Showing 45001 words to 48000 words out of 243403 words
chike da ɓachin rai ya juya ya nufi chikin gida da sauri Aunty Farida tabi bayan sa.
Saman doguwar kujera mai zaman mutun 3 ya zauna yana furzar da iska mai zafi daga bakin sa, gefen sa Aunty farida ta zauna chike da tausayin ɗan uwan na ta ta fara magana "kayi hakuri Aryan ba dare ba rana muna addu'a In Sha Allah diyana zata dawo garemu" shiru yayi dan ya kasa magana, karar shigowar sako wayar sane yasa ya ɗago tare da fitar da wayar yana sauke zazzafar ajiyar zuchiya, yasha ruwan mamaki lokacin da yaga wadda ya turo masa sakon, number Bgs ne ya turomasa sakon wani address, fita yayi daga wajen massage ya shiga contact ya fara kiran layin Bgs
Wayar tana ta ringing har sai da ta kusa katsewa tu kun nan Bgs yayi picking "Hello my blood Ykk? ya Uk? daga ɗayan ɓangaren Bgs yace "am fine what of U? "same here bro i saw Ur massage this address is for who? Shiru Bgs ya ɗanyi na yan sakanni kafin yace "am sorry tun jiya naso na turomaka ina busy ne akan batun kama su marwan da yan ta adda su kayi, alkhairin da na ɗauka maka akan ka bani 2daya zan nemo maka matar ka to shi ne na chika, address ɗin in da matar ka take ne" a'sukwane Aryan ya miƙe chike da farinchi yace "nasani na san zaka iya fiye da hakan, my blood 1 in million nasan ba dan busy da kake ba da ka ɗaɗe da nemo min ita, Allah ya maka albarka ya Allah yasa ka gama da duniya lfy daman nasan in ba kai ba ba wadda zai min wanan aiki chikin kankanin lokaci haka wai kasan me ma? Shiru Aryan yaji Bgs bai amsa ba chiro wayar yayi daga kunnen sa sai yaga ashe already Bgs ya katse kiran tun ɗazun farin ciki da zumuɗi ne yasa bai ma san lokacin da Bgs ya katse kiran ba
Hanyar fita palon ya nufa chikin sauri ya manta ma da Aunty farida suke zaune, muryar tane ta katse shi da chewa "Aryan lfy ni kabar ni a duhu me Prince ɗin ya tura maka? "Aunty farida ke kam ki jirani ina zuwa" ba tare da ya jira amsar taɓa ya fice daga palon, sauri sauri ya umarchi sojojin sa akan su shiga mota,
da gudu suka shehshege chikin motar, suka tayar, da wani mahaukachin gudu suka bar gidan, sai faɗa Aryan ke musu akan hanya akan su kara sauri, dan shi gani yake kamar idan bai yi sauri ba ahikenan zai rasa diyana, map na wayar sa ya buɗe ya shigar da address ɗin a wajen, da mamaki yake kallon waje basu da nisa da gidan Aunty farida, tunanin yake to anya wayan nan suna da hankali kuwa? ashe ma suna kusa? babu in da ba a baza hoton diyana a garinnan ba, zasuche basu gani bane, da bazasu kai ta police station ba,suka ajiyeta awajen su nan take yaji ransa yayi mugun ɓaci sosai amma da ya tuna yau zai ga diyanar sa sai ya ji ransa ta ɗanyi sanyi, daga ɗan nesa da gidan su Ahzan sukayi parking na motochin su, fitowa Abdol yayi ya buɗe wa Aryan chikin sauri Aryan ya fito yana kallon wayar sa, shiru ya ɗan yi yana so ya tantanche wani gidane gidan su Ahzan daga chikin gidajen layin, call ne ya shigo wayar sa, ganin kiran Bgs ne yasa ya ɗauki wayar da sauri.
"Hello my blood" daga ɗayan ɓangaren Bgs yace "ka kara gaba kaɗan gidan na gaban ka" murmushi kawai Aryan yayi dan yasan in dai Bgs na son yin abu tofa 30mins yayi yawa angama da wannan matsalar sai dai wata "Aryan kaje ba sai ka katse kiran ba ina ganin ka" "ok my blood" chike da jarunta Aryan ya fara taku, chikin sauri jibga jibgan sojojin sa suka diro daga saman nasu motocin suka bi bayan sa, hannu ya ɗaga musu alamar baya bukatar su bi sa, yana tafiya Bgs na faɗa masa in da zai bi, dai dai kofar gidan su Ahzan Bgs yace "nagama aiki na all the best my blood" yana gama faɗin hakan ya katse kiran juyowa Aryan yayi kallo ɗaya yayiwa gate ɗin gidan su Ahzan yaji ya tsani ganin gidan kwata kwata ƙarisawa bakin gate ɗin yayi chike da kyamar gidan yasa kafa ya taka gate ɗin a hankali dan ba zai iya sanya hannun sa a kazamin gate ɗin gidan nan ba
Da gudu mai gadin gidan su ya nufo wajen gate ɗin ya bude kofar, a tsorace mai gadin ya fara kallon Aryan from head to toe duk da Aryan ya rame sosai kallo ɗaya zaka masa kaga chikakken jarumin namiji ɗamtsen hannun sa kawai mai gadin yake kallo, kamar zasu fasa riga dan murɗewa da Chika, chike da tsoro Mai gadin yace "sannu ranka ya daɗe" kafa Aryan ya sanya ya shigo chikin gidan ba tare da yayi Magana ba, dan yana tabbacin diyana na chikin gidan nan, Bgs baya binchike akan abu sau biyu idan yayi binchike yace ga result tofa wannan result ɗin haka take babu tantama, idan kuma har diyana na chikin gidan nan tofa babu wanda zai rage a gidan nan bai ansa hukunchin ba.
A harabar gidan ya tsaya ya zura hannu a aljihun sa yana bin gidan da kallo kamar mai binchiken wani abun
da sauri mai gadin ya nufi chikin gida, jim kaɗan ya fito tare da Ahzan, kallon Aryan Ahzan yake kamar ya sanshi bin kirar jikin Aryan yayi da kallo duk tsawon da Ahzan yake da shi a kafaɗar Aryan ya tsaya "malam lfy ka shigo mana gida ba da izinin mu ba? chewar Ahzan yana magana a tsorache dan yadda ya kalli fiskan Aryan bai ga alamun annuri ba bai ga alamun wannan fuska ta san menen dariya ba" A wulakan che Aryan ya kalli Ahzan from head to toe, chike da jin haushi ya buɗe baki zai yi magana kenan sai ga hanan da Ummi sun fito, zasu shiga part ɗin su deen kallon Ummi kawai Aryan yake lokaci guda yani harshen sa ta masa nauyi tambayar kan sa yake wai shin gaskiya idon sa ke faɗa masa ne ko karya, runtse ido yayi da karfi ya furta "ke zo nan" a tare Hanan da Ummi suka juyo kallon Aryan Ummi take sosai ji take kamar ta sanshi ji take kamar ta taɓa ganin sa, chikin tsawa da tsoro Ahzan yace da su hanan "me ya fito da ku zaku wuche ku komane ko sai na same ku awajen" chikin sauri suka juya suka koma chikin gidan, chike da iyayi Ya juyo yana kallin Aryan "malam ka fice daga gidan nan tun ban kira yarana sun fitarmin da kai ba, daman ka karya doka ka shigo gidan mutane ba tare da izinin suba" shiru Aryan yayi yana tunanin hukunchin da ya dache da Ahzan
hannu Ahzan yasa yana kokarin ture Aryan akan ya fita daga gidan iya karfin sa ya sanya yana ture Aryan amma ina ko motsi Aryan bai yi ba.
gaba ɗaya ganin Ummi yasa jikin sa ya mutu baya son bugun mutun yanzu amma yazama dole Ahzan yaji kamshin lahira yanzu, damko wutar Ahzan Aryan yayi ya ɗaga shi sama yayi wurgi da shi gefe, wani ihun azaba Ahzan ya saki wadda yasa gaba ɗaya family Alhj Abbas fitowa da gudu, nan take Aryan yaji ransa yayi mugun bachi gadan gadan ya tinkari Ahzan kafar sa ta damko, ya ɗaga shi ya sake wurgi da shi gefe, wani wawan bugu ya kai masa a gefen chiki, kwata kwata Ahzan ya kasa ihu ma sai zazzare ido kawai yake kuka yaki fitowa, wani razannen ihu Mum Ahzan ta saki wadda ya sa Aryan ɗagowa ya kallin in da suke karaf idon sa ya sauka kan razanannen fuskan Ummi da ta kankame hanan hawaye na zuba daga idon ta, dafe kai yayi yana kallon ta baya son kukan da take, alama ya mata da hannu akan tazo kara kankame hanan tayi alamar tsoron sa take, shafa kan sa yayi da hannu ya chije lips nashi na kasa da karfi chike da jin haushi ya daka mata tsawa "zo nan nace" jikin ta har kerma yake ta kariso in da yake tsaye sai kuka take kasa kasa, daga ɗan baya kaɗan ta tsaya, hannu yasa ya fiskota ta faɗa kan faffadar kirjin sa rungumeta yayi sosai yana sauke nauyayyar ajiyar zuchiya gaba ɗaya jama'ar dake wajen, suka zuba masu ido, sai mutsu mutsu Ummi keyi ajikin sa yana kankame da ita da hannu ɗaya, yasa ɗayan hannu ya chiro wayar sa daga aljihu ya fara kiran layin Shahram, bugu ɗaya Shahram ya ɗaga "kuzo ku kwashe jamar dake chikin gidan nan dukka ku wuche dasu Kano, ku miƙasu ga D P O sai na dawo" yana gama faɗin hakan ya katse kiran, ya ɗan duƙa ya saɓi Ummi a kafaɗar sa, ya nufi gate ɗin gidan sai kuka Hanan take ta rungumi mum, duk iskanchin irin na Deen yau sai da ya nitsu kamar bashi awajen ya rungumi mum ɗin sa yana zare ido kamar an tare ɓera a tarko
Aryan na fita gidan rundunar jibga jibgan sojojin sa suka diro chikin gidan gaba ɗaya wayan da suke gidan suka tattare kowa dake chikin gidan har da mai gadi suka nufi airport suka wuche kano da su,
Gidan Aunty farida Aryan ya wuche da Ummi, Aunty farida na zaune a palo tayi shiru abun duniya ya ishe ta tunani take awani duniya diyana take yanzu.
Dauke da Ummi a saman kafaɗar sa ya shigo palon bakin sa ɗauke da sallama, chikin sauri Aunty Farida ta miƙe murya na rawa tace "diyana Aryan ina.. bata karisa maganar ba ta yake jiki zata faɗi da sauri Aryan ya tare ta, da hannu ɗaya ya sauke diyana daga saman kafaɗar sa ya rike Aunty farida da kyau ya kwantar da ita saman doguwar sofa dawo da kallon sa yayi kan Ummi dake tsaye tana zazzare blue eyes nata "ke ɗauko min ruwa a fridge" ya ƙarisa maganar tare da nuna mata in da fridge ɗin yake, ba musu ta nufi wajen ta ɗauko ruwan faro mai sanyi ta kawo masa ansa yayi ya buɗe bakin robar ruwam ya tarbo a hannun sa ya shafa ma Aunty farida a fuska, ajiyar zuchiya ta sauke tare da waro idon ta waje, mikewa yayi ya koma saman sofa mai zaman mutun 2 ya zauna ya sunkuyar da kan sa kasa, miƙewa zaune Aunty farida tayi chikin en ena tace "my diyana zo ki zauna kusa da ni mana, juyawa Ummi tayi tana neman ta ina diyanar take, ɗago kai Aryan yayi yana kallon ta, chikin sanyin murya yace "zo "yayi maganan yana mata alama da hannun sa, chike da tsoro ta karisa wajen sa hannun ta ya kama ya zaunar da ita kusa da shi chikin sanyin murya ya fara magana "me yasa kika tafi ki bar wajen da Aunty farida tace ku zauna ku jira ta? Me yasa baki sanar da wayan chan banzayen ke matar Kga bane? Shiru Ummi ta ɗanyi kamar mai tunani chan kuma tace "wacece kuma Aunty Farida? Ni ban san kuba dan Allah ka mai dani wajen Aunty Hanan tsoro nake ji" tana magana kamar zarayi kuka, zuba mata ido kawai Aryan yayi yana kallon ikon Allah yau diyana ce zata che bata san shi ba?
Masu karatu sai mun haɗu ranar Saturday idan Allah ya kaimu yau naje kunshi ne shi yasa baku samu long page ba
Jinjina da fatan alkhairin gare ku matanen duk karfin izzata paid group
Godiya da fatan alkhairin gare ku mutanen duk karfin izzata comments section group ina ganin comments naku ina godiya Allah ya bar zumunchi
Aisha baita jidda my mum
Aunty Asma'u
Aunty asmy
Sister shamsiya
Maman Amir
Maman Amira
Queen Haseena
Aunty Aisha
Aisha bello ashlady
Aisha gala dima
Baby Zahra
Sis Halima
Aunty kharima
Da duk sauran wayan da basu ji sunan su ba, ina miko sakon gaisuwa
Jinjina gareku the talent troupe writer's fatan nasara garemu
💖The Talent Troupe Writer's 💖
Wannan page ɗin sadaukar wane gareki masoyiya Gidan Aunty ya Allah ya baki lfy Allah yasa kaffara ce
💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*
Duk mai buƙatar littafin bDuk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai
Book 2
Page 16
......Aunty farida ta kasa magana dan ganin abun take kamar a mafarki, shi kan shi Aryan ji yake Kamar mafarki yake, kuka diyana ta farayi tana jan hanchi, chikin sauri Aryan yace
"kukan me kuma keke? Me akamiki?"
Chikin kuka tace "ni ku mai dani gidan mu wlh tsoron ku nake ji kuma dan Allah kar ku dake ni"
jawota Aryan yayi ta faɗa jikin sa ya rungume sosai a jikin sa, chiki sanyin murya ya fara magana
"ya isa kukan haka kinji ko? Wayan chan da kika zauna da su basune yan uwan ki ba wanchan gidan ba shine gidan kuba, nan shine gidan ku kunji ko?
Dago kai tayi daga kirjin sa chikin kuka ta fara magana "daman yaya Ahzan ya faɗamin ina da iyaye da yan uwa, sai dai bai san in da yan uwan nawa suke ba, Shiyasa ba zai mai da ni gida ba kenan yanzu kune yan uwan nawa? Mai da kan ta yayi saman kirjin sa ya kwantar yana shafa bayan ta ganin hakan yasa Aunty farida ta miƙe ta bar palon
"Kin san me nake so dake? Tana kokarin ɗago kai daga kirjin sa tayi magana ya mai da kan nata ya kwantar yana faɗin "ban che ki ɗago kai ba ban che kiyi magana kiyi kwanchiyar ki kawai kiyi shiru ki saurare ni"
shiru tayi ta lafe a jikin sa, tana kuka kasa kasa, chigaba da magana yayi
"daga yau karki sake zanchen wayan chan kazaman, mune yan uwan ki, nine mijin ki, kuma yayan ki, ki manta da wayanchan idan ki kayi kuskure sake yimin maganar su tofa zan hukun taki dan a yanzu duk duniya ba abun da na tsani ji da kuma gani kamar su, yanzu zamu koma asalin family hause namu mai yiwuwa idan munje chan zaki iya tuna wani abun kin ji ko?"
daka tawa yayi da magana yana ɗan shafa wuyar ta, ji yayi numfashi ta ya sauya alamar ta masa barchi a jiki nauyayyar ajiyar zuchiya ya sauke tare da sanya hannu ya ɗago haɓar ta sosai ya zuba wa face nata ido, godiya da kirari mai tarin yawa yarin ƙa yiwa Allah, ji yake sabuwar son ta da kaunar ta na ratsa shi kasa jure kallon face natan yayi, ya rankofo da kan sa dai dai sai tin face nata, Slowly ya kawo ɗan bakin sa kan nata sai kerma lips na shi keyi, sumbatar ɗan ƙaramin bakin nata yayi chikin sauri ya chire bakin sa dan ji yayi tamkar an tsira masa allura from head to toe gangan jikin sa ta an shi sakon.
a hankali chikin da bara ya kwantar da ita saman sofan ya miƙe tsaye ya chiro wayar sa ya kira layin Aunty farida, har wayan ya katse Aunty farida bata ɗaga ba, mai da wayar aljihu yayi ba tare da ya sake kiran taba.
Sauri sauri Aunty Farida ta sauko daga sama ta dawo palon tana faɗin
"Aryan lfy kake kirana?"
"Lfy daman zamu wuche ne"
"haba Aryan why ba zaku bari sai gobe ba?"
"No Aunty farida ga dukkan alamu yarinyar nan ta samu matsala a brein nata kwata kwata fa bata san wacece ita ba bata san mu ba ta manta kowa da komai,so nake mu koma kano a yau adu bamin lafiyar brein nata da ma lfy jikin ta gaba ɗaya"
dogon numfashi Aunty farida ta ja tare da sauke ajiyar zuchiya kafin tace
"hakane Aryan to shikenan Allah dai ya sa ba wata matsala babba bane"
kasa kasa yace "Amin tare da juyawa ya sanya hannu ɗaya ya ɗauki diyana ya saɓa ta a kafaɗarsa suka nufi waje, sai addu'a da fatan alkhairi Aunty farida ke musu har suka fice daga palon.
Kano
Zaune saman sofa a ɗakin sa haidar yake shikaɗan yana latsa waya shiru ɗakin kamar babu kowa sanyin A.c da daddaɗan kamshin Air freshener ke tashi,
chike da yanga da duniyan ci zulaihat ta shigo ɗakin babu ko sallama, jikin ta sanye da wasu shegun riga da wando wadda suka matseta sosai, gaba ɗaya halittar jikin ta a bayya ne, bata sanya breaziya ba wayan nan shayyayyun breast natan kamar silifas awaje, ta sanya wani shegun takalma a kafarta sai wani taunan chingam take, kusa da Haidar taje ta zauna chikin kissa da kisisina irin na yan duniya ta fara magana "hiii Haidar Ykk? ba tare da ta jira amsar shi ba ta chi gaba da magana Amma kai daga gani kanin wanchan mutumin ne ko? Maman ku ɗaya ko? Dan naga kuna kama sosai gaskiya ba karya kaima kyakkyawa ne tun ranan da na gan ka awajen chin abinci a palon Abba naji na kyatsa, idan ba damuwa zamu iya ɗaukan hoto?
Ko kallon in da take Haidar bai yi ba bare ta sa ran zai mata magana da alama bai ma jin me take faɗe dan ya sanya blth a kunne, kara matsowa tayi kusa da shi ta chi gaba da Magana
"am pls zaka kai ni shan ice cream? Daga nan sai muje wajen shakatawa idan zamu dawo sai mu biya ta wajen shopping dan inason sayan kayan haɗin shisha da ita kanta tukunyar shishan" ta karisa maganar tana kokarin rungumar sa.
chikin sauri ya miƙe tsaye ya buɗe baki yana kokarin yin magana,
miƙewa tayi chikin sauri ta rungume shi, nan take ya ɗauke diff kamar an ɗauke wutan nefa kamar ya