Showing 147001 words to 150000 words out of 243403 words

Chapter 50 - DUK KARFIN IZZATA BOOK 2 COMPLETE

02 Feb 2025

46737

ma ba zai yiwu ba dole na ɗau mataki.

cikin sauri Aunty farida tace "bari na bi bayan sa dan kar yaje yayi wani abun" shiru Abba da Ammi sukayi Abba na nadamar tursasawa bgs akan ya saki hiyana da sukayi gashi sun kara kwaɓe abun bgs bai taɓa ɗaga murya yafi na su ba yana musu biyayya iya iyawar sa koda baya son abu idan suka ce suna so yana hakura ya musu amma yau da bakin sa yake mayar musu magana dan sunce ya saki hiyana lallai bgs na kaunar hiyana da gaske dolene musan abun yi a ɓangaren Ammi kuwa tunani take "idan muka bar yaron nan bai saki yarinyar nan ba mun yi son kai mun cuceta itama yace mai yanci kamar kowa kai ai yazama dolema ya sake ta in ba haka ba ba zan yafewa kai na ba na cutar da marainiyar Allah" shiru sukayi kowa yana ta tunani a ransa ba wanda ya iya ce da ɗan uwan sa uppan.

A ɓangaren bgs kuwa yana fita Part nashi ya nufa cikin ɓarin rai ya ɗauko takar da da biro daga cikin drawer mirror ya zauna a bakin gado ya ɗan yi rubutu mai ɗan tsawon layi biyu sanna ya yage pepar ya naɗe ya miƙe ya nufi hanyar fita yana kokarin fita Aunty farida na shigowa ko kallon in da take bai yi ba ya wuce abun sa,da sauri ta juya tabi bayan sa.

Kai tsaye part ɗin Ammi ya nufa yana taku irin na jaruman maza kallo ɗaya zaka masa kagane yana cikin tashin hankali da matsanancin ɓacin rai,
Palon Ammi babu kowa kai tsaye ɗakin su Zahra ya nufa,suna zaune saman gado suna ganin sa suka mike cikin tsoro Zahra ta sauko gadon ta raɓa gefen sa ta fice daga ɗakin da sauri amrat da lamrat suka bi bayan ta,ganin su Zahra sun fita ne ya sanya Aisha da Zainab suka bi bayan su
diyana na zaune ko a jikin ta ko kallon in da yaka bata yi ba ta dukufa kan wayar Aryan tana buga game,kallo ɗaya hiyana ta masa ta kau da kai amma ta tsorata ai nun da ganin yanayin da yake ciki wani mugun haushin sa ne ya kara karuwa a zuchiyar ta.

Takowa yayi zuwa bakin gadon nasu cikin tsawa yace "gashi!!" Kallon takardan da ya rike hiyana tayi kafin tace "menene?" A fusace ya wanke mata fuska da wawan mari hakan yayi dai dai da shigowar Aunty farida cikin tsawa yace "ni zaki cewa menene!!? Me kika bukata daga waje na!!?" Kuka ta saka masa mai ban tausayi wurga mata ta kardar yayi ya juya ya bar ɗakin yana fita diyana ta rungume ta suka fara rera kuka tare,shiru Aunty farida tayi ta rasa ina zata bi tabi bayan bgs ne dan ta san yana cikin ɓacin rai zai iya aikata wani abun da ba shi ba ko dai ta tsaya ta rarrashi hiyana
jiki ba kwari ta juya tabi bayan bgs tana son rarrashi hiyana amma tana tsoron abun da bgs zai iya aikatawa na gaba kuma.

Tana shiga bedroom nashi shi kuma yana fitowa hannun sa ɗauke da trolley,waro ido waje tayi kafin tace "Safras ina kuma zakaje? Ko kallon in da take bai yi ba yayi wucewar sa zuciyar sa na tafasa tana masa raɗaɗi ɗamtsen hannun sa ta kama tana faɗin "please Safras ka tsaya mu fahimci juna kasan cewa kana son hiyana ko ka tafi wlh ba zaka dai na tunanin taba dan son ta na ran ka ka tsaya mu shawo kan matsala komai zai yi dai dai kawata Hajj fateema tana hanyar zuwa ta duba jiki na idan tazo zamu haɗu mu shawo maka kan hiyana dan Allah ka mai da trolley ɗin nan" a sukwane ya juyo ya kallin hannun nasa da ta rike ba tare da yayi magana ba bashi ta saki hannun nasa,cigaba da tafiya yayi ba tare da yayi magana ba,da sauri ta sake shan gaban sa cikin muryan rarrashi ta fara magana "ni nasan kana son hiyana kuma zakayi wanna tafiyane saboda ita dan Allah kayi hakuri ba dan kowa ba wanna karon ni zakayiwa daga nan zuwa dare zamu shawo maka kan matar ka yanzu haka hajj fateema ta shigo kasar nan tana Airport tana katisowa zamu gama dai dai ta komai In Sha Allah ka yarda dani" tsabar ɓacin rai da kyar ya iya buɗe bakin sa yace "Aunty farida kinsan banson maganar wanna kawar taki kin san meke tsakani na da ita dan haka ki dai na yimin maganar ta sanna kuma kin san gaba ɗaya gidan nan har Aryan bayan sister yake bi ba wanda yake bin bayana so na san ba zan yi nasara awajen sister ba shiya sanya na bata takardan nata kamar yadda ta bukata ki bani hanya na wuce tun kan rai na ya gama ɓaci" "no Prince no zamuyi nasara nima nasan awan nan gabar ba wanda zai bi bayan mu amma In Sha Allah zamuyi nasara kayi kuskure da gangancin bawa hiyana takarda sanna kayi kuskuren marin ta da kayi muda muke neman sulhu menene abun mari pls ka rinƙa rage zafin zuciya wlh gaskiya hajj fateema ta faɗa maka idan baka rage zafin zuciya ba zuciya zai kai ka ya baro ka gashi yau ka ɓatawa Ammi da Abba rai sosai abun da baka taɓa yi ba yanzu dai mu koma ciki ka ajiye trolley nan muje ka bawa su Abba hakuri sai mu san ya zamu ɓullowa lamarin" shiru yayi kamar mai nazarin wani abun,Aunty farida na kokarin sake yin magana Omar ya shigo ɗakin da sallama,
a tare suka kai kallon su kan Omar cikin girmamawa Omar yace "Aunty farida yaya Prince Abba na kiran ku yana palon sa yace kuyi sauri" "to gamu nan zuwa" cewar Aunty farida juyawa Omar yayi ya fice daga ɗakin dawo da kallon ta kan bgs tayi tace "muje ko" sakin trolley nashi yayi ba musu yayi gaba yana taku irin na jaruman maza,bayan sa tabi suka fice daga palon.

Suna fita harabar gidan motar su hajj fateema na danno kai da murna Aunty farida ta tarbe su a tare suka shiga palon Abba da hajj fateema shikam bgs daman bai tsaya ba Aunty farida na tsayuwa wajen hajj fateema shi kuma ya wuce abun sa.

Kowa ya hallara a palo hiyana na kwance jikin Ammi tana kuka ga takardan da bgs ya bata a hannun ta kallo ɗaya zaka yiwa Abba da Ammi ka gane yau suna cikin tashin hankali mara misaltuwa. gyara zama Abba yayi yace "ku bani hankalin ku a nan, ina son daga yau...bai karshen maganar ba sallamar su yaya bello ta katse shi Omar ne kaɗai ya iya amsa musu sallamar, kusa da Omar yaya Bello ya zauna ita kuma Hasana ta zauna kusa da diyana hajjo kuwa ta wuce kusa da su lamrat cigaba da magana Abba yayi "yauwa Bello daman ko baka zo ba zan sa akiramin kai dan wanna magana ta shafi kowa dake cikin gidan nan Aryan ina son ka nemo min mahaifiyar Sadiq da Aisha dan Omar yazo min da batun yana son Aisha kai kuma Yusuf ku tafi da Zainab Maiduguri gidan iyayen ta dan kaji ainihin abun dake faruwa ka kwantar mata hakkin ta kayi abun da ya dace, sanna sai magana akan sakin da Safras yayi wa hiyana ina son daga yau....bai Kai karshen maganar ba yaya Bello ya katse sa ta hanyar mikewa yana faɗin "Ummi kece!?" Yayi Maganar yana kallon hajj fateema gaba ɗaya palon sun zuba masa ido miƙewa hajj fateema tayi tana kallon yaya Bello sosai lokacin guda ta zaro ido waje tare da yanke jiki ta faɗi kasa sumammiya, da sauri Aunty farida Aunty mardiya Aunty salma Aunty Maryam sukayi kan ta suna kiran sunan ta "maman twins!!! fateema!!!" Shiru cikin sauri Abba yace "Ku kawo ruwa a zuba mata kai bello daman ka san tane? Aina kasan ta? Murya na rawa yaya Bello yace "Eh Abba na san ta"


To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu





💋 Duk Karfin Izzata 💋


💋The talent troupe writer's 💋



By Star Lady

Page 42


___kasan tane Bello!?" "Eh Abba na santa maman su hiyana ce" "what!! Cewar Ammi chak Aunty farida ta tsaya da zuba wa Hajj fateema ruwa da take ba shiri bgs ya ɗago kai tare da waro ido waje kallon hiyana diyana tayi yayin da itama diyanar ita take kallo, kallon bgs Aryan yayi dai dai lokacin da shima bgs ɗin ya juyo yana kallon sa a tare Khalid da Yusuf suka juyo da kallon su kan bgs dan sun san meke tsakanin sa da hajj fateema, tirkashi wanna shine tashin hankali cikin tsarguwa Abba yace "ba ance maman su rasuwa tayi ba!? "Aa Abba mudai kawai tun ranar da ta haifi amrat bamu sake ganin ta a kauyen ba ta tafi ta bar amrat jaririya ba'ayi ko suna ba duk kuma wanda ka tambaya ina Ummi ko yaga Ummi sai yace maka bai san taba tun abun na baku mamaki har muka dai na duk kauyen mu babu wanda bai san Ummi ba dan mutuniyar kirki ce amma tun ranar data ɓata kowa ka tambaya sai yace bai san taba daga ni sai innata sai bappan su hiyana sai kuma bappa na mune kaɗai bamu manta Ummi ba amma gaba ɗaya jama'ar kauyen mu sun mantata har su hiyana.
lokacin da suka fara girmane na fara basu labarin suna da mahaifiya amma ta rasu su rinƙa yi mata addu'a wanna ne ya sa gaba ɗaya su hiyana suka ɗauka Ummi ta rasu nayi neman ta daga kauyen mu har makwantan kauyuka amma shiru ban gantaba haka muka cigaba da zama,su hiyana su kaɗai a gida ba kowa daga baya sai bappa na yace wa bappan su ya kamata yayi wani Auren tun da baa ga Ummi ba da farko bappan su yaki yace ba zai iya yiwa Ummi kishiya ba dan yana sa ran ko bajima ko ba daɗe zata dawo. sai da bappana ya dage da yi masa maganar yana nuna masa anfanin hakan zanyi ne dan su hiyana,shine ya hakura ya auro inna habiba dan karan da bappana ya masane yasa ya yarda ya auri inna habiba wadda ta kasance kanwar baban mune,tun farkon auren su bappa ya fara sauyawa akoi wata ranar Alhamis ina zaune kasan itace ni da bappana muna hira yake cemin "Bello Ahmadu ya sauya sosai kamar ba shi ba ina tunanin akoi abun dake faruwa" shiru na ɗanyi ina tunanin irin dukan da yayiwa hiyana jiya nasha ruwan mamaki dan bappan su hiyana bai taɓa dukan suba cikin damuwa nace "bappa nima na lura da hakan domin jiya dan hiyana ta taɓa paipain goggo habiba ya kamata ya mata duka ita kuma goggo habiba kotazo ta anshe ta Allah bappa ina ganin asiri aka yiwa bappan su hiyana" girgiza kai bappa yayi kafin yace "aa Bello kamar da wuya anya asiri zai iya kama Ahmadu cikin sauki haka" "bappa asiri zai iya kama shi mana ko ka mantane bappan su hiyana baya son magani kuma shi baya shan maganin tsari sai dai ya bawa su hiyana" gyaɗa kai bappa yayi kafin yace "hakane to amma gaskiya yayi ganganci, dole yanzu mu kuma mu taimaka mishi in anjuma zanyi magana da habiba idan ma ita ta masa to wlh tun wuri ta kwance asirin nan wanna ai zalunci ne kisa mutun ya tsani ƴaƴan sa kin sa kwata ya zama kamar ba mutun ba ko waje yanzu Ahmadu baya fita sai dai yayi ta zama a cikin gida idan sunji yinwa ki kama kaza ko zabo ku yanka zanga ta tsiya idan kuka cinye dabbobin gaba ɗaya" mun jima muna hira da bappa awajen kafin daga bisani na tashi na wuce gona.

Bayan kwana uku da magana da bappa na sake yi masa zancen dan naga bai ce komai ba har yanzu gashi bappan su hiyana yana azabtar da su hiyana sosai,tun mutane basu sani ba har yan kauyen sun fara sani awanna lokacin dana sake yiwa bappana magana sai cemin yayi na dai na damunsa,abun ba karamin mamaki ya bani ba,amma na daure na fito ina neman mafita amma na rasa tun diga wanna lokacin ne na fara koyan haɗa maganin gargajiya da kuma yadda ake haɗa asiri da warware sa wajen wata tsohuwa dake kusa da kauyen mu.
lokacin da hiyana ta kai shekara 12 na lura lokacin zata iya abu idan na koya mata sai na fara koya mata yadda ake haɗa asiri da warware na koya mata yadda zata haɗa magani duk wadda na koya mata sai na mata nasiha akan karta cuci kowa a rayu ina koya matane dan ta tainaki mutane bayin Allan hiyana tana da ƙwaƙwalwa da kaifin basira duk abun dana koya mata ta rike daga nan ne na fara koya mata karatun Kur'ani dan tana da nitsuwa sosai ba kamar diyana ba. Wata ranar asabar inna da bappa su hiyana sukayi faɗa inna ta buga masa sandar kiwo a kafa kowa yasan indai sandar kiwon cikakken bafulatani ne to akoi ɓahe a jikin sa wadda idan mutun bai da tsari a jikin sa akan bugesa da shi yana iya mutuwa to da yake shima bappa duk kanwar jaa ce sai abun ya ja masa ciwon kafa wasa wasa ciwo na daɗa girma anyi magani har an gaji tun yana takawa a hankali hankali har ya dai na tafiya gaba ɗaya,.su hiyana sun ci wahala wajen bappan su bayan auren inna habiba da yayi,tun da bappan su ya dai na takawa da kafar sa inna habiba ta zama itace jagaba akan komai nashi yana ji yana gani zata ɗauki shanu ta tura birni a sayar mata tazo tayi ta kashe kuɗin abanza, har bappa ya zauna baya tafiya asirin da inna habiba ta masa akan tsanar su hiyana bai sake saba dan bai son su zo kusa da shi haka zasu takure awaje dan lokaci basu da ɗaki ɗaki biyu ne a cikin gidan daga na bappan sai na Ummi wadda yanzu ya koma na inna habiba ko ruwan sama ake haka zasu kwana a waje ruwa ya musu duka cikin taɓo da dotti suke kwana gashi ba wanda ya isa duk kauyen nan yace zai ɗauke su dan kowa bala'i tsoron inna habiba yake. Akoi wata ranar da Allah ya bani aron dama inna habiba bata nan na lallaɓa na shiga gidan su hiyana bappana na barci na shafa masa maganin makarin asirin da ta masa, Allah da ikon sa kuma asirin ya karye da kai na na rinƙa shafawa bappan maganin tsarin jiki,bayan asirin ya karye ne bappa ya dawo hayyacin sa lokacin kuma komai ya kure masa komai ya lalace baya iya tafiya yasha kuka yana neman gafarar su hiyana daga lokacin ya rungume su a jikin sa ya sani na gina musu ɗaki amma duk da haka inna habiba bata dai na azabtar da su hiyana ba bappa naji yana gani haka yaran nan suke wahala ba yadda zai yi inna bata jin maganar sa bata ma bi ta kansa tun da ya dai na tafiya ta dai na kulashi ta dai na bashi abinci ko yaushe Ni nake fakan idon ta in kawo masa abinci dan in ta sani bazata yarda ba tafiso yinwa ya kashe su,haka zataje ta sai da shanun sa ta ɗauki kuɗin tayi chefane tayi girki amma bazata bawa bappa ba kuma bazata bawa su jiyana ba ga uban aikin dake jibga musu hiyana itake mata girki diyana tayi mata wanki kaya sanna ta ɗebo ruwa lamrat tayi shara da wanke wanke lokacin amrat batayi wayo sosai ba amma duk da haka sai ta sa amrat ɗin ma gyaran ɗaki da yi mata tausa bayan sun gama dukka wanna aiki sai kuma su tafi tallar nono ga duka da take musu kamar jakuna,ko sunje tallar nono ba'a saya mutanen gefen kauyen mu suna gudun su saboda idon su ba wanda yake sayan nono su wasu ma ce musu suke mayu ne su,wani lokaci idan ina da kuɗi sai ince musu su shanye nono su sha da safe su sha da rana su sha da yamma idan sun tashi komawa gida sai na basu kuɗin nono su kaiwa inna amatsayin sun sayar da nonon idan kuma bani da kuɗi haka zan hakura ina ji ina gani inna ta musu ɗan banzan duka wani lokaci har ciwo take ji musu dan bata musu dukan hankali. A haka muka cigaba da rayuwa har Allah ya karɓi ran bappa kafin ya rasu ya barmin wasiya akan ya bani amanar su hiyana dan gaba ɗaya kauye ni kaɗai na rage mai zuwa wajen sa sanna ya faɗa min akoi address ɗin gidan su maman hiyana a cikin ɗan akwatin nan dan Allah na kai su wajen yan uwan maman su domin su samu saukin wahalar da suke sha wajen inna karna bari inna ta kashe su,akoi hoton maman su hiyana kala biyu a cikin akwatin idan na kai su hiyana yasan bazasu gane su ba dan yan uwan maman su basu san su ba amma idan na nuna musu hoton Ummi zasu gane ta,na ansa tare da masa alkawarin yin hakan bayan rasuwar sa naso ɗaukan shanu ɗaya na sayar muyi kuɗin mota na kai su amma inna habiba ta tada bala'i,ta hanani lokacin ne tamin katanga da duk wani abu da ya shafi su,nasha kuka ina tunani da jimamin yadda zan cika alkawarin dana ɗaukar wa bappa,haka na cigaba da hakuri ina addu'a ina ganin halin kunci da suke ciki ranar da bappa na cika kwana 7 da rasu ina gona na samu labarin wai zaa ɗaura Auren buba da hiyana ba karamin tashin hankali na shigaba na rasa ya zanyi na rasa ta ina zan fara dakatar da wanna Aure dan nasan wanene buba kanina uban mu ɗaya babu abun da ban sani ba akan shi cikin ikon Allah Allah ya kawo Ammi ta ceci marayun Allah.

Ya kai karshen maganar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login