Showing 180001 words to 183000 words out of 243403 words
yake maganar nan da ita kwata kwata arayuwar sa bai san yawan magana idan yayi magana ya wuce 5mins kan sa har ciwo yake masa to amma ba yadda zai yi dole yayi magana da ita dan sauraron voice nata ne kawai zai iya sa yayi barci,jin yayi shiru yasa tace"yaya Prince sai da safe" "ke kika kira ne?"gurgiza kai tayi tana faɗin"a'a"shiru yayi ya rasa me zai sake cewa dan iya maganar da ya iya dukka ya mata gashi bai gaji da jin voice nata ba bare yace sai da safe dafe kansa yayi ya fara tunanin "wai su Khalid da suke ɗaukan tsawon lokaci suna hira da matan sun nan me suke cewa?" yayi nisa cikin tunanin abun da ya kamata ya faɗa mata har zufan dole ya fara haɗawa dan tsabar shiga tension ya rasa samun kalmomin da zai mata magana da su shi ba iya magana yayi ba bai san me ake kira da soyayya ba idan ba yanzu da so ta kama sa ba sai zufa yake duk da sanyi Ac dake ɗakin,zazzakar voice nata ne ya katse sa da cewa"yaya Prince barci nake ji"tayi maganar cikin shagwaɓa hakan ba karamin birki ta shi ta kuma yi ba bai san lokacin da yace"kizo mu kwanta"sai jin yayi tace"aa ni kam a nan zan zauna tsoron ka nake ji"jin amsar da ta bashi ne yasa ya gane abun da yace mata"kiyi addu'a karki manta"yana kai karshen maganar ya katse kiran ya maida wayar ya ajiye ya fara tunanin"wai me namiji ya kamata ya rinƙa faɗa wa wadda yake so ne?"ɗauko wayar tasa yayi ya kunna data ya fara bincike akan soyayya nan yaci karo da kalaman soyayya ya fara karantawa kamar haka"kece bugun numfashi kece rayuwa ta bazan iya barci ba tare dake a gefe na ba idan kika rabuda ni mutuwa zanyi kullun hoton ki nake fara gani kafin nayi barci bayan na farka hoton ki nake fara gani kafin nayi komai ba zan iya cin abin ci ba idan banji voice naki ba"dogon tsaki yaja tare da wurgi da wayar yana faɗin"shirmen banza dana wofi yanzu daman abun da su Aryan suka zauna suke kenan?me i can't do this no sense wasting of time"komawa yayi ya kwanta zazzakar voice nata na masa yawo a kunne in da ta shagwaɓe murya tace"yaya Prince barci nake ji"ji yaƙe kamar ya jawota ya rungume ta amma ba hali,da wanna tunanin barci yayi awon gaba da shi
A ɓangaren hiyana ma lokacin da ya katse kiran sai ta fara nadamar me yasa tace masa tana jin barci gashi ya katse kiran bata gaji da jin voice na shi ba lokacin guda taji mugun son shi na kara shigar ta tausayin sa ya kamata"Allah sarki da kyar yake magana kamar dole sai faman in ina yake yadda ma zaka gane da kyar yake maganar baya son yawan magana a rayuwar sa amma duk dan ya sani farinciki yake ta kokarin kakalo maganar dole Allah sarki yaya Prince karka damu In Sha Allah zan koya maka magana sosai"tana cikin tunani taji wayar yayi kara alamar shigowar sako tana dubawa massage na shine cikin sauri ta bude ta fara karantawa"my Eshat believe me I love you more than my life trust me i will make you happy all day in your life"cool murmushi ta saki duk da ba ta gane wani abun da ya rubuta ba bata san fassarar sa ba kai wayar tayi saitin ɗan karamin bakin ta ta manna wa wayar kisa tana faɗin"ina son ka nima ina son ka mijina"tana rike da wayar har barci yayi awon gaba da ita, already ita Ammi daman ta wuce ɗakin Abba tayi kwanciyar ta asuba ta gari.
8am ya farka slowly ya waro manya manyan idon sa waje a hankali ya mike zaune tare da zuro kyawawan dogayen fararen kafofin sa masu ɗauke da dogayen yatsu masu kyau gaske ga bakin lallausan gashi kwance kan yatsun nashi kusa da fararen farcen sa,mikewa yayi ya nufi toilet.
After 45mins ya fito ɗaure da towel a kugun sa ya nufi gaban mirror sauri sauri ya shafa kyakkyawa tsadedden body lotion nashi tare da gyara lallausan gashin kan sa sanna ya feshe jikin sa da body spray mai bala'i kam shi da daɗi ya wuce dressing room.
jim kaɗan ya fito sanye cikin dakakkiyar shadda fara tas halve jumpa jumpar bata karisa kai guiwar sa ba takalma sauciki brown yasa tare da hula brown yayi kyau sosai kamar shi yayi kansa ya ɗaura agogon diamond sanna ya ɗauki wayar sa ya fito a palon kasa ya ci karo da Aryan da diyana suna breakfast ko kallon in da suke bai yi ba ya wuce kafin diyana tace ina kwana har ya fice abun sa kai tsaye part nasu Abba ya wuce.
ɗakin Abba ya fara zuwa kwance ya samu Abba saman gado yana sharan barci,juyawa yayi a hankali ya fita dan kar ya tashi Abba yasan Abba ya gaji da yawa zirya tsakanin us da Nigeria dole yayi ta barci.
Yana fita ɗakin Abba ya shiga ɗakin Ummi da mamaki Ummi ke kallon sa da kyar ta iya amsa gaisuwar sa gani take kamar a mafarki bgs bai taɓa zuwa gai dasu da safe ba sai yau ganin Ummi ta shagala da mamaki yasa ya fice da sauri dan bai san African time,yana fita ya shiga ɗakin Ammi abakin kofa ya tsaya ya zuba mata ido yadda take cin abinci ta hankalin ta kwance tana zaune saman sofa ga plate shake da soyayyen kaza da cup na haɗaɗɗen tea a table ɗin gaban ta bata ma san da shigowar sa ba yasha ruwan mamaki lokacin da idon sa yayi arba da kyakkyawar face nata yau tayi kwalliya sosai diyana ta mata make up ta fito kamar ba itaba tayi kyau kamar ita tayi kan ta ɗan bakin nan nata yasha jan janbaki ta tasa soyayyen kaza a gaba tana ci tana shan tea Ammi na toilet tana wanka,a hankali ya tako ya shigo cikin ɗakin kusa da ita ya zauna ta tura nama a baki ta ɗago kai ta kalle sa cikin jin kunya ta sunkuyar da kai kasa tana kokarin magana yayi saurin ɗago habar ta da hannun sa ya haɗe bakin su waje guda ya zura harcen sa cikin ɗan bakin nata ya anshe namar dake bakin ta cikin wasa ya ɗan ciji harshen ta sanna ya zame bakin sa ya fara taunan namar da ya anshe daga bakin nata ciki shagwaɓa tace "wash me na maka da ka cije Ni?"tayi maganar tare da yin kasa da kan ta kunyar yadda yake kallon ta ya hana ta cigaba da magana hannu yasa cikin plate ɗin ba tare da yayi magana ba ya ɗauko wani nama yasa a ɗan ƙaramin bakin sa ya fara tauna.
sai da ya tauna sosai sanna ya ɗago habarta tare da haɗe bakin su waje guda a hankali ya fara tura mata naman cikin dan bakin nata yana kallon kyakkyawar face nata runtse ido tayi dan bazata iya kallon sa ba hakan yayi dai dai da fitowar Ammi daga toilet ganin abun dake faruwa yasa ba shiri ta juya ta koma cikin toilet ɗin a ranta tana salati"kai dole humaira ki bi mijin ki ban iya iyashegen kun nan haka kawai"zama tayi saman kujerar dake cikin toilet ɗin tana zancen zuci shiko bgs bai ma san da Ammi ta gansu ba a hankali yake tura mata namar a bakin ta ganin tana kokarin kwace kan tane yasa ya kara matsowa ya rungumeta da kyau ta yadda bazata kwace masa ba kusan tare suka ci namar daya tauna musun,dan sai ya tura mata a bakin ta tana kokarin hadiyewa sai ya sa harshen sa ya sake ɗebowa ya mai da bakin sa a tare suka cinye bakin su manne da na juna bayan sun cinye ma yaki sakin bakin nata sai da yayi ta wasa da harshen sa cikin bakin ta iya son ransa sanna ya sake ta,da gudu ta yunkura zata bar wajen yayi saurin damko ta ya jawo ta ta faɗa jikin sa kukan shagwaɓa ta sa masa tana bubbuga faffaɗar kirjin sa tana faɗin"yaya Prince ni bana so ka sake ni"dai dai lokacin Khalid da Zahra suka shigo dan gaida Ammi ganin su Khalid yasa ya sake ta cikin sauri ta mike ganin Khalid yasa ta kasa fita daga ɗakin ta koma ɗan gefe da shi ta zauna dan wani mugun kunya ne ya lulluɓeta ji take kamar ba kaya ajikin ta bazata iya bin gaban Khalid ta wuce ba kasa tayi da kan ta cike da kunya tace"ina kwana yaya Khalid"saman sofa Khalid ya zauna Zahra na rike da hannun sa ta zauna kusa da shi cike da kulawa yace"lafiya lou sister ya karfin jiki?"da kyar ta iya amsawa da"jiki yayi sauki"shikuwa bgs ko ajikin sa wayar sa ma ya fitar ya fara latsawa"Aunty hiyana ina kwana"cewar Zahra ta kasan ido hiyana ta harare ta kafin tace"lafiya lou yakika?" "Lafiya lou yaya Prince ina kwana?" "Kasa kasa yace"lafiya"tare da mikawa Khalid hannu sukayi musabaha mikewa yayi ya fice ya koma part nasu dan cire kayan hausawan nan gaba ɗaya cikin takura yake da kayan dama saboda Eshat ɗin sa yasa kayan.
dai dai zai shiga part nasu yayi karo da Aryan na fitowa baya kaɗan Aryan yayi ya bashi hanya ya wuce sai da ya ɗan wuce sa sanna Aryan yace"da alama bgs ya ajiye bindiga ya ɗau fure"a sukwane bgs ya juyo ya kalli Aryan gera ɗaya Aryan ya ɗaga masa alamar eh"wai ni bgs basu Ammi kaje gaidawa bane me kuma ya haɗa kayan ka da jambakin sister?"a sukwane ya kai kallon sa jikin sa yasha ruwan mamaki lokacin da idon sa ya sauka akan shatin ɗan karamin bakin ta ta ɓata masa farin kayan sa da jan jambakin a dai dai sai tin kirjin sa tunawa yayi da lokacin da ya jawota jikin sa ta faɗa saman faffaɗar kirjin lokacin ɗan karamin bakin ta ya sauka awajen,dawo da kallon sa kan Aryan yayi ya wurga masa harara kafin ya juya ya haura sama murmushi Aryan yayi kafin ya fice a ransa yana faɗin"ba dai mata ba to ka godewa Allah ma da ka saura da kwarin ka"ya kai karshen zancen zucin nashi lokacin da yayi sallama a bakin kofar ɗakin Ammi,nan ya samu Khalid Zahra hiyana suna hira Ammi na toilet tana son fitowa sun hana ta fitowa,dan haka sai tayi zaman ta cikin toilet ɗin kawai saboda bata shigo da hijabi ba.
"Aunty hiyana ina Ammi ne wai?"cewar Zahra"Ammi ta shiga wanka tun ɗazun"jin haka yasa Aryan ya mike yana faɗin"ok idan ta fito kice munzo gaishe ta sai da rana zan dawo"yana kai karshen maganar ya fice cikin sauri,da sauri Khalid ma ya mike yabi bayan Aryan ya rage daga hiyana sai Zahra matsowa kusa da hiyana Zahra tayi ta fara magana kamar mai raɗa"Allah Aunty hiyana wani lokaci kina yin abu kamar mara wayo meyasa kike yiwa yaya Prince haka?Allah idan baki dai na yi masa wulakanci ba kika kuresa sai ya kyale ki ya nemi wata kina ganin yadda mata ke son sa suna rububin sa kawai ki manta da duk wani abun da ya miki abaya yanzu tun da yana son ki da gaske kema ki nuna masa soyayyar sa da ya dade a ran ki kina ɓoyewa ki rungumi mijin ki idan ba haka ba Allah zaki dawo kina dana sani"harar ta hiyana tayi kafin ta fara magana"danasanin me zanyi?ba sai ya kara yin auren ba ni ina ruwana da shi"dariya Zahra tayi kafin tace"eyee da dai ban san irin bala'i son shi da kike yi bane sai ki wani ɗaure min fuska kice zaki min iya shege to na san komai sanna kuma ji yadda kikace ya kara auren akule fa kikayi maganar tsabar kishi har da wani kara ɗaure fuska wai ya kara auren mana nan kuma tafasa zuciyar ki ke miki kikayi maganar abeg malama idan zaki hakura ki rungumi babyn ki ku cigaba da soyewa gwara kiyi kiyi sauri ki samo mana baby mai kama damu again mu zama yan huɗu"ta kai karshen maganar tare da sake kwashe wa da dariya"wai Aunty hiyana kin iya iskanci yasin jifa a hotel ɗin nan baki da lafiya kina cewa bakin son sa ya rabu da ke amma da ya zo fita wani kallon so da kauna da kike masa ta kasan ido yana fita har da sauke ajiyar zuciya jima lokacin da ya shigo ɗakin kin kasa hakuri sai da kikayi ta satar kallon sa ina fa ganin ki ko yanzu dakike mana wani borin kunya kina cewa ya sake ki ina ganin ki daɗin rungumar da ya miki kike ji kawai iskanci ne irin naki"a kule hiyana ta kai mata duka da gudu Zahra ta mike ta faɗa saman gadon Ammi tana dariya tana faɗin"mu za'a wa iya shege wallahi na dai na bin bayan ki daga yau ina bayan yaya Prince"da gudu hiyana ta hau gadon dan Zahra ta kuleta daukan pillow tayi ta fara kai wa Zahra bugu tana kokarin yin magana idon ta ya sauka akan kyakkyawar face nashi yana tsaye jikin kofar shigowa ya harɗe hannu a kirji ya zuba musu ido lumshe idon ta tayi ra sake buɗe wa dan ta tabbatar shine ko ba shi bane ya sauya kaya zuwa kananan kaya wando jeans blue da t-shirt baki ba karamin kyau kayan suka masa ba kasa tayi da kanta ta sauko daga gadon ta koma saman sofa ta zauna cikin zolaya Zahra ta cigaba da magana ba tare da ta lura da shigowar bgs ba"Aunty hiyana na yaya Prince ana son yayana ana kai wa kasuwa wallahi idan kika bari yaya Prince ya kwace miki zaki gane shayi ruwane dan yadda kike bala'i son shin nan ya kyaleki ya nemi wata mutuwa nasan zakiyi ki bini a hankali ki lallaɓani na hakura na kara shawo miki kansa idan ba haka ba wata mata zan samo masa haɗaɗiya kyakkyawa wadda ta fiki kyau wai ni Aunty hiyana me yaya Prince ya miki nema kike wani dagewa baki son shi?wallahi tun wuri ki farka nagaya miki ki rungumi babyn ki ato ni barima kiga na tafi wajen Aunty farida ta kara min wasu shawarin yadda zan rike nawa babyn gam karya kalli wata dan ni kaɗai akayi shi Allah Aunty hiyana kin yi Sa'a fa ko da kike gabin yaya Prince shiru shiru nan wallahi mugun ɗan soyayya ne ya iya love in gaya miki ki manta da komai ki rungumo babyn ki ku cigaba da gashi kema ki fara karɓan abun da muka karɓa ida.......bata kai karshen maganar ba yunkurawar da tayi zata mike idon ta ya sauka kan kyakkyawar fiskar nan tasa ya ɗaure ta tamau kamar hadari mutuwar kwance tayi ta kasa miƙewa nan take jikin ta fara rawa ta fara tunanin abubuwan da ta faɗa da surutun da tayi addu'a take Allah yasa bai ji taba ganin yadda Zahra ta nitsu jikin ta sai rawa yake yasa hiyana kwashewa da dariya mai sauti har da dafe ciki zuba mata ido yayi yana kallon yadda take dariya aransa yana faɗin"auta dole na hakura na yafe miki kodan saka Eshat dariya da kikayi rabon dana ganta tana dariya haka ya jima gaskiya tun kafin auren mu watarana dana shigo palon Ammi na samu kuna hira da dariya gaskiya Eshat dariya na miki kyau"duk abun da suke Ammi na kallon su dan tuni ta fito daga toilet ta shiga dressing room ta shirya ta fito.
Sai da hiyana tayi dariyar ta mai isar ta sanna tace"Aunty Zahra na ina masifar son ki yasin"ta kai karshen maganar tare da kara kwashewa da dariya a katse Zahra tace"wallahi Aunty hiyana bana so"juyawa bgs yayi cikin sauri ya bar wajen dan sun so bashi dariya ita kan ta Ammi dake tsaye bakin dressing room sai da ta kwashe da dariya.
ganin bgs ya fice ne yasa Zahra mikewa zaune tana hararar hiyana a kule tace"muguwa kin san yaya Prince ya shigo ne ko ki ɗan min siginal na dai na zuba kamar ruwa kika kyaleni dan mugunta yanzu sai Allah kaɗai ya san hukuncin da zai min wayyo Ammi na na shiga uku wallahi na ma dai na bin bayan sa dukkan ku biyu ba ruwana daku kuje can ku karata"ita dai hiyana tikar dariya kawai take dan yadda Zahra ke magana ba ƙaramin dariya take kara bata ba,wuce su Ammi tayi ta fice ta nufi ɗakin Abba dan taje ta gaishe sa mikewa hiyana tayi ta dawo gado ta kwanta tana faɗin"ki wuce yaya Khalid fa na kiran ki Aunty Zahra"mikewa Zahra tayi ta nufi kofar fita a kule tace"ae,ko baki ceba dole na tafi wajen mijina idan mutun ya isa shima yaje wajen mijin sa mana"ta kai karshen maganar tare da ficewa daga ɗakin,gyara kwanciya hiyana tayi tana faɗin"can ta matse miki dai ni baki ishe ni kallo ba"shiru ta kwanta ba jimawa barci yayi awon gaba da ita.
1pm
Tana cikin barci taji an sureta kamar yar baby da kyar ta waro idon ta waje kyakkyawar fiskar mijin ta tayi tozali da shi mayar da idon nata tayi ta lumshe da murya irin na mai barci tace"yaya Prince ka sauke ni bana so"shiru yayi bai kula ta ba kai tsaye saman kujerar table ɗin cikin abinci ya sauke sanna ya zauna a kan nashi kujerar kusa da ita waro manya manyan idon ta tayi da kyau ta kallesa sanye yake cikin kayan aiki kara waro ido waje tayi ta ganshi da kyau shirye yake cikin kayan aikin sa kasa magana tayi tayi shiru ta sunkuyar da kai"my Eshat yinwa nake ji tun safe ban ci abinci ba pls ki bani a baki"girgiza masa kai tayi tana faɗin"aa ni bazan iya ba" "Eshat ba zaki iya ciyar dani abinci abaki ba?"gyaɗa masa kai tayi alamar eh"ko da hakan zai iya zama cin abinci na ta karshe a duniya?"ji tayi zuciyar ta ya bada dum dum kasa kasa ta ɗan kallesa a ranta tana tunanin"anya ba wasa dani