Showing 225001 words to 228000 words out of 243403 words
hawaye daga idon sa "No Aryan yanzu ba lokacin kuka bane lokacin murna ne" cewar bgs matsowa su Yusuf ma su kayi suka fara rarrashi sa.
After some minutes Aryan ya yi shiru yana kallon su ya yin da suma shi suke kallo "Bgs wanene Major?" Cewar Khalid kallon Aryan bgs ya yi kafin yace "Na rufe babin Major bana son a sake buɗe sa" kakalo murmushi dole Aryan ya yi kafin yace "Ita dai gaskiya ko bamu bayyana ta ba zata bayyana kan ta Khalid zan faɗa muku wanene Major, Major ɗan uwana ne ɗan yayan Aunty Amarya mijin Aunty maryam yarima mai jiran gado nasan kun san shi dan baku ga face na shi bane yasa kuke tambaya munyi aiki da Major a baya na tsawon shekaru a lokacin yana gaba da mu awajen aiki ogan mu ne sau uku bgs yana kama shi akan hada hada da miyahun kwayoyi yana safarar manya manyan makaman da gomnatin ke shigowa da sojiji da su yana sacewa ya sayar wa ya ta'adda a ɓoye Major yana aiki da manya manyan criminals ba tare da sanin hukumar soja ba, bgs kuma yana yafe masa ne saboda yana ganin ɗan uwana ne karo na uku da bgs ya kama Major a Maiduguri ne lokacin mun je Nigeria ya kama Major yana sayar wa da yan ta'adda makaman sojojin Nigeria daga nan bgs ya masa video dan samun shaida ya gurfanar da Major gaban manyan mu a lokacin a matsayin Major na babban soja sai aka koresa daga wajen aiki tare da rufe sa na tsawon wata uku a gidan yari amma fa bai yi ko wata ɗaya ba aka sake sa bgs bai sake bi ta kan sa ba kasan cewar sa na ɗan yayan Aunty Amarya mun rufe babin sa mun manta da shi ashe shi bai manta ba yana bibiyar rayuwar mu har ni da na kasance ɗan uwan sa ma bai kyale ni ba bayan Major ya fito daga gidan yari ya bar kasar nan ya koma Nigeria in da ya koma ya sanar da su Aunty Maryam wai ya ajiye aikin soja baya bukata a lokacin Aunty Maryam ta kirani ta sanar min sai na nuna mata kamar ban san komai ba tun da shima bai nuna mata wani abu ba sai nace mata ta kyale sa mana shi da ra'ayin sa yayi abun da yake so tun daga lokacin ban sake jin zancen Major bama mum samu karin girma abubuwa da dama sun faru dama mu bamu taɓa zuwa gidan Aunty Maryam ba bare muce wata rana in munje zamu haɗu da shi in ta kai ce muku wanna shine Major mijin Aunty Maryam sarkin da ake kokarin na ɗawa a Gombe yanzu" ya kai karshen maganar tare da miƙawa zaune bgs na kokarin yin magana wayar sa ta fara kara yana dubawa yaga Shahram ne a hankali yayi picking call ɗin tare da sanya wayar a hand-free yana faɗin "Hello" daga ɗayan ɓangaren Shahram yace "Sir yanzu anwar ya kirani daga office Major ya mutu a ɗaure tun jiya" kallon Aryan bgs ya yi kafin yace "Gani nan zuwa" yana faɗin haka ya katse kiran "Alhadulillah an rage mugun iri" cewar Aryan yayi maganar tare da miƙe wa tsaye ya nufi kofar fita yana ɗan tangal tangal saboda yinwa da yake ji kwana biyu ba abinci yana tafiya yana faɗin "Bari na duba my Jidda" bin sa da kallo suka yi har ya fita sanna bgs ya dawo da kallon sa kan Yusuf yace "Yusuf kaje kasa a shirya gawar Major a turata Nigeria saboda Aunty Maryam sanna karka yi abun da zai sa su Aunty Maryam su fahimci abun da ya faru a barshi akan mutuwa Major yayi ku masa sutura daga nan ta yadda da anje za'a kai shi makwancin sa abu na karshe daga nan a kashe zancen Major na rufe babin sa" ya kai karshen maganar yana kokarin juyawa ya bar ɗakin cikin sauri Yusuf yace "Bgs ya batun wancan matar kuma?" "Wace mata fa" bgs ya tambaya yana juyowa ya kalli Yusuf ɗin "Matar da ta kashe baban su My Baby dan jiya my baby ta sanar da ni abun da ke faruwa tace min kace a bar matar sai kazo Nigeria ka mata hukunci me abun yi a kan ta tun da naga zuwa Nigerian ka dai ba yanzu ba" "Kasa a kashe ta, ta hanyar rataya" yana kai karshen maganar ta juya ya fice daga ɗakin da sauri Yusuf ma ya fice daga ɗakin dan yaje ya aiwatar da aikin da bgs ya sa shi jiki ba kwari Khalid da Fahad suka fito daga ɗakin kowa ya nufi part na shi
Sudan
A yan kwana biyu da su Abba suka yi sun saba da mutanen Sudan yanzu sun haɗe sun zama jini ɗaya tamkar sunyi shekaru a tare sai murna suke yau ta kama ranar Jummaa misalin karfe 8 na safe gaba ɗaya family sarki Abdullah sun haɗu a palo sa dan yau su Abba zasu koma ana sallamar juna ji suke kamar karsu rabu gashi a nan su Abba zasu baro Hajj Fateema amma Abba yace idan tayi musu koda 1 month ne sai ta dawo Nigeria ba yadda Abbo ya iya ba zai iya cewa Abba a'a ba sai ya hakura ya yarda akan idan Hajj Fateema tayi wata ɗaya sai ta koma Nigeria suna yar hira da sallama da juna Uncle Aliyu ya shigo da sallama ɗauke a bakin sa amsa masa sallamar suka yi su Abbo suna ta kallon shi dan basu gane shi ba Abba ne yace "Wato Aliyu sai yau kayi niyar zuwa ko?" Karisowa cikin palon uncle Aliyu yayi sai tashin kamshin daddaɗar turare yake yana sanye cikin wata dakakkiyar shadda fara tas mai bala'i kyau da tsada ya sanya hula da takalma bakake idan ka ganshi sai ka rantse bai wuce ɗan 25 years ba. Kusa da Abba yaje ya zauna yana faɗin "Kayi hakuri yaya wallahi abubuwa ne suka min yawa da naso zuwa tun jiya to amma tun da g....bai kai karshen maganar ba idon sa ya sauka kan Hajj Fateema cikin sauri ya miƙe tsaye yana faɗin "Kece a nan kuma?" Kallon sa Hajj Fateema tayi kafin a ruɗe tace.....✍️✍️✍️✍️
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu
💋Duk Karfin izzata 💋
By
Star Lady
Page 62
....."Me ya kawo ka gidan mu kuma?" Kallon su Abba ya yi kafin yace "Yaya ina ka san wan nan matar?" "Meke faruwa ne ku mana bayani mana" cewar yaya Abdussalam sarkin zuciya "Aliyu meke faruwa ai na kasan Fateem?" Cewar Abba ƙasa uncle Aliyu yayi da kai kafin ya fara magana "A saudiya na santa tun ranar da na fara ganin ta na kamu da son ta na bita amma sai tace min tana da Aure na ɗauka karya kawai take min bata son yimin magana ne hakan yasa nayi ta bibiyar ta ina ta kura mata har daga karshe dai na gane da gaske tana da Aure lokacin da nake bibiyar ta tayi ta zagina da faɗa min maganganu marasa daɗi dan kare mutuncin Auren ta ni kuma naki dai na binta har sai dana tabbatar da gaske tana da aure naji ciwo a rai na sosai maganar dana ke muku wajen shakara 6 baya kenan Fateema itace mace ta farko dana fara so arayuwa ta na bita, tun da na gane tana da aure shike nan ban sake jin son wata a rai na ba shi yasa kuke ta min zancen Aure na share ku dan ni a rai na ita kaɗai nake so ita kaɗai ne a rai na shiyasa na ki yin Aure na cigaba da zama na kawai" ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya nufi waje yana faɗin "Yaya muje ni bana son ganin Fateema dan matar aure ce ni kuma zuciya ta har gobe akoi son ta a ciki bana son ganin matar wani" ya kai karshen maganar tare da ficewa ya bar palon kallon Abbo Abba ya yi yace "To Abbo munzo da kokon bara a baku Auren Fateema amma karku sanar da shi sai ta gama takaba zamuzo a ɗaura aure ba tare da ya sani ba bazata zan masa dan shekara da shekaru ina matsa masa yayi aure yaki sai yanzu Allah ya ƙaddara" murmushi Abbo yayi yana faɗin "Na bashi Auren Amina har abada Allah ya kai mu lokacin" da fara'a Ammi ta amsa zancen da cewa "To sai a bar ta ta gama takabar ta a nan sai munzo biki kawai sai mu tafi da ita yanzu ba zancen yin wata ɗaya ta dawo ta zauna da yan uwan ta sai munzo ɗaurin Aure sai mu wuce da ita kawai bayan an ɗaura" kasa Hajj Fateema tayi da kan ta miƙewa Abba yayi yana faɗin "Muje kar muyi tafiyar dare". Har wajen motocin da zasu kai su Abba airport su Abbo suka rakasu suna sumu sallama tare da tunatar da Abba akan kar su manta batun turo su Hiyana da mazajen su da fara'a Abba ya amsa da In Sha Allah ba zasu manta ba zasu zo ba jimawa. Da haka sukayi sallama su Abba suka shiga mota suka wuce Airport daga nan suka hau jirgin da ya kawo su suka koma Naija cike da tsarabar Sudan sai murna suke.
Nigeria
Suna dira Nigeria suka samu mummunar labarin mutuwar mijin Aunty Maryam wato Major haka washe gari suka shirya suka wuce Gombe dan zuwa gaisuwa. Kwanan su uku a Gombe suka juyo tare da Aunty Maryam dan ta dawo gida tayi takaba.
A ɓangaren Inna kuwa su Abba basa nan Yusuf yasa aka rataye ta bayan dawowar su Abba ne suka samu labari Abba da kansa ya ansa ɗan da ta haifa ya miƙa wa Ummi yace ta rike sa da amana da murna ta ansa ɗan aka fara bashi madara yaron kyakkyawa da shi kamannin sa ɗaya da bappan su yaya Bello yana cike bulbul abun sa Ummi bata da matsala ta amsa ɗan ta san cewa laifin wani baya shafan wani Abba ya hana a faɗa wa su Diyana ɗan inna ne dan yasan idan suka sani yaron ba zai taɓa tashi cikin jin daɗi ba dan haka sai ya sanar da su akan ɗan Inna ya rasu ya bawa Ummi akan idan sun zo sun tambayi ɗan waye Ummi tace musu daga Katsina ta ɗauko shi da haka Abba ya rufe maganar.
After 2 days Aliyu Haidar takwarar uncle Aliyu wato Haidar ɗin Ammi ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa saudiya sai murna yake sun dai dai ta da Fariza sai murna yake sosai ya dawo tare da Hindu mai aikin Hajj Fateema suna shiga gida kai tsaye palon Abba ya wuce da Hindu nan ya samu su Abba gaba ɗaya suna zaune suna tattaunawa akan bikin Ahmad da Omar dan tare za'a haɗa da sallama ɗauke a bakin sa ya shigo palon nan idon gaba ɗaya jama'ar palon ya dawo kan sa wuce wa ya yi kusa da uncle Aliyu wato takwarar sa dake zaune kusa da Abba ya zauna yana faɗin "Wayyo na gaji" Abba na kokarin yin magana Aisha da Sadiq suka miƙe a tare suna faɗin "Mama" sunyi maganar suna kallon Hindu mai aikin Hajj Fateema kallon Hindu Abba yayi kafin ya dawo da kallon sa kan su Sadiq kallon su Hindu take ta kasa magana mamaki ya kama gaba ɗaya jama'ar palon sun kasa magana Ammi ce tayi ta maza tace "Aisha maman kuce?" Da sauri Aisha tace "Eh Ammi itace maman mu ina da hoton ta tun bamu girma sosai ba ta tafi aiki a saudiya ta barmu bata kara dawowa ba" ta kai karshen maganar tare da sakin kuka mai tsuma rai alama Ammi ta mata da hannu akan tazo da sauri ta tafi ta faɗa jikin Ammi tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, sosai Ammi ke rarrashe, shi kan Sadiq ya kasa magana zubewa kasa Hindu tayi tare da sakin kuka tana faɗin "Wallahi na san ban kyau ta muku ba akan neman duniya nayi watsi da ƴaƴana ku yafe min" jinjina kai Abba yayi kafin yace "Eh gaskiya kam Hindu baki kyau ta ba ko kaɗan in da hanyar kyau tawa ma yabi baki bishi ba har da ƴa mace kika watsar kika tafi dama dai mazane dukkan su biyu to da da ɗan sauki kin san haɗarin da mace take da shi kuwa? Har alkawari Allah ya yiwa wadda ya samu ya mace Ubangiji yace duk wanda ya haifi ƴa'ƴa mata uku ya basu tarbiya har ya aurar da su basu taɓa zina ba ya wa wanna mutumin alkawarin gidan aljanna ƴa mace ce ke kai iyayen ta wuta farat ɗaya haka kuma ita ke iya zama sanadiyyar shiga aljanna iyayen ta farat ɗaya ƴaƴa mata ba abun wasa bane abun a sa musu ido da basu kulawa ne kamar yarda manzon Allah (SAW) yace mata na sa rauni hakane dayawa daga cikin mutane idan akace musu mata na da rauni suna ɗukan abun, kamar mace bata da karfi ko bazata iya yin abun da na miji yayi ba, to ba haka annabi yake nufi ba abun da annabi yake nufi da raunin mace zuciyar su mata suna da abubuwa biyu zuwa uku a zuciyar su wadda shi annabi ke nufi da raunin mace, abu na farko mace na da kawa zuci abun da ake cewa kawa zuci ya kunshi tausayi san yan uwan ta, mace ba zata iya tafiya waje tayi sati tana lafiya ba tare da ta nemi gida taji halin da suke ciki ba saɓanin ɗa namiji wadda zai iya tafiya yayi shekara ba tare da ya tambayi ina kanin sa wane aa ina wane amma mace tana kiran gida sai ta lissafo ɗaya bayan ɗaya ta tambaya suna ran ta a ko da yaushe mace ce tana da tausayi fiye da namiji dan shi namiji yana da dakakkiyar zuciyar da ko abu ya bashi tausani zai iya jurewa ya hakura ya cire abun ya watsar saɓanin ita mace da duk yadda ka kai da yi mata abun da ba daɗi idan abun rashin daɗi ya same ka sai ta tausaya maka barina ɗauki misali da su Diyana yanzu haka duk abun da Habiba ta musu nan muddin aka ce musu Allah sarkin yaron nan bai da kowa zai taso cikin wahala da rashin jin daɗi wallahi da wuya na gama rufe baki basu yi rige rigen cewa zasu ansa yaron ba duk wani abun da mahaifiyar yaron ta musu zasu mance da shi wanna shine kalan raunin da annabi ke nufi bawai mace ba zata iya yin wani aiki da namiji yayi da sauran su ba yanzu zaka iya sarrafa zuciyar mace ko mai girman ta kuwa abu kaɗan zaka mata ta sauya daga yadda take shakara da shekaru wanan ɗaya ne daga cikin babban haɗarin barin yar ki mace ki tafi neman wani abu wai shi kuɗin, abun da a duniya zaki bar shi ki sani ƴaƴan nan da kike gani kamar ke kike da hakki a kan su to suma suna da hakki a kan ki kuma ki sani ɗaya bayan ɗaya sai Allah ya tambaye ki ya kika kula da su a ranar da baki baya karya dole ki faɗi duk wani abu da kika musu tarbiyyar su da sauran su, wan nan babban kuskure ne ya kamata ku gyara ku ja ƴaƴan ku mata ajiki ku zama tamkar kawayen su kuyi wasa da dariya da su ta yadda zaku saba ya zamto bata ɓoye miki komai nata a matsayin ki na mahaifiyar ta karki wani nuna kamar kin haifeta kin girme mata aa ki jata a jiki ku zama kawaye dan duniyar yanzu ta wuce tunanin mai tunanin ba dan Allah ya tsare yaran nan da karinyar sa ba kina tunanin a zaman nin nan zaki dawo ki same su ne? To ya kamata wan nan ya zama izini gare ku mata Allah ya kyau ta" Abba na yin shiru Ammi da Ummi suka ansa sai da suka wa Hindu faɗa mai ratsa zuciya sanna Ammi ta umarci Aisha da ta rakata ɗakin su taje tayi wanka ta huta wucewa Aisha tayi tana kuka ta fita jiki ba kwari Hindu ta bi bayan ta tana mai danasanin abun da ta aikata sai kasa take da kai dan kunyar ƴaran nata take kallon su Ammi Abba yayi kafin yace "Kuje zamu karasa maganar bikin da daddare" yana kai karshen maganar ya mike ya wuce bedroom na shi da haka su Ammi suka fice kowa ya koma part na shi uncle Aliyu ma ya wuce part na shi.
After 4 month
Us
Tsaye suke Yusuf Aryan Fahad Khalid a bakin labour room da Lamrat ke ciki tana nakuda sai safa da mar wa Yusuf yake yana ta faman haɗa zufa shiru su Khalid suka tsaya suna addu'ar Allah ya sauke ta lafiya dai dai lokacin bgs ya iso shida Hiyana dake ta masa kuka sai ya kawota taga Lamrat shi ne ya bar wajen aiki dole yaje gida ya ɗauko ta ya kawota kallon Aryan yayi yana faɗin "Ta haihune?" Girgiza kai Aryan ya yi yana faɗin "A'a tun da suka shiga da ita likitocin basu fito ba" "Ok ni zan koma kome yake ciki ka sanar da ni awaya ga Eshat nan" ya kai karshen maganar tare da dafa kafaɗar Yusuf dage zagaye wajen yana faɗin "Addu'a zaka nitsu ka mata ba zagaye ba" ɗago idon sa da suka rikiɗe suka yi jaa Yusuf yayi yana kokarin yin magana Dr ta fito hannun ta rike da baby boy tana ta murmushi da sauri Hiyana ta tari Dr tana murmushi tasa hannu da nufi ta ansa