Showing 39001 words to 42000 words out of 86876 words

Chapter 14 - DAN SARKIn SAUBAN COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

7420

umurnin a Fara wasa."

Anan take jarmai da Audu suka shiga dukan junansu da bulala ba girma ba arziki,
Ko wanne k'ok'ari yakeyi yakai d'an uwansa k'asa."

Sosai Audu ya daku ya jigata jikinsa da fuskarsa suka fara fitar da jini, amma yaki ya fad'i sai buga in buga sukeyi da jarmai Wanda jikinsa kawai ne yayi kwancen bulala, jini bai fitaba,
Kuka safna ta fashe dashi a lokacin da taga jarmai yana neman cin galaba akan Audu domin jini har ya fara wankewa Audu fuska amma har yanzun bai fad'i k'asaba, Wanda da zarar ya fad'i shikenan jarmai ya ci galaba a kansa."
hakan Audu yake dukan jarmai
jarmai yake dukan Audu, a can jarmai yasami sa'ar Audu ya doka masa bulala a tsakiyar kai, anan take Audu yasaki wata irin k'ara ya fad'i k'asa a some."

Da gudu Safna tanufi wurinsa tana kuka tana jijjagashi tana fad'in katashi Audu katashi meyasa kabari Azzalumi yaci galaba akanka?" kana gani za'a auramun azzalumi,
ta d'aga murya cikin sauti sai da gaba d'aya wurin ya amsa tace Audu katashi ."

Dariya Jarmai yasaki cike da jin dad'in samun nasara,
Hakan masu goyon bayansa suna murna tare da ihu suka d'aukeshi suka d'agashi sama suna juyashi,
Yashiga yiwa kansa kirari kamar hakan "saini jarmai angon Safna mainasara, sai ni Jarmai d'an maigari ba Wanda ya isa ya tab'ani ya zauna lafiya."

Snn ya sauka daga d'aukar da aka suka masa,
Yanufi wurin safna dake durk'ushe a gefen Audu tana jijjigashi tana kuka tana fad'in tashi Audu karka mutu,
hannu jarmai yasaka ya ruk'o hannunta ya mik'ar da ita tsaye ya Janyeta a wurin,
tana tirjewa tana dukan hannunsa a kan yasaketa yak'i yasaketa sai da yafito da ita tsakiyar fili ya d'aga hannunta sama yana fad'in saini jarmai na Safna,
Safna ta wace idan akwai wani Wanda yakeji da kansa yafito mukara idan uwarsa bata haifi wani ba."

Safna tana kuka idonta akan sauban, Wanda ya runtse ido jikinsa sai rawa yakeyi alamar ransa a b'ace yake."

Cikin zafin nama sauban yamik'e tsaye tare da cire rigar jikinsa sai ciccira yana neman yashiga filin shad'in,
Safwan ya rik'eshi hakan fadawa sukayo kansa suka rik'eshi suna fad'in ranka ya dad'e meye had'inka da shiga filin shad'i?"
bazaka iyaba, ka rufamana asiri bamaso mujewa maimartaba da mummunan labari."

Hannu biyu yasaka ya turesu gefe d'aya dukansu sai da suka fad'i k'asa har safwan,

jikinsa sai rawa yakeyi yanufi wurin jarmai ya fisge hannun safna daga hannunshi ya turata gefe d'aya snn ya duk'a ya d'auki bulalar da Audu ya jifar k'asa
Yanuna Jarmai yana fad'in,
Kana fad'in sunanka Mai nasara amma yau kasanyawa ranka daga yanzun sunanka marar nasara,
domin bakomai akeyin nasara akansaba,
har yanzun Safna bataka bace Safna ta mai raboce tsakanin ni da kai."

Da gudu safna ta nufo wurin yarima tana kuka takai durkushe a gabansa tana fad'in banaso na rasaka, domin bazaka iya da wnn Azzaluminba kayi tafiyarka kawai."

janyeta yayi a gabansa domin ya tsani ganin kukan nan nata a idanunta, ransa ya kuma b'aci jijiyoyin kansa duk suka firfito jikinsa sai rawa yakeyi yana kallon jarmai."

Dariya Jarmai yasaki yana kallon yarima yace "d'an birni zaka iya karawa dani?"

Bai iyar da rufe bakinsaba cikin zafin rai Sauban ya sakar masa bulala a tsakiyar gadon bayansa, wacce anan take wurin ya tulb'e da jini,
Ai kuwa shima jarmai yashiga kaiwa yarima duka kota Ina,
Idon yarima a rufe suke saboda b'acin rai da zuciya bayajin dukan da jarmai yake masa shima cikin zaffin nama yake kaiwa jarmai duka anan take bakin jarmai ya fashe da jini abinda bai tab'a faruwa dashiba,
Dukansa sosai sauban yakeyi dukanda bayaji baya gani domin idonsa a rufe suke,
Dukan da ya kaimasa a tsakiyar kai yasaka jarmai zubewa k'asa a some."

Ihu mutan gari suka d'auka suka tunkaro sauban suka d'ashi sama suka shiga juyashi kamar yanda Al'ada take."

umurni ya bada akan a saukeshi sakamakon kansa da yakeji yana Sara masa,
Ana saukeshi Safwan yanufo wurinsa ya mik'a masa riga yasaka, da gudu safna ta nufoshi ta fad'a kan jikinsa tasaki kukan farin ciki,

Hannu yasaka ya rungumeta tare da runtse idonsa, sai da suka d'auki minti goma a hakan snn ya Janyeta a jikinsa aka bashi umurnin ya rik'a hannunta ya d'aga sama kowa yagani kamar yanda Al'ada ta tanadar kamar ynda jarmai yayi."

D'aga Hannunta yayi idonsa a rufe sakamakon biyu biyu da yake ganin mutane, ya kasayin magana,
Maigari yana ganin hakan yaturo dagaci yayi magana a maimakon yarima,
Yagaci ya fara magana kamar hakan "yarima Safna takace ka mallaki safna idan akwai Wanda yakeda ja yafito su Kara da yarima,
shuru kowa yayi, ba mai bakin magana,
Sai da dagaci ya maimaita har sau uku ba Wanda yakeda ja,
Snn wuri ya d'auki kuwa da sowa,
Masu bakin ciki sunayi masu farin ciki sunayi."

Ganin yarima yana Neman fad'uwa cikin sauri fadawa suka rik'ashi suka nufi gidan gona dashi."

a nan take taro ya fara watsewa inda aka yayyafawa Jarmai ruwa, anan take ya farfad'o daga suman da yayi yana borin kunya yana fad'in ina yariman yake yafito mukara a karo na biyu waye yafad'a masa anaja da Jarmai."

Sowa mutan gari suka shiga yimasa cike da murna don kuwa anan take Allah ya cire masu tsoronsa a ransu."

Duk abin nan da akeyi fadawan da Saudat ta turo suna kaimata rahoton komai har Dukan da akayiwa yarima da cinye shad'in da yayi duk sunfad'a mata
Suka k'ara da cewa ranki ya dad'e yarinyar ta cacci hakan kodan saboda kyawon da Allah ya Mata,
Dan kuwa yarinyar kyakkyawa ce yanda kika san Al'ajana."

Wani irin ihu Saudat tasaki tayi jifa da wayar hannunta ta cire d'ankwalin kanta tana fad'in k'aryane wlh, na rantse da Allah sainayi Ajalin duka zuri'arsu





*Tofa*




*Mrs Anas NASA*✍
[9/4, 7:56 AM] Hayat: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍



🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*Page 25*





"Tamkar mahaukaciya hakan saudat ta koma sai ihu takeyi tana jifa da duk abinda yatari gabanta, tana fad'in k'arya ne wlh ba wata shegiya data isa ta aure mun miji,
in har inada rai ina motsi a doron k'asa."
Cikin sauri tamik'e tsaye tanufi wurin wayar wacce tayi jifa da ita can gefe d'aya,
Allah yasa bataci screen ba,
Ido rufe Tashiga Neman number mahaifiyarta sarauniya Bilkisu."

Bugu d'aya zuwa biyu sarauniya Bilkisu,
Tabada umurni a d'auki wayar
Cikin sauri Kuyangi suka d'auki wayar tare da Kara mata a kunneta,

Muryar safna taji tana kuka sosai kamar wacce akayiwa mutuwa."

Cikin tashin hanki da hanzari ta karb'i wayar daga hannun kuyanga ta juya ta kallesu tayi masu umurnin subar d'akin,

Da hanzari suka fita daga d'akin,
cike da tashin hankali take cewa my daughter meya faru kike kuka?"
A duniya na tsani naji kukanki banason zubar hawayenki meyake damunki?" Meyake faruwa?"
Me kikeso?"

Kuka saudat takeyi sosai, tana fad'in mommy Sauban ne,
Mommy sauban kishiya zaiyi mun, Sauban aure zaiyi mommy"

"Aure sarauniya bilkisu tace cike da firgici,
K'arya ne wlh bai isaba,waye shi da zai yi maki kishiya,
nawa kike yaushe aka haifeki,
da a turai muke ko a cikin lissafin aure ba'a d'orawa akanki bare azo akan maganar kishiya,
Na rantse da Allah 'yata bazata zauna da kishiya ba
kamar yanda nima bana zama da ita."

'yar Gidan Uban waye?" Wani matsayi keda ubanta?"
'Yar gidan wanne hamshak'in ne a cikin garin Adamawa?"

Saudat na kuka tace "ba 'yar gidan uban kowa bace,
'yar k'auye ce ko a k'auyen a can cikin k'auyen Fulani k'azamai marasa wanka masu warin nono da manshanu."

tasaki kuka tana fad'in Yana tsananin sonta domin har da dukansa akayi akan son da yake Mata wai duk a cikin Al'adar k'auyen ne. Domin kawai yasameta, mommy ya zanyi da rayuwata nashiga ukuna."

mommy ta fusata tace baki kishiga ukuba, domin "Bai isaba wlh sai dai ya mutu akan son da yake mata amma bazai tab'a aurenta ba, ba zai tab'a kawota cikin gidanki a matsayin kishiya ba."

har Abada sauban bazai tab'a yimaki kishiyaba in dai inada rai da numfashi a duniya,
Waye sauban waye ubansa ko uwarsa da tana a raye bata isa ta ja daniba bare shi din banza."

Mataki na farko da zamuyi amfani dashi shine,
duk wata zuri'ar da ita yarinyar suke Alfahari da ita sai mun hallakasu."

Gobe zanturo dakaru tare da kayan aiki gaba d'aya su ruguza k'auyen da duk a halin dake cikin k'auyen ke harda ma mutanen dake rayuwa a cikin k'auyen,
A cinnawa gidansu wuta duk su k'une, bana buk'atar koda ganin gawarsu ayi."

A tashi k'auyen gaba d'aya kowa ya huta, kinga idan mukaYi hakan Ankare da matsalarta ki sanyawa rayuwarki bake ba kishiya har Abada indai inada rai da lafiya ynda ban zauna da kishiyaba hkn kema har abada bazaki zauna da itaba."

Dariya Saudat tasaki cike da farinciki tana fad'in "nagode mommy na Dan hakan nake tsananin k'aunarki fiye da daddy domin kece Mai sharemun hawayena bakyason ganin kuka na,



*Kuyi hkr d wnn yau banajin yin typing din*






*mrs Anas Bawa*✍



[9/8, 12:57 AM] Hayat: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍



🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*Page 26*






"A kan gado fadawa suka ajiye Sauban inda yake rufe da ido shi kad'ai yasan zugin zafin da yakeji a bayansa,

Safwan ya taimaka masa yacire masa rigar jikinsa yana masa fifita, ganin shatin bulala ya kwanta a bayansa yayi masa jajir akan lallausar fatar jikinsa Abu ga farin mutum gwanin ban tausayi."

Cike da jin haushi safwan yace "meye hakan ka janyowa kan ka kaga kuwa yanda jikinka da bayan ka, da duk ilahirin jikinka yayi?
Wani irin so kakeyiwa safna Wanda har kake neman hallaka kanka da rayuwarka,
a kan macce, na rantse da Allah ko ni kaina da nafika damuwa da macce bazan iya wnn wahalar ba,
nafison na barta ko wacce ce har Abada in dai har sai anyimun irin wnn dukan za'a bani ita, haba ga mata nan 'yan birni birjek sai ka darje saika zab'a."

Ni yan zun ban san yanda zanyi da kaiba gashi wnn zuwan bamuzo da doctor ba kamar yanda muka saba zuwa dashi a duk lokacin da zamuyi tafiya mai nisa."

Wani bafade yashigo da sallama ya tsuguna a gaban safwan yana fad'in ranka ya dad'e mahaifin yarinyar akayi shad'inta ne,
tare da yarinyar suke neman iso."

Mere baki Safwan yayi domin cike yake dajin haushin halin da sauban ya jefe kansa a kan macce,
A bazata yaji muryar sauban yana fad'in "kace masa ya shigo."

Sauri Safwan yayi ya juya ya Kalli sauban, yace "Ashe dama kana iya magana kabarni inata surutu ni kadai kamar mahaukaci."

Harara sauban ya jefa masa tare da jan tsaki."

Sallama Baba ta katse Safwan daga maganar da yakeyi, son ya mayarwa sauban."

Baba ya shigo Safna tana biye dashi a baya wurin zama Safwan ya nuna masa akan kujera tare da gaidashi."

Amsa gaisuwar yayi tare da girgiza Kai,
ya zauna k'asa yana fad'in Barni na zauna anan ya isa,

Tsaye safna tayi idonta a kan yarima tana kallonsa cike da tausayi ganin duk jikinsa yayi ja akan kwancin bulala,
Shima idonsa a kanta yana kallon fuskarta anan take yaji wani irin farin ciki da kuzari sunzo masa a lokaci d'aya, ya dafa gado ya Tashi zaune tare da yanyo rigarsa ya rufe jikinsa ya Kalli baba yace "Baba ina wuni."

Lafiya k'alau Baba yace yaya k'arfin jikinka?".

"Alhmdulillah sauban yace idonsa nakan safna dake sharar hawayen tausayinsa."

Baba ya Ciro wani magani a Aljihunsa ya tashi daga inda yake yanufi wurin yarima yana fad'in "ranka ya dade magani nakawo maka Wanda zai taimakeka wurin kariyar dafin bulala."

domin muna amfani dashi a duk lokacin da hakan ta faru, musamman ga Wanda akayi shad'i dashi Saboda yana karye dafin bulala yanda bazata kwanta ajikinkaba bare tayi maka tabbo."

Murmushi sauban yasaki yace "nagode Baba,

Baba yace "bakomai zaka iya gyarawa na Shafa maka A duk inda bulalar ta kwanta maka."

Gyara kwanciya sauban yayi ya ajiye rigar da ya rufe jikinsa gefe d'aya,
Baba ya matso ya shiga shafa masa maganin a duk inda bulala ta kwanta masa."

Sosai jikinsa ya d'auki zafi alamar akwai zazzab'i a tare dashi, idonsa a kan Safna wacce take tsaye a Bayan Baba tana kallon yanda kwancin bulala duk ya b'ata masa kyakkyawar fatar jikinsa, hawaye tausayinsa kawai ke zuba a idonta,

Wanda duk wani d'igo na hawayenta jinsa yakeyi har cikin zuciyarsa tamkar ana yayyafa masa ruwan zafi yakeji,
saurin runtse idonsa yayi cike da k'unar zuci domin baya son ganin zubar hawayenta ko kad'an a rayuwarsa."

A hakan Baba ya kammala Shafa masa maganin ya gyara masa kwanciya ya nemi wuri a kusa dashi ya zauna, Baba yayi gyaran murya yace Allah yabaka lafiya insha Allah wnn maganin zai taimake ka sosai zakaji k'arfin jikinka da walwalarka duka zata dawo,
Ranka ya dad'e idan ba damuwa inaso zanyi magana da Kai."

Bud'e idonshi sauban yayi ya tashi zaune yana kallon Baba da Safna wacce ganin Baba ya zauna itama taje kusa dashi ta zauna a gefensa,
har yanzun hawaye ke zuba a idonta tana gogewa da bayan hannunta,
Kallonta sauban yakeyi yana jijjina wnn soyayyar dake tsakanin Baba da Safna domin ya lura yana tsananin sonta itama hakan."

Baba ya fara da cewa "hakika kayi namijin k'okari wurin karawa da Jarmai a wurin shad'i, kuma daga k'arshe Allah yabaka nasara akansa Wanda duka Mutanen gari suke cike da mamakin hakan har yanzun,
Kamar yanda kasani jarmai yakanyi shad'i akan yasami macce idan yasa meta yayi nasarar Aurenta daren farko yake keta mata mutumcinta yayi mata illah sosai Zara kasa moruwa, da yawa daga cikin wad'anda ya aikatawa hakan wasu sun mutu wasu sun nakkasa yanda bazasu tab'a moruwaba har Abada."
Ranka ya dad'e nasan kasami wnn labarin ne shiyasa ka shiga shad'i domin ka taimaki rayuwar Safna ba wai dan kana sonta ba har cikin zuciyarka,
Alfarmar da nake nema a wurinka itace, ka taimaka mun ka Auri Safna koda baka sonta saboda tafita daga cikin wnn k'auyen Wanda zamanta a cikinsa a halin yanzun yanada hatsari sosai a rayuwarta da tawa baki d'aya,
musamman idan jarmai ya gyallara ido ya dinga ganinta, tana yawo a cikin garin nan."
Ranka ya dade koda baka ra'ayin Aureta bata cikin tsarinka,
Ina neman Alfarma a Karo na biyu shine a cikin bayinka KO kuyanginka ka nemo Wanda ka yarda dashi ka yarda da hankalinsa ka aura masa Safna,
Babba burina a rayuwa shine Safna tabar garin nan,
Tasami inda zata zauna cikin kwanciya hankali da natsuwa."
Ka dubi maraicinta Safna bata da iyaye Allah shine gatanta."

Sharad'in shad'i a garin nan shine, idan kayi shad'i kamar a yau,
A gobe duk Wanda yacinye zai tura mahaifansa a wurin maigari domin asaka ranar Aurensa da yarinyar,

Ranka ya dad'e miye mafita kai nake saurare."

Murmushi sauban yasaki domin duk magagganun da Baba yakeyi yanajinsu suna durar masa har cikin zuciyarsa tsantsar tausayin Safna mai zafi yakeji yana dakar masa zuciya,
Idan yabari yabawa wani aurenta bai san yanda zai amsheta ba, bai san yanda zai tausaya mata ba,
shi ya kamata ya amshi Aurenta domin yafi kowa sanin ko wacece safna domin ya rik'eta tsakani da Allah yaji tausayin maraicinta ya share Mata hawayenta,
Da duk wahalar da Tasha a baya tazama tarihi a rayuwarta."

cikin muryarsa ta marasa lafiya yace "Baba ni Zan auri Safna,
Ni Zan zauna da Safna domin tasami farin ciki mai d'orewa, yanda zata manta da batada iyaye ta manta da ko ita wacece a duniya."

Yau komai dare Zan koma gida gobe zan turo maimartaba da fadawa domin a nemamun Auren Safna."

Wani irin murmushin farin ciki Safna tasaki Wanda yasa Sauban shima murmusawa,
Yaci gaba da fad'in Ka kwantar da hankalika Baba babu abinda jarmai zaiyiwa Safna tin daga yanzun har zuwa lokacin da zatabar garin nan, kafin na wuce zanga maigari zan zauna dashi zamuyi magana."

Godiya sosai Baba yake masa har sai da sauban ya dakatar dashi,
Snn Baba yayi masa sallama tare da fatan samun lafiya yanufi hanyar waje Safna tana biye da Baba a baya."

Kallo sauban yabita dashi yana murmushi Wanda baisan yana yinsaba,
har zasu fita daga d'akin sauban yakira Baba yace "Baba Ina neman Alfarma zanyi magana da safna."

Cak Safna taja ta tsaya a inda take,
Baba yana murmushi yace badamuwa ya kalli Safna dake tsaye ta sunkuyar da kai yace "kije wurin yarima ki kula da kanki,
Snn Baba ya wuce yanufi gida."

Tsaye tayi wuri d'aya a inda take takasa motsawa,
kanta a sunkuye cike dajin kunya."

Kallonta yakeyi cike da Burgewa domin yana son macce mai kunya,
Juyawa yayi ya kalli safwan Wanda yake zaune a kan kujera latsar waya kawai yakeyi azahirance kamar baisan abinda akeyi ba,
Amma Duk abinda da akeyi yanaji a kunnensa kuma yana gani da idanunsa,
mamakin sauban yakeyi a yanda soyayya tayi masa mugun kamu wacce baisan yanayin taba,
Bai san tayi masa mummunan kamu ba."

Sauban yana kallon Safwan ya had'e fuska yace " malam saika fita magana zanyi da ita."

Banza Safwan yayi dashi kamar badashi yakeyiba."

A hasale Sauban yace Safwan kanajinafa nace kad'an bamu wuri magana zanyi da Safna."

Sai a lokacin Safwan ya kallesa yasaki murmushi cike da tsokana yace "cewa zakayi nad'aga nabaka wuri soyayya zakayi da safna."

Harara sauban ya kai masa yace "ka d'auka kowa irinka ne, mutu macce."

Dariya mai sauti Safwan yasaki yanufi hanyar waje yana fad'i waye ni ai duk abinda nakeyi shafin maine dan ka zartani a fagen soyayya yarda ne kawai bakayiba."

Mere baki sauban yayi yabishi da harara, sai da yaga fitarsa snn ya koma kan safna wacce take a tsaye a bakin k'ofa sunkuye da kai cike da jin kunya."

Muryarsa taji yana kiran sunanta cikin wata irin murya Mai taushin gaske,
"Safna kizo mana."

Sannu a hankali take takawa kanta a sunkuye a k'asa ta nufi wurinsa."

Murmushi yake saki a fuskarsa ganin batason had'a ido dashi,
A gabansa tazo tayi tsaye kanta a sunkuye gefen gado yanuna mata a kusa dashi yace " zauna a nan."

Da sauri ta d'aga kai ta kallesa ta kuma sunkuyar da kai tace "A

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login