Showing 36001 words to 39000 words out of 243403 words

Chapter 13 - DUK KARFIN IZZATA BOOK 2 COMPLETE

02 Feb 2025

46741

mutanen haka suke sun fi son a sansu ta aikin su ba ta suna ko fiskar su ba" "hakane Ahzan kana da gaskiya to Allah dai yasa mu dace" "amin Omar sai munyi waya" yana gama faɗin hakan ya katse kiran tare da sauke nauyayyar ajiyar zuchiya ya miƙe ya fice daga ɗakin.

UK

misalin karfe 1:30pm jourfree ya shigo ɗakin Bgs da nufin ya gyara masa ɗakin, ganin Hiyana a sume ne ya bashi mamaki, da sauri ya koma kitchen ya ɗauko ruwa ya dawo ɗakin, kusa da ita ya tsugunna ya zuba mata ruwan, a razane ta mike tana faɗin "yaya prince kayi hakuri wlh ba zan sake ba na tuba" "what are U saying madam? Jourfree ya jefo mata tambaya, dawo da kallon ta tayi kansa chikin sauri ta mike tsaye tana gyara hijabin jikin ta, kasa kasa tace masa " "as from today i don't want to see U here again, pls get out" chikin tsoro jourfree ya juya ya fice a ɗakin dan ba zai iya jayayya da maganar hiyana ba kuma bai san ya zasu kwashe da Bgs ba lallai akoi dirama.

Aiki hiyana ta shigayi tama manta ya sata frog jump, yace karta tashi har sai ya dawo aiki, duk da zafin da kunburin da kafarta suke hakan bai hanata ta fara tikar aiki ba wanke masa toilet tayi tas ta shinfiɗa masa gado ta gyara ko ina ta sanya masa turaren ɗaki mai daɗin kamshi, karfe 1:55pm ta kammala aiki ta ɗauki kayan ta ta nufi hanyar fita ɗakin har ta kai bakin kofa sai kuma ta juyo, tace "kai yau dai tun da baya nan wlh sai na je wajen hutawan shin nan nagani, dawowa tayi ta nufi kofar glass dake kusa da toilet, a hankali ta tura ta shiga wajen

wani iska mai shegen daɗi ne ke kaɗawa awajen saman kujera taje ta zauna tana bin wajen da kallo, mikewa tayi ta ɗauko ruwa da glass cup ta dawo ta zauna ta zuba ruwan a cup ta fara sha sanyin ruwan na ratsa ta sai wani lumshe ido take, tana sauke Ajiyar zuchiya, Almost 15mins tana zaune awajen har barchi ya fara ɗaukan ta, alamar tafiyan mutun da tajine yasa ta miƙe chikin sauri tana karanto duk addu'ar da tazo bakin ta, dan neman Allah ya tsareta daga faɗawa hannun Bgs.

dai dai zata fita shi kuma yana shigowa a razane ta ja da baya, chikin fushi da bachin rai fuskar shin nan kamar hadiri a daure tamau ya damko wuyar ta ya jata zuwa karshen wajen, chikin tsawa yace "ke bana che karna sake ganin ki a daki na ba shine zaki shigomin har nan" tsabar tsorata hiyana ta kasa magana, ta kasar ido ya kalli kasar benen, san nan ya dawo da kallon sa kanta, sai faman girgiza masa kai take ta kasa magana, wurgi da ita yayi kasan benen chike da ɓachin rai ya juya ya koma chikin ɗaki, wayar sa ya ɗauka ya kira jourfree, chike da izza da bada umarni yace wa jourfree yana bukatar a chan za masa komai dake wajen shakatawar sa na chikin ɗakin yana gama bawa jourfree umarni ya wuche cikin toilet.....

Hiyana kuwa tana fadawa chikin katon pool dake wajen, da kyar ta iya sai ta numfashi ta Allah ma yasa ta iya ruwa tun a kauye dan tun suna yara suke zuwa rafi, da kyar ta iya fitowa, kasa tafiya tayi ta zauna a bakin pool ɗin tana kuka kasa kasa dan sautin kukan nata ma baya fita sosai


NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

💖The Talent Troupe Writer's 💖


*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*


Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

Book 2

*Episode 13*


.......sai 6pm Hiyana ta lallaɓa ta zagayo ta koma chikin gida a babban palon kasa tachi karo da yaya khalid, zai koma part nasu, sugunnawa tayi har kasa "yaya khalid ina wuni" "me ya fitar dake waje sister? Shiru ta ɗanyi tana tubanin abun da ya dace ta faɗa masa "Bgs ne ya miki wani abun ko? Dan naga hawaye a face naki" Chikin sauri ta girgiza kai tana faɗin "aa yaya Khalid ba shi bane" kallon ta khalid yay fara yi from head to toe, kawar da kai gefe yayi chike da bakin chiki yace "ok jeki yi wanka ki chanza kaya kizo part nawa ki sameni kuma kizomin da wayar ki" sai lokachin ta tuna ashe tana da waya, jiki ba kwari ta mike ta haye sama, tana tafiya tana tunani, wai shi yaya prince ai na ya keson na sa rai nane ya kashe ni ma ya huta kawai na gaji nagaji sa irin azabtar dani da yake wayyo Allah dan isar ka ya Allah ka kawomin ɗauki, da wannan tunanin ta shiga palon su, zaune saman sofa mai zaman mutun 3 ta samu Fahad yana sanye da jallabiya fara yana latse latse a waya, tsugunnawa tayi har kasa "yaya Fahad ina wuni" sai lokachin ya ɗago ido kallo ɗaya ya mata ya kauda kan shi gefe chike da bachin rai ya mike har wani huchi yake kamar wani zaki ya nufi betroom na Bgs batare da yache da ita komai ba.

kwanche saman gadon ya same'sa idon sa a lumshe, kallo ɗaya Fahad ya masa ya gane bai yi barchin ba, chike da fushi ya fara magana "yaya prince ka dubi girman Allah ka tausayawa sister wai dan Allah me ta maka ne da har ka tsaneta haka pls ko dan farincikin Ammi da Abba ka rinƙa tausayin sister, ina kakeson yarinyar nan ta sa ranta dan Allah dai, ko so kake watarana zuchiyar ta ta buga ne? ba ni kakewa ba amma duk sanda kayi mata wani abun jinake zuchiyara kamar zafa fashe, ji nake kamar zan mutu, nasan kana son mu baka son ɓachin ran mu kana kauchewa duk abun da zai samu bachin rai, to kasani fa wlh idan kayiwa sister wani abun gaba ɗayan mu ji muke kamar zamu mutu dan ɓachin rai, mu muna sonta muna kaunar ta, munason farinchikin ta kamar yadda mukeson na Auta, karka manta fa wlh ina da tabbacin Ammi tafi son Hiyana sama da yadda take son Auta, wlh ko dan Ammi dole naso yan uwana, lokachin da aka aura min Amrat ban son ta amma dana fahimchi yaran nan sune farincikin Ammi, sai na hakura na rungumi matata Allah da ikon sa kuma chikin ƙanƙanin lokachi ya dasamin son ta a rai na, dan Allah yaya prince ka bawa sister kulawa ko dan Ammi, da Abba ina da tabbacin hakanne kawai burin da ya rage musu a rayuwa pls yaya prince ba dan kowa ba dan Allah.

Ba tare da ya bude ido ba yawa Fahad alama da hannu akan yazo, ba musu yaje ya zauna a gefen sa
Wani wawan mari ya sakar wa Fahad ɗin a kumatu tare da mikewa zaune ya wato idon sa waje, chike da ɓachin rai ya fara magana "kayi girman da zakazo ka tsaya a kai na kanamin magana haka ko? Chikin sanyin murya da danasanin Fahad yace "kayi hakuri yaya prince bachin rai ne yasa hakan amma am so so sorry ba zan sake ba" shiru Bgs yayi bai sake magana ba "yaya prince dan Allah ina neman wata alfarma" zuba masa ido kawai Bgs yayi batare da yayi Magana ba, "dan Allah yaya prince kabar sister ta dawo ɗakin ka wlh ban son ganin ta a palon nan kuma kaga tana da tsoro sosai" shiru yayi na tsawon 2mins kafin yace "me ya samu ɗakin na ta? Da sauri Fahad ya kara juyowa da kyau yana fuskantar shi dan jin yadda Bgs ɗin yayi magana chikin sanyi murya da alama zasuyi nasara "yaya prince ai ton lokachin da ta kalli snake a ɗakin take tsoron shiga" zuro dogayen kafofin sa kasan fadon yayi ya miƙe batare da yace da Fahad komai ba ya nufi wajen hutawan sa dake chikin ɗakin, shiru Fahad yayi yana addu'a a chikin zuchiyar sa Allah ya ɗora su a kan Bgs Allah ya sa ya yarda hiyana ta dawo ɗakin sa, Almost 30mins yana zaune daga ƙarshe dai ya mike ya fice daga ɗakin chike da sa ran zasu iya yin nasara awan nan karon dan, yadda yaji yaya prince yayi magana a hankali.

Zaune saman sofa a palo ya samu hiyana ta takure waje guda da alama sanyi takeji, "sister tashi kije ɗakin ki ki chanza kaya" chikin rawar murya tace "yaya Fahad wlh tsoron ɗakin nake ji bazan iya shiga ba" shiru yaɗan yi kafin yace "ok ɗauki kayan naki muje na rakaki part ɗin yaya Aiman sai kiyi wanka a chan ki chanza kaya" ba musu ta mike ta ɗauko wasu riga da sket masu shegen kyau black colour, ta nufoshi gaba yayi ta bishi a baya, har part na Aiman.

Zama Fahad yayi saman sofa a palo san nan yayiwa Hiyana nuni da betroom din yace taje tayi wanka yana jiranta a nan, dan ya lura tsoron part ɗin take.

Jikinta sai kerma yake ta shiga betroom ɗin Aiman wani makeken hoton'sa ta fara chin karo da shi a gefen gado yana sanye da jeans da t-shirt ya ɗaura rigan aikin sa a sama kayan yana ɗan murmushi, ganin hoton Aiman ba karamin tayarwa Hiyana hankali yayi ba, nan take hawaye suka fara zarya akan fuskanta, tana kuka tana bin ɗakin da kallo karaf idon ta ya sauka kan wani makeken Frame mai kyau gaske wadda ke ɗauke da hoton Bgs yana tsaye da kakin sojoji ya rike Ak47 a hannun sa, ba karamin kyau yayi ba fiskar nan tashi kamar kullun babu alamar annuri ko kaɗan,kurawa hoton ido tayi tana ta kallon sa tana goge hawaye ta, 15mins ta ɗauka tana kallon hoton kafin ta wuche ta nufi toilet a gurguje tayi wanka ta fito, shiryawa tayi chikin riga da sket din ta nufi gaban mirrow ta tsaya tana kallon kanta

Ba karamin kyau kayan suka mataba sun fito mata da ainihin suran jikin ta,

kai kallon ta tayi kan kirjin ta gaba ɗaya rabin boobs nata awaje kasan chewar wuyar rigan babban ne sosai gashi kayan sun manne da jikin ta sun matse ta sosai, tsaki ta ja ta sanya hannu ta tara kyakkyawar lallausan bakin gashin kan ta a tsakiya ta daure ta kitse bindin gashin ta watsa shi baya wadda ya kai har karshen bayan ta, kunyan fita hakan take ji gashi hijabin Amrat ya jike kuma yayi datti sosai, shiru ta tsaya a ɗakin almost 10 mins tana tunanin yadda zata fita da kayan nan a hakan ma wai ta zaɓo kayan masu ɗan fasali kenan, data ga dai tsayuwa ba zai tsinana mata komai ba sai ta, dauki kayan ta da ta chire ta kare kirjin ta dasu ta kama hanyan fita tana tafiya gaba ɗaya a takure take har ta fito palon

Yadda ta bar Fahad haka ta fito ta same'sa yana zaune yana latsa waya, jin Sallamar tane yasa ya ɗago kai kallo ɗaya ya mata ya kau da kai tare da mikewa yayi gaba yana faɗin "to muje" bayan sa tabi hannun ta rike da kayan da ta chire ta kare kirjin ta dasu, part nasu suka koma.

Yana shiga palo ya wuche betroom na su ita kuma hiyana ta zauna saman sofa, ta kame jikin ta waje guda, dan ji take kamar babu kaya ajikin ta a haka har barchi ya fara ɗaukan ta gyarawa tayi ta kwanta ba jimawa barchi yayi awan gaba da ita

KHALID

wunin yau gaba ɗaya Zahra ta wuni ne tana kuka khalid yayi rarrashi har ya gaji taki yin shiru taki chin komai tun safe ga zazzaɓi da ya rufe ta, Sosai Khalid ya shiga damuwa, ya rasa meke masa daɗi
........zaune yake gefen gado yayi tagumi ya rasa meke masa daɗi, Zahra na kwanche saman gadon tana kuka kasa kasa, chikin shesshekar kuka tace "yaya Khalid" chikin sauri ya juyo tare da haurawa saman gadon ya karisa in da take, hannun ta ya kama chikin nashi murya kasa kasa Kamar mai raɗa yace "am sorry my wife kiyi hakuri kinji? Chikin dashewar murya tace "yaya Khalid ka dai na damuwa kaji bana son ganin ka kayi shiru kana tunanin nan" "my wife in dai baki dai na kukan nan ba baki chi abinchi ba, ba zan dai na damuwa ba" "to yaya khalid kamin tausa dan ko ina chiwo yake min idan na samu sauki zan chi abinchin kaji? Chikin sauri ya fara yimata tausa yana faɗin "yanzu nan ma ina gama yimiki tausan nan zaki samu sauki sai na baki abinchi da kai na ko? Kakalo murmushi dole Zahra tayi ga hawaye na bin gefe da gefen fuskar ta tace "to amma iya tea kawai zan sha" "ok to ko tea din ma yayi bari na kawo miki" batare da ya jira amsar taba ya sauko daga gadon ya nufi, waje.

Jim kaɗan ya shigo hannun sa ɗauke da kyakkyawar cup, mai ɗauke da tea mai zafi gefen gadon ya zauna tare da ajiye cup ɗin a saman drawer gefen gadon, hannu yasa ya ɗago ta ya ɗaurata kan chin yar sa, ya ɗauki tea ɗin ya fara bata a baki, a hankali hankali take dan sha har ta shanye "in karo miki wani ne? "Aa yaya Khalid ya isa haka wannan ma da kyar fa na shanye" batare da ya sake magana ba ya ajiye cup ɗin a saman drawer, san nan ya miƙe tare da ita a jikin sa suka haura saman gadon.

Kwanchiya yayi, tana manne a kirjin'sa, a hankali yake shafa bayan ta yana mata raɗa a kunne tun Zahra na share sa har ta fara biye masa suka chigaba da zubawa juna kalaman love.

Maiduguri Nigeria


Ahzan ne zaune saman karfet a betroom din mum ɗin sa yayin da mum ke saman gado suna hira
"Ahzan kana ganin hakan shine dai dai? "Eh mum ya kamata mu taimaka mata" "amma Ahzan abun ne da ban mamaki anya Dr walid bai yi kuskure ya baka result na wata ba, a mai makon na Ummi dan ni dai ban ga alamar Ummi na bukatar aure ba" "mum baki ji Dr yace yanzu ne abun ya fara kamata ba idan ta kara 1 week ba tare da an mata aure ba, shine abun zai bayyana karara kuma kinga idan hakan ta faru ba zanji daɗi ba" "Ahzan Hanan fa zata girmi Ummi sosai dan yadda nake ganin Ummi ba zata wuchi 16 years ba kawai tana da wadatatchen halittace, ni anawa ganin idan ma hakane to chiwon hanan ya kamata ya fara kamawa ba Ummi ba" "mum kowa da kike gani a duniyar nan da irin tasa kaddarar, ai wanna chiwon bai bi ta shekaru ba" "hakanne Ahzan kana da gaskiya to shikenan zanyiwa dadyn ka salim magana" "to mum amma fa karki sanar da kowa batun chiwon nata dan kar su fara magana akai" "ai wannan abun kunya ne baki ba zai iya faɗi ba" "yauwa my mum san nan kinji Dr yace kar a wuche 1 week baa mata Aure ba idan aka wuche za'a samu matsala, ba ƙaramin tausayi yarinyar ta bani ba shi yasa ma na yanke shawarar Auren ta kawai, dan in shere mata hawayen rashin iyaye" "In Sha Allah zaka samu ladan hakan" "Allah yasa my mum, amma mum yana ga baki shirya zuwa wajen aiki ba jiyama fa baki jeba lfy" "wlh Ahzan gaba ɗaya jikina a mache ne bana iya komai sai kwanchiya kawai" shiru Ahzan yayi yana tunani a ranshi "kai gaskiya maganin na aiki da kyau am sorry mum ba zaki iya komai ba kwakwalwan ki ma bazata yi aiki ba bare kiche babu irin wan nan chiwo a duniya, dole sai abun da na tsara miki shi zaki yi, bazaki iya fita ko nan da tsakar gida ba har sai an ɗaura Aure na da Ummi dan karki bata min shiri nasan kina fita zaki samu lbr ana neman Ummi dan haka babu in da zakije sai bayan Aure, shima dady salim yanzu zanje nayi maganin sa dan idan yazo kawai ya amince da zanchen Aure na da Ummi, babu wan da zai zo gidan nan da sunan yazo biki salon suga Ummi, su tonamin asiri Auren sirri za'ayi
"Ahzan tunanin me kake? Da sauri ya dago kai tare da mikewa ya nufi hanyar fita daga ɗakin yana faɗin "babu wani tunanin da nake mum ina tausayin yarinyar ne kawai" ya kai karshen maganar tare da ficewa daga ɗakin, gyara kwanchiyar ta mum tayi a saman gadon ta ta lumshe ido ta chigaba da barchinta da ta fara.


KANO

da sallama ɗauke a bakin sa Aryan ya shigo fada, kallo ɗaya Abba dake zaune kan kujerar sarauta ya masa ya kau da kansa gefe dan bai san ganin Aryan a chikin wannan hali kwata kwata, saman kujerar kusa da Abba yaje ya zauna "Aryan yaushe ka dawo? "Yanzu na dawo Abba" "to ya ake chiki Allah dai yasa diyanar ce" "aa Abba ba ita bace, wadda suke magana a kanta wai mahaukachiya che wani ya buge da mota to kaga ita kuma ai ba mahaukachiya bace shiyasa ban ma bi ta kan maganar tasu ba ina jin hakan nayi dawowata kawai" "eh lallai Aryan na yarda kana chikin matsananchin tashin hankali wadda yasa baka iya tantanche abubuwa" juyowa Aryan yayi da kyau yana kallon abba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login