Showing 144001 words to 147000 words out of 243403 words

Chapter 49 - DUK KARFIN IZZATA BOOK 2 COMPLETE

02 Feb 2025

46768

anyi rarrashin duniya taki yin shiru kuma taki matsawa kusa da shi.

Yauma kamar kullun misalin karfe 8 na safe tana kwance kusa da shi tana kuka kasa kasa,idon ta duk sun kunbura ta sauya kamar ba ita ba bgs na zaune gefen ta ya zuba musu ido yana jin tausayin su na ratsa shi Aunty farida na gefen bgs tasamu lfy sumul sumul abun ta. Su Khalid kuwa suna wajen ansan gaisuwar rasuwar Aunty Amarya

A hankali Aryan ya waro idon sa waje tare da ɗaga hannun sa ɗaya ya ɗaura bayan diyana dake kwance kusa da shi ta bashi baya tana kuka l. kasa kasa da murya kamar mai raɗa yace "my jidda me ya sanya kike kuka? Ko so kike ki ƙaramin ciwo kan ciwo ne? kin san fa kukan ki ciwo ne agareni a yanzu bayan Abba bgs Aunty farida ke kaɗai nake kallo naji daɗi a raina ki dai na kukan nan haka ya isa, ji nake kamar kina chakamin mashi a zuciya ta idan kina kuka" a sukwane diyana ta juyo cikin shessheka tace "yaya Aryan dole zan yi kuka ba kai ne ka... Bata karisa maganar ba ya rufe mata baki da hannun sa tare da jawo ta jikin sa yana ɗan bubbuga bayan ta sai lokacin idon da ya sauka kan bgs da Aunty farida,yana kokarin yi musu magana bgs yayi saurin ɗaga masa hannu alamar yayi shiru dawo da kallon sa kan diyana yayi cikin zolaya yace "my jidda ba kince baki so na ba me kuma ya saki kuka dan zan mutu?" "Yaya Aryan ka dai na faɗin haka wlh bazaka mutu yanzu ba kuma Ni bance bana son ka ba ina son ka mijina ina son ka sosai" "eyeee babyn yaya Aryan yau ta dai na jin kunya har da cemin miji da ina da lfy danayi sujudur shukur na godewa Allah" miƙewa bgs da Aunty farida sukayi suka bar ɗakin dan sunga Aryan da diyana sun fara sakin layi.
Rungume ta sosai Aryan yayi yana rarrashin ta ita kuwa sai zuba masa shagwaɓa da kalaman love take "my jidda waya koya miki kalaman soyayya" ya tambaya yana gyara mata kwanciya ɓoye fuskar ta tayi a girjin sa kafin tace "a littfin Romeo na Princess Teema na koya" shafa gashin kanta ya fara yi yana faɗin "wayace ki rinƙa karanta Novel?" "Yaya Aryan ina karanta Novel ne dan na koyi yadda zan rike ka" waro ido waje yayi tare da sakin ta yana kokarin mikewa zaune,da gudu ta mike ta bar ɗakin,bin bayan ta da kallon yayi har ta fice murmushi ya saki kafin yace "Nagode wa Allah daya nunamin ranar nan da jidda ta ta sauya har da zubamin kalaman soyayya" ya kai karshen maganar tare sa zuro kafar sa kasa ya mike da kyar yana taga taga har ya fice daga ɗakin ya nufi wajen Abba.

Yau ne Abba ya kira meeting na karshen akan issue marigayya Aunty Amarya, gaba ɗaya family sun taru a palon.
Abba cikin nitsuwa Abba ya fara magana "Aryan na san baka sani ba Allah ya yiwa mahaifiyar ku rasuwa tun shekaran jiya ina fatan kuma zaku yafe mata abun da ta aikata muku? Ni dai har ga Allah na yafe mata haka Aisha da Hauwa'u suma sun yafe mata kuma zan zo naji kun faɗa da bakin ku kun yafe mata sanna ku cigaba da neman mata gafara wajen Allah" a tare suka amsa da "Allah ya yafe mu tare Abba mun yafe mata" ajiyar zuciya Abba ya sauke kafin ya cigaba da cewa "to sai batu akan mulki munyi magana da Aliyu zai dawo Nigeria next week ya ansa mulkin sanna na sanya antona asirin da Hajara ta binne a kan mulkin nan,gaba ɗayan ina mai sallamar ku akan ku koma bakin aikin ku tun da komai ya dai dai tun" "no Abba komai bai dai dai tu ba dole na kama wanda ya sanya aka kama su Khalid" cewar bgs jinjina kai Abba yayi kafin yace "haka ne to Allah ya bada Sa'a akoi wani mai magana!? Shiru palon yayi Aryan ya sunkuyar da kai kasa yana mai takaicin rasuwar da Aunty Amarya tayi ba tare da ta nemi yafiyar mutanen da ta cutar a rayuwa ba.

"Abba ina da magana" cewar hiyana nan take kallon ya dawo kanta "to hiyana ina jin ki menene maganar taki faɗi" sunkuyar da kanta kasa tayi cikin jin kunya ta fara magana "Abba kasa yaya Prince ya sake ni bana son shi bana son zama da shi mugune" a sukwane bgs ya ɗago yana kallon ta gaba ɗaya su Khalid kara waro ido waje sukayi suna kallon ta Abba da Ammi ba karamin girgiza da jin maganar nata sukayi ba daurewa Abba yayi yace "lfy hiyana kike son yayan ki ya sake ki!? "Abba ba lfy ba yaya prince ya cutar da ni arayuwa ta sosai nayi hakuri har nagaji bazan iya ba wlh Abba yaya Prince yana gab da kashe idan kuka sake bari na da shi" nan hiyana ta shiga basu lbr duk abun da ya faru na muguntar da bgs ya rinƙa yi mata daga farko har karshe.

Tirkashi nan take ainihin ɓacin rai da tashin hankali ya bayyana karara a kan fuskar Abba da Ammi cikin fushi Abba yace "tabbas babu makawa Safras zai sake ki yanzu kuwa ba sai anjima ba" waro ido waje bgs yayi tare da sunkuyar da kansa saka kamar mai tunani wani abu "Auta ku tashi ku je ɗaki bari muyi magana" cewar Aunty farida mikewa Zahra hiyana diyana amrat lamrat sukayi suka bar palon,kallon Omar da Haidar Aryan yayi tun bai yi magana ba suka mike da sauri suka fice.

"Safras ina mai umartan ka da ka rubuta takardan sakin hiyana ka kawomin yanzun nan" cewar Abba Aunty farida na kokarin yin magana Abba ya dakatar da ita yana faɗin "kar wanda ya samin baki a maganar nan dole ya sake ta ashe Safras zaka iya kashe yar uwar ka dan kiyayya kajefota daga sama ta faɗa cikin ruwa sanna duk bai isheka ba sai ka harɓeta da bindiga? To wlh ka rubuta sakin ta yanzun nan ka bani a nan na aura mata wanda take so" mikewa bgs yayi ya nufi hanyar fita yana faɗin "bari na kawo maka Abba" mutuwar zaune su Aryan su kayi lallai bgs wato ma bai damu ba bari ya kawo akar dan sakin tab


To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu




💋 Duk Karfin Izzata 💋


💋The talent troupe writer's 💋



By Star Lady

Page 41



Yana fita part nashi ya wuce. Yana shiga bedroom ya wuce toilet wanka yayi a gurguje ya shirya cikin wando 3 cutar baki mai laushi ya sanya farin singlet fari tas ya gyara gashin kansa ya tara ya ɗaure sanna ya feshe jikin sa da perfume mai daɗin kamshi ya haye gado ya kwanta tare sa jawo blanket zuwa kirjin sa ya lumshe ido hankali kwance barci mai daɗi yayi awon gaba da shi.

Almost 1h su Abba na zaune suna jiran sa babu bgs babu labarin sa,Abba na kokarin yin magana Aunty farida ta mike tana faɗin "bari na dubosa" bata tsaya jiran amsar Abba ba ta wuce da sauri dan tasan Abba zai iya hanata zuwa kuma tana son yin magana da Bgs.

da sallama ɗauke a bakin ta ta shigo bedroom na shi yana kwance abun sa hankalin a kwance ba karamin mamaki Aunty farida ta sha ba ganin sa cikin kwanciyar hankali yana zuba barci
saboda mamaki da kyar ta iya karisawa bakin gadon ita atunanin ta zatazo ta samesa cikin damuwa ashe ashe shi barcin sama yake itace ta damu kan ta. Hannu ta sanya ta taɓa shi tana kiran sunan sa "Prince!! Prince!!" da kyar ya iya waro idon sa waje guntun tsaki yaja tare da kawar da kansa gefe yana faɗin "menene!? Mamaki ne ya kara bayyana akan face nata "lallai Prince kabar iyayen mu zaune suna jiran ka kazo kayi kwanciyar ka" "to Aunty farida me kikeson nayi saboda Allah dai" shiru Aunty farida ta ɗan yi kafin tace "kaje ka kai musu takarda sakin hiyana mana" a sukwane ya ɗago manya manyan idon sa nan tare da kara zaro su waje ba karamin tsorata Aunty farida tayi ba ganin yadda ya zaro ido,"saki fa Aunty farida kika ce!? gyaɗa masa kai tayi alamar eh saki, girgiza mata kai yayi kafin yace "never wlh" "ban gane never ba ba kai kace baka son taba? Tun da baka son ta sai ka sake ta ai" tsaki yaja kafin yace "koda bana son ta ba zan sake taba dan yanzu ina jin daɗin zama da ita ta iya duk wani abun dana ke bukata" ita kam Aunty farida ta rasa bakin magana shiru ta ɗan yi mamakin bgs ya fara yi mata yawa "kasan me Prince? Wlh yadda Abba ya ɓata rai yau idan kaga baka saki hiyana ba to tabbas mutuwa Abba yayi" shiru ya ɗan yi kafin yace "Aunty farida ya zan yi ni gaskiya ba zan iya rabuwa da ita ba" "kana son tane? Juyowa yayi da kyau ya kalli Aunty farida yace "aa ni bana son ta amma dai zan zauna da ita" "yau naga ikon Allah Prince wani irin rashin adalcine wanna baka son ta kuma kace bazaka rabu da ita ta Auri wanda take so ba wanna ai zalunci ne" "Aunty farida ki dai na zancen ta Auri wani rai na yana ɓaci sosai" kara waro ido waje Aunty farida tayi kafin tace "Prince anya kasan me kake yi kuwa? To wlh nima zan dai na bin bayan ka ka tashi ka rubutawa hiyana sakin ta ka kaiwa Abba tun wuri ya za'ayi nazo ina son mu shawo kan matsala kuma kana neman ka ɓata min rai" kwanto da kansa yayi kan cinyar Aunty farida cikin sanyayyar murya ya fara magana "Aunty farida izuwa yanzu nasan kin san ina son sister amma ban san me ya sanya kike neman wahalar da ni ba me yasa kike son kara min zafi kan zafi ba zan iya rabuwa da sister ba ina kaunar matata" shafa gashin kansa ta fara yi tana faɗin "ban san ka fara son hiyana ba hasashe nake shiyasa nake tambayar dan na tabbatar amma idan da gaske kake son hiyana a matsayin mata me ya sa ka harbeta da bindiga?" Mikewa tayi zaune kafin ya fara magana "Aunty farida awanna gaban bani da zaɓi ne dole na harbeta" "ban gane ba kamin bayani" "Aunty farida bindiga suka sa mata a kai sukace idan nayi wani motsi zasu harbeta kuma tabbas zasu harbetan domin daman dan su kashe ta suka kamata alokacin bani da zaɓin data wuce ni da kai na na harbeta idan ban harbeta ba su zasu harbeta kuma a kai zasu harbeta kinga idan ko suka harbeta a kai ba makawa mutuwa zatayi,shiya sa ni na harɓeta a in da na san bazata mutuba,kinga,zasuyi tunanin ban damu da ita ba bazasu damu wajen duba ta mutu ko bata mutuba abu na gaba idan ban harbeta ba zata zamomin barazana wajen hanani kashe su dan zan zamo ina faɗa da su kuma ina tunanin ta kar wani ya cutar da ita zata rabamin hankali gida biyu zata iya jawowa ayi nasara a kai na abu na uku ita kan ta zata tsorata da ganin faɗan dana ke da su kin sani tana da matsala a kai tun bugun da Maryam ta mata duk da cewa abun ya ragu amma har yanzu da saura to idan ban harbeta ba wlh ƙwaƙwalwan ta zai iya samun damuwa dan bata da taurin zuciyar da zata tsaya tana ganin ana kisa a gaban ta abu na huɗu....cikin sauri Aunty farida ta rufe masa baki tana faɗin "dalili na farko ma ya gamsar dani lallai awanna lokacin bakada zaɓi dole ne ka harbi hiyana yanzu muje kayi mata bayayi ka faɗa mata kana son ta hiyana macece mai tausayi da hankali zata fahimce ka" girgiza kai yayi yana faɗin "No Aunty farida awan nan karon bazata saurare ni ba duk abun da zan faɗa mata zata ga kamar still wasa zanyi da hankalin ta" "me yasa kace haka? "Good question last 2 weeks kafin muzo nan na nuna ina son ta kuma lokacin har ga Allah ina kaunar ta amma ina jiye mata tsoron zama da nine shi ya sanya nake kokarin cireta a rai na,bayan mun dawo nan akoi wata rana da Aryan yazo ya tunzurani akan ta ya sa nace bana son ta kuma taji duk abun da nace tana tsaye a bakin kofar shigowa ɗakin taɓata rai sosai tayi kukan da nida kai na sai da nayi dana sanin faɗin hakan danayi akanta,Aryan ya bita ya bata hakuri ita ɗin macece mai hakuri data dawo ɗakin nan bata nunamin komai ba amma acikin kwayar idon ta naga tsananin tsanata da jin haushi na alokacin nayi ƙoƙarin sake jan ta ajiki na dan na goge wanna haushin da tsanata da ta fara amma ban kai ga yin nasara ba aka sace su kuma ga rashin lafiyar ki to kinji yanzu bazata taɓa yarda dani ba nasan da hakan nariga nayi kuskure tun farko" jijjina kai Aunty farida tayi kafin tace "eh kayi kuskure gaskiya kayi wasa da zuciyar ta sosai duk da haka nasan har yanzu da sauran son ka a zuciyar ta tukun nan ma yaushe ka fara son ta?" kawar da kan sa gefe yayi kafin yace "wlh sharrin Cameran ɗaki na ne ya fara samin son ta kullun idan ina zaune a office ba abun da nake sai in kunna cameran gidan in yi ta kallon Aikin alkharin da take min wani lokaci in ganta tana gyara gado wani lokaci tana wanke toilet wani lokaci tana wanka gasu nan dai abubuwa kala kala na alkhari take min har abun ya dawo min kamar Tv ba ran da zanje office ban zauna nayi ta kallon abun da take ba wani lokaci idan tayi wani shirmen sai tasani murmushi sau da dama idan rai na ya ɓaci Cameran ɗaki kawai nake kunnawa idan na fara ganin shirmen da take sai na ji na watsake ina son sauraron karatun Qur'ani idan tanayi saboda ta iya rera kiraa sosai a haka ta fara sauyamin zuciyata sai kuma dana zo naga abun alkharin da tayiwa Ahmad alokacin naji daɗi sosai ji nayi kamar na rungumeta na faɗa mata ina kaunar ta sai kuma na fasa lokacin ne na kara tabbatar wa kai na tana da zuciya mai kyau" tun da ya fara magana Aunty farida ta zuba masa ido har sai daya kai karshen ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya "eh lallai Prince ka faɗa soyayya dumu dumu idan ba soyayya ba yaushe zaka tsaya kana yiwa mutun wanna dogon bayani kai da cewa yes ma wahala yake ma kafin ka faɗa sai ka ɗauki yan mintoci tab dole mu san abun yi" kawar da kansa gefe yayi ya ɗaure fuska yana kokarin yin magana wayar Aunty farida tayi kara tana dubawa taga sakon Aryan ne "Abba yace bgs ya same sa a bedroom nashi yanzu nan bai yarda ya kara 2mins bai zoba nakira layin sa bai ɗaga ba na masa tex ba reply" abun da sakon Aryan ya kunsa kenan mikawa bgs wayar tayi ya ansa ya karanta sakon sanna ya mike ya nufi hanyar fita,da sauri itama ta mike tabi bayan sa.

Zaune a bakin gadon Abba suka isko Ammi Abba kuwa yana tsaye kallon ɗaya zaka musu kaga matsanancin ɓacin rai da tashin hankali a tattare da su. Saman sofa dake cikin ɗakin bgs da Aunty farida suka zauna cikin ɓacin rai Abba yace "ka bani kunya Safras ban taɓa zaton zan maka umarni akan abu kuma kaki bi ba ai koma ban maka umarni ba marainiyar Allah bata da kowa sai mu ka sata agaba ka rinƙa azabtar da ita gaskiya baka yiwa kanka adalci ba kuma ka cutar da zuciya ta yanzu duk bama wanna ba ka rubuta min takardan ta kamar yadda ta bukata ka bani" kasa kasa yace "Abba ni ba zan iya sakin taba gaskiya" a fusace Ammi tace "what!!? Wlh baka isaba sai ka sake ta" "Ammi kiyi hakuri amma ni bazan iya sakin matata ba ina son zama da ita" "kana son zama da ita ko dai kana son karasa kashe ta wlh tun ranka bai ɓaci ba ka sake ta na faɗa ma" Aunty farida na girgiza masa kai tana ƙoƙarin dannar sa amma ina zuciya ta kwashe sa cikin fushi ya mike yace "ni bazan saki matata ba!!" "ina magana kana cemin bazaka sake taba!?" "Koma me zakuce kuce ni dai ba zan sake taba ba kuma wanda ya isa yasani na sake ta" Ammi na kokarin sake yin magana Abba ya dakatar da ita dan ya lura bgs fa baya cikin hayyacin sa bai san me yake faɗe ba idan Ammi ta biye masa za'a iyayin kwaɓaɓiya dan a hankalin da yake cikin nan duk abun da yazo bakin sa faɗe zai yi,alama Abba yayi wa Aunty farida akan ta lallaɓa bgs su tafi ɗaki. Mikewa tayi tace "Prince muje ko" cikin fushi yace "Aunty farida wlh ba zan saki sister ba ba wanda ya isa ya rabani da matata dan haka ki kyaleni wlh yau....bai kai karshen maganar ba ya dakata sakamakon ɗaga hannu da Aunty farida tayi a fusace zata maresa tsare ta yayi da ido ta kasa karisa kai hannun ta kan face nashi jikin ta har rawa yake saboda ɓarin ran abun da bgs ke kokarin yiwa iyayen su,cikin tsawa yace "me yasa kika dakata ki karisa mana!! Ki mareni nace!!!ki mareni mana!!" kasa Aunty farida tayi da hannun ta tana danasanin ɗaga hannun da tayi zata maresa yanzu gashi ta sake kwaɓe abun suda suke neman sulhu yanzu ta kwaɓe komai,a zuciye bgs ya juya ya fice daga ɗakin sai huci yake cikin ransa yana faɗin "akan mace yau Aunty farida take kokarin marina?no hakan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login