Showing 174001 words to 177000 words out of 243403 words

Chapter 59 - DUK KARFIN IZZATA BOOK 2 COMPLETE

02 Feb 2025

46733

manta da ita sai ya sawa baban su hiyana sona haka ko akayi ban wuci kwana uku da dawowa ba ranar da maman su hiyana ta haifi amrat aranar ta bar gidan ta bar kauye gaba ɗaya,nan muka sake komawa wajen bokan arana ta biyu ma sai da na bashi kai na sanna ya amince ya mana aikin mallaka min baban su hiyana sai yadda na yi da shi a takaice dai bayan munyi Aure da baban su hiyana na mallake sa sosai baya kula kowa sai abun da nace har ƴaƴan sa baya kulawa to akoi lokacin da asirin da na masa ya karye hankali na ya tashi dan alokacin ya sake ni da yake ya kamu da ciwon kafa baya iya komai sai ce masa nayi babu inda zanje a gidan zan zauna Allah sarki bawan Allah haka ya rabu da ni nayi kokarin komawa wajen bokan da kawata sadiya ta haɗamu dan ni tun lokacin da yamin aiki nayi aure daga shi har sadiya ban kara bi ta kan su ba atunanina ba zan bukaci komai ba kuma,dana isa wajen bokan sai aka cemin ai ya jima da mutuwa wai wani aiki yayiwa wata aka kunce aikin sai ya dawo kansa aikin,dan da yazo mutuwa yana ihu yana faɗin habiba kin cuceni kinsa nayi aikin da aka warware sa ya dawo kai na jin hakan yasa na gane aikin da yayiwa maman su hiyana ce ta dawo kansa na girgiza ainun na ji tsoron kar maman su hiyana ta dawo ban gama kwashe dukiyar Ahmadu ba nan na fara tunanin ya zan ɓullo wa lamarin na fara tunanin kashe Ahmadu sai na tuna ko na kashe sa ban isa in taɓa dukiyar sa ba kowa ya sani al adar kauyen nan ne,baka isa ka taɓa dukiyar mutun idan ya mutuba har sai an raba gado gwarama yana yare zaka iya taɓa wa wanna a gaban sane nayi tunani da dama ban samu mafita ba daga karshe na yanke shawarar ziyartar Sadiya kawata ko zan samu ta bani shawara lokacin danaje gidan sadiya kishiyar ta ta sanar dani asirin sadiya ya tonu ta gudu ta bar kauye ta tafi dan kar mutane su kashe ta ta tafi birni neman kuɗi jiki ba kwari na juya na dawo gida nazo dai dai zan shiga gida na haɗu da Innar buba na tsaya muka gaisa to dama muna shiri da ita sosai da Innar bello ce bama shiri dan ita innar bellon nan ta cika wa'azi dayawa bayan mungama gaisawa take tambaya ta lafiya ta ganni haka ina ɗari ɗarin gaya mata dan karta faɗa wa yaya na amma sai na daure na faɗa mata ina gama bata labari ta kwashe da dariya ta riko hannuna tace muje,ba musu na bita muka kutsa cikin daji nan ta kaini wajen nata bokan wadda ya min cikin nan da farko nace ina son yayiwa baban su hiyana asiri ta yadda zai ban dukiyar sa dukka da kansa ya gwada ya gwada abun yaki yiwuwa yace min hakan bazata yiwuba domin baban su hiyana yana da tsari a jikin sa sosai bello ya masa maganin tsari ajiki a lokacin,nace ya bani maganin da zan kashe shi da kai na dan inason muci gadon sa,sai yace ba wani magani da zai kamasa sai dai in dai da kai na zanje na yankasa da wuka ko na dannesa da pillow haka muka kamo hanya aiki bai samu ba jiki ba kwari muka nufi gida a hanya innar buba ke sanar dani mu kashe bappa sai mu aurawa hiyana buba cikin ruwan sanyi sai mu kashe diyana amrat lamrat ita kuma hiyana sai ta haifi yaro ɗaya sai mu kashe ta daga baya mu kashe yaron dan bamu bukatar jinin su dukiya zai zamo namu da murna na amince da shawarar ta ido na ya rufe da son duniya bayan na dawo gida na kara ninka wa su diyana azaba kan wanda nake musu duk dan wuya ta kashe su Allah sarki Allah yasa suna da tsawon rai watanar jummaa babu kowa a gida na shiga ɗakin bappan su yana kwance saman yar gadon sa yana barci da a wawtata da wuka zan yanka shi sai Innar buba ta hana tace mu danne sa da pillow dan kar asirin mu ya tonu haka ko akayi yana barci nasa pillow na danne sa na haye saman ruwan cikin sa tunyana yunkurin kwace kansa har ya saduda ya fara furta Kalmar shahada bappa na da taurin rai sai da na ɗauki wajen 15mins ina danne da shi baya numfashi sanna ya mutu farkon dannesa da nayi ina iya jiyo me yake faɗe banda sunan maman hiyana da su hiyana ba abun da yake kira daga karshe ne daya tabbatar mutuwa zanyi ya fara furta kalmar shahada ina kashe sa na fice naje na sanar da innar buba mukayi ta murna a tare a gari kuwa nayi kamar ban san komai ba bayan rasuwar sa nayi kokarin a ɗaura Auren hiyana da buba ta hanyar zuwa wajen bokan mu ya rufe mun bakin jama'ar kauyen ta yadda za'a ɗaura auren ba tare da cececuce ba haka ko akayi boka ya rufe bakin kowa akan mutuwar bappa da auren hiyana ana gab da za'a ɗaura auren Aisha yar baban su hiyana tazo ta ɗauke su suka tafi birni tunda suka zo sau ɗaya har yau ban sake ganin su ba amma duk da haka ban kyale su ba sai da nasa aka haukata diyana akan kunce tsarin da bappan su ya musu,wanna shine takaitacen abun da na aikata" salati gaba ɗaya wajen yasa a fusace Hajj fateema ta mike tana faɗin"da iya cutar da ƴaƴana kikayi zan iya hakuri na barki da Allah amma kin cutar dani dayawa daga karshe kika kashe min mutumin dana fiso fiye da kowa aduniya na gudu na bar iyaye na saboda shi na bar komai na saboda shi na bar cikin masarautar mu saboda shi kin cuceni dayawa habiba dole ki ansa hukunci"tana kai karshen maganar ta mike da sauri ta fice daga gidan tana kukan kashe bappa da inna abiba tayi.

Kallon Aunty salma Aunty Maryam tayi tace "muje koh?"a tare suka mike suka bi bayan Hajj fateema chan jikin mota suka hangota tana tsaye ta dukar da kai kasa tana cikin matsanancinyar damuwa,karisawa wajen sukayi Aunty maryam tace "muje ne?"girgiza kai Hajj fateema tayi kafin tace"aa nayi waya da Abba zai yi magana da sarki yola za'a turo jami'an tsaron su wuce da habiba da uwar buba sai na ga tafiyar su sanna zan wuce"da sauri Aunty mardiya tace"gaskiya kamata yayi Yusuf ko Aryan ne zasu basu hukunci dan inna ce Prince ba makawa kashewar parad ɗaya zai musu" "eh zancen ki gaskiya ne idan yan sanda sun kama su sai a wuce dasu kano Yusuf ya musu hukunci"cewar Aunty salma shiru wajen yayi basu sake magana ba kowa da abun da yake tunani

Iya comments iya read more ba dai wadda zatace bai yi update ba daga yau na dai na Long page sai an dawo yin comments gobe idan Allah ya kai mu 1 read more zaku samu sanna na kashe update na weekend ❌


To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu



💋 Duk Karfin Izzata 💋


💋The talent troupe writer's 💋



By
Star Lady



Page 49



KANO

ABBA & AMMI

zaune suke a palon sa su biyu suna hira cikin nitsuwa Abba yace "Aisha ina son ki bani hankalin ki sanna ki bani nitsuwar ki ki sa aranki komai ya faru da bawa mukaddari ne daga Allah sanna ki ɗauki hakan a matsayin jarabawa" shiru Ammi tayi ta tattara hankalin ta dukka ta bawa Abba kirjin ta na dukan uku uku dan tun da taji Abba yace hakan tasan ba lafiya ba,cigaba da magana Abba yayi "kuskure dai mun riga munyi duk da cewa haka Allah ya kaddara amma nima ina da nawa laifin ni nake hana ki zuwa kallon yan uwan ki har abubuwa suka rinƙa faruwa wallahi rashin zumunci bai yi ba kwata kwata,ko da sau ɗaya ne a sati ya kama ka rinƙa wai wayan yan uwanka ko ka kirasu awaya dan jin ya suke amma ke na hana ki zuwa wajen yan uwan ki tsawon shakara 7 zuwa 8 ina mai baki hakuri ta wanna ɓangaren ki min afuwa" ita dai Ammi shiru tayi ta zuba masa ido zuciyar ta na dukan uku uku burinta kawai taji me Abba ke son sanar da ita "fateema ta sanar min ɗazun habiba ita ta kashe mahaifin su hiyana da hannun ta yanzu mun sa jami'an tsaron sun kama ta" zubur Ammi ta mike tana faɗin "what!? Habiba ne ta kashe Ahmadu da hannun ta!!?no ba wasu yan sanda da Za'a haɗa ta dasu ni da nake da hukuma da doka gaba ɗayan ta a gida dole ta karɓi hukunci dai dai da abun da ta aikata a ɗaure min ita ba wanda zai mata hukunci sai Safras shine dai dai zai iya hukuntata akan abun da tayi"mamakin yadda Ammi ke magana har da kiran sunan bgs ya hana Abba magana da alama yau Ammi ta fusata sosai ta fita hayyacin ta"A'isha koma ki zauna" ba musu ta koma ta zauna tana faɗin"ban yarda kowa ya taɓa habiba ba idan ba Safras ba shine zai iya yi mata hukunci dai dai da abun da tayi dan bana son amata kisan farat ɗaya" "A'isha habiba tayi laifi dayawan da dole ta ansa hukunci kisa ni da kai na nace a rufe ta sai komai ya dai dai Safras ya dawo hayyacin sa ya mata hukunci habiba ita ta haukata Hajj fateema sanna ta haukata diyana ta azabtar da su hiyana bayan nan ga laifin zina ga shirka babban laifi fiye da komai a duniya haɗa Allah da wani wa iya zubillah bayan nan ga kisan kai ai dole habiba ta karɓi hukunci kisa taje can lahira ta samu Ubangiji data haɗa da wani ya mata nashi hukunci,shirka shirka shirka babban laifi ne number 1 a duniya wadda idan kana aika tashi ka mutu ba makawa jahannama kai tsaye zaka tafi babu wanda Allah ya tsine masa sau biyar a Qur'ani sai boka ai idan mutun yana da hankali ma wallahi ko sau ɗaya Allah ya tsine wa mutun bazaka kusancesa ba bare har sau biyar kai jama'a ya kamata murinƙa tunawa zafa mu mutu muje mu samu Allah da kuke haɗawa da wani awanna lokacin shi kan shi wanda ka haɗa da Allah neman ta kansa yake yana neman Rahman Allah kuma ba samu zai yi ba daga shi har masu binsa zasu samu azaba mai tsanani basu samu Rahman Ubangijin ko ɗigo,ya Allah ka kiyashe mu haɗa Allah da wani Allah ka bamu ikon rike ka kai ka ɗai" "Amin ya Allah" Ammi ta amsa da shi,cigaba da magana Abba yayi "sanna magana ta gaba Aisha yau kwanan 16 ke nan da accident na su Safras ina son ki sani ba accident su kayi ba zan faɗa miki hakan ne ba wai dan ki tada hankalin ki ba ko kice zaki shiga tsakanin mata da miji zan faɗa miƙi ne dan ki kaiwa hiyana agaji dan har yanzu bata ko motsi idan har na isa da ke karki tofa wani magana mara daɗi cikin maganar nan dan Safras yayi nadama abun da bai taɓa a rayuwar sa saboda son hiyana ya kwanta a hospital nan dukka yaran nan a tunanin su na haifesu ne kawai basu san cewa dasu nake kwana dasu nake tashi a rai na ba duk abun da suke akan ido na suke komai abun da ya faru Safras ya kusanci hiyana cikin fushi bayan haka baya cikin hayyacin sa shine aka samu matsala yanzu tana gidan sa na us karki nuna musu kamar kin san komai ki kyale su a matsayin accident ɗin yanzu ki shirya kije ki kula da hiyana tana bukatar kulawar uwa kusa da ita duk da cewa har yanzu bata farka ba amma komai na jikin ta ya dai dai ta bugun numfashi ta ya dai dai ta sai dai ciwo da bazaa rasa ba zata iya farkawa akowani lokacin awanna lokacin tana bukatar kulawar uwa da kuma soyayya kin san irin wanna abun idan ya faru da mutun wuya mutun yake rayuwa idan ya rayu kuma wani sai kiga ya farka da taɓin hankali saboda razana da yayi bana fatan hakan ya faru da ita ina fatan ta farka lafiya lau nasan zataji tsoron Safras sosai karki bari wani magana na Safras ya je kunnen ta kisa ta manta da Safras har sai komai ya dai dai ta sai ta samu sauki sosai a hankali zamu komar da ita dai dai kuma mu nuna mata Safras na son ta da gaske"tsabar tausayin hiyana Ammi bata san lokacin da hawaye ya fara bin kumatun ta ba"haba Aisha menene abun kuka addu'a zaki mata ki shirya da wuri amma ina son ki san wani abu ɗaya duk in da Safras yake zai zo wajen ku dan yanzu ma bai yarda hiyana ta mutuba yanzu haka yana gadon asibitin ma yana bincike akan ta tabbas zai zo duk da nasa a canzawa hiyana gida Aryan yayi kuskuren kai ta gidan Safras,yanzu cikin sauki Safras zai gane tana raye shi da yake da Camera a gidan da bana shi ba ina ga gidan sa kuma kin san akoi Cameran kuma yana bincika Cameran tabbas zai ga kwanciyar hiyana a gidan sa tayi jinya dan haka zai nemota ko ina ne shiyasa ban wahalar da kai na wajen kai ta wani kasa ba na barta a us ɗin dan nasan ko ina na kai ta zai nemota ni wani lokacin ma kai fin ƙwaƙwalwan Safras na bani mamaki da tsoro idan ya tsaya yayi tunani akan abu tofa komai wuyar abu sai ya samo solution akai ina fatan kafin ya bar asibiti ya fara neman ta Allah ya bata lafiya sanna idan ya zo gare ku karki shiga tsakanin sa da matar sa koda tana jin tsoron sa ki basu waje shiya san yadda zai shawo kanta dan duk duniyar nan yanzu shi kaɗai zai iya sa hiyana ta sauko ta yarda da shi yasan yadda zai yi ya gyara abun da ya ɓata dan haka ki basu waje ki musu fatan alkhari dan yanzu ban son abun da zai sake ɗaga wa Safras hankali saboda yanayin da yake ciki ba zan iya jure ganin sa cikin tashin hankali ba nafi son sa fiye da komai yanzu a rayuwata ki kula da hiyana sosai dan Allah"shiru Ammi tayi tana mamakin wanna lamari "lallai Safras bai kyau taba amma ba yanda zanyi dole nabi umarnin mijina dan naga dai dai a rayuwa" da wanna tunanin ta mike ta fice daga palon,dogon numfashi Abba yaja tare da sauke ajiyar zuciya kafin ya mike ya shiga bedroom nashi

*Uk*

Zaune Aryan yake kusa da bgs yana fuskantar Aunty farida dake zaune saman lallausan kujerar dake cikin ɗakin hospital ɗin ba laifi bgs ya samu sauki sosai sai dai yanzu ya koma gidan jiya da rashin magana dan idan Aryan zai kwana yana masa magana sai ya ɗauki mintoci kafin ya ɗaga musu kai ko ya girgiza kai amma magana da baki kam shiru kake ji abun har ya fara bawa aunty Farida tsoro dan gwara da abaya ma idan kawa bgs magana ko da zai ɗauki mintoci amma zai amsa maka da baki saɓanin yanzu sai dai ya ɗaga kai kwata kwata bai san ana magana kusa da shi,dan isu magana da Aryan har dafe kai yake alamar sun dame sa tun ranar daya farka ya tambayi ina hiyana Aunty farida tace masa ta rasu tun lokacin bai sake magana ba suyi magana har su gaji baya amsawa har sun fara sabawa da yanayin sa.
Shiru suka zauna kowa da abun da yake tunani mikewa bgs yayi ya cire ruwan da aka sa masa tare da zuro kyawawan kafafun sa kasa ya mike tsaye ya rame sosai kamar ba shi ba"bgs ina zakaje? Cewar Aryan shiru yayi ko kallon in da Aryan yake bai yi ba ya wuce ya nufi hanyar fita daga ɗakin kallon Aunty farida Aryan yayi yana kokarin yin magana Aunty farida ta rigashi da cewa"lallai Prince shi ciwon ma karo masa sabon wulakanci tayi eyee ko kallo bamu ishe saba kenan?"girgiza kai Aryan yayi kafin yace"aa Aunty farida kin san fa daman can haka yake saboda sister yasa ya sauya ya fara magana to yanzu dai sai kuyi hakuri sai komai ya dai dai ta sister ta dawo kila mu dace ya dawo ya cigaba da magana ko ba yawa ne"hararar sa Aunty farida tayi tana faɗin"dama ya za'ayi ka ansa laifin Prince tun da bakin ku ɗaya sai ka tashi muje ai wai masu jinya ne,mara lafiya ya tafi ya barmu a shanye kamar wasu babbakankun kaji"mikewa Aryan yayi ba tare da ya sake magana ba mikewa itama tayi suka jera suka bi bayan bgs.
lokacin da suka fito ba bgs kuma ba Fahad dake zaune a wajen,da sauri suka nufi parking space na hospital ɗin suna mamaki wato shi bgs bazai ma jira asallame su ba.
Ko da suka je ba su bgs kuma ba motar Fahad tsaki Aunty farida taja kafin ta wuce ta nufi nasu motar shi Aryan abun ma dariya yaso bashi. Suna cikin tafiya a kule Aunty farida tace "lallai Fahad wato shima har da bin Prince ɗin duk sun haɗu sun mai damu mahaukata" "haba Aunty farida wlh ba haka bane ina da tabbacin bgs yace zai yi tuki da kansa ne Fahad yace bari ya tukasa gudun kar asamu matsala tun da ba gama samun lafiya yayi ba kin fa san halin bgs dan Allah karki ga laifin Fahad ko nine a matsayin da Fahad yake abun da zanyi kenan" "hmmmm bayan bakin ku ɗaya ke nan ba"shiru Aryan yayi bai sake magana ba dan yasan Aunty farida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login