ta wacce hanya zatabi ta kawar da sauban da mahaifiyarsa a doron k'asa."

Ana hakan Sauban sai Kuma girma yakeyi Yana wayo Wanda a yanzun shekararsa biyu baya da wurin Zama sai fada kusa da sarki, wani lokacin tare da sarki suke kwana a d'aki d'aya saboda k'aunar da sarki yake Masa,
Sauban jarumine tin Yana k'aramunsa ba k'aramun Abu ne yake sakashi kukaba, ko fad'uwa yayi hakan zai tashi da kansa batare da an tayar dashiba, Kuma
ba alamar kuka ko Jin ciwo a tare dashi, snn baya da yawan magana tin Yana k'aramunsa domin ko magana ake Masa idan ba yaga damar amsawa ba baya amsawa shuru yakeyi tamkar bayaji, wani lokacin Kuma sai dai ya d'aga hannu alamar ya amsa.
Wnn halin nasa yasaka sarki yake matuk'ar son shi domin jinin sarauta ne Yake yawo a jikinsa,
hakan Yana nuni da cewa jarumin maza ne, za'ayi fafatawa dashi a fagen fama,
Dan hakan sarki ya d'auki harmar bashi wani magani Mai saka jarumta da kaifin basira tare da kuzari."

Shekarar Sauban biyu da rabi mahaifin Bintu ya rasu wato sarkin zamfara,"
Mutuwar da tarazana Bintu tare da sarki da Abdullah da Kuma Hajjah."

Bintu tayi bak'in cikin mutuwar mahaifinta sosai,
Wanda kuka da kewarsa ya kasa tsaya Mata a fuska,
Abdullah sai aikin lallashinta kawai yakeyi."

Bayan wata d'aya aka nad'a babban d'an sarkin zamfara wato yayan Bintu a kan kujerar mulkin."

Bayan an nad'a sabon sarkin zamfara, akazo wurin rabon gado anan ake fad'a Mata tin kafin mahaifinsu ya rasu ya bar wasiyar cewa gidan gonarsa dake Adamawa a can cikin wani k'auye Mai suna lissa, ya bawa Bintu gidan gonar kada a sakashi a cikin rabon gado saboda tin Bintu tana k'arama take matuk'ar son gidan gonar Dan haka natane ya Bata, a fad'a Mata hakan a Kuma dank'a Mata ta kardunsa a hannunta."

Bintu taji dad'in kyautar gidan gonar da mahaifinta ya Mata tashiga yi Masa Addu'ar samun rahamar ubangiji,
Domin itama tana tinanin gidan gonar a ranta tana Addu'ar Allah yasa idan za'ayi rabon gado ya fad'a a cikin gadonta Domin tana tsananin son wurin tin tana k'ara hakan wani lokacin sarki zai d'auketa sushiga jirgi ya kaita gidan gonar domin kawai farin cikinta,
Har zuwa girmanta Wanda ta mayar da zuwa gidan gonar duk k'arshen wata take zuwa tana kwana biyu a cikinsa tare da kuyangi tana nishad'i da farin ciki domin duk lokacin da tsinci kanta a cikinsa tana jinta cikin wani farin ciki marar misaltuwa hakan zata dinga murmushi da annashawa a cikinsa tanaji a jikinta akwai wani farin ciki babba Wanda ya danganci rayuwarta a cikin gidan gonar, Wanda Yake Cikin k'auyen Lissa a k'ark'ashin k'aramar hukumar mulkin Adamawa State."

Bayan an kammala rabon gado,
Bintu ta dawo gida tare da Abdullah da Sauban,
Hakan Abdullah yaci gaba da kular mata da gidan gonar tamkar mahaifinta Yana Raye."

duk k'arshen wata suke zuwa ziyara gidan gonar kamar yanda takeyi a can baya,
tare da shi da ita da Sauban a lokacin Yana da shekara uku a duniya,
Hakan Yana matuk'ar sanyata farin ciki, Yana cire Mata damuwar rashin mahaifinta da tayi."

Ana hakan Bintu ta Fara laulayin samun wani cikin,
Wanda Abdullah ya fahimci cikine da ita ya shiga farin ciki,
Anan take gidan sarautar kowa ya d'auka Bintu ciki ke gareta duk kowa yashiga murna da farin ciki duk Wanda ka kalli fuskarsa a lokacin Yana cikin murna da farin cikin samun cikin bintu."

Amma Banda Jamila domin k'ura takai Banga tsakaninta da Bintu duk abinda za'ayi sai dai ayi saboda bazai yuwo ta Kuma haihuwa a gidan Nan ba."

Ana hakan cikin Bintu ya Kai wata hud'u,
Tafiya ta Kama Abdullah zuwa Bauchi wurin nad'in sarautar babban Abokinsa Kuma Amininsa wato Yarima Hayat Wanda mahaifinsa sarkin Bauchi ya mutu, za'ayi bikin d'ora d'ansa Hayat akan kujerar sarauta."

Yaso yatafi da Bintu sai dai yanayin jikin nata ne batajin dad'in sa,
Kuma yasan zainab bazata bishiba saboda Bata k'aunar d'agawa daga gidan tayi ko tafiyar wuni d'ayace saboda kada tabar kujerar mulkinta."

Hakan ya shirya yayi tafiyarsa shi kad'ai cike da kewar matansa musamman Bintu wacce take cikin lalurar laulayi."

Tafiyarsa tayi matuk'ar yiwa Jamila dad'i,
Dama ta shirya ai watar da komai na mutuwar Bintu tare da d'anta Sauban tako wacce hanya tinda maganin boka baya tasiri a kanta, idan tasan wata ai Bata San wataba."

Hakan yasa tayo hayar manyan 'yan ta'adda domin su kashe Bintu da d'anta Sauban,
Anan tabasu Kayan bayin gidan suka saka a jikinsu Dan gudun kada a ganesu,
Kasan cewar gidan cike Yake da bayi da kunyangi suna shawagi Rana da dare."

Wani dare Bintu tana kwance ita kad'ai, a lokacin Sauban Yana tare da sarki,
Domin tinda ta Fara ciwo Yake kwana a wurin maimartaba,
Acan cikin baccinta taji sautin muryar gardawa a kanta cikin sauri ta bud'e idonta,
Ai Kuwa tayi arba da gardawa sanye da kayan bayi,
Wanda da zarar ka gansu kasan ba bayi bane,
Addu'a tashigayi d'aya daga ciki ya Sanya hannu ya make Mata Baki a anan take jini ya cika Mata bakin gaba d'aya."

Yunkurin tashi takeyi d'aya cikinsu yabita ya haye kanta ya sanya filo ya danne kanta,
Sai da yaga Bata motsi alamar ta mutu snn ya dagata suka gyara Mata kwanciya kamar wacce take bacci snn suka fita suka bar d'akin."

Basuyi tinanin Ina d'anta Yake ba,
Sukayi ficewarsu.

Suna fita sukaci karo da Jamila, sukayi Mata nuni da aiki yayi kyau, ta mik'a masu jakar kud'insu suka fita ta hanyar baya."

Safiya tana wayewa a gidan sarautar hankalin kowa a tashe cewar ankwanta da Bintu ba'a tashi da itaba,
Mutuwar da tafirgita kowa a gidan duk Wanda kagani cike Yake da bak'in ciki fuskar kowa sai zubar da hawaye takeyi."😭
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍



🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*DIDECTED TO Fateemah M Uthman*





*Page 8*





Abdullah Yana cikin jama'a ana hidimar bikin nad'in sarautar Abokinsa Hayat gabansa sai fad'uwa ykeyi yarasa dalili, anan take jikinsa ya soma rawa yaji a duniya ba Wacce yakeso yagani sai Bintu, anan take ya Tina halin da ya barta na tsananin laulayi,
Hakan ya fito daga cikin taron mutanen batare da anlura dashiba ya shiga motarsa tare da fadawansa suka d'auki hanyar komawa gida baiyi sallama da kowa ba."

Saukarsu kenan bai wani jira aka bud'e Masa murfin motarba ya bud'e da kansa gabansa Yana fad'uwa,
Kai tsaye b'angaren Bintu yanufa jikinsa sai rawa yakeyi ji Yake akwai abinda ya Sami Bintu
Tafiya yakeyi kamar zai tashi sama burinsa ya gansa a b'angaren Bintu Wanda duk inda ya gifta fadawa da bayi sai kallonsa sukeyi cike da tausayi wasu suna sharar hawaye.'

Bai lura da kowa ba domin idonsa a rufe yake hakan yasa bai fahimci kallon da ake masaba bai Kuma fahimci kukan da bayi da kuyangi sukeyi ba, hakan yasanya gaba cikin sauri ya Isa b'angaren Bintu, Wanda tin a k'ofar b'angaren nata ya ganshi cike da mutune sai a lokacin ya lura da yanayin fuskokin mutanen dake wurin zaune ko wanne ya rafka tagumi,
ko wanne cike yake da damuwa wasu suna matsar hawaye."

Gabansa ya fad'i cikin Azama ya tinkari d'akin Bintu Wacce aka kammala shiryata cikin sitirarta tana sanye da linkafani fari fes Wanda yayi Mata kyau fuskarta sai wani Annuri take fitarwa ga murmushinta Mai sanyi a kan fuskarta,
Kai tsaye ido rufe yazo wurinta ya durk'usa Yana fad'in Bintu tashi nadawo Yaya jikin naki, ko mutafi asibity ne,? Bintu kitashi Mana Yana girgizata?"
Ji yayi andafashi ta bayansa yayi saurin juyawa yaga Hajjah ce tana matsar hawaye abinda tin tashinsa bai tab'a gani a idon Hajjah mahaifiyarsa ba, ya Kuma rud'ewa,
Hajjah ta d'agoshi ya mik'e tsaye ta rungume shi tana fad'in Abdullah sai dai kayi hakuri domin Bintu ta rigamu gidan gaskiya ankwanta da ita ba'a tashi da itaba."

Wani irin razana yayi yasaki jikin Hajjah yanufi wurin gawar Bintu yashiga girgiza Yana fad'in kitashi Bintu Baki mutuba kitashi." Ina shuru ba motsi Bintu ta mutu,
Wani irin kuka yasaki Mai tsoma zuciya Yana rungume da gawarta."
Tausayi ya Bawa duk mutanen dake wurin suma sukashiga zubar da hawaye Mai k'arfi."

Ana hakan sarki ya shigo tare da sarkin zamfara dama su ake jira ayi Mata sallah akaita gidanta na gaskiya,

Ganin kukan da Abdullah yakeyi yabawa sarki tausayi ya d'agoshi ya rungumeshi Yana fadin daina kuka Yarima Addu'a ya kamata kayiwa Bintu adai adai wnn lokacin Addu'arka take buk'ata, in har kacika masoyinta,
Kasani ko wanne Mai Rai zai mutu muyiwa kanmu fatan cikawa da imani Bintu lokacinta ne yayi."
Hakan sarki yayi ta kwantarwa Abdullah da hankali har yayi shuru ya daina kuka ya koma Kukan zuci wanda yafi komai zafi,
Hakan aka d'auki Bintu akayi Mata sallah snn aka kaita gidanta na gaskiya."

Sai da aka Kai Bintu aka dawo snn Jamila tafito daga b'angarenta tana kukan munafurci tana fad'in bintu da Sauban Allah ya jik'anku hak'ik'a munyi Rashi babba a gidan nan"

Kyara kalamanki Sauban Yana raye bai mutuba,
Sautin muryar Hajjah taji ya dura a kan dodon kunnenta,
Wanda yasa tayi saurin d'aga Kai a zabure ta kalli Hajjah da Anna sai Kuma Sauban dake kusa da Anna Yayi shuru Yana kallon kowa d'aya bayan d'aya bini bini sai ajiyar zuciya Yake saukewa
jama'a duk sun zagayesu ana amsar gaisuwa."

Kallon da Jamila tabi Sauban dashi cikin firgita yasa Hajjah ta d'ora a alamar tambya a kanta, hakan Anna wacce ta anyana a ranta tabbas mutuwar Bintu lokaci d'aya akwai wata sarka'nkiya a cikinta Amma insha Allah komai zai bayyana gaskiya zatayi halinta."

Saitin muryar Hajjah ta kumaji tana fad'in " Sauban ba zai mutu a yanzun ba sai ya hau kujerar mulkin mahaifinsa bayan yayi murabus, kalaman Hajjah kenan karo na biyu."

Zaro Ido Jamila tayi cikin sarkewar murya tace "tuba nakeyi ranki ya dad'e nayi kuskure abinda akacemun kenan."

Ta Kuma kallon Sauban tace "zo Nan yarona hak''ika nayi farin ciki da ganinka Cikin k'oshin lafiya Allah ya jik'an mahaifiyarka."

Ko kallon inda take Sauban baiyiba domin ko can dama baya yarda da ita, basa Zama inuwa d'aya da ita,
Sabida duk suka had'a wuri d'aya daga ita sai shi sai tayi Masa mugunta
Musamman idan Abdullah ya d'aukoshi ya shigo dashi sashenta bazai fitaba sai ta fakaici idon Abdullah tayi Masa muguntar da zata sakashi kuka har ya daukeshi ya mayar dashi wurin mahaifiyarsa."

Ganin ko kallon inda take Abdullah baiyiba, taji haushi ta mik'e tsaye tana fad'in Allah ya bamu hakurin rashin bintu."
Bayi suka amsa da Amin gimbiya Allah ya biya ya k'are Mana lafiyarki."

Muryar Hajjah taji tana fad'in Allah yasa da gaske akeyi komai zai fito fili asiri zai tonu za'ayi hukunci marar dad'in ji da sauraro idan gaskiya tayi halinta, daga Abdullah sai Sauban a fagen sarauta domin sune suka cancanta, ko bayan ran kowa a wurin nan."

Murmushin da yafi kuka ciwo Jamila tayi Bata tankawa Hajjah ba illah ma tayi kamar bada ita takeba ta wuce ta fita."

Tana shiga sashenta tashiga cire Alk'yabbar jikinta tayi jifa da ita tashiga Kiran jakadiya, cikin hanzari jakadiya ta zube gabanta,
Jamila ta dubi jakadiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login