Showing 57001 words to 60000 words out of 86876 words

Chapter 20 - DAN SARKIn SAUBAN COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

7423

dai kamar yanda kowa yakeyi,
Tunda naga sun harbi mahaifinki jini yana fita a k'afarsa na fad'i wurin na suma ban kuma sanin abinda yafaru ba,

ashe mahaifinki anan shima ya fad'i ya suma yana rungume dake gam a k'irjinsa."

Bamu kuma sanin abinda yake faruwa ba sai dai muka farka muka ganmu kwance akan gadon asibity babu ke babu labarinki suntafi dake."

Tafiya dake da sukayi bak'aramun tashin hankali ya janyoba domin duk wani a halinmu da masoyanmu sai da suka shiga cikin tashin hankalin b'atanki."

Bayan komai ya lafa aka barwa jami'an tsaro aikinsu sukaci gaba da bincike lungu da sak'o shuru ba wani labari mai Kama da ansan inda kike."

A kullum inaji a jikina baki mutuba zaki dawo garemu dan hakan duk abinda na mallaka da sunanki a cikinsa hakan mahaifinki."

Bayan shekara biyar da b'atanki kishiyata hajiya Nana na kwanta ciwo anan take ta shiga tonawa kanta asirin cewa "itace tasaka yan fashi suka saceki suka jefar dake a can nesa da gari, saboda batason ta bud'e ido ta ganki saboda irin son da mahaifinki yake nunamaki tasan duka dukiyarsa kice zaki mallaki rabinta, bayan ita Allah baibata haihuwarba,

Anan Tafara neman yafiya a wurinmu dani da mahaifinki muka dinga kuka,
Domin mahaifinki yana tsananin son hajiya Nana da tausayinta musamman rashin haihuwar da batayiba, sosai yake nuna Mata k'auna da tausayi wani lokacin har tunani nakeyi yafi sonta a kaina,
Amma da irin wannan sakamakon zata saka mashi,
Kuka mukeyi sosai a wurin muna tunanin wanne irin girman laifine muka mata Wanda yakai zata saka a k'arb'e mana tilon yarmu."
muna wurin Allah ya k'arb'i rayuwar Hajiya Nana, tana neman yafiya a wurinmu."

Suhailat Kinji dalilin rabuwarmu dake, Suka rungume juna gaba d'ayansu cike da k'auna da farin ciki juna"

Bayan komai ya lafa Safna tabasu labarin duka rayuwar da tayi tun tashinta har zuwa girmanta har kawowa lokacin da umma ta bugeta a mota,
bata b'oye masu komai ba har irin taimakon da sauban ya mata da fagen shad'in da yashiga ya taimaketa bata auri barde ba."

Sosai suka tausaya mata sukaji dad'in taimakon da sauban ya mata anan take Alhaji Habib yaji sauban ya shiga ransa koda baisan kowaye shiba."
Sunyi jimamin mutuwar Baba Wanda ya rik'eta hannu biyu, inda Alhaji Habib ya d'auki Arwashin zaiyi bincike akan mutuwar Baba yaji yana raye ko ya mutu."

Bayan kwana biyu gidan yacika da farin cikin bayyanar Suhailat inda yan uwa da abokanan arziki sai zuwa sukeyi suna masu barka da arziki inda duk Wanda ya kalli safna yasan jinin Hajiya Laila ce da Alhaji Habib."

Waya Alhaji Habib ya d'auka ya danna lambar sarki domin ya shaida masa bayyanar 'yarsa Suhailat."

Sosai sarki yayi murna dajin hakan daga nan yake shaida masa cewar shima d'ansa sauban yana asibity akwance rai a hannun Allah yana tsakanin mutuwa da rayuwa."

Subahanallahi Alhaji Habib yace tare da cewa "meyake damunsa?"

Sarki ya sauke ajiyar zuciya yace "ciwon soyayya yakeyi, soyayyar ma ta wata yarinya shegiya marar asalima, kaduba ka gani Alhaji Habib ina matsayin Sarki Wanda ya tashi a gidan sarauta gidan asali mai cike da tarihi Mai kyau ace d'ana Wanda nafi k'auna,
yakeso ya ruguzamana komai namu yashigo mana wata al'ada Wanda tinda aka haifeni tun zamanin kakan ni da iyaye bantab'a ganin d'an Sarki ya auri shegiya marar asaliba."

Alhaji habib yace "kayi hakuri ranka ya dade kasan yaran yanzun ka haifesu baka haifi halinsuba, ni dai shawarata anan itace kabashi abinda yakeso domin wnn al'adar masarauta ce ba Addiniba,
kasani marayuma ya'yane ba laifin yarinyar bane laifin iyayenta ne da suka haifata bata hanyar sun nah ba,

Kabawa sauban abinda yakeson hakan shine kwanciyar hankalinka da nasa,

Sarki dake tsaye a gefen gadon sauban Wanda aka sanyawa oxygen domin janyo numfashinsa Wanda gaba d'aya baya motsi, ko hannunsa baya motsawa tamkar matacce hakan yake."

Yake cewa Alhaji Habib nariga da na rantse sauban baxai auri shegiyaba marar asali, sai dai ya mutu na binnesa da hannuna, akan na zubar da 'yancin masarautata da asalinta."

Wani irin tari sauban yayi Wanda jini ya fara zuba a bakinsa,
Wani k'oton gudan jini sare ya fad'o a cikin bakinsa, yasaka Sarki yin jifa da wayar hannunsa cikin tashin hankali yanufi wurinsa yanakiran likita."
[3/30, 9:56 PM] Hayat: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍



🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*Page 34*






A firgice itama Safna take kallon hajiya falmata ganin yanda take jifarta da wani irin kallo mai cike da tuhuma tare da firgici,
Kuma matsowa tayi ta rik'o hannun hajiya falmata tace "umma kiyi hakuri idan maganar danayi itace ta firgitaki bazan sakeba ki gafarce ni."

Kasa magana Hajiya falmata tayi illah taci gaba da kallon safna d'aya bayan d'aya,
Tabbas wannan Suhailat d'in tace tadawo gareta ashe bata mutuba Ashe tana da rabon sake rayuwa tare da tilon 'yar ta,
Wani irin kuka ta fashe dashi ta rungume safna suka fad'a kan gado a tare Wanda safna sai zarar ido takeyi hankalinta a tashe tarasa dalilin yin hakan."

Sosai ta rungume safna kamar wacce zata sub'uce mata sai shinshinarta takeyi tana share hawayen dake zuba a fuskarta,
Zaro ido kawai safna takeyi domin gaba d'aya kanta a d'aure yake tarasa dalilin wnn rungumar da umma take mata uwa uba ga hawaye da take gani suna fita a idonta."

Kalaman da taji umma tana fad'a tana kuka sune suka d'aure Mata kai tare da girgizata, suka sakata a rud'ani

"dama nasan zaki dawo garemu dama nasan baki mutuba na dad'e inaji a jikina baki mutuba "yata zaki dawo garemu nida mahaifinki muna matuk'ar kewarki tare da shaukinki, sulaihat ke yar muce naga alamomi da yawa a tare dake Wanda yake nuni da hakan,

Hawaye suke zuba a idon safna tana girgiza kai tace "umma kada kucutar dani dan kunganni banida gata, ku taimaki rayuwa kubarni nayi tafiyata k'auyenmu amma kada kuce ni 'yarkuce,
saboda a k'auye na tashi bansan kowa nawaba, Inna marikiyata ta fad'amun cewa iyayena cikin shege sukayi suka haifeni suka jefar dani a gefen hanya,
Sannan baba Wanda ya taimakeni yanuna son tamkar yarsa ya fad'amun cewa a gefen gari ya tsinceni anjefar dani ta yaya zakice ni yarkuce." Ku daina danganta kanku dani, kubarni nayi rayuwata batare kamar yanda kuke da nayar taimakona."
Wlh zanyi maku biyayya tamkar yarda kuka mahaifa amma ni ba 'yar kubace."

cikin d'aga murya hajiya falmata tace "suhailat ke yarmuce ke ba shigiya bace ta hanyar sunna aka haifeki,

Turo k'ofa akayi Alhaji Habib naira yashigo tare da sallama da gudu Hajiya falmata tasaki safna ta nufeshi ta rungumeshi tana fad'in Alhaji farin cikinmu yadawo garemu 'yarmu tadawo garemu, Suhailat dinmu tadawo itace muka taimaka,
hannu biyu yasaka ya rungume matarsa ya d'ora kanta asaman kirjinsa yana bubbugar bayanta yana fad'in daina kuka hajiya ki natsu kiyimun bayani ina Suhailat din take ne?"

Safna da tuni ta sulale tabar d'akin tin lokacin da taga umma ta fad'a akan jikin Abba ya kuma mayar da hannu ya rungumeta duk sai taji kunya ta kamata, anan take tana sharar hawaye ta sulale tafita tanufi d'akinta wanda umma tanuna mata acewar shine d'akin nata a nan zata dinga kwana."

Kai tsaye kan gado ta fad'a tasaki kuka mai sauti, kuka kawai takeyi tana sharar hawaye tarasa kukan da takeyi na farin ciki ne ko a kasin hakan,
Tabbas tinda Allah ya had'ata da wad'an nan mutanen takejin k'aunarsu irin ta iyaye ta shegeta, a lokaci d'aya tasamu kanta a cikin farin ciki marar misaltuwa,
Tasaka bayan Hannunta tashare hawayen fuskarta tana fad'in wanne dalili yasa suka d'aukeni sukabar garin nan dani suka jefar dani a k'auye a gefen hanya?'
Mena masu? Menatare masu suka jefar dani a dai dai lokacin da nake Neman kulawarsu?"

Sauban ya fad'o Mata a rai, ta fashe da kuka Mai sauti tana fad'in kazo gareni katafi dani, nasan kafi kowa sona da tausayi,
Mijina ko a wanne hali zaka shiga idan kaji nabar k'auye na b'ata ba'asan inda nakeba."
zamewa tayi ta kwanta tana kuka ta janyo fillow ta rungume tana tunanin fuskar sauban yanda yake murmushi mai nuna tsantsar tausayinta da k'aunarta,
Wasu daga cikin kalamansa ta tuna da yake cewa "Safna ki kwantar da hankalinki ki daina kuka ni Zan taimakekii zan zama gatanki zan d'aukeki a cikin k'auyen nan natafi dake cikin birnin Adamawa a cikin gidanmu na sarauta Zan baki farin ciki zan mantar dake rashin iyaye da kikayi.

hannu biyu tasaka ta damk'e fillow tare da runtse ido tana fad'in gani a kusa dakai a cikin garinku mijina ta yaya zanganka kacikamun Alk'awarin da kayimun, domin na tabbata kafi iyaye na tausayina da k'aunata." Tabbas dolene na bar gidan nan na shiga cikin gari lungu da sak'o domin na nemoka na zauna tare dakai na rayu dakai rayuwa ta har Abada."

Tana hakan wani irin bacci mai k'arfi ya Figeta Wanda bata shirya yinsaba."
Dattijiyar nan tagani bafulana wacce ta taimaketa a cikin daji, Wacce tasaba gani a duk lokacin da take cikin damuwa tana share mata hawayenta,a cikin baccinta
tsaye take a gabanta ta had'e fuska Sab'anin duk zuwan da take mata cikin murmushi take ganinta,wnn karon daga ganinta ranta a b'ace yake tsaye take a gaban Safna tana kallonta, wanda itama Safna ita take kallo,
cikin b'acin rai tace "meyasa zakiyi butulci ga iyayenki bayan kece farin cikinsu,
Iyayenki basuda laifi a sanadin b'atanki,
Kin bani mmki safna a maimakon kiyi farin cikin had'uwarki da iyayenki sai akasin hakan,
To kisani muddun Kika bar gidan nan da sunan guduwa zancire hannuna ga duk kan lamarinki Zan sakamaki ido, ina mai tabbatar maki mundun Kika gudu kikabar gidan nan zakiyi rayuwa Mai tsanani Wanda zaki gwammace gara zaman k'auye da ita.'


Hannu biyu safna ta had'e wuri d'aya alamar ban hakuri tana fad'in kiyi hakuri Inna bazan gudu ba,
Kifad'amun gaskiya Da gaske sune mahaifana?" Sune suka haifini?"

"Kwarai kuwa sune mahaifanki sune farin cikinki
Kema kece farin cikinsu."

Ta mik'a mata towel Mai had'e DA kayan sanyi masu shegen kyau tare da zanen da aka tsinceta dasu sanye a jikinta,

Kayan da ita dai safna tasan tabarosu a gida a cikin d'akinta,
Wad'anda ta rigada ta sadak'ar da sunriga da sun b'ata, saigasu a hannun wnn dattijiyar kirki Tana mik'o mata,
tace ga kayanki kirikesu a wurinki sune zasu kuma tabbatarwa iyayenki ke 'yarsu ce jininsu ce."

Karb'ar kayan safna tayi ta rungume a jikinta tana murmushin jin dadi domin taji dadin ganin kayanta wad'anda take ajiya da b'oyo tamkar kud'i."
d'aga kan da zatayi domin tayi Mata godiya sai gani tayi ta b'ace mata bako alamunta,

A firgice ta farka daga baccin da ya d'auketa abin mamaki ta ganta rungume da kayan jarintarta a jikinta.
Zaro ido tayi cike da mamaki ta rungume kayan tana zubar da hawaye."

A d'akinsu Hajiya falmata.
"Alhaji na rantse da Allah wnn yarinyar 'yatace Suhailat wacce tab'ata naga shaidu da alamomi wad'anda baxan tab'a mantawa a jikin 'yataba."

Shuru Alhaji habib yayi yana naxarin maganar matar tashi wacce take rungume a jikinshi, domin shima tun lokacin da yayi ido biyu da yarinyar yaji yana k'aunarta anan take yaji wani irin yanayi a tare dashi tamkar yana tare da jininsa yakeji."

Meye shedar taki wacce take nuni da 'yarki ce Hajiya?"
Ta tashi daga jikinsa ta zauna a gefen gado tace "Suhailat 'yata tun fad'owarta duniya na d'aga Kai na kalleta a lokacin da take tsala kuka a nan kalli bakinta har zuwa lebbonta naganta da tabo a leb'onta Wanda a lokacin sai da nanumaka kasancewar tabon gadon mahaifiyarmu ne, Wanda duk wata zuri'a tamu saika sameta da wnn tabon a gefen leb'o,
Suhailat 'yata tin tana jariri babu abinda ya banbataka da ita hatta 'yan yatsun hannunta dana k'afa duka nakane Kai ta d'ebo, musamman idan tayi mafarki tana dariya tamkar Kaine kake murmushi,
Yau naga duk abinda nake lissafa maka shi a tare da 'yata Wanda kaima kasan da hakan, Dan hakan katashi mutafi mugabatar mata da kanmu a matsayin mahaifanta domin 'yarmuce ba yar kowa bace."

Baiyi musuba hakan ya mik'e yabi bayan Hajiya falmata suka nufi d'akin safna,
Tura k'ofa sukayi suka shiga gaba d'ayansu tare da sallama."

Amsa masu safna tayi tana zaune a tsakkiyar gado rungume da kayan jarintarta."

Karaf idon su Hajiya falmata da Alhaji Habib ya sauka akan kayan wad'anda har su mutu bazasu manta dasuba a jikin yarsu wad'anda tana sanye dasu a jikinta a b'ata,
Kayan da Alhaji Habib yasayo da hannunsa a lokacin da ya tafi dubai, ganinsu yayi a jikin wata jaririyar balaraba suka bashi sha'awa sai da yashiga kasuwa ya nemosu yasaya a lokacin Hajiya falmata tana da tsohon ciki d'an wata tara."

A tare suka zaro ido suka had'a baki sukace Suhailat,
Hajiya falmata ta ruga ta rungume Safna tana fad'in wlh 'yar muce tadawo garemu Alhaji kaga zahiri KO."

Alhaji Habib murmushi farin ciki yakeyi y d'aga hannu sama yana hamdala a wurin ubangijinsa."
[3/30, 9:56 PM] Hayat: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍



🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*Page 36*






Shigowar Hajjah kenan a d'akin taga yanda gudan jini yake fita a bakin sauban Sarki yana kansa yana girgiza shi cikin tashin hankali yana fad'in "katashi sauban kada.mutu kabar mahaifinka,
Bintu ta mutu ta barni bana so kaima katafi ka barni."

Hankalin Hajjah a tashe tanufi ofice d'in likita cikin tashin hankali ta tura k'ofa tashiga tana fad'in likita sauban ya mutu yakazo ka taimakemu."

cikin hanzari likita ya ajiye biron hannunsa ya biyo bayan hajjah domin yatafi yaga halin da sauban yake ciki."

Sarki akan gadon sauban yana share masa jinin dake fita a bakinsa cike da tashin hankali yake cewa kada kamutu kabarni sauban katashi Zan baka dukkan abinda kake so."

Turo k'ofar da likita yayi, yayi dai dai da kuma turo wani gudan jini a cikin bakin sauba,
Cikin hanzari likita yanufeshi yashiga bashi taimakon gaggawa, ganin abin ya citura yakasa dawowa da numfashinsa gashi ga dukkan alama zuciyarsa ta kusan bugawa gaba d'aya ta daina aiki."

Ya juya ya kalli Sarki da hajjjah tare da safwan Wanda shigowarsa kenan, sai sharar hawaye yakeyi ganin mawuyacin halin da abokinsa yake ciki,
Likita ya bada umurnin duk sufita waje zaiyi aikinsa."

Hakan suka fita jiki ba kwari,
Hajjah ta kalli Sarki tace "umurni nabaka ba shawara ba, abawa sauban abinda yakeso idan ba hakan ba mudun sauban ya mutu bazan b'ata yafe makaba,
Dafe kai sarki yayi ya kalli mahaifiyar tasa hajjah yace "umma kiyi hakuri tun farko nayi kuskure danak'i goyon bayan sa akan abinda yakeso,
Da ace na Amince masaba da ba'a kawo hakan ba,
Nima nayi Alk'awarin duk inda safna take a cikin garin nan sai na sanya annemowa sauban ita ya aureta in har hakan shine samun lafiyarsa da kwanciyar hankalinsa."
Ya juya ya kalli Safwan yace
"Safwan kanada hoton ita budurwar abokin naka?"

d'aga Kai Safwan yayi alamar eh cikin yanayin rashin k'arfin jiki,
Yaciro wayarsa a Aljihunsa ya shiga ma'ajiyin hotuna yashiga kamo hotunan safna Wanda ya d'aukeso tareda sauban suna cikin farin ciki a k'auye,
Ya nunawa Sarki, Sarki ya karb'a yana kallo ya fahimci yanayin da suke ciki a lokacin da akayi masu hoton ya tabbatar da bak'aramar shakuwa bace tashiga tsakanin sauban da yarinyar dibon yanda yake murmushinsa Mai tsada Wanda bakoda yaushe yakeyin irinsa ba sai idan yana cikin farin ciki, ya girgiza kai ya mik'awa Safwan wayarsa,
Snn ya juya yakira bafadensa na hunnun damarsa yace kaje Safwan yatura maka duka hotunan sauban da yarinyar da yakeso a wayarka akwai abinda zanyi dasu."

Haka kuwa akayi duka hotunan safwan ya turawa bafaden,
sarki yace ka barsu a wayar ka Zan nemeka."

Suna tsaye jigun jigum a wurin suna zaman jiran fitowar likita domin suji abinda zai fad'a akan sauban fatansu daya kada ace masu ya mutu."

Suna hakan Saudat ta iso wurin tare da mahaifiyarta wad'anda sunci ado sai kyalli sukeyi tamkar wad'anda zasutafi wurin gasar nuna gwani a wurin Kwalliya ko wacce sai k'amshi take zubawa suna sanye da Alkybba wacce take nuni da jinin sarauta ne,
Kowa sai ido yake binsu dashi yana kallo cike da mamaki kamar wad'anda zasu tafi gidan biki,
musamman Saudat saikace ba mijinta bane kwance a kan gadon asibity tamkar gawa,

Wurin Hajjah da Sarki suka nufa mahaifiyar Saudat tamasu ya Mai jiki cike da nuna mulki da isa,

Ba itace a gabansu ba, Dan hakan basudamu da nuna mulkin da takeyiba Dan kuwa idan mulki take nema to a gaban,sarki take,

Bayan sun gaisa ne hajjah tayimata ya hanya,
Ta amsa tana mai daukar wayar hannunta wacce aka kirata da ita,

ta dan janye daga nesa da,wurin tana waya, bayan ta k'are wayar ne suka nemi wuri a can gefe d'aya suka zauna itada saudat da mahaifiyar tata gimbiya bilkusu taci gaba da sak'awa saudat magganu akan ciwon sauban, tana fad'in ai idan har sai ya auri shigiyar yarinyar nan gara ya mutu a hakan, KO kuma ya dawwama a cikin ciwonsa, me akeyi da kishiya wlh kishiya Annobace fitinace keni da babanki yayimun kushiya gara Allah ya k'arb'i rayuwarsa ya mutu kowa ya huta."

Saudat tayi saurin kallon mahaifiyarta tace "Kai mommy daddy kikeyiwa fatan mutuwa,
Nikam banason daddy ya mutu garadai ya k'aro auren ya maki kishiya goma da daddy na ya mutu."

"Rufemun baki gimbiya bilkisu tace a tsawace sakarai kawai wacce batasan ciwon kantaba, ni mahaifiyarki kikeyiwa fatan kishiya?
Ta mik'e tsaye tace "Zan tafi Allah yabawa mijinki lafiya,
Nasan ko badad'e ko bajima sai ya auri yarinyar da yakeso tinda inada labarin cewa tana nan da ranta bata mutuba tana cikin garin nan kingani nemanta baxai masa wahalaba, idan daddynki baiyimun kishiyaba ke mijinki zaiyimaki ya auri wacce yake so ya nuna mata soyayya sab'anin ke, dakece kike sonshi bashine yake sonki ba, duk lokacin da kika janye Addu'ar da kikayiwa mahaifinki na ya k'aromun kishiya kizo Zan taimakeki kamar yanda nasaba, kisani ke 'yatace d'aya tilo wacce nake tsananin ji da ita, amma kisani akan kishiya kowa Zan iya juyawa baya domin nakwaci 'yancina, akan kishi komai Zan iya aikatawa mutum idan yanemi yayi mun Addu'ar k'arin kishiya nabarki lafiya tayi tafiyarta tare da yiwa su hajjah da Sarki sallama wad'anda suke tsaye nesa dasu can a gefe d'aya cikin tashin hankali."

Tsaye Saudat

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login