Showing 3001 words to 6000 words out of 243403 words
a ɗaki
"Kai Aryan idan har na isa da kai to ka saki yarinyar nan yanzu dan ni bazan haɗa zuri'a da masu kiwon shanu ba, chikin jin haushi Aunty Maryam tace "haba Aunty amarya dan Allah ki kyale yaya Aryan yaji da abun da yake ji mana" "zaki min shiru ne ko sai na zabga miki mari wlh yau idan kunga Aryan bai saki diyana ba tofa mutuwa nayi tana magana tana huchi kamar wata zakanya
"Ba yau ba yanzu zan rubuta wasiya idan kika kuskura koda mutuwa nayi ki ka sanya Aryan ya rabu da matar sa tofa sai kin fuskanchi hukunchi mai tsanani gaske" chewar Abba
Chike da izza Aunty amarya tace "wlh babu wan da ya isa yasa na bar ɗana ya zauna da wan chan kazamar yarinyar, rai a matukar ɓache Bgs ya miƙe tare da miƙar da Aryan ya riko kafaɗar sa suka nufi waje tun lokachin da Aryan yasan Aiman ya rasu kullun yake chikin rashin lfy bai da wani kuzari sai yawan tunani
Miƙewa Aunty farida tayi tare da faɗin "ku tashi mutafi tayi magana tana kallon su hiyana, a tare suka miƙe gaba ɗayan su har da su Aunty Maryam suka nufi waje.
Palon ya rage daga Abba Ammi Ummi sai Aunty Amarya, shiru sukayi suna jin yadda Aunty amarya ke surfa ruwan bala'i dole sai Aryan ya saki diyana,Abba batare da yayi Magana ba yasa hannu a aljihun sa ya chiro wayar sa, ya shiga contact ya fara kiran wata number wadda akayi saving da My Brother.
Kira ɗaya a ka ɗaga sanya wayan a hand-free Abba yayi chikin girmamawa ya fara magana "Assalamu alaikum, daga ɗayan ɓangaren aka amsa da wa'alaikumus salam jin muryan wadda ya amsa Sallamar yasa Aunty amarya tayi sauri kwache wayar a hannun Abba ta katse kiran tana faɗin "dan girman Allah kayi hakuri karka sanar wa yaya wlh in dai Aryan ne na barshi yaje ya chigaba da zama da matar sa har abada Allah ya basu zaman lfy Allah yasa a gane ta" tana kai karshen maganar ta miƙe tare da ajiyewa Abba wayar sa a gefen sa ta nufi waje da sauri tana faɗin Allah na tuba kayafi min, duk bachin rai da raɗaɗin rasuwar Aiman dake damun Abba hakan bai hanashi yin ɗan murmushi ba dawo da kallon sa yayi kan Ammi da Ummi ya fara magana
"Aisha kije ki sanar wa farida nache ta shirya hiyana ta mata duk abun da ya dache ta kai ta part ɗin mijinta, ita kuma salma ta shirya Zahra itama ta kai ta part na mijinta, ke kuma hauwa'u ki sanar da mardiya akan ta shirya lamrat da amrat suma ta kai su part na mazajen su, suyi sauri yana kai karshen maganar ya miƙe ya nufi betroom nashi.
Kallon Ummi Ammi tayi chikin fargaba da tsoro abun da zai biyo baya tace "ki tashi muje mu isar da sakon ko? "To kawai Ummi tache a tare suka miƙe suka bar palon
After some hours
Aunty farida da Hiyana ne zaune a bakin gadon a ɗakin su hiyana Aunty farida ta tsara mata make up sosai
hiyana tayi kyau sosai kamar ka sache ta ka gudu da ita, sanye take chikin wata danƙareriyar lace pink colour ta yafa mayafi fari a kanta, chikin nitsuwa Aunty farida ta fata magana
"My Hiyana na san baki son Yaya prince Amma kiyi hakuri wan nan itache kaddarar ki kuma kisani hakan kamar jarabawa che Allah ya jarab cheki to kiyi kokari ki chinye jarabawar ki, kuma awan nan karon mu zaki tai makawa kinji ko? ina mai rokonki da ki daure nasan kina da hakuri sosai kuma nasan zaki iya to ki kara hakuri nasan zaki sha wahala zama da yaya prince amma ki daure In Sha Allah zamuyi nasara a kanshi kinji ko? kuma In Sha Allah kema zaki fara son shi yanzu zan faɗa miki ta yadda zamu fara yakar sa
abu na farko duk da nasan baya san ganin mace a kusa da shi amma ya zama dole kirin ƙa kasanche kusa dashi koda kuwa baya so
Abu na biyu ki dai na saka hijabin da kike sawa ki koma saka kananan kaya idan kin san yana gida, na uku zan roki maki alfarma a wajensa ko da yake ma koban roke saba nasan Abba zai che ke zaki rinƙa kai masa abinchi, kinga a nan ma zamu iya yin nasara, san nan idan ya dawo daga wajen aiki kiyi kokari ki saba masa da chire masa takalmi da socks da kan ki, nasan zaki sha wahalan hakan Kuma nasan zai iya chewa baya so to amma ko yache hakan karki dai na kirin ka yimasa kinji koh?
Kuka Hiyana take sosai kamar ranta zai fita rungumota Aunty farida tayi sosai tana bubbuga bayan ta tana bata hakuri awan nan yanayi Ammi ta shigo ta samesu "feeda Abban ku fa yace kiyi sauri ki kai Hiyana part na mijinta tun ɗazun fa su salma suka kai su Zahra" "to kawai Aunty farida tace tare da miƙewa ta kamo hannun Hiyana suka sufi wajen
Wani hawayen farinchiki Ammi taji ya zo mata burinta ya chika hiyana ta zama matar ɗan ta, sai dai awani ɓangare na zuchiyar ta kuma tana tausayawa hiyana sosai dan tasan Hiyana ba karamin wahala zata sha a wajen Bgs ba amma ta ɗauki kudirin taya hiyana yaki ta kowani hali
Maiduguri
ɗankareriyar mota kirar marcedes Benz che ta shararo a guje gudu mai motar yake sosai kamar zai tashi sama,ji kake kiiiiiii mai motar ya kwashe wata mahaukaciyar yarinya da ta zo tsallaka titi, wata mahaukachiyar birki yaja chikin sauri ya buɗe kofar motar ya fito kyakkyawa ne sosai fari tas dashi, chike da tashin hankali ya nufi inda yarinyar ke kwanche a saman titi ko motsi batayi kamar ta mutu ga jikin ta duk jini kanta ya fashe sosai, wani dogon salati yayi kafin ya karisa in da take juyawa yayi gabas da yamma babu kowa a kan hanyar, dawo da kallon sa yayi kan yarinyar, zuba mata manya manyan fararen idon sa yayi yana kallonta, gani yayi hannunta ya ɗan motsa alamar bata mutuba chikin sauri ya duka ya ɗauke ta ya nufi mota da ita gidan baya ya buɗe ya kwantar da ita ya rufe kofar ya buɗe gidan gaba ya shiga da sauri ya kunna motar yaja ta da gudu ya nufi asibiti da ita
Yana yin parking a chikin asibitin ya fito ya ɗauke ta chak ya nufi chikin asibitin da ita, kai tsaye office na Babban Dr ya nufa, batare da yayi Sallama ba dan tsabar ruɗewa shiga office ɗin yayi kai tsaye, Dr na zaune yaga an shigo masa office chikin sauri ya miƙe yana faɗin "Ahzan lfy!? subhanallah wan nan fa!? Yayi maganar yana nuna yarinyar da Ahzan ɗin ke ɗauke da ita chike da tashin hankali Ahzan yace " Dr walid ka taimake ni wlh yanzu shigowata garin nan ke nan ina sauri na karisa gida na buge yarinyar nan
Hannu Dr walid yasa yana masa nuni da gadon dake chikin office ɗin yana faɗin "ka kwantar da ita tun da Allah yasa kai ma babban police ne yanzu zamu fara dubata, Ahzan bai jira Dr walid ya karisa maganar ba ya nufi gadon da sauri ya kwantar da yarinyar, chikin sauri Dr walid ya fara shirya kayan aiki
Fitowa waje Ahzan yayi ya zauna saman wata kujera tare da chiro wayar sa daga aljihu kira ya danna tare da manna wayar a kunnen sa, kira ɗaya akayi picking, chikin rawar murya Ahzan ya fara magana "eh dady na shigo amma fa akoi matsala" chikin tsorata dady yace "wani matsala kuma Ahzan? "Accident na samu na buge wata mahaukachiyar yarinya che yanzu haka muna asibiti" "subhanallah ka turomin address ɗin Asibitin da kuke ganin nan zuwa" to kawai Ahzan yace tare da katse kiran ya shiga massage turawa dady address din asibitin yayi san nan ya mai da wayar aljihun sa ya dafe kan sa da hannu biyu....
Dan girman Allah kumin afuwa jiya nache zanmuku page 2 to ina baku hakuri da rashin chika alkawari da nayi wlh ban samu charji bane sai wuraren 4 shiyasa amma In Sha Allah zuwa gobe zakuga sako masu zafi amin afuwa
NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖
*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*💫STAR LADY💫*3
💖The Talent Troupe Writer's 💖
*DUK ƘARFIN IZZATA*
💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*
Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai
Book 2
*Episode 3*
Da sallama ɗauke a bakin ta Aunty farida ta shigo chikin palon Bgs rike da hannun Hiyana daketa faman sharara kuka dan ita gani take shike nan kwanan ta ya kare, kai tsaye betroom nashi suka nufa ita kanta Aunty farida fargaban shigar betroom ɗin take
Zaune yake a bakin katafaren gadon sa sanye da jallabiya baka ya dafe kansa da hannu biyu yana kallon kasa da alama wani tunani yake, jin Sallamar Aunty farida che ya sa ya ɗan ɗago kai kaɗan, batare da ya kalli in da suke ba kasa kasa ya Amsa sallamar, ƙarisowa chikin ɗakin sukayi jin shesshekar kuka yasa ya ɗago idon sa kallo ɗaya ya musu ya kauda kansa gefe yana kara yamutse fuska gefen gadon Aunty farida ta zauna tare da zaunar da Hiyana a gefenta, Chike da So da kaunar ɗan uwan nata tafara magana
"Prince ina ne ɗakin Hiyana? Shiru yayi kamar bai ji me Aunty farida tace ba "Prince Magana nake maka fa nache inane ɗakin Hiyana!? Ta karisa maganar tana ɗan kwaɓe fuska alamar bataji daɗin shiru da ya mata ba, shiru dai Bgs bai yi magana ba kamar ma bai san da shigowar mutane ɗakin ba, shiru Aunty farida tayi bata sake yi masa Magana ba dan a tsorache take da shi Almost 10mnt suna zaune shiru chikin muryan rarrashi Aunty farida ta fara magana
"Haba prince dan Allah ka bani amsa mana nasamu naje na kaita ta kwanta ta ɗan huta" shiru shiru kamar bai san da zaman su a ɗakin ba ganin hakan yasa Aunty farida ta miƙe ta kama hannun Hiyana ta nufi waje da ita ɗakin dake kusa da nashi Aunty farida ta shiga rike da hannun Hiyana, komai na chikin ɗaki iri ɗayane da nashi sai dai ban ban chin colour domin komai na ɗakin sa farine tas na hiyana kuma sky blue, a bakin katafaren gadon dake chikin ɗakin Aunty farida ta zaunar da Hiyana ta juya batare da tayi magana ba ta nufi waje gaba ɗaya ji tayi jikin ta yayi sanyi wani mugun tausayin hiyana ne ya sake dira a ranta, tunani take tana tafiya lallai Prince ya tabbata baya son hiyana ko kaɗan Allah sarki bai war Allah, ɗakin Bgs ta koma
Da Sallama tashigo ɗakin kamar yadda ta barshi haka ta dawo ta same sa gefen sa ta dawo ta zauna chike da fargaban abun da zai biyo baya ta fara magana
"Kayi hakuri Prince na san ba'a kyau ta maka ba amma idan ka daure kayiwa iyayen mu biyayya zamuyi nasara arayuwa kaji? shiru Bgs yayi bai yi magana ba da alama bai da niyar magana kwata kwata, chigaba da magana Aunty farida tayi "pls ɗan uwana kaji tausayin yarinyar nan marainiya che ba uwa ba uba kuma kana sane da irin wahala da ta sha arayuwar ta to dan Allah ko da ba zakuyi zama a matsayin mata da miji ba ina neman alfarma da ka ɗauke ta kamar yadda ka ɗauke ni dan Allah idan kamin hakan ka gama min komai pls" wani iska mai zafi ya furzar daga bakin sa kafin ya fara magana
"Pls Aunty babba zaki iya tafiya!!" chikin sauri Aunty farida ta ɗago tana kallon sa shima ita yake kallo ba karamin razana tayi da kallon yadda green eyes nashi suka sauya izuwa jaa sosai ga jijiyoyin kan san nan duk sun tashi duk da A.c dake ɗakin hakan bai hana shi zufa ba chikin murya irin na rarrashi Aunty farida tace "dan Allah prince ka saurare ni nasan baa kyau ta maka ba amma kasani ba laifin Hiyana ba che wlh bata san komai ba yarinya bai war Allah ita kanta yanzu kukan dana sanin zuwan ta duniya gaba ɗaya ma take, ta sha wahala a rayuwar ta pls my blood ka karɓi Hiyana a matsayin kanwa ba mata ba kaji? ta karisa maganar kamar zata yi kuka kawar da kansa gefe yayi chikin nitsuwa ya fara magana
"Naji zan yi tunani a kan hakan zaki iya tafiya"wani nauyayyar ajiyar zuchiya Aunty farida ta sauke dan tasan halin Bgs idan yace zai yi abu to zai yi ne addu'a take Allah ya ɗora su a kan shi, da wan nan tunanin ta miƙe ta fice daga ɗakin, wani dogon tsaki yaja tare da miƙewa ya kwanta yana kwaɓe fuska
A ɓangaren Khalid kuwa
Aunty salma rike da hannun Zahra wadda ke ta kuka suka shiga palon sa, kwanche suka same sa saman sofa mai zaman mutun 3, yana ganin su ya miƙe zaune yana faɗin "sannu ku da zuwa" murmushi Aunty Salma tayi tana mai farin chikin yau ɗan uwan ta yayi Aure kuma abun farin chikin ma Autan su ya Aure
Gefen sa Aunty salma ta zaunar da Zahra san nan ta koma gefe ɗaya ta tsaya chike da farinchiki ta fara magana "to ga amanar kan wata na baka ka kulamin da ita sosai fa" da murmushi a kan face nashi yace "gaskiya na karɓi wan nan Amanar hannu dubu dubu In Sha Allah zan kula da sis love na sosai kamar kwai a kan bajejjen faranti" dariya Aunty Salma tayi kafin tace "oh Allah ko kunya ta bakaji ba ko? Sunkuyar da kansa kasa yayi chikin raha yace "to Aunty babba gashi nan naji kunyar taki" tsaki Aunty salma taja chikin wasa tare da nufar kofar fita tana faɗin "ai, Ni ban soma Abba ya baku matan naku yanzu ba so nai ya bari sai nan da wata 2 masu zuwa" tana kai karshen maganar ta fice daga ɗakin
Dawo da kallon sa Khalid yayi kan Zahra dake ta faman sharɓan kuka, hannu yasa ya goge mata hawaye chike da so da kauna yace "my wife kukan me kuma ki keyi ne? Shiru Zahra tayi bata tan ka shi ba kuma bata dai na kukan ba, murmushi Khalid yayi tare da miƙewa ya naɗe hannun rigan sa ya duƙa ya ɗauke ta chak kamar yar baby ya nufi betroom nashi da ita
A tsakiyar katafaren gadon sa ya zaunar da ita tare da zama daga ɗan gefen ta ya kwan to da kan sa kan chinyar ta kasa kasa ya fara magana
"My wife wai kukan menen hakan? Baki san zama da nine? Sunkuyar da kai kasa Zahra tayi ta chigaba da kukan ta, "oh my god Khalid ya furta tare da miƙewa zaune yasa hannu ya ɗago haɓarta, chike da so da kauna yasa harche ya lashe hawayen nata tas tare da haɗe fuskokin su yana kallon chikin idon ta "now zaki yimin magana ne ko kuma dai sai na chiji ɗan bakin nan naki? Chike da shogoɓa tace "Ni Allah yaya Khalid bana so ka mai dani part ɗin Ammi na" murmushi yayi kafin yace "au shine dalilin kukan naki? Gyaɗa masa kai tayi alamar eh "ok to bari zuwa gobe zan mai dake kinji amma yanzu tashi muje na miki wanka na shiryaki muje na baki abinchi a baki" turo ɗan bakin nan nata tayi chike da shagoɓa tace "ni na iya wanka da kai na ai"
"Aa ni gaskiya ban yarda ba kizo kawai muje na miki idan ke kikayi bazaki fita sosai ba, bata san lokachin da dariya ya kubche mata ba zuba mata ido yayi yana kallon yadda take dariya sai da tayi mai isar ta san nan ta raba fuskantar da nashi tana faɗin "to ai ni nake wankana tun dama chan kuma ina fita sosai ai a haka ma ka ganni kache kana so" ta karisa maganar tare da rufe fuskar ta da hannun biyu "eyeee a lallai my wife ta girma babu zan chen ɗaga kafa kenan" "ɗaga kafan me kuma dama ai ni ban che kaɗaga kafaba" "au haka kika che? "Eh mana yaya Khalid ni ban che ka ɗaga kafa ba to ma idan ka ɗaga kafar ka kai ta ina
Fisgota yayi da karfi ta faɗa kan kirjin sa, rungumeta yayi sosai yana faɗin "ai ko ba zan ɗaga kafar ba" ɗago da fuskan ta tayi daga kan kirjin nasa chike da shogoɓa tace "yaya Khalid ka kusa karyamin hannu fa Allah" "sorry my wife to muje na kai ki toilet kiyi wanka ko?tun da bakya so na miki, Ba tare da ya jira Amsar taba ya miƙe ya ɗauke ta chak ya nufi toilet da ita.
A ɓangaren Yusuf kuwa Aunty Mardiya na fita ya matso kusa da Amaryan sa kasa kasa yace "my baby ya jiki? Kan ta a sunkuye tace "da sauki amma har yanzu kai na na min chiwo sosai" eyya sorry kinji In Sha Allah zai dai na yimiki chiwo yanzu dai ki kwanta ki huta bari naje wajen Abba a fada ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya nufi waje ita kuma lamrat karisa hayewa saman gadon tayi ta kwanta ba jimawa barchi yayi awan gaba da ita
A ɓangaren Fahad kuwa
Koda Aunty mardiya ta shigo tare da Amrat shiru palon babu kowa kai tsaye