Showing 33001 words to 36000 words out of 86876 words

Chapter 12 - DAN SARKIn SAUBAN COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

7418

Sauban yabiyo bayansa, cike da mulki da k'asaita, Yana fito yashaki k'amshin garin yayi saurin lumshe idonsa tare da d'aga kansa sama cike da farin ciki Yaci gaba da shak'ar iskan garin Wanda Yake yawan sanyashi farin ciki da Annashawa."

Gidan gonar yashiga k'arewa kallo Yana Mai murmushin Jin dad'i da farin ciki a fuskarsa."

Sai da ya d'auki minti goma a hakan fadawa duka sun zagayeshi snn ya juya yafara tafiya suka rufa Masa baya zuwa cikin gidan gonar a wurin da suke sauka idan sukazo."

Fad'in fad'i da girman wurin tare da tsaruwar wurin Bata lokaci ne Amma iya tsaruwa wurin ya tsaru babu abunda babu a cikinsa Dan gane da kayan fruit da duk wani Abinda ya danganci shuke shuke,
A can d'aya b'angaren Kuma wani wurin hutawane Wanda aka zagayeshi da manyan kujerun k'arfe domin zama,
Sai Kuma gefe D'aya da na hango wani babban dining table ne da alama shima an ajiyeshi ne domin zama asha fruit,
sai Kuma wasu manyan d'akuna guda uku da na hango a jere da juna wad'anda anyisu ne domin hutawa musamman idan tafiyar kwana tasameka, babu abunda babu a cikin d'akunan na dangane da kayan buk'atar rayuwa, d'aya daga cikin d'akunan wanda Naga Anfi k'awatashi da komai a cikinsa Bintu take sauka wani lokacin suke kwana a duk lokacin da sukazo tare da maimartaba Suna hutawa."

A can d'aya b'angaren dake kallon Bayan gari,
wani Babban wurin wanka ne anzagayeshi da furanni Wad'anda suka k'awata wurin,
cike wurin Yake da ruwa gwanin ban sha'awa."

Idan Kika matsa gaba kad'an fanfuna ne tare da rijiyoyi wad'anda sarki yasaka aka Gina domin jama'ar k'auyen su dinga Shigowa ta k'ofar baya suna dibar ruwa kasancewar k'auyen suna fama da k'arancin ruwa amfani."

K'auyen Lassa k'auyen ne na fulani, ko fulanin ma irin fulanin dajin Nan masu masifar kyawo wad'an suke rayuwa a cikin daji tare da shanunsu da 'yayansu da matansu."
Domin duk inda ka wurga idanunka tungayen fulanine tare da bukkokinsu dake k'ank'afe a tsakiyar k'auyen sai tarin shanu da suke shawagi suna kiwo a cikin k'auyen."

K'auyen Lassa basa Wasa da Al'adunsu na fulani wad'anda suka tarar anayi suka gada tin daga iyaye da kakan ni hakan Kuma suna girmama Wanda Yake d'aukar Al'adunsu da muhimmanci ."

*****************

D'aya daga cikin kujeren dake jere a wurin Sauban yaje ya zauna ya d'ora k'afa d'aya Kan d'aya daga cikin kujerar Yana sauke murmushin farin ciki, domin idan bai Manta ba rabonsa da gidan gonar Nan ya shekara uku."

Fadawansa tsaitsaye a kansa Suna gadinsa, inda safwan Yake can wurin Mai gadi Yana surutu saboda yasan koda yazo wurin Sauban ba wata Hira zasuyiba Kuma shi mutum ne Wanda bayason yaji anyi shuru da baki."

Hannu ya d'agawa fadawa alamar kowa ya Kama gabansa suje su huta
Tare da nuna masu d'aya daga cikin d'aku Nan dake jere a wurin ya furta idan Kuna buk'atar wani abin kushiga ciki zaku samu dukan abin bukata ya nunawa jami'an tsaron d'aya d'akin yace kuma idan kunada buk'atar wani abin kushiga nan akwai komai ,
snn yace "duk Wanda Yake buk'atar yaci duk abinda yakeso yashiga cikin gidan gona babu shamaki ya tsinka dukan abinda Yake buk'ata kowa yayi abinda ransa yakeso."

Yana gama fad'in hakan ya Sanya Kai yanufi d'akin da yafi ko wanne ado da kyau yayi shigewarsa."

Suna ganin ya shiga suka shiga yimasa godiya cike da farin ciki snn ko wanne ya nufi cikin gidan gonar domin tsinkar 'ya'yan itatuwa."

Da shigarsa d'akin Kai tsaye wurin k'aton hoton mahaifiyarsa yanufa Wanda Yake lik'e a gaban bangon d'akin,
Wanda tayishi tin tana budurwa kafin tayi aure tana sanye da Alk'yabbarta ruwan Madara tana murmushi a fuskarta tamkar kakirata ta amsa."
Hannunsa yasaka yashiga shafa hoton tare da runtse idonsa Yana tsananin kewar mahaifiyarsa, sai da ya d'auki kusan minti biyar a hakan snn ya bud'e idonsa ya nufi wurin d'aya hoton Wanda sukayi a tare a lokacin Yana Dan shekara uku tare da mahaifinsa, inda Yake zaune a kan k'afarta ta Sanya hannu biyu ta rungume sa a jikinta tana kallonsa cike da k'auna,
shi Kuma mahaifinsa yana kallonsu dukansu suna sakarwa juna murmushi cike da burgewa a hakan aka d'auki hoton."

Rungume hoton yayi hawaye suka shiga zuba a idonsa yashiga fad'in "Allah ya jikanki umma Allah ya Kai haske a kabarinki."

Hakan yabar wurin yanufi Kan lafiyayyen gadon dake d'akin ya kwanta rigingine yayi filo da hannuwansa ya dulmiya cikin duniyar tunani."

Sautin hayaniya yaji a Bayan window wacce take kallon k'ofar baya da alama rikici akeyi domin yaji sautin muryar macce kamar tana magiya."

Mik'ewa yayi yanufi jikin window domin ganin abinda Yake faruwa yad'an zuge labule ya rik'a k'arfen window da hannu biyu Yana hango abinda ke faruwa."

Wata farar yarinya ya hango 'yar kimanin shekara goma Sha biyar, tana sanye da kayan fulani a jikinta kanta ba d'ankwali sai Yar sarkar da suke sanyawa a tsakiyar Kai anyi mata kitso Wanda ya zubo gaban fuskarta zuwa gadon bayanta, hannunta dauke da fanteka alamar ruwa takeso ta d'iba maigadi ya hanata shine take Masa magiya Akan ya barta.
Sai fad'in yakeyi cikin hausarsa ta fulani marar dad'in Jin "Allah SAFNAH Bazan barki ki d'ebi ruwa a dai dai wnn lokacin da yarima D'an birni yake hutawa ba,
Wato so kikeyi ki janyo mun kura daga aiki na kenan,
Yanuna ta da sanda Yana fad'in "Safna kiyi tafiyar ki tin muna shaida juna"

Durk'ushe takai a gabansa tana magiya idonta Yana zubar da hawaye domin tasan yau idan Bata d'ebo ruwan Nan ba kashinta ya bushi."
Tashiga fad'in sale ka taimakeni kabar Ni na d'ibi ruwan Nan."

" Ya kuma har zuka Yana fad'in wlh Allah bazan barki ba, Safna kiyi tafiyar kawai."

Sautin muryar yarima yaji a bayansa Yana "fad'in zoki d'iba,
Ya juya ya kalli sale yace "dama hakan kakeyiwa Al'umma idan suka zo dibar ruwa?"

Da sauri sale ya zube gabansa Yana fad'in "ranka ya dad'e kayi hakuri ba halina bane ba hakan nake masuba, yau ne kawai ko yau din Dan naga kazo kana hutawa ne gudun kada su dameka."

Shuru yayi bai tankawa sale ba,
Idonsa Yana kan SAFNA wacce sai Jan ruwa takeyi a rijiya tanayi tana share hawayen fuskarta da alama tana cikin damuwa."

Kyawon yarinyar da farinta yake kallo Domin Fara ce fes har Farinta ya fara sir kawa da yellow,
kyakkyawa ce ajin farko sai dai k'azantar jikinta abin kyamata ce, don kuwa kayan da ke sanye a jikinta na fulani fararene da alama Amma akan daud'a har sun koma ruwan k'asa."

Yana tsaye a wurin ta kammala cika fantekar ruwanta ta d'auka ta d'ora a saman Kai ta juya cikin sauri zata fita,
Karaf sukayi Ido biyu da yarima Yana tsaye Yana kallonta, jikinta ya soma rawa domin duk a tunaninta yayi tafiyar sa,
Hankalinta Yana kan dibar ruwa burinta tayi ta cika tanufi gida domin gudun azabar da da isko,
A gabansa tazo dauke da fantekar ruwan a kanta ta durk'usa tana fad'in nagode D'an birni Allah yabaka abinda kake buk'ata."

Kallonta Yake a can k'asan lab'b'ansa ya amsa da "Ameen."

Wanda tuni Safna tanufi hanyar fita daga wurin cikin sauri domin ta Isa gida takai ruwan tin kafin lokacin da aka d'ibar Mata yacika.
Sai da yaga tab'acewa ganinsa snn ya juya ya kalli Sale yace tashi a gabana daga yanzun duk Wanda yazo dinar ruwa kabarshi, musamman macce,
Saboda macce darajar gareta ba'a wulak'anta macce."

Kayi hakurin ranka ya dad'e bazan sakeba,

Bai Kuma saurarensa ba ya juya yayi tafiyar sa."

Juyawarsa yaci karo da Safwan ya nufo shi Yana murmushi Yana fad'in "yarima me kakeyi anan naje nemanka baka d'ak'i."

Bai tankawa safwan ba sai da yayi gaba Yana tafiya snn yace naxo zagaya."





*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍



🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*Page 18*





"Rok'onsa taci gaba dayi, tana Kuka tana fad'in "dan Allah kayi tafiyarka, nagode da taimakonka, mutane da yawa sunyi k'ok'ari wurin su taimakeni Amma daga k'arshe basu Kai labari ba,
Banason wani abin yasameka na rokeka kabar wurin nan tin kafin su kuma dawowa su tarar da Kai."

Ganin duk ta firgice yasa hankalinsa ya k'ara tashin tausayinta ya yashigesa yaji Koda zai mutu bazai tab'a barinta cikin wannan Halin ba."

Rik'eta yayi da hannu biyu,
Domin ganin a firgice take, yashiga girgizata domin tadawo hayyacinta,
cije lebonsa na k'asa yayi Yana kallon kyakkyawan fuskarta Mai cike da kwarjini,
Sannu a hankali yakira sunanta cikin taushin murya "SAFNA ki natsu Mana babu abinda zai sameni, ko sunzo wurin Nan ba abinda zasuyimun."

Girgiza Kai tashigayi domin tasan Halin Jarmai Sarai ga duk Wanda yagani Ya rab'eta ko Yana magana da ita."

Ta kwance hannunta daga rikon da ya Mata tana kallonsa tare da ja da baya tana girgiza Kai tana fad'in kayi tafiyarka ce nagode da taimakonka, kabar ni a yanda ka ganni."

Kafin ya Bata amsa a can ta hango ta wagarsu JARMAI sun nufota, hakan Yake da zarar tafito kiwo ko dibar ruwa zai dinga zagayenta, yanaso ya Kama Wanda zaigani yana Mata magana,
mudun ya Kama Wanda tsotsayi ya hau kansa a ranar sai dai wuyarsa ta haifi wani domin sai ya mashi dukan mutuwa."

Tana ganinsu ta Kuma firgicewa ta rud'e cikin tashin hankali,
tashiga tura Sauban Bayan wani iccen bedi tana fad'in "boye a nan gasu nan zuwa, idan suka tarar da Kai dukanka zasuyi."

Tura Sauban takeyi alamar ya boye, sai gani tayi yayi tsaye ko motsi ba yayi,
Ganin hakan ta fashe da kuka domin tasan kwanan Sauban a yau ya K'are,
Suna k'arasowa wurinta suka hango shi a gabanta,
Ai Kuwa gaba d'ayansu suka daga sanduna suna fad'in wani Mai k'aranren kwana ne Yake magana dake."

Suka nufi Sauban gadan gadan zasu doka Masa sanda,
saurin zuwa gabansa tayi ta kareshi tana fad'in kada kucutar dashi ba magana yakemun ba Nima a Nan na tarar dashi bansan koshi wayeba."

Tsaye Sauban Yake Yana kallonsu cike da mamaki da Al'ajabi,
Kallonsa sukayi domin ganin ko waye, domin idonsu ya rufe basu tsaya kallon fuskar ko waye ba,
Ido biyu sukayi da yarima,
Cikin sauri suka zubar da sandunan hannunsu suka zube k'asa suna fad'in "ranka ya dad'e ayi hakuri tuba mukeyi bamusan kaibane."

Murmushi yarima yasaki ya Sanya hannu a Aljihu ya Ciro kud'i ya basu yace "zaku iya tafiya."

Cikin sauri hannuwansu yana rawa suka k'arb'i kud'in suna godiya suka wuce cike da murna da jin dadi domin yau sunsamu kud'in Shan sigari🤒

Ajiyar zuciya ta sauke had'ida goge hawayen fuskarta ta d'aga Kai ta kalli Sauban Wanda idonsa akanta Yana kallonta,
Ido biyu sukayi tayi saurin janye idonta daga kallonshi,
shi kuma idonsa kyar akanta Yana k'are Mata kallo."

Waigawa yayi bayansa yaga wani k'aton dutsi cikin muryarsa Mai taushi yace mutafi can yanuna Mata inda Yake nufi."

Bamusu tabi bayansa tafiya yakeyi cike da mulki da Isa,
Ita Kuma sai Kare Masa kallo takeyi ta bayansa, tana fad'i a ranta " iya had'uwa D'an binni ya had'u gashi kyakkyawa zuciyarsa Mai tausayi."

Saman dutsin ya zauna itama ta janyo wani k'aramun dutsin da ya nuna mata da hannu a alamar ta d'auko shi ta zauna,
taje ta d'auko yayi Mata alamar ta zauna,
A gefensa ta ajiye dutsin ta zauna tare da sunkuyar da kanta k'asa,

Shanun da tafito kiwo Yake kallo yanda suke faman cin ciyawa, suna kiwonsu gwanin ban sha'awa."

Juyawa yayi ya kalleta har a lokacin tana sunkuye da Kai tana Wasa da Zara zaran Yan tsun hannunta,
Cikin taushin murya yakira sunanta yace "Safna tayi saurin d'ago Kai ta dubeshi domin jitayi sunan yayi matuk'ar Dadi a bakinsa."

Yace "kin yarda Dani?"
Kin yarda bazan cutar da keba?"
Kinaso na taimakeki na fitar dake daga kuncin da yake damunki?"

Daga Kai tayi "Alamar eh."

Yace "ke wacece?"

Waye mahaifinki?"

wnn Jarmai din waye shi a wurinki?"

Share hawayen da suka zubo Mata a fuska tayi tace
"kamar yanda nafad'a maka sunana Safna,
Ni 'yar garin Nan ce, mahaifina sunansa Jabiru ana kiransa da JAURO,
tinda na tashi bansan dad'in rayuwaba, a kullum cikin kuka nake da k'unci tare da wahalar rayuwa Mai tsanani a wurin uwar rik'o na,
Wacce a farko na d'auka itace mahaifiyarta sai daga baya da BABA yake fad'amun cewar ba itace mahaifiyata ba,
Sabida yaga irin wahala da tsangwamar da nakesha a wurinta
Yasa wata Rana ya zaunar Dani a lokacin Bata Nan tafita wurin biki,
Yake fad'amun cewar nayi hakuri da duk abinda INNO zatayimun nasani cewar ba itace mahaifiyata ba, asalima Bata tab'a haihuwaba Dan hakan yasa Bata San zafi da darajar 'ya'ya ba,
Yace "SAFNA Kiyi hakuri da kaddarar rayuwa da tasameni domin kuwa har ni Nan banine mahaifinki ba,
Na tsinceki ne a k'ofar gari a lokacin nadawo daga kasuwa misalin k'arfe 8 na dare a lokacin nayo Daren dawowa gida,
Anan Naga wani kwali a jiye bakin hanya jariri Yana ta faman kuka a cikinsa,
Lek'a kaina nayi a cikin kwalin naganki kwance kina sanye sanye da kayan sanyi da hula da Safar hannu da k'afa masu shegen kyau
An dunkuleki da towel Mai kyaun gaske kasancewar lokacin sanyi NE hannunki Yana sanye da zoben zinari Mai tsadar gaske,

Tausayina ya kamashi ya duka ya daukeni ya rungumeni a jikinsa yanufi wurin maigari Dani,
Anan yayiwa maigari bayanin a inda ya tsinceni."

Sosai maigari ya girgiza da maganar,
Hakan safiya ta waye a ka shiga cigiyata ko Allah yasa za'a Gane iyayena a tunaninsu Koda barayine suka shiga wani gida suka satoni idan iyayena sukaji sanarwa zasuzo su karbeni."
.shuru ba Wanda yazo yace yasan ko Mai Kama Dani,
Washe gari maigari ya yanke shawarar akaini birni a ajiyeni a gidan marayu."

Baba ya nuna Yana sona zai rik'eni domin baitaba haihuwa ba, shekararsa 20 da matarsa,
Hakan maigari ya Amince yabawa baba ni,
Ya kaima matar sa INNO."

INNO batayi farin cikin amsoni da baba yayi ba, Dan da farko cewa tayi bazata amsheni ba, sai da taga zata rasa igiyar aurenta snn ta amsheni."

Tin Ina makaramata nasan wahalar rayuwa domin da zarar nayi Kashi ko fitsari Inno zata dinga dukana tana zubamun ruwan sanyi a jiki,
Tin baba Yana fad'a Yana magana har ya Kai ya daina yashiga Jin shakkunta Wanda da alamar takaishi an d'aure Masa baki a wurin boka."

Hakan na girma duk wani aiki na gida nice keyinsa Dan Gane da girki d'ibar ruwa kiwo faskaran iccen da za'ayi sawwa dashi duk nice keyinsa,
lokaci take d'ibarmun da zarar lokaci yacika bandawoba zan Sha wahala a wurinta zata Sanya bulala ta dakeni daga k'arshe bazata bani abincin da zanciba a ranar da yunwa zan kwana"

Allah yayi Mai farin jinin jama'a
A yanda naji ana fad'a cewar ni kyakkyawa ce duk cikin k'auyen Nan ba Wanda ya kaini kyau, Dan hakan ake mantawa da rashin asalina saboda kyawona masoya suke turuwa a kaina."

Duk Wanda yazo neman aurena INNO take korarsa musamman idan ta fahimci Dan gidan mutumci ne, Wanda tasan idan ya aure Ni zanje na huta."

Duk abin Nan da akeyi baba bai San abinda akeyiba,
Shi a ganinsa rashin samun mijin aure da banyiba,
Wata k'ila Aljanu suka aure Ni, Dan kuwa duk sa'ata sunyi aure wasu har sun haihu, Ni har yanzun shuru ba miji gani kyakkyawa ajin farko."

Mutum d'aya ne ya jure korar jummai da tsangwamarta ya nace akaina cewarsa tinda Yana Sona sai ya aureni babu Wanda ya Isa ya Hana,
Sunan shi AUDU."

Audu D'an sarkin kiwo ne dake cikin k'auyen mu,
Sosai Yan matan garin suke ruguguwa a kansa domin yace Yana sonsu bai furta hakan ba sai a kaina."

Bana son Audu sam a Raina domin ni duniyar ma gaba d'aya taficemun a Rai fatana Akoda yaushe Allah yayi mun mafita, ta Alheri ya bayyanarmun da iyayena domin naji dad'in da yasa suka jefar dani a lokacin da nake da buk'atarsu." Hakan Nan nake kula Audu nasanyawa rayuwata zan aure shi Koda bana sonshi, kodan na huta da azabar Inno."

Ana hakan D'an maigari JARMAI JAN WUYA shima yafito neman aure na,
Sosai Inno tayi farin cikin fitowar Jarmai domin tasan da zarar sun Kara da Audu wurin shad'i,
ba makawa zai cinye Audu, dele a d'aura mun Aure da Jarmai,
duk yarinyar da jarmai yace Yana so a garin Nan sai ya aureta Koda Bata sonshi Dan kuwa, za'ayi zab'en fidda gwani a filin shad'i kamar yanda Al'adarmu ta fulani take duk akayi shad'i Jarmai keda nasara,
duk mutunen garin sun San da hakan,
Yanzun shekara 7 kenan duk shad'in 'akayi shine ke cinyewa, Kuma a Nan take za'a aura Masa yarinya, dare D'aya Yake farketa batare da yaji tausayintaba sai ya gama biyan buk'atar gareta har na tsawon sati daya snn yake sakota wasu yaran mutuwa sukeyi wasu Kuma sukan kamu da ciwon yoyon fitsari, wasu Kuma Allah ya taimakesu su gyaru,
yarinya bakwai Jarmai ya aura a cikin garin Nan duk hakan yake masu."

Ta share hawayen fuskarta taci gaba da cewa, "yanzun saura wata biyu ayi shad'in mu, zasu Kara tsakaninsa da Audu duk Wanda yacinye shi zan aura, nasan jarmai ke da nasara domin duk mutanen gari sun shaida hakan."

Tin daga ranar da aka saka ranar shad'inmu duk Wanda yagani, ya rabeni da sunan yana sona, ko yana mun magana indai namijine sai Jarmai yayi Masa bugun mutuwa."

Mutum biyu Yana kashewa Akan sun furta suna Sona,
Hakan ya Hana Audu yin magana Dani,
Shi kad'ai Yake magana Dani duk a cikin garin Nan, Dan hakan idan nafito kowa baya son ya ganni bare yayimun magana Domin gudun wahalar Jarmai,
Idan nafito kiwo zai dinga zagayena duk ranar da Mai rabon wahala yasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login